Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mi ki alƙawarin zan kai ki school ɗin,  dan haka ki na iya tafiya ki kwanta sai da safe."
Rungume sarauniya Aneesa ta yi, ta mai ƙara godiya akan hidimar da ta ke yi ma ta, san nan ita ma ta yi ma ta sai da safe, ta wuce ɗakin ta.
******************************A ka ce biki na farar kaza, balbela ba gaiya ba. Waje ne aka shirya sosai, ya haɗu ƙwarai da gaske, musamman wajen da Amarya da ango za su zauna, an shirya wurin da duwatsu ruwan zaiba, ma su  ɗankaran kyau, a bayan duwatsun ruwa ne ke zubowa farare ƙal! sai kujeru ma su ɗigon zinari guda biyu, ƙasan kujerun an zuba irin waɗan can duwatsun, ga furanni ma su kyan gaske(ban taɓa ganin irin su ba) sai hanyar da Amarya da Ango za su bi, gadace ƴar siririya ta duwatsun lu'u-lu'u ma su hasken gaske...
Ɓangare ɗaya wajen da baƙi za su zauna, shi ma ba a magana.
Kafin ka ce kwabo, an taru sosai, maza da mata, manya da yara, sai kai komo su ke yi,  kowa da kalar ta shi halittar, duk halittun da sarauniya ta lissafo wa Aneesa, to yau ga su, gani ya kori ji...
Sau ɗaya gaban Aneesa ya faɗi, bayan ta kalli waɗannan halittun, kwata-kwata ba ta ji wani tsoro ba. sai ma kai da kawo
da ta ke yi a cikin su...
Amarya da Ango ne su ka fito da suffar tsuntsaye farare fat ma su girma, sai wani ɗigon baki da ke cikin idanuwan su, a hankali su ke  bin gadar da aka ta na da domin su, a hankali har su iso wajen zaman su...
A haka ko ne Aljani zai fito ya gabatar da kan shi, a gaban Amarya da Ango,san nan ya a je mu su ta shi kyautar, wannan ita ce al'adar su, Aljanun ruwa da na su ƙungiya, Aljannun kan tudu da ta su tawagar, da sauran nau'ukan aljanu...
A na cikin gudanar da biki,  wata farar Dila mai bindi tara, ta bayyana mai lallausar gashi, duk hankulan  kowa ya koma kan ta.
Murmushi gimbiya Hoor ta yi, ita ma sarauniya murmushin ta ke yi,sabo da sanin ko wace ce ta shigo. Sarki fu'ad da tawagar shi, sun mai da hankalin su wajen sanin ko wace ce wannan..
Bayan ta isa wajen Amarya da Ango ta miƙa gaisuwa, san nan ta koma wajen sarauniya ta zauna,  nan ta ke sarki fu'ad ya gano wace ce farar Dilar mai bindi tara, domin kuwa wurin da ta zauna Aneesa aka tanadarwa shi. Murmushi sarki fu'ad ya yi, ya na mai girgiza kan shi, sabo da ya san da sa hannun   sarauniya a ciki...
Haka dai aka yi kaɗe-kaɗe da raye-raye, da kuma nuna wasu ba jinta, aka ci abinci kala-kala ga sunan birjik
Tabbas wannan bikin ya na ɗaya daga cikin bukukuwan da ba za a manta da shi ba nahiyar ga ba ɗaya...
A na gab da kammalawa ne, sarki  fu'ad ya tashi  ya yi jawabi ya nuna farin cikin sa ga baƙi na kusa da na nesa, waɗanda su ka halarci wannan taro, tare da yi mu su fatar komawa garuruwan su lafiya, sannan taro ya watse...
washe gari, aka ɗaura Auren gimbiya Hoor  da Angon ta  saif Hashir, a ranar aka wuce da Amarya saudiyya, kasancewar shima Angon ɗan uwan salman ne.
A lokacin ne na ga yadda Aljanu ke na su shirin, idan za a raka amarya.
Amarya ce zaune  cikin karagar zinari mai hannuwa, dakaru talatin ne ke ɗauke da wannan karagar. Haka aka fara tafiya cikin sararin samaniya, tawagar farko aljanu ɗari da hamsi, sai Amarya da ke tsakiya, sai kuma bayan ta aljanu su ɗari uku ne ke take ma ta baya, ciki har da Aneesa  wadda ta sauya yanayin ta (siffa) zuwa wata  ƙatotuwar maiki(eagle)
Wani katafaran masarauta su ka shigo, mai mugun kyau, wadda ke cikin  tsakiyar garin Riyadh, masarauta ce ta ji da faɗa, wadda ta ninka masarautar farisa sosai. Dangin Ango sun karɓe su hannu bibbiyu, san nan aka wuce da Amarya sashinta, sarki fu'ad da kansa ya riƙe hannun gimbiya Hoor zuwa ga Angon ta, ya damƙa mi shi amanar ƴar uwar sa. san nan ya kalli gefen da Aneesa ta ke zaune ya yi ma ta alamar ta zo su wuce. Cikin kuka gimbiya Hoor ta rungume ɗan uwan ta, ta na kuka mai tsuma zuciyar ma abota shaƙuwa, daƙyar aka ɓanɓare ta daga wajen sa, san nan ta dawo gefen  Aneesa ta riƙeta, ta ce atafau...sai Aneesa ta kwana,  cikin dabara sarki fu'ad ya karɓi Aneesa su ka kama hanya, sai masarautar farisa...
Bayan sati ɗaya, sarauniya ta tambayi Aneesa school ɗin da ta ke so, ta ce ma ta PRINCESS NORA BINT ABDUL RAHMAN UNIVERSITY ta ke son  zuwa, wadda ta ke cikin garin RIYADH Saudi Arabia.
Haka kuwa aka yi, kafin ka ce kwabo, sarauniya ta samar ma ta admission a school ɗin, Aneesa ta fara zuwa.
A ɓangaren  sarki fu'ad, ya ri ga ya gama tattaunawa da  sarauniya akan mission ɗin sa da ya ke son aikatawa, ta kuma ba shi goyon baya, akan cika burin sa.
Wannan kenan...
                 ************
****************   ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤               ************
****************                   ************
                    WAIWAYE
Tun lokacin da su kawu Bala su ka yarda Aneesa a jeji,, sun so su kashe Aneesa, amma ɗaya daga cikin ɓarayin da su ka ɗauko, ya ce wlh ba su isa su kashe ta ba, sabo da mutum biyu su ka ce, za su kashe da bindigogin su, haka dai kawu Tukur ya yi shiru, amma ba dan ya so ba su ka wuce .Gudun kar asirin su ya tonu, ba su zame ko ina ba, sai wani ƙauye da ke ku sa da RUMA,  anan su ka  kutsa cikin jejin ba su damu da duhun dare ba, su dai kawai buƙatar su ta biya, shikenan. kafin su isa wajen bokan sai da su ka cire kayan jikin su tsaf,  su ka tsaya zindir haihuwar uwar su, sabo da biyan buƙatar duniya(wa iya zubillah) su ka dinga yi mishi kirari, sai ga boka ya bayyana agare su, wani tsummirerren tsoho ne ba bu kyan gani, sai wari da ke tashi daga jikin sa,  nan ta ke su kawu Tukur su ka faɗi buƙatar su, na son a haukata mu su Aneesa, kuma a rufe bakin duk wani wanda zai kawo mu su cikas a cikin lamarin su. Wata muguwar dariya  boka  ya yi, sai can ya gimtse  dariyar sa  wanda nan ta ke muninsa ya bayyana, san nan ya daka mu su tsawa, sai da  kawu Bala ya saki fitsari, dariya boka tsimmirerre ya sa ke yi, ganin kawu Bala ya saki fitsari,  "za a samu nasara, amma za ku kawo min yankakkun jariran  sauro guda talatin, da koren  bunsuru mai ƙaho biyar,   idan ku ka kawo waɗannan to aikin ku zai yi kyau"
"A ta re su ka haɗa baki wajen cewa, boka tsimmirerre a ina za mu samo waɗannan abubuwan da ka lissafa? sai dai ko idan za mu biya sai ka ba aljanun ka su samo ma na"
wata ƙwarya boka ya miƙo mu su ta re da  buga mu su tsawa, to maza ku zazzage duk abun da ke cikin aljihun ku" jiki na rawa su ka zazzage du ka kuɗin su ba ta re da sun san adadin su ba. san nan ya sake buga mu su tsawa, "ku tashi kuban waje la'anannu"
Da sauri su ka tashi, su na tafiya da baya da baya har zuwa inda su ka aje kayan su, su saka su ka tafi...
Yau Barhim estate rikice ta ke, sakamakon harin da aka kai gidan Alh. Abdul'aziz mai noma,  jami'an tsaro ne birjik tun daga farkon estate ɗin har cikin gidan margayin, su na bincike akan gawarwakin mamatan, ya yin da ɓangare ɗaya ƴan jarida ne ta re da ma aikatan gidan talabijin, ko wanen su ya na son ɗauko rahoto, domin yaɗawa ga al'umma...
Aunty nafisa ce, ta shigo parlon ta kasancewar yau ranar asabar ce ba bu aiki, lauya ce mai zaman kan ta,cikin tashin hankali mai gidan ta ya shigo cikin parlon kamar an jefo shi, "Alh lafiya? me ya faru?! " yanzun nan abokanan aiki na su ka  kira ni  wai banga abun da ke faruwa a  Tv ba, ba ri na kunna ingani, ban san mai ya sa jikina ke ba ni, ba alkhairi b...bai kai aya  a zancen sa ba, ya ji sallallamin matar sa, wadda aka kira yanzu a waya...sai kuma aka yi daidai da an hasko gawarwakin su Alh Abdul'aziz ta re da matar shi Haj. Halima...
Suman tsaye Aunty nafisa ta yi, ganin gawar ƴar uwar  ta ɗaya tilo ta re da mijin ta, ba bu rai a ta re da su...
KU BA RI NA ƊAUKO BIRO NA DA YA FAƊI A ƘASA😜
INA YI WA DUK KAN MASOYANA BARKA DA JUMA'A, DA FATAR ANYI JUMA'A LAFIYA?💎
KAR KU MANTA ƘOFA TA A BUƊE TA KE DOMIN BA DA GUDUNMUWA KO SHAWARWARI👇
08144066758 KO KU TUNTUƁE NI AKAN LAYIN WHATSAPP 👇
      08162058867
KU DAI KU CI GABA DA SUBURBUƊAMIN
***COMMENT***
***SHARE***
***VOTE***
***LIKE***
ZA KU IYA SAMUN WANNAN LITTAFIN A #WATTPAD#
KO KUMA KU ZIYAR CI SHAFIN
(AREWA BOOKS)
GA DUK WAƊAN DA BA SU KARANTA
(ASHE BA SO BA NE) MA ZA KU GARZAYA www.dlhausanovels.com.ng  
TA KU HAR KULLUM, MAI SON FARIN CIKIN KU....
💖ƴar mutan Argungu``` 💖

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
**Zumunta ko mugunta on typing...✍️
                   NA
Fatima Zara Alhassan ❤️
                (ƴar mutan Argungu)
ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚
GARGADI!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️
K/wata/27/11/2022
FREE  BOOK📚
SHAFI NA 20
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
******************************************************* suman tsaye Aunty nafisa ta yi, ganin gawar ƴar uwarta ɗaya tilo ta re  da mijin ta, ba bu rai a ta re da su...
Da sauri Alh Bashir ya zaunar da ita, ganin ba bu abun da ke motsi a jikin ta, sabo da tashin hankali, ruwa ya ɗebo ya shafa ma ta a fuskar ta har sau uku, san nan ta sauke a jiyar zuciya, ta re da fashewa da kuka, ta na mai jijjiga mijin ta... " Alh dan Allah ka ce min ba gaskiya ba ne, abun da na gani,  cikin kuka mai tsuma zuciyar ma abota saurare."
shi ma cikin jarumta ya ke ba ta haƙuri " Nafisa dan Allah ki yi haƙuri, wlh ba bu wanda  zai wuce lokacin sa, mu ma idan lokaci ya yi dole mu tafi, ko muna so ko ba mu so" shi ma bai san lokacin da hawaye su ka zubo mi shi ba, sabo da sanin shaƙuwar da ke tsakanin yaya Halima da nafisa, kuma ita ce uwarta da ubanta, tun da iyayen su, sun  rasu, ɓangare ɗaya kuma ga Alh Abdul'aziz wanda kowa  ya san shi a cikin jahar katsina, samun mutumin kirki irin Alh Abdul wallahi sai an tona.kukan nafisa ne ya katse shi...har ta ɗauki makullin mota za ta fita, ya yi saurin riƙe ta, su ka fita ta re, har ya ta da mota, komai ya tuna? sai ya yi sauri ya koma cikin gida,bai yi minti ɗaya ba, ya fito su ka wuce BARHIN ESTATE
unguwar cike ta ke da mutane, haka su ka kutsa motar su har bakin gate ɗin gidan. Bai ko ida tsayar da motar ba, Aunty nafisa ta fito da gudu, za ta shiga cikin gidan, amma jami'an tsaro su ka ce ba za ta shi ga ba, isowar Alh Bashir wajen ya miƙa mu su ID card ɗin matar sa, mai nuna cewa ita ɗin babbar lauya ce a babbar kotun katsina, shima ya miƙa na shi ID ɗin a matsayin shi na ɗan kasuwa...
Ba ta re da ɓata lokaci ba, aka ce su shiga ciki. ko da su ka shiga har an lulluɓe gawarwakin da farin ƙyalle, ga kuma su kawu Tukur zazzaune da doguwar carbin su, su na ja su na kuka, se ka rantse da Allah ka ce kukan gaske ne, mijin Aunty ya isa wajen su ya yi mu su gaisuwa, ya na kuma ba su haƙuri, ganin yadda su ke yin kukan haiƙan...
ɗaya daga cikin jami'an tsaro ne ya zo wajen su Aunty ya na yi mu su bayani akan cewa " ɓaraya sun tafi da  Aneesa, ana su binciken da su ka yi, amma su kwantar da hankalin su, insha Allah za su yi ƙoƙari su ga cewa sun kuɓutar da ita"
Haka dai wuri ya kacame da koke-koke ba bu mai lallashin wani... Aka yi wa mamatan sallah aka kai su makwancin su.
Bayan sadakar kwana uku,  su kawu Bala su ka bi jiro da maganar rabon gado. Aunty nafisa ta ce sam ba za a raba gado ba sai an gano Aneesa, haka dai su ka yi kaca-kaca kowa ya watse. Tun daga lokacin kuma, ba bu wanda ya sa ke maganar Aneesa, ballan ta na a je maganar rabon gado,har ta ƴan sanda ba bu wanda ya sa ke komawa kan batun, ita kan ta Aunty nafisa, an mantar da ita batun gaba ɗaya, haka ta zubar da zancen komai ta kama aikin ta.Amma duk ranar da ta wuce ta  gaban  Aneesa ENTERPRISES, sai ta ji gabanta ya faɗi, ta na son tuna a ina tasan sunan, haka dai za ta wuni ranar, ta  ra sa abin da ke yi ma ta daɗi...
Su kawu Tukur da Bala kuwa duniya sabuwa ta ke a wajen su, domin yanzu su ke riƙe da kamfanin sarrafa AYA, wato  MAI NOMA ENTERPRISES  da kuma na Auduga, ANEESA ENTERPRISES
sai wasu gonaki da su ka sayar, su na sharholiya...
******************************************
CI GABAN LABARI            
*******A daidai bakin kamfanin  MAI NOMA ENTERPRISES,  wata haɗaɗɗiyar mota  ta faka ƙirar  BMW fara, hankalin jama'ar da ke wajen duk sun koma kallo su ga wanda zai fito daga cikin motar.
Buɗe  ƙofar  aka yi a hankali, san nan wanda ke ciki ya fito ya rufe ƙofar. A hankali ta ke tafiya kamar ba tason ta ka ƙasa, kai tsaye ta shiga cikin kamfanin, ya yin da ma'aikatan ke kallon ta su na mamakin wannan al'amari, wasu kuma na   farin cikin ganin wadda ke gaban su...
Fitowar Kawu Tukur kenan daga office ɗin sa, ya yi mugun gani, cikin sauri ya ke tafiya domin ƙara tabbatarwa kan sa, gaskiyar abin da ya ke gani a gaban sa.
Da hanzari ya ke tafiya, jikin shi na makarkata, ya zo daidai ku sa  da ita, aka yi rashin sa'a ya take ƙasar babbar rigar sa, ya tafi luuu... zai faɗi a ƙasa, cikin zafin nama a ka riƙe shi kafin ya kai ga faɗuwa.
Ɗagowar da zai yi, su ka ido biyu, sai kawai ka ji fatatatattt...ya sa ki zawo
****************   ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤               ************
****************                   ************
HMMM MASOYAN ZUMUNTA KO MUGUNTA INA FATAR KUN SAN KO WACE CE??😃                   
KAR KU MANTA ƘOFA TA A BUƊE TA KE DOMIN BA DA GUDUNMUWA KO SHAWARWARI👇
08144066758 KO KU TUNTUƁE NI AKAN LAYIN WHATSAPP 👇
       08162058867
KU DAI KU CI GABA DA SUBURBUƊAMIN
***COMMENT***
***SHARE***
***VOTE***
***LIKE***
ZA KU IYA SAMUN WANNAN LITTAFIN A #WATTPAD#
KO KUMA KU ZIYAR CI SHAFIN
(AREWA BOOKS)
GA DUK WAƊAN DA BA SU KARANTA
(ASHE BA SO BA NE) MA ZA KU GARZAYA www.dlhausanovels.com.ng  
TA KU HAR KULLUM, MAI SON FARIN CIKIN KU....
💖ƴar mutan Argungu``` 💖

````ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
**Zumunta ko mugunta on typing...✍️
                   NA
Fatima Zara Alhassan ❤️
                (ƴar mutan Argungu)
ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚
GARGADI!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️
K/wata/17/12/2022
FREE  BOOK📚
SHAFI NA 21
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
******************************************************* 
Ɗagowar da zai yi, su ka ido biyu, sai kawai ka ji fatatatattt...ya sa ki zawo
A gefe ɗaya kuma, ma'aikatan kamfani ne tsaye su na kallon ikon Allah.
Ka ma hannun sa Aneesa ta yi san nan ta ce "kawu sannu,  zo mu je ka zauna.
ganin yadda ma'aikatan  ke kallon su, shiyasa ita ma ta zuba mu su idanuwan ta, kafin ka ce kwabo kowa ya ka ma gaban sa.
Bayan ta kai kawu Tukur  office ɗin sa, ta ce ya shiga toilet ya gyara kan sa.

Cikim firgici da bin umarnin ta, ya  shiga toilet ya gyara jikin sa ya fito
Amma har yanzu mamakin ganin Aneesa bai sake shi ba.
Shin gaskiya ne ko mafarki?  Aneesa  ce yau a gaban shi,  ya aka yi ba ta mutu ba?  bayan boka ya ce ba za ta taɓa dawowa ba! Shine kuma yau ta dawo har ta ke  ba shi umarni? kai wallahi wannan mafarki ne
Murmushi ta yi ganin yadda kawu Tukur ya rikita kan sa
"kawu ina wuni ya bayan rabuwa?"
Cikin rawar jiki da munafurci kawu ya fara kuka..." Aneesa ɗiya ta ina ki ka shiga  mu na ta neman ki ba mu gan ki ba?
Ba bu inda ba mu duba ba, amma ba mu gan ki ba, har gidajen talabijin da rediyo ba bu inda ba mu kai cigiyar ki ba, amma shiru kamar an aika bawa garin su...
Mun shiga tashin hankali sosai  ni da Adamu, a lokacin da mu ka ga gawar ɗan uwan mu shi da matar shi kwance a cikin jini ba bu rai a ta re da su,  gefe ɗaya kuma ga ɓatan ki!"
"Allah sarki kawu,  ita rayuwa da ma haka ta ke, na kuma gode da kulawar ku, kuma insha Allahu yanzu na dawo cikin ku ba bu inda zan tafi.
Kuma a shirye na ke naga na ƙwato  haƙƙi na, kuma ba zan ya fewa duk wanda ke da hannu wajen kisan iyaye na ba!
Da sauri kawu ya ɗago kan sa ya na kallon Aneesa jin abun da ke fitowa daga bakin ta. To yanzu idan tasan su ne su ka kashe ma ta iyayen ta ya za ta yi?
Kai ba zan taɓa ba ri ta sa ni ba.
Ya na son ya yi magana da ita, amma sai ya ga ta cika mi shi office sabo da kwarjini
maganar ta ce ta katse mi shi tunanin da ya ke yi
"Ni kuwa kawu, ya aka yi ban ga kawu Adamu ba? Ko ba ya nan ne?"
Cikin in,in,niya   kawu ya ce "ya na nan ba ri na kira mi ki shi."
Ya ce hakane sabo da ya samu hanyar guduwa.
Da ƙarfi ya turo ƙofar office ɗin kawu Adamu, kamar wanda aka tunkuɗo daga waje
A fusace kawu Adamu ya ɗago dan ganin wane ɗan rainin hankali ne ya shigo mi shi office a firgice haka!!
Ganin kawu Tukur ya yi tsaye a can gefe ya na mai da numfashi
Cike da mamaki ya ke  kallon kawu Tukur wan  da ya haɗa uban zufa, sai faman zare idanuwa ya ke yi kamar wanda ya yi wa sarki ƙarya
"Kawu lafiya? me ya same ka haka ka ke ta haɗa zufa?"
"Adamu wallahi fatalwa na gani, ko kuma ince ma ka na yi gamo, wallahi yan zun nan na ga aljana da idona Adamu!!!"
"Bushewa da dariya  kawu Adamu ya yi, har ya na duƙewa a ƙasa. Haba yaya, wane irin gamo kuma ana zaune ƙalau? 
yanzu dai zauna mu yi magana. Ta re da bushewa da wata dariyar...
Cikin fushi kawu Tukur ya ce wane irin zama kuma Adamu? ina yi ma ka maganar na yi gamo, amma ka ke ɗaukar magana ta kamar wasar yara! Shi ne har da yi min dariya! wato ga mahaukaci sabon kamu ko?
Sallamar Aneesa ce ta katse maganar kawu Tukur...
Tashin hankali wanda ba a sa mi shi rana!
A firgice kawu Adamu ya ke cewa," innahu sulaimanu wainnahu bismillahir rahmanir rahim!! lallai yaya da gaskiyar ka nima fatalwar ta fito min, dan Allah ki yi haƙuri wallahi ba da ni aka kashe iyay...
Wani mazga kawu Tukur ya kaiwa bakin kawu Adamu, sabo da kar ya fallasa asirin su.
A tunanin  kawu Adamu fatalwa ce ta mazge shi,  nan ta ke ya zube ƙasa  ya na kuka, ya na dan Allah ta yi haƙuri
Cikin takaicin abun da ɗan uwan na shi ke yi, shiyasa kawu Tukur ya sa ke dunƙule hannu da niyyar ya kai wa Adamu naushi,
Aneesa ta ta re.
         "A'a kawu wanda ka yi mishi ya isa, dan Allah ka yi haƙuri"
Haka dai Aneesa ta yi mu su bayani, su bar tsoron ta ita ba fatalwa ba ce
Amma duk da haka  ba su saki jikin su ba.
Haka dai su ka yanke shawarar Aneesa za ta koma gidan kawu Tukur da zama.
Bayan kwana biyu, Aneesa ta bijiro da maganar ta na son a buɗe case ɗin mutuwar iyayen ta.
Ba bu yadda su kawu ba su yi ba, akan tabar maganar sabo da ko an buɗe case ɗin ba ta da wani shaidu da za ta bai wa kotu,  amma ta ce a tafau sai anbuɗe.
Su kawu ne zaune shi da Adamu, su na tattaunawa akan yadda za su ɓullowa lamarin Aneesa.
"Adamu mai zai hana  mu kashe Aneesa har lahira, yadda za mu ci gaba da cin duniyar mu da sinke, ba ta re da kowa ya zarge mu ba.
Sabo da wallahi idan ba haka mu ka yi ba, to ina mai tabbatar ma ka yarinyar nan za ta ɓallo ma na ruwan dafa mu.
Ka duba ka ga yadda ta ke kallon mu, ba bu tsoro ko shakkun komai a ta re da ita, kai tsaye ta ke gaya ma na magana, wanda kai kan ka kasan da can ba haka ta ke ba."
"Yaya  wallahi ni kam tsoron yarinyar nan na ke ji, da zarar ta kalleni sai na ji jikina kamar wanda aka tsoma cikin firiza( freezer)  wani tashin hankalin ma, sai ka kalli cikin idanuwan ta.
Gaskiya yaya kar mu kashe ta, tunda mun so kashe ta a karon farko ba ta mutu ba, kawai yanzu mu barta ta yi rayuwar ta,
Sabo da duk yadda za ta yi, ai ba za ta taɓa gane cewa mu muka kashe ma ta iyaye ba.
          Yaya kawai mubar ta, ta shigar da ƙarar idan ta ga ba bu wani shaidu, ai dole ta haƙura. Amma ya ka gani?"
"shiyasa aka ce yaro, yarone wallahi. Kar ka manta fa, ta re da kai mu ka yadda yarinyar nan a daji, yanzu kawai rana tsaka ta dawo ma na, ba ta re da tayi mana cikakken bayani ba, kuma kai kan ka kasan boka tsimmirarre ya tabbatar ma na zai haukata ta,  amma kawai sai mu ka ga yarinya ta dawo, kuma cikin shiga ta kamala, ka dubi dalleliyar motar da ta zo da ita. Sabo da haka dole  mu sa ka ma ta ido sosai akan duk wani shige da fic ce da za tayi, in har ba ta shiryawa wannan case ɗin ba, wallahi ba za ta ce a ta da shi ba. Amma ka yi tunani da kyau..

****************   ❤❤❤❤❤❤❤❤
❤❤❤❤❤❤               ************
**************                   ************
Cikin shirin zuwa gona, malam kabiru ya fito, daga cikin  ɗakin sa, ya tsaya a baranda  ya na ƙwala kiran Murja..murja..
Na'am malam ga ni nan zuwa...
"wai dan Allah har yanzu ɗumamen bai samu ba ne? ban son rana ta yi ma na a gida."
Cikin ladabi inna murja ta aje kwanon samira a gaban  mai gidan ta, ta na cewa
" malam ayi haƙuri kasan yanayin itacen ba sa wani ci,  ga shi kuma anyi mu su ruwan sama, da ƙyar na samu wutar ta kama.   Ta re da miƙewa ta ɗebo ruwa cikin kwanon sha, ta aje a gaban shi.
Godiya ya yi ma ta, san nan ya ce ta ɗauko mishi tabarma zai je waje su ci shi da baƙon sa.
Miƙewa inna murja ta yi,  ta je ta ɗauko mishi. Karɓa ya yi, ya je ya shimfiɗa a cikin soron gidan. San nan ya fita ƙofar gida, akwai ƙaramin ɗaki a wajen, nan ya nufa ya na ƙwanƙwasawa.
Wani dattijo ne ya fito daga cikin ɗakin, ɗauke da murmushi akan fuskar sa, wanda idan ka kalle shi da kyau kasan cewa damuwa ce ta tsofar da shi da wuri haka,
ya miƙawa malam kabiru hannu su ka yi musabaha.
Bayan sun gaisa, malam kabiru ya yi mishi bismillah su je su ci abinci.
Wannan al'adar malam kabiru ne, kullum safiyar Allah, haka zai ɗauko mu su karin kumallo ya zo su ci ta re  da baƙon sa.
Duk wanda ya ga yadda su ke gudanar da rayuwar su, zai ga shaƙuwa sosai a tsakanin su...
Bayan sun gama karin kumallo su

Please Login or Register in order to submit comment