Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemi lauyan da ke ƙara ya gabatar da kan sa, cikin shirin lauyoyi ya tashi, ni sunana Barrister Aminu Bello ɗan tsoho, kuma ni ne lauyan waɗan da su ka shigar da  ƙara. jinjina kai alƙali ya yi, san nan ya ce zauna mun gode.
San nan alƙali ya sake cewa, ina lauyan da ke ka re waɗan da ake ƙaraShima cikin shirin lauyoyi ya tashi ya ce, sunana Barrister Hamza Sani, ni lauyan gwamnati ne, ni ke ka re haƙƙin waɗan da ake ƙara. jijjiga kai alƙali ya yi, san nan ya ce zauna mun gode.
San nan alƙali ya fara da cewa, "mun buɗe wannan shari'a 29/1/2023 sabo da rashin ƙwararrun shaidu, shiyasa mu ka ɗage shari'ar har  zuwa  13/2/2023
Ina fatar duka ɓangarori biyun kun zo ma na da shaidu?  sabo da yau ne zama na ƙarshe...
Rubuce-rubuce ya yi, san nan ya ce, Barrister Aminu ka gabatar da shaidun ka. cewar alƙali
Tashi barrister Aminu ya yi, ta re da kallon gefen da  jama'a su ke, amma bai ga Aneesa ba,  su kawu kawai ya gani, su na haɗa ido su ka yi mi shi dariya, kuma ya na da tabbacin dariyar mugunta ce su kawu ke yi mishi. Toh ina Aneesa?  tambayar da ke yiwa kan sa kenan...
Maganar alƙali ne ya katse shi, Barrister mu na sauraron ka...
"ya mai shari'a ina son aba DPO Hassan  dama ya gabatar  da shaidun mu na gaba. an ba kaBayan DOP ya shigo da yaran su ka tsaya a wajen da ma su shaidu ke tsayawa, Barrister Aminu ya zo wajen su ya tsaya. San nan ya ce, "ina son ku gabatarwa kotu ko ku su waye ta re da sana'ar ku...
"Ni sunana Bilya,amma ana cemin  ɗan ƙaruna, ba ni da wata sana'a fac ce fashi da makami...
"kai fa? Barrister Aminu ya tambayi ɗayan yaron
Ni sunana  Haruna, amma anfi sa ni na da ɓauna, ni ma dai sana'ata fashi da makami ne,  daga ganin yadda su ke yin magana kasan cewa sun bugu a hannun ƴan sanda.
Tsayuwa barrister Aminu ya gyara,san nan ya ce,  "Me Alh Abdul'aziz Mai Noma  ya yi mu ku, ku ka tafi har cikin gidan sa, ku ka kashe shi, shi da matar sa?...
"objection my lord, Ya kamata abokin aikina ya iya kalaman sa...
Barrister Aminu a kiyaye, cewar alƙali
Duk yadda Barrister Aminu ya so yaran su karɓi laifin da su ka aikata, amma abu ya ci tuura. ya yi mamakin yadda labari ya sha banbam...
Ana cikin haka sai ga su Duna sun kutso kai cikin kotum da gudu, da alama security'n wajen ne su ka hana su shigowa, da ƙyar su ka shigo.
Ganin hayani ta yi yawa, shi ya sa alƙali buga gudumar shi, ya na cewa "silent pls!!!"
Nan da nan kowa ya natsu, kallon sa ya kai wajen su Duna, san nan ya ce " me ya sa za ku shigo kotu ku na yi ma na hayaniya, ba kusan cewa dokace ga masu yi ma na hayaniya ba?! ko an faɗa mu ku nan wajen wasa ne?!"
Cikin saukar da kai, duna ya ce "ranka shi daɗe, ƙarar wasu mu ka kawo. kuma su na nan zaune a cikin wannan kotun, yanzu haka ma case ɗin su ake yi.Cikin tashin hankali kawu Tukur ya miƙe tsaye ya  na nu na su Duna, ya  na cewa wlh ƙarya ku ke yi, ba ku da wata alaƙa da shari'armu!"
Tsawa alƙali ya yi wa kawu, "ina ruwan ka da su? wajen ka su ka zo, ko kuma wani ya ba ka izinin magana?!
Cikin jin kunya kawu ya ba da haƙuri, san nan ya koma wajen zaman sa
San nan alƙali ya dubi su duna ya ce, "ku sa ni, ba a ƙara akan ƙara, idan karar wasu ku ka kawo, to ku je ku rubuta statement, san nan a fara shari'a."
Bayan nazarin ko wane ɓangare da Barrister Aminu ya yi, sai wani tunani ya shigo shi. Abu na ɗaya da ya fahimta akan waɗan nan matasan shi ne, su na da alaƙa da wani aiki wanda su kawu su ka sa ka su yi, kuma ya na da tabbacin akan Aneesa ne, idan kuwa hasashen shi ya zama gaskiya, toh lallai waɗan nan su na cikin shaidun shi na ga ba...
Gyaran murya alƙali ya yi, san nan ya dubi barrister ya ce  " Barrister da alama ba ka da ƙwararrun hujjoji akan wannan shari'a
Sabo da haka zamu yi watsi  da wannan shari..." a dakata akwai shedu" wata murya ta faɗa.  kallo ne ya koma ga wannan mutumin mai magana.
  ƴar mutan Argungu``` 💖
















❤️ZUMUNTA KO MUGUNTA❤️
            .   NA
                       FATIMA
ZARA
  YAR MUTAN
      ARGUNGU❤️
      بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ               
A dakata akwai shedu" wata murya ta faɗa.  kallo ne ya koma ga wannan mutumin mai magana.
A je gudumar alqali ya yi, ya na kallon mutumin da ya yi wannan magana
wanda har yanzu ya na bakin kofa.
kallon barrister Aminu dan tshoho alkali ya yi, san nan ya ce " barrister koma wajen zaman ka, sabo da wannan shari'ar ba ta bukatar lauyoyi...
Murmushi Barrister ya yi, san nan ya ce " Nagode ya mai shari'a"
(abun da ya sa alkali ya ce Barrister Aminu ya zauna, saboda ya gano cewa shari'ar mai sauki ce, amma mutane na son mayar da ita mai wahala.)
Sai da alkali ya karewa mutumin kallo tsaf, san nan ya ce, "  wanene kai? kuma daga ina ka ke? kuma meyasa ka dakatar da ni?!
A hankali malam kabiru ke takowa, har ya kawo in da ma su shaidu ke tsayawa.San nan ya fara da cewa...
"Ya mai shari'a,da farko dai sunana kabiru, na biyu kuma ni mutumin KAITa ne...na uku kuma  ina rokon  katu ta ba ni dama in gabatar  da wani mutum, wanda shi ne  zai yi ma na bayanin amsa ta uku.
"Ambaka dama"
"Nagode ya mai shari'a"
Murmushi malam kabiru ya yi, san nan ya je ya shigo da malam Bako, su ka tsaya wajen da ma su shaidu ke tsayawa
Tun shigowar malam Bako, kotu ta hautsine da hayaniya, shi kansa Alkali mamaki ya isheshi. (sabo da fuskan malam Bako ba boyayye ba ne a katsina)
Sai kuma ga shigowar Aneesa, duk mutanan da ke cikin kotu, sun saki baki da hanci su na kallon wannan abun al'ajabi...
Fadin tashin hankalin da su kawu ke ciki, bata baki ne!!!
Jikin sa na tsuma ya kira sunan diyar ta shi,Aneesa...
Tsaye ta ke waje daya ta ka sa yarda da abun da ta ke gani tsaye a gabanta
Shin da gaske mahaifinta ne, ko kuma mafarki ta ke yi?
kamar malam Bako ya san abun da zuciyar Aneesa ke fada ma ta...


Rungume ta ya yi, ya na mai fashewa da wani irin kuka mai taba zuciyoyin ma'abota saurare...
Hakan da ya yi ma ta, shi ya tabbatar  ma ta cewa ba mafarki ba ne. Rungume shi ta yi tana kuka mai ban tausayi...
Duk wannan abun da ke faruwa, sarauniya ta re da iyalan ta, su na gefe daya su na kallo. Amma ba bu mai ganin su sai mutum biyu, Aneesa da kuma malam Bako.
Rushewa su ka yi  da kuka, su na mai rungume junansu..
Bayan kamar minti biyar, alkali ya ba da umarni a saurara.
Kotu ta yi tsit! kamar ba mutane cikin ta
San nan Alkali ya mai da dubansa gefen da malam Bako ya ke,  san nan ya ce" mu na sauraran ka.."
Tsayuwar shi malam Bako ya gyara sabo da juwar da ya ke gani, kar ta zubar da shi kasa.
San nan ya fara da cewa, Sunana Abdul'aziz kamar yadda ku ka sanni...
Haka ya  ba kotu labarin sa tun daga farko har karshe...
Jama' a da dama sun tausaya mi shi, wasu har da kuka.
Bayan gama sauraran shi,
alkali ya ba su duna dama su fadi iya abun da su ka sa ni, haka su ma su ka fadawa alkali duk yadda su ka yi da su kawu.
Nan ta ke alkali ya sa akama su kawu, 
  za su yi shekaru biyar a gidan yari ta re da horo mai tsanani, 
daga karshe kuma za a rataye su, sabo da an kama su da laifin kisan Hajiya Halima matar Abdul'aziz mai Noma.
(Ku yi hakuri akan yadda na gudanar da shari'a🤣ban taba shiga kotu ba).
Haka dai shari'a ta watse kowa ya kama gabanshi.Daga kotu ba su zar ce ko ina ba sai gidan Aunty Nafisa, sister Halima, anan kam sun sha tarbo kamar ta hadiye su, sabo da murna.
Nan da can Aneesa taqi ba ri mahaifin ta ya matsa ko ina, shima haka.
Anan Aneesa ta ba su labarin su sarauniya, tun daga farko har karshe...
Alh. Abdul'aziz ya yi kuka kamar ba gobe
San nan ya cewa Aneesa, "  Dan Allah ina zanga wadannan bayin Allah inyi mu su godiya?  ta re da fashewa da kuka...
Rungume shi Aneesa ta yi, ita ma ta na share na ta Hawaye.
"Baffa dan Allah kabar kuka, wallahi ko a yanzu ka ke son ganin su, za su bayyana a cikin parlon  nan".
Hannu ta sa ka a cikin aljihun wandon ta, sai ga shi ta fito da kahon da sarauniya ta ba ta.
A hankali ta ke busawa, cikin amo mai dadin saurare, wanda ita kanta Aneesa ba ta san ta na da irin ta ba.
Bangon parlon ne ya fara rawa, sai kuma can  ya tsaya cak! kafin kiftawa da Bismillah sai ga su sarauniya sun bayyana a tsakiyar parlon.
Da gudu Aneesa ta zo ta rungume ta, murmushi sarauniya ta yi ta na mai shaafa kan  Aneesa.
"Su Aneesa yau anga Baba, kin man ta da maman ki" cewar sarauniya ta na murmushi.
Cikin mamaki da kuma al'ajabi,  ta re kuma da tsoro, Aunty Nafisa ita da mijin ta ke cewa Bismillah ga wuri ku zauna dan Allah.
Godiya su sarauniya su ka yi, san nan su ka zauna.
Nan fa aka yi ta gaishe-gaishe, tsakanin su sarauniya da su Baban Aneesa.
San nan Baban Aneesa ya fara godiya  fiye da tunanin mai karatu.
Aunty su ma sun taya Baban Aneesa godiya.
Sarki fu'ad ne ya yi gyaran murya, san nan ya fara da cewa, " Alhamdulillah, Allah shi ne abun godiya.   Mu na godiya a gare shi, da ya nuna mana wannan rana, yau Aneesa ga ki ga Baban ki cikin ikon ubangiji.
San nan abu na biyu, mu na kara godiya akan alkhairin da ku ka taba yi ma na, ni da mahaifiya ta,
ta re kuma da yar'uwa ta ga ta nan,( ya nu na gimbiya Hoor)
duk da nasan cewa ba lallai ne ka iya tunawa ba,
sabo da shekarun akwai yawa,
amma nasan ba za ka man ta lokacin da maciji ya so ya sari Aneesa ba?   A lokacin ta na tare da wuni zomo riqe a hannun ta? 
Toh wannan zomon ba  dabba ba ne, kanwa ta ce.
kuma mun ji dadin taimakon ta da kayi a wancan lokacin.
Tun ranar da abun ya faru, mahaifiyar mu ta so ta yi mu ku godiya, sai dai kuma ta ji tsoron kar ta je garin godiya , ta firgita ku.
Shiya sa  aka ce "Alkhairi danqo ne, ba ya faduwa kasa banza" komai daren dadewa sai ka tsince shi a gaba.
"Tabbas haka ne yaya na, shiya sa ya na da kyau hatta dabbobi mu dinga tausaya mu su,  ba wai mu ce ba ri mu gallaza mu su, sabo da su dabbobi  ne  ba sa jin komai. A'a kar mu yi haka tun da su ma rai ne da su.
Daga karshe ina rokon Allah ya ba mu ikon gyarawa, ya kuma sa ma na tausayi a cikin zuciyar mu".
Ga ba daya parlon su ka ce amin.
Motsi malam kabiru ya yi, san nan ya ce" Jama',a toh nikam ina ga anan zan barku,  sabo da kunsan yanayin hanya ba ta da kyau,  ga ra in isa gida tun gari bai yi duhu ba."
Murmushi Baban Aneesa ya yi,  "tab! ai wallahi ba ka isa ka tafi yanzu ba sai komai ya kammala."
malam kabiru na dariya ya na cewa " Ai dole ka ce haka ma na, tun da ga shi na kawo ka cikin iyalan ka."
Ruko hannun sa Alh. Abdu'aziz ya yi, "haba aboki ko ince dan uwa,   ka yi hakuri ka kwana ma na,  ka ga gobe kafata kafarka sai in mai da ka wajen masoyiyar ka ma na? ta re da yi mi shi dariyar tsokana...
Cikin jin kunya malam kabiru ya ce, kadai yi alkawaari"
"Eeh"
Haka dai su ka zauna su  ka shaa firar su, yadda ku ka san jinsi daya.
Daga karshe su sarauniya su ka yi su mu sallama za su tafi.  Ta re da cewar kofa a bude ta ke, duk ranar da Aneesa ke son zuwa wajen su, toh su na maraba da ita.
Kuma su na son dan Allah in so samu ne, a bar Aneesa ta ci gaba da makarantar da ta ke yi.
Alh. Abdu'aziz ya kuma yi wa sarauniya alkawari zai bar Aneesa ta ci gaba da karatun ta acan in sha Allah.
Dakyar Aneesa ta bar su sarauniya su ka ta fi. Wan nan kenan
Washe gari, kotu ta tattara duk wa su takaddu na mallakan Alh Abdul'aziz Mai Noma ta ba shi kayan shi.
Dukiya ta dawo hannun sa.
Bayan ya koma gida, su ka kama hanyan garin su malam kabiru.
Gabda sallan la'asar su ka iso,  sabo da shima Alh. Abdul ya ce a ranar ya ke son ya koma gida
Har cikin gida malam kabiru ya yi mishi jagora su ka gaisa da matar shi.
Bayan sun gama gaisawa, ya ciro takardu daga cikin aljihun sa, ya mikawa malam kabiru, ta re da dauko biro daga cikin aljihun gaban rigan sa, ya mika mishi.
Cike da mamaki malam kabiru ke kallon shi! Wadan nan takardun fa? malam kabiru ya tambaya.
Murmushi Alh Abdul ya yi, san nan ya ce,
"A duniya kafin a samu mutane irin ku sai an tona.  kun taimake ni sosai kai da malam idris alokacin da na ke bukatar taimako, ba ku kyamace ni ba, kun jawo ni jikin ku, kuma kun nu na min so tamkar dan uwan ku, a lokacin da na wa yan' uwan  su ka ruguzamin ta wa rayuwa, shin me zanyi mu ku in biya ku? Wallahi ba bu, duk wani abu da zan ba ku wallahi ban biya ku ba, wannan kuma Allah kadai zai iya biyan ku ba ni ba.
Sabo da haka wadannan takardun na kamfanina ne guda biyu, daya ta Auduga daya kuma na Aya, ka zabi daya daga cikin su sai ka saka hannu ya zama na ka,
dayan kuma zan ba malam idris shi ma ya sa ka hannu.
kuka malam kabiru ke yi sabo da rasa bakin godiya...
Haka dai su ka rabu cikin mutumci
Bayan ya koma katsina bai zarce ko ina ba sai makabarta, in da malam Idris ke gadi, anan ya tadda malam Idris shi ma ya ba shi dayan kamfanin.
Daga nan kuma ya wuce gidan Aunty, inda  ya bar Aneesa.
Ita ma Aunty ya ba ta gidan shi da ke Barhim Estate kyauta.
Sauran kadarorin sa kuma ya sayar da su,
ya ba wa mijin Aunty a gina mi shi masallatai da rijiyoyi, su zama sadaqatul jariya ga matar sa Halima, ta re da iyayen sa .
San nan ya yi wa su Aunty sallama, da cewar gobe  za su bar kasa ga ba daya.
Su Aunty sun yi sun yi, ya yi hakuri ya zauna a Nigeria, amma ya ce shi sam ba zai sake rayuwa a cikin ta ba.
Amma ya na son gobe kafin su wuce, ya ga su  Kawu.
Yau tun da safe ya dauki Aneesa, sabo da ya na son su je su gama abun da za su yi  because jirgin su na qarfe 2pm ne.  
kai tsaye su ka wuce Gidan yarin katsina.
Ba ta re da bata lokaci ba aka turo  su kawu.
kallo daya  za ka yi mu su, kasan cewa ba qaramin wahala su ka shaaba.
Daga jiya zuwa yau, har sun fita hayyacin su (Allah ka karemu daga muguwar kaddara).
Su na ganin mu su ka fashe da kuka, mai tayar da hankalin ma'aboci sauraro!!!
"Mun tuba mun bi Allah! Abdul dan girman ubangiji ka ya fe ma na abubuwan da mu ka yi ma ka?!!!
Wallahi tallahi sharrin shaidan ne... (cewa kawu Tukur).
Har kasa kawu Adamu ya kai ya na cewa, "Abdul mun zalunce ka, mun yi ma ka mugunta, kuma mun yi ma ka hassada.
Bayan Ubangiji ya daukaka, kuma ka sa ke rungumomi, ba re da ka duba MUGUNTAR da mu ka yi ma ka ba, ka sake jawo mu jikin ka, ka ba mu duk kan wa su  abubuwa na rayuwa, amma daga baya mu ka yi ma ka butulci.
Dan Allah dan uwana ka ya fe ma na duk abubuwan da mu ka yi ma ka, ba dan halin mu ba?!" kuka ya ke yi kamar ransa zai fita.
Dago shi daga kasa Abdul ya yi, ya na cewa:  Kubar kuka na ya fe mu ku duniya da lahira, Allah ya fe ma na gaba daya.
Yaya  tun farko ya kamata kusan da haka, ba sai da lokaci ya kure mu ku ba, a lokacin da ba zan iya taimakon ku ba, (shi ma ya na share  hawayen da ke zubowa  daga fuskar shi)
Na so kusan ma'anar zumunta tun farko, sabo da kusan  bambanci tsakanin ZUMUNTA KO MUGUNTA?
A lokacin na yi tunanin bazan kai labari ba, shiya sa na cewa Aneesa  idan har ubangiji ya yi ma ta tsawon rai, ta samo ma'anar zumunta ko mugunta,  hakan zai ba ta damar sanin wane irin zama ne mu ke  yi tsakani na da yan' uwana.
Sai ga shi cikin ikon ubangiji, ashe ni ne wanda zai samo wadannan ma'anonin gudana biyu!"
ZUMUNTA:
SHI NE KYAUTATAWA DA JINKAI DA BIBIYAR YAN' UWA( MA'ABOTA ZUMUNTA) TA HANYAR SADAR DA DUK KAN ALKHAIRI GA RE SU DA KAWAR DA DUK KAN SHARRI DAGA GARE SU GWARGWADON IKO.
ZIYARTAR SU DA AMSA KIRA DA GAYYATARSU DA KUMA TAIMAKA MU SU DA DUKIYA DA KUMA TAUSASA MAGANA GA RE SU DA KAWAR DA KAI DAGA KURA-KURANSU, DA YI MU SU ADDUAR ALKHAIRI.
FALALAR SADA ZUMUNTA
Yana sanya tsawaitar rayuwa
Wadatar zuciya
Bunkasar dangi
Samun yardar Allah
Samun shiga Aljanna
KUMA YAWANCI WADANNAN FALALOLIN AN CIRO SU NE DAGA HADISAN ANNABI (SAW) .
HADISIN MUSLIM DAGA ABU HURAIRA(RA)CEWA, ANNABI (SAW)YA CE:
"WANDA YA KASANCE YA BA DA GASKIYA DA ALLAH RANAR LAHIRA , TO YA SADAR DA ZUMUNCIN SA."
HAR WAYAU SUN KARA RUWAITOWA DAGA NANA AISHA(ALLAH YA KARA MA TA YARDA)  DAGA MA'AIKI (SAW) YA CE:
"ZUMUNTA TA NA MAKALE A JIKIN AL'ARSHI, TA NA CEWA: WANDA YA SADAR DA NI, ALLAH YA SADAR DA SHI, WANDA KUMA YA YANKE NI, ALLAH YA YANKE SHI."
A WATA RUWAYAR KUMA, AN KARBO DAGA SAYYIDINA ANAS (RA) YA RUWAITO.
MA'AIKI (SAW) NA CEWA:
"WANDA YA KE SO A YALWATA MA SA ARZIKIN , KUMA A JINKIRTA MA SA A RAYUWAR SA , TO YA SADA ZUMUNTANTAR SA."
          (BUHARI DA MUSLIM SU KA RUWAITO ).
MUGUNTA!!!
TA NA KARKASHIN HASSADA, A HANKALI MUGUNTA KE RIKIDA ZUWA HASSADA!
KU NA TUNANIN MUGUNTA CE KU KE YI MIN, BA KU SAN CE WA HASSADA CE TA CI ZUCIYOYIN KU SANNU A HANKALI BA.
MANZO ALLAH (SAW) YA GARGADE MU KAN (MATSALAR) HASSADA DA IRIN ILLAR DA KE TATTARE DA ITA, IN DA YA CE,
"KASHE DINKU DA HASSADA , SABO DA ITA TA NA CINYE KYAWAWAN AYYUKA KAMAR YADDA WUTA TA KE CINYE KARARUWA."
            (ABU DAWUDA NE YA RUWAITO HADISIN).
HAKA NAN KUMA SABO DA YA SA AL'UMMAR MUSULMI TA KASANCE TABBATACCIYA , DUNKULALLIYA A WAJE DAYA BA TA RE DA TA SAMU MATSALA BA, SAI YA JA HANKALINTA GA HADISIN BUHARI  YA RUWAITO A CIKIN LITTAFIN ARBA'UNA HADIS NA NAWAWIY (HADISI NA 35).
"ANA NEMAN TSARI DAGA MAI HASSADA LOKACIN DA YA BAYYANA MUMMUNAR MANUFARSA TA YIN HASSADAR, LAMARIN DA YA NA IYA YIN KOMAI DON GANIN YA CIMMA BURINSA NA MUGUNTA.
A jiyar zuciya Abdul ya yi, san nan ya kara da cewa, " shiya sa tun mu na yara, mahaifin mu ya so ku samu ilmin addini, amma ku ka bijirewa batunsa!
Duk yadda ka samu ilmin addini ba za a hadaka da wanda bai taba neman sa ba."
"Rungume Abdul su ka yi, "mun gode Abdul...mun gode..
Kar ku damu, Allah gafurun rahimun ne, kuma maji rokon bayinsa, ku yi tayi istighfari Allah ya yafe mu ku."
"Dan Allah Aneesa ki ta fe ma na, ba dan halin mu ba?"
"Ni ma na ya fe mu ku, duniya da lahira.
Allah ya sa mufi karfin zuciyoyin mu."
Su ka amsa, "Amin"
Haka dai Abdul ya ja hannun diyar sa, su kabar gidan yari, ta re da jin tausayin yan'uwan na shi.
Duniya kenan! Ba ka zo ba ma, ta na jiranka balle kai da ke cikinta!"
BAYAN WA SU SHEKARU...
Princess Noura Bint Abdulrahman University, ta ke yaye dubban dalibanta, cikin su har da Aneesan Sarauniya 😀
Sarki Fu'ad ta re da iyalansa(ya yi Aure.  Da farko ce wa ya yi shi ba zai Auri kowa ba fac ce Aneesa. Sai da sarauniya ta yii mi shi jan ido san nan.
Ta kuma zaunar da shi ta fada mi shi cewa, shi kansa ya san ubangiji ya Haramta Aure a tsakanin jinsin su da na Bil'adama.
Sai a lokacin ya dawo cikin hayyacin sa.
Wannan kenan)
Bangare daya kuma gimbiya Hoor ce ta re da ya'yanta 2
Sai Baban Aneesa da tashi Balarabiya, sai kuma sarauniya wadda yanzu girma ya fara nu na wa.
Ita kan ta Aneesa an saka bikin ta, nan da wata shidda(6 months)
Yadda su ke gudanar da ZUMUNTAR  SU kamar jinsi daya!
Alhamdulillah!!
DUKA-DUKA ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA WA MAI SU NA ZUMUNTA KO
MUGUNTA?KURA-KURAN DA KE CIKIN SA ALLAH KA YA FE MIN.
INA KUMA KIRA GA YAN'UWANA DON ALLAH KU DAUKI ABU MAI AMFANI KU ZUBAR DA MARAR AMFANI👋 NGD
GODIYA TA MUSAMMAN GA MA SU BIBIYAR LITTAFAI NA,  KUMA MASOYA NA, ALLAH KA BIYA MU SU DUK KAN BUKATUN SU NA ALKHAIRI ❤️
MU HADU DA KU A LITTAFI NA GABA MAI SUNA (BAYAN WUYA...?)
LITTAFI NE MAI DAUKE DA, ZAZZAFAN SOYAYYA, HAKURI, DOGARO DA KAI DA SAURAN SU...
           YAR❤️MUTAN❤️ ARGUNGU

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be

Please Login or Register in order to submit comment