Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

on typing...✍️
Writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
wannan labarin kagagge ne. Ban rubuta shi don cin zarafin kowa ba, idan yazo daidai da rayuwar ka, toh akasi ne, sabo da haka a kiyaye!!!
Godiya ta musamma ga mabiya littafi na, nagode sosai Allah ya sa ka mu ku da alkhairi 👌
Fatima iman ibrahim ina godiya sosai❤️
SHAFI NA 7
      Bismillahir- rahmanir rahim
kuma da sharadin duk ranar da kika dawo wallahi sai na sare kan ki, kuma bazan yi kaffara ba!! Na ba ki rabin saa'a ki yi nesa da kasar, komai kama da ke aka ce angani, toh kiyi kuka da kanki,. San nan sarauniya Ayra ta sa ke juyawa gefen dakaru, ta fitar da duk wadanda su ka bijirewa mijinta, ta sallame su, ta re kuma da gargadin su, matukar su na son ran su, toh kar ta kara ganin su acikin wannan nahiyar. Ta ce wa sauran su fa ra shirye- shiryen nada Yarima fu'ad akan karagar mulki....Wannan shi ne takaitaccen tarihi na...
A jiyar zuciya Aneesa ta yi, ta re da kara kallon fuskar fu'ad, ita kam tasan wannan kyau haka sai dai aljani. san nan ta ce: "ina yi ma ka ta'aziyya akan rasa mahaifin ka, da kuma ta ya ka murnar kifar da zalunci kadaura adalci. Hakan ya sa nasan ba bu MUGUNTA acikin zuciyar ka, dama ace kowane jinsin Aljanu haka su ke...da an samu zaman lafiya a duniya, sabo da dayawan su, su ke kara ba da gudunmuwa wajen tashin hankulan bil'adama...
Murmushi ya yi, ta re da jinjina waayo irin na ta. "kai komai murmushi? Amma kuma wallahi ya na ma ka kyau... kin ganki ko? Surutun ki ya yi yawa, kuma kar ki sa ke cemin KAI, daga yanzu ni yayan ki ne, kinji ko? "Toh mai martaba sarkin farisa...hararar ta ya yi, shiyasa tayi saurin  cewa: Wai...yaya fu'ad. Dariya su ka yi gaba dayan su...
"Amma yaya fu'ad, ya aka yi kasan suna na, da kuma sunan iyaye na? Wannan ba abun mamaki ba ne, dan nasan sunanki.
Tun kina yar karamar ki, nasan ki.
Baki bude ta ke kallon sa, san nan ta jeho mishi tambaya. Tun fa ina karama ka ce? Toh ta ya ya kasanni? Sabo da ke na ke zaune a wannan wurin, kin ga kuwa ai ba abun mamaki ba ne, sanin sunan ki?
"Amm...  Aneesa surutu...zan fada miki amma sai nan gaba.Kuma kema sai kin bani labarin ki...
Yanzu dai kika ce mu jinsin mu, mun fiye MUGUNTA ko?! Kai yaya fu'ad, har fa maganar ta wuce... a wurin ki ba, kamar yadda ki kasan akwai azzalummai acikin mu, haka kuma akwai su acikin ku, son zuciya da neman duniya, shiyasa bil'adama ke tsoron aljannu, amma maganar gaskiya aljanu su ke tsoron mutane, amma fa ada can... kafin zamani ya canza. Yanzu sabo da neman bukatu wajen aljanu da mutane ke yi, shiyasa aljanu ke juya su yadda su ke so, sabo da ba Allah acikin zukatan wasu. Amma da ace za su  rike Allah kuma su  dage da adu'a toh wallahi da ba bu wani aljani da zai rabesu da nufin cutarwa...sai dai kash! wasu mutanen sun mai da aljanu abun bautawar su...sun manta cewa akwai Allah a madakata ya na jiranmu.... Allah ya sa mufi karfin zuciyoyin mu, ameen...
"Haka ne yaya fu'ad, mutane na manta cewa addua takobin mumini,  Allah ya ganar damu gaskiya ya kuma ba mu ikon aiki da ita amin.
SUNANA ANEESA ABDUL'AZIZ ABUBAKAR  MAI NOMA...Kamar yadda ka fada abaya...
MUHADU A SHAFI NA 8 DON JIN LABARIN ANEESA...✍️
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA
PLS
08144066758
YAR MUTAN ARGUNGU``` ❤️🥰📚










```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
*Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
Zumunta ko mugunta on typing...✍️
Writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
Kagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma kara dankon zumunci 💙❤️
FREE BOOK📚
TSOKACI AKAN LITTAFIN
LABARIN ANEESA ZAI FARA NE TUN DAGA KAKANNIN TA.
SHAFI NA 8
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
********************************************************
WACE CE ANEESA?
JAADA, kauyane acikin kebbi State,
Haba zainaba saunawa zan fada miki, ki daina damuwar kan ki, akan wannan batu, fisabilillahi! Ko yaushe ke ce cikin damuwa akan wane dalili? Haihuwar nan dai ta Allah ce ba wani ne ke ba kan sa ba, ballan ta na ki ce in kin damu za ki samu, duk abun da ki ka ga Allah bai ba ka ba, toh akwai dalilin sa na yin hakan. Indai ni ne wallahi bazan taba yi miki gorin haihuwa ba, sabo da nasan komai lokaci ne,toh akan me zan sa ka kaina cikin damuwa...Matsala daya ce kuma akan iya  ce,  na san  kina hakuri akan abubuwan da take yi miki, kuma na yaba na gode,. Tun dazu da malam Abubakar ke magana ta na gefe daya zaune akan gadon kaara, ta yi tagumi...Sai yanzu ta samu damar yin magana bayan ya kai aaya."Malam nifa ban ki ta taka ba, kawai ina tunanin abun da zai kai ya komo ne akan maganar da IYA ta yi, na cewa ka kara Aure! Ba cewa na yi  ka bijirewa umarnin mahaifiyar ka ba, ina dai duba makoma ta ce muddin aka yi wannan Auren, Sabo da ba lallai ne ayi min adalci ba, ta na mai share hawayenta....
Rike hannuwan ta biyu ya yi, yana cewa..."Idan ki ka yi mi ni haka wallahi ba ki yi min adalci ba! A kullum ina rokon Allah kar ya ba ni ikon juya miki baya zainaba...muryar IYA ce ta katse mu su zancen da su ke yi...cikin tashin hankali su ka mike a lokaci daya. Ah,a Iya sannu da zuwa, bismillah ga wuri zauna...
"kai dallah tafi can kaban wuri, shashasha wanda bai san ciwon kansa ba! Tun yaushe na ke binka akan ka kara Aure ,amma kayi kunnen uwar shegu da ni. Sabo da ga ka isashshe mijin isassa koh?  Sai kuma ta fashe da kuka... jama'a ku kawo dauki Dana ya bijire min, wallahi nidai lokacin mu ba haka ake yi ba, da zarar ka ce wa yaro kar ya tsallaka wallahi ba zai tsallaka ba....ta jawo gefen hijabin ta, ta na sharar majina...
Iya dan Allah ki yi hakuri, cewar zainaba."Ai dole ki ce inyi hakuri tun da an cuce ni! Atoh an cuce ni mana,shiyasa ki kayi sumi-sumi da kai ana cewa Iya ayi hakuri, salon jama'ar gari su ji su ce ni ce muguwa, ba su san cewa nan kuwa ni ce wadda ake cutarwa ba, ko wane gida ka shiga, sai ka ga yara dugui-dugui, ni kuma gani am mai sheni yar iska gantalalliya, mutum ya yi magana ace mishi rigimammiyar tsohuwa, kin dai san  can da ina son ki,ganin ba ki aje mini jikoki ba ne ki kaga na sako ki gaba kamar figargiyar tantabara,amma yanzu duk abun da ku ka yi min wallahi na yafe muku duniya da lahira,toh bayan kai da matar ka wa ag gareni? Dole ne inso abun da ka ke so Abubakar,ai kana kokari da ni sosai Allah ya biyaka.  Toh nidai yanzu ba wannan ne ya kawo ni ba,mai zai hana ka Auri Atika yar gidan malam Tukur, yarinya ce mai hankali,Toh ni dai ba hankalin ne ya burge ni ba, kasan danginsu irin haihuwa ne, akan haihuwar su kowa ya san duk shekara sai anyi suna a gidan...
"Iya mun fa dade da wuce wannan wurin, haihuwar nan ba fa mutum ke ba kansa ba,ko mata nawa zan kawo cikin gidan nan, idan Allah bai nufa ba, ba yadda zamu yi, sabo da haka komi lokaci ne, maganar wata Atika a ajeta gefe gaskiya...
Haka iya ta fita daga gidan ta na kuka, wai Abubakar ya ci ma ta mutunci shi da matar sa...Bayan fitar iya, zainaba ta kalli mijinta, dan Allah malam ka je ka ba ta hakuri, in dai sabo da ni ce wallahi na yadda ka Kara Aure. Ba ason bata ran mahaifa, hakuri ake da su...amma ki na ganin abun da iya ke yi dai-dai? A dai yi hakuri kasan sha'anin tsufa...
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUN MUWA
PLS
08144066758
YAR MUTAN ARGUNGU``` ❤️💙


```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Bayan wuya **
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta? on typing...✍️
Writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
kagaggen labari ne,sabo da haka idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. Littafi na ba na sayarwa ba ne,wallahi duk wanda ya saida shi ban yafe ba!!!
GODIYA👌
Ga mabiya karatun lattafai na, Allah ya saka mu ku da alkhairi 🥰
JINJINA
Ga yan uwa na Allah ya kara dankon zumunci, ameen ❤️❤️❤️
FREE BOOK 📚
SHAFI NA 9
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
************************************************Akwana atashi asarar mai rai, ga shi har anyi bikin Abubakar da Atika. acikin shekara daya Atika ta haihu, zo kuga murna awurin Iya, yaro ya ci sunan Tukur watoh mahaifin Atika, sabo da tsaye tayi ta ce atafau, ba za a saka ma yaronta sunan kowa ba, sai na mahaifin ta. Iya ido rufe ta ce a saka...
shekara daya tsakanin haihuwar Tukur, ta sake haifo wani yaron kuma ,haka ta murje idanuwan ta, wallahi  sai sunan da ta ke so za a saka, hakan ya sa suka yi rigima sosai da Abubakar, sabo da shi ya na son a saka sunan mahaifin sa. Haka iya ta lallaba Abubakar ya yi hakuri a saka wanda ta ke so. Ita ma iya yanzu abun na Atika ya fara ba ta haushi.Haka aka yi suna yaro ya ci sunan Adamu.
Haka Atika ke ta murza mulki a cikin gida, gori da habaici ba wanda Zainaba ba ta gani ba, don ma wata rana malam Abubakar na taka ma ta burki idan ya na nan. Murnar iya ta koma ciki, sabo da Atika ba ta barin yaranta su je wajen iya, tun abun na ma ta ciwo, har ta zubawa sarautar Allah ido. Wasa-wasa har Atika ta yi shekaru shida agidan malam Abubakar. kwatsam! Sai ga ciki ya bai yana ga zainaba, zo ku ga murna wajen malam, kamar ba a taba haihuwa a gidan sa ba. Haka ita ma iya, ba a barta a baya ba, duk wani abu da zainaba ke so jiki na rawa ta kawo ma ta shi. Aka ce "rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya", toh hakan ce ta kasance a gidan malam Abubakar, zainaba ta haihu lafiya, ta samu Yaro... Ranar suna aka sa ma yaro sunan mijin iya watoh Abdul'aziz, amma su na kiransa da Abdul. Sabo da iya ta ce kar a boye sunan. Haka yaro ya taso cikin gata, duk abun da ya ke so, iya za ta sai da dabbobin ta, ta saya mishi. Malam Abubakar kuwa arxikin sa ya karu, ba bu inda ba asan malam Abubakar mai noma ba. Haka ya tattara yaran sa, ya saka su a makarantar boko da na islamiyya.
Bayan sun gama primary school, ya kai su boarding school KANTA COLLEGE.  Ya yin da ya'yan Atika su ka gama, shi kuma Abdul na ss1, iya ta rasu...Haka malam  Abubakar ya sa ka suTukur da Adamu gaba, akan dole su ci gaba da karatu, san nan kuma su ci gaba da noma, sabo da gadon gidan su ne kuma dai ai sana'ar hannu ce. Amma su ka yi tsaye suu sam, ba za suyi noma ba, sabo da aikin wahala ne,haka innar su Atika ta daure musu kar suyi noma. Malam abubakar bai ce musu komai ba ya kyale su.Bayan takad dun su sun fito ya tura su Alieru university, Tukur na karanta law, Adamu kuma likita. Da farko sun mai da hankalin su akan karatun su, amma daga baya su ka biyewa yan iskan abokai, su na shekara ta biyu aka koresu, amma malam bai sa ni.Ranar da malam ya ji an kore su, ran shi ya mugun baci. Duk da haka ya ba kowan ne su gona, ya ce su je su yi noma, ba zai sake hasarar kudaden sa, tun da ba karatun su ke yi ba!
Bayan Abdul ya gama KANTA COLLEGE shi ma ya wuce ALIERU UNIVERSITY. Ya karanta Agriculture. Ashe karar sa ta karshe ne ya hadu da Haleema,yar jahar katsina ce, a BARHIM ESTATE iyayenta su ke da zama... alokacin ta na 300 level.
Domin shawarwari ko gudunmuwa
pls 0814406675
yar mutan Argungu``` ❤️📚`````









ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
marubuciyar...✍️
**bayan wuya**
**ashe ba so ba ne**
**zumunta ko mugunta? on typing...✍️
writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
Gargadi!!!
kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free Book ne, ban ya fe duk wanda ya sayar da shi,akiye!!
Jinjina 👌
ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen❤️💙💚
Godiya:
ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode❤️
Ban manta da ke ba fatima iman Ibrahim ❤️
ta re da Abubakar Birnin tsaba👌
FREE BOOK 📚
SHAFI NA 10
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
**************300level ta ke...
A cikin shekara daya abubuwa da yawa sun faru, ciki har da zuwan malam makkah da kuma Auren su Tukur da Adamu, da kammala bautar kasar Abdul.  A gefe daya kuma Abdul ya aje takardun sa, zai kama wa malam aikin noma,a cewar sa ya kamata yanzu malam ya huta haka nan... Haka Abdul ya dinga shige da fice akan har kan Noma,  duk wanda ke cikin JADA ya san Abdul sabo da kwazonsa da kuma sauki da ya ke wa jama'a akan kayan abinci...
shiyasa babba da yaro ba bu wanda bai san Abdul'aziz Abubakar mai Noma ba,ya yi fice sosai a yankin Arewa...hakan ya jawo mishi bakin jini a wajen yan uwansa, a cewar su, su ne manya su ya kamata a fi sa ni, ba kanensu ba!!! Tun su na boye kiyayyar da su ke yi mishi, har su ka fitoh fili...
Malam yayi na shi kokarin ya fahimtar da su cewa kowa rabon sa ya ke ci,ba bu mai cin arzikin wani aduniya, kuma wannan abun kunya ne ace su rasa wanda za su yiwa hassada sai dan uwansu! Amma haka za su bad'awa idanuwan su toka, su ta ke zancen malam...
Yau kusan sati d'aya malam bai da lafiya, kuma yaqi ba ri akai shi Asibiti, haka kullum ya ke ta ra iyalansa, ya na bar musu wasiyya, da su rike ZUMUNTA 🤝 a tsakanin su, kar su bar shedan ya yi tasiri a cikin zuciyoyin su...
Tun d'azu malam ya ke kallon Abdul wanda ya yi rama kad'an, akan ciwon malam. Har ga Allah ya na tausayawa Abdul, sabo da irin yan 'uwan da Allah ya ba shi, sam ba su da tausayi koh jinkai ga kanensu, kan su kawai su ka sa ni, ga shi yanzu baya da lafiya amma Abdul kawai ya damu da shi sai kuma mahaifiyar shi,wallahi ya na tausayin zainaba, shine uwarta shi ne ubanta, amma ya san ko bayan ransa, ba za ta yi rashi ba, sabo da ya na da yakinin Abdul ba zai taba barin mahaifiyar shi, tayi kuka ba, idan ya tuna wannan yakan ji dadi...
Abdul ne ya dafa shi yana cewa " Baba ya na ganka ka na kuka kuma kana dariya? Murmushi malam ya yi san nan ya ce " ina farin ciki ne da Allah ya ban D'a mai hankali da kuma hangen nesa, haka kuma ina kuka ne sabo da zan bar ka ta re da kuraye, ma su farautar rayuwar ka,a yayin da kai kuma ba ka ma san da su ba, Abdul kar ka yadda Allah ya jarabce ka da laluran da ba ta da magani, kar ka yadda Allah ya daure maka kaddara da ba ta da iyaka, duniya cike ta ke da mugaye,kowa da ka gani son kanshi ya ke, kowa da ka gani son abin duniya ya ke yi,kasan dai rijiya mai gaba dubu, idan ka fada kafin aciro ka ai kasan ka shek'a lahira, toh haka tafiyar kaddara ta ke, na farko ba a tanada ma ta wuri,san nan tafiya ce da motar da ba bu matuki,tafiya ce da koh kana hanya koh ba ka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa za ka koma yi...
kasan yadda tafiyar take a cikin tsananin zafin sahara? Toh lallai wannan shi ne zanen kaddara...
Domin shawarwari  koh gudunmuwa
pls 08144066758
**yar mutan Argungu``` ``` ❤️💙```````````







ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?📚
MARUBUCIYAR...✍️
***Ashe ba so ba ne***
***Bayan wuya...***
***zumunta ko mugunta? On typing...✍️
Writing by-Fatima Zara Alhassan ❤️
GARGADI!!!
Kagaggen labari ne,sabo da haka ban yadda wani ko wata su juya min littafi  ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!
JINJINA 👌
Ga yan'uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma hada kanmu,muyi zumunta❤️💙
GODIYA
Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bi sa iyawar sa, da kuma yardarsa.Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna (ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?)
MATAIMAKA
**Abubakar Shu'aibu Bala BIRNINTSABA**
**Usman isah Rio**
**iman fatima Ibrahim**
GAREKU MAKARANTA
Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne, idan har kunga wani gyara toh kofata a bude ta ke(08144066758).
Free Book
SHAFI NA 11
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
*************kasan yadda tafiyar ya ke acikin tsakanin zafin sahara? Toh lallai wannan shi ne zanen kaddara, tafiya acikin sahara ga zafi , ga babu guzuri, kuma ba bu takalmin da zai rage ma ka zafin sahara, yunwa da kishirwa...sai ya rage ma ka taki kadan domin cimma manufar ka da burikan ka na rayuwa,sai kuma kayi katari da alkalamin kaddara, wac ce ta ke rubuta fari da baki. A lokacin za ka ji duniya ta yi ma ka zafi , kowa ya koma ya zuba ma ka ido. Allah sarki! sai ka ga lokacin duk inda za ka nufa cike ya ke da azzalumai. Duk inda za ka dafa mugaye cike su ke a gurin, kowa kokari zai yi domin asami dama daya tal! Haka zalika za ka ga ma kusantan ka su ne miyagun mutane, sabo da hassada da MUGUNTA, ba za su du ba ZUMUNTAr da ke tsakanin ku ba.
Abdul'aziz kar ka sake lokaci ya yi ka na me jin haka, tabbas  inaji ajikina wani abu zai faru da kai, amma ban san komai akan hakan ba,amma ina rokon Allah ya sa ko ma minene toh ya kasance  alkhairi,sabo da haka kar ka yadda duniya ta ba ka damar amsar wasikar jaki, rayuwar da aka gina bayan an saka Allah acikin ta, ba ta lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'ewa, idan kaga abu ya sa me shi, toh ubangiji ya yi hakane domin ya gyara mishi lamarin shi...
A jiyar zuciya Abdul ya yi, ya na mai kallon mahaifinsa,ta re da nazarin maganganun sa, tabbas wannan ita ake cewa" Hausa mai ban haushi" Idan har mutum bai zurfafa tunani ba, ba zai gane inda maganganun nan su ka dosa ba, abu na karshe kuma da ya fahimta anan shi ne, mahaifinsa na son ya kula sosai akan yan'uwansa, sabo da kiyayyar da suke nuna mishi,wanda shi kansa ya san da wannan...amma har ga Allah ba zai ce ga dalilin mahaifinsa na yi ma shi wadan nan zantukan ba...murmushi Malam ya yi sabo da ganin halin da Abdul ya shiga, shi adole ya na son sanin ina maganar ta dosa. "Abdul sanin gaibu sai Allah, ban ce  maka lallai wani abu zai faru ba, cewa na yi inaji ajikina,  ka  ci gaba da addua ni ma zan ta ya ka yi in-sha Allah. Ta shi ka tafi, Allah ya yi ma ka albarka...
A sanyaye Abdul ya fito daga dakin mahaifin na sa, ya shiga wajen mahaifiyar sa.  d'aga kai inna zainaba ta yi ta na kallon tilon d'anta, ta na kuma hango tarin damuwar da ke kwance a fuskar sa. Bayan ya zauna ta gabatar ma shi da abinci, ta na mai kara nazarinsa da kyau.
Kadan yaci abincin ya rufe kwanon, sabo da ba ya da appetite. "Abdul me ke damunka? ka na kallon kanka kuwa? kaga yadda duk ka bi ka rame...? "inna nima wallahi ban san meke damu na ba, amma ina ga ciwon malam ne, kuma yaki ba ri akai shi Asibiti! Ajiyar zuciya ta yi "wallahi nima ciwon malam na damu na, kwanan nan wasu irin mafalkai na ke yi masu ban tsoro." cikin tashin hankali Abdul ya ke kallon mahaifiyar shi..."inna wane irin mafalki ki ke yi, wanda ya sa ki ke zubar da kwalla?" "Abdul kasan cewa malam shine uwata shine ubana? malam ya rikeni tsakani da Allah, ban ce ba bu maza irin malam ba,amma dawuya asamu masu tausayi, soyayya,wadata iyali, hakuri da mace, da sauran abubuwan da ke faruwa a cikin rayuwa, fashewa ta yi da kuka, Abdul idan na rasa malam ban san me zanyi ba! ina yawan mafalkan ku kai da malam, ina ji ajikina kamar wani abu zai faru da ku...! "``` YAR MUTAN ARGUNGU``` `````` ... ✍️❤️


ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA?📚
Marubuciyar...✍️
***Ashe ba so ba ne***
***Bayan wuya***
***zumunta ko mugunta*** on typing...✍️
Writing by-Fatima Zara Alhassan ❤️
DOKA!!!
Wannan littafi kagagge ne,sabo da haka
ban yarda wani ko wata su yi amfani da kalma daya daga cikin littafi na ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!
SADAUKARWA
Ga iyaye na domin nuna godiya ta a gare su❤️
GAREKU MASOYANA❤️
Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne idan har kunga wani gyara, toh kofata a bud'e ta ke domin ga number waya ta nan don isar da sako kai tsaye zuwa gare ni...08144066758(WhatsApp number 08162058867)
SHAFI NA 12
  BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
**********************************************"Ina ji a jikina kamar wani abu zai faru da ku...!" Rungume mahaifiyar shi ya yi, ya na cewa "Inna ba ko yaushe mafalki ya ke zama gaskiya ba, mu ci gaba da yin sadaka domin ita ce ke kore duk kan masifu, idan kuma wannan abun na cikin kaddarar mutum, toh sai ya kasance abun  ya zo mishi da sauki..."
Bayan ya ba ro d'akin inna, directly na sa d'akin ya wuce, ya zauna ya na tunanin maganganun da iyayen shi su ka fada mi shi,ta re kuma da nazarin su, toh me hakan ya ke nufi? Du ba agogon hannun sa ya yi, 11:30pm na dare, hakan ya sa ya tashi ya je ya d'auro alwala domin gabatar da sallar nafila, ba zai yi wasa wajen fad'awa ubangiji bukatun shi ba...
Yau gidan malam Abubakar cike ya ke da tashin hankali, sakamakon rasuwar malam,wanda ba iya kacin iyalansa ba,har ta mutanan gari sun ji wannan mutuwar! Haka aka yi jana'izar sa, ta re da d'unbin mutane, ta ko ina jama'a sun taru, sai dai muce Allah ya jikansa ya kuma sa ya huta tare da dukkan kulumin musulmai baki daya...
Bayan sati biyu aka shiga rabon gaado, amma Abdul hankalin sa ba ya  kan rabon gaadon, sabo da mahaifiyar sa da ke kwance a gadon asibiti ba ta da lafiya, kamar tasan lokacinta ya yi, ha ka za ta saka Abdul gaba ta na yi mishi wasiyya.  Allah sarki inna zainaba, ita ma kwanan ta biyar cif a Asibiti ta ce ga garin ku...
Dauko gawar ya yi, ya zo gida da ita aka yi ma ta wanka,  sannan aka yi ma ta sallah aka kai ta makwancin ta, wanda duk mai rai sai ya riski haka, ya Allah ka sa mu gama da duniya lafiya,mu  cika da imani...
Duk wanda ya  Kalli Abdul zai san cewa ya yi babban rashi, ba bu iyaye sannan ba bu dangin iyaye, a gefe d'aya kuma ga rashin mutuncin da Brothers din sa , su ke yi mi shi, hatta gaadon sa da ya ke da hakki akan sa, duk sun tattara sun handame, sai sauran filayen su na noma, ya kai karar su amma abanza, kun dai san yadda azzalumai su ke a wannan lokacin...a lokacin ne ya dauko takardun shi  na makaranta domin neman aiki, amma bai samu ba. Duk manyan mutanan da ya san ya yi huld'a da su a baya, haka ya dinga bin su domin samun madafa amma shiru ka ke ji " kamar an aika bawa garin su"  sabo da a wannan zamanin na mu, sai ka na da shi ake yi da kai,wallahi da zarar ba ka da shi, toh kai da ban za duk d'aya ku ke, mai karfi shi ake k'arawa k'arfi, kai kuma talaka a k'ara durk'ushe ka. Toh hakan ce ta faru ga Abdul'aziz Abubakar mai Noma; Cikin iyawar ubangiji sai ga shi wa su mutane sun ba shi aron gonakin su ta re da ba shi gudunwar kudi,  wa su kuma su ka  ba shi iri na shuka, ya yi murna

Please Login or Register in order to submit comment