Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daɗi sosai....
cikin saa'a( 1 hour) sai ga su a bakin masarautar su fu'ad.  Masarauta ce mai girman gaske, daga shigowar ka cikin masarautar za ka fara jin kiɗan algaitu ma su sauti mabambanta.
A hankali ya saukar da ni daga kan bayan sa, nan ta ke kuma ya rikiɗe zuwa fu"ad ɗin da na sa ni, haka mu ke ratsa wurare ma su ban sha'awa da ɗaukar ido, ka na ƙara shiga cikin masarautar ta na kuma ƙara yi ma ka kyau.  wata hanya ce yarima fu'ad ya bi da ni, sai  da numfashi na ya tsaya na wa su  daƙiƙu,wuri ne wanda tun da na ke a duniya ban taɓa mafarki ko jin labarin wuri mai kyau da  ban sha'awar sa ba, ga furanni ma su ƙamshi  launika iri-iri, ƙorama ta na kaiwa ta na kawowa gwanin ban sha'awa, ga ƴaƴan itatuwa nan iri- iri,ga tsuntsaye nan su na waƙoƙi da mabambantan sautuka ma su natsar da zuciyar mai sauraro. kai a taƙaice dai irin wannan wuri alƙalami na ya yi kaɗan wajen rubuta mu ku irin tsaruwar wajen...Wani irin taku ya ke yi irin na ƴaƴan sarakuna, duk inda mu ka ratsa Bayi ne ta ko ina birjik su na kawo mi shi gaisuwa, haka ya ke ɗaga mu su hannu ya na wucewa,. Isarmu kofar palace ɗin ke da wuya, sarauniya Ayra ta re da gimbiya Hoor, su ka rungume shi, su na yi mi shi lale marhabin da sarkin farisa...
San nan su ka da wo kaina su ka rungume ni su na cewa " barka da zuwa masarautar farisa, mu na farin ciki da  zuwan ki"  Jarumta na aro, san nan na ƙawa ta fuska ta da murmushi, na ce "nagode"  hannu na su ka riƙe mu ka shiga cikin gida.
Haukar da na yi a waje a she bakomai ba ce, wani irin parlor ne mu ka shiga wanda zan iya cewa duk faɗin nigeria ba za asamu parlor mai girma da faɗi, uwa uba akai ga kayan more rayuwar da ke cikin sa ba, gaskiya ba za a samu ba.A hankali sarauniya Ayra ta zaunar da ni a ɗaya daga cikin kujerun diningtable ɗin da ke wurin wanda aka cika shi da kayan abinci nau'i daban-daban, wannan shi ake kira in ba ka ci ba ni waje...
Gimbiya Hoor ta zubamin abin da ta ga kamar shi zan iya cinsa, ta aje mini a ga ba na, ta re da sakar min murmushi, wanda na lura yin murmushin kamar a jinin su ne, da fa kafaɗa ta tayi ta na mai cewa "sister bismillah"  nima murmushin na sakar ma ta ina mai cewa " nagode"
Bayan mun gama cin abinci, aka kaini ɗakin da zan zauna, uhum ba a cewa komai ( idan na ce zan zaiyano mu ku haɗuwar ɗakin,  wa su sai su ce na yi ƙarya, shiyasa zan bar ku da kan ku, ku ƙiyasta kyansa).
Ina gama wanka na rama sallolin da ake bi na, san nan nayi azkar,ina mai ƙara jinjina hukuncin ubangiji, wallahi har yanzu ganin na ke yi kamar mafarki ne, har yanzu na ka sa yarda abun da ke faruwa gaske ne. Da wannan tunanin ne barci ɓarawo ya yi gaba da ni...
Kiran sallar magrib ya sa ka Aneesa miƙewa daga kwancen da ta ke, ta nufi banɗaki (toilet) domin ɗauro alwala.Ba ta tashi akan daddumar ba har sai da aka kira sallar isha'i, ta miƙe domin gabatar da sallah. Sallemewar ta ke da wuya, ta ji an turo ƙofar ɗakin a hankali, gimbiya Hoor ce ta shigo ta re da mai da marfin ƙofar ta rufe, da sallama ɗauke a bakin ta. Miƙewa Aneesa ta yi ta na naɗe dardumar sallan, murmushi ta sakawar gimbiya Hoor ta re da cewa "ina wuni gimbiya," " lafiyalau Aneesa ya baƙunci?"
Murmushi kawai Aneesa ta yi, san nan gimbiya Hoor ta ce " Sarauniya ta ce ki zo ki ci abinci ke kaɗai ake jira...
Kai tsaye su ka nufi ƙayataccen diningtable, a zaune su ka iske sarauniya ta re da yarima fu'ad, da alamu su kaɗai ake jiran isowar ta su...
Cikin ladabi Aneesa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe su, amsa ma ta su ka yi san nan , sarauniya ta ce ta tashi ta hau kujera su ci abinci. Bayan sun fa ra cin abincin ba ka ji sautin komai, kowa ya mai da hankalin sa wajen ƙoƙarin ba wa cikin sa haƙƙin sa. Sarauniya ce ta fa ra miƙewa, ta re da kallon ɓangaren yarima fu'ad san nan ta ce " yarima idan ku ka gama cin abinci ina son yin magana da ku, ku sa me ni a ɓangare na." San nan ta wuce ba ta re da jiran amsar su ba.
Wu cewar sarauniya ba da jimawa ba, su ma su ka kammala, san nan su ka nufi ɓangare ta...
Wani babban parlor Aneesa ta ga sun shigo, a jiyar zuciya ta sauke a lokacin da ƙafar ta, ta lotse cikin wani lallausan kafet(carpet) lokaci ɗaya kuma wani ƙamshi ya bugi hancin ta, mai sanyayyen daɗi, ( sandal nur kenan,   turaran wuta ne amma kamar na feshi, ya na sanya kwanciyar hankali a cikin gida. Ma za ku garzaya Hway incense🌹 domin ɗauko rabon ku, ana sayar da ɗaiɗai ko sari. )
zama su ka yi akan lutsa-lutsan kujeru.
San nan sarauniya ta fa ra da cewa...
HAR WA YAU DAI KAR KU GA JI DA NI, WAJEN YI MIN 👇
               **comment**. &     **share**
ZA KU IYA SAMUN LITTAFI NA #Wattpad#
SAI NA JI KU❤
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLS
      👇
08144066758
TA KU HAR KULLUM📚
❤ƳAR MUTAN ARGUNGU``` ❤

```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
Zumunta ko mugunta on typing...✍️
                   NA
Fatima Zara Alhassan ❤️
        (ƴar mutan Argungu)
ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚
GARGADI!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️
K/wata/29/10/2022
FREE  BOOK📚
SHAFI NA 17
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
******************************************************* Bayan sun zazzauna , sarauniya ta fara magana kamar haka... "Aneesa zo nan ki zauna, sabo da inji daɗin warware mi ki bakin jakar da na ɗaure,  sabo da na san zuciyar  ki cike ta ke  da tambayoyi maƙil, ta re da ƙawa ta fuskar ta da murmushi..."
Murmushi Fu'ad ya yi, san nan ya ce "Aneesa yanzu kam ke ga ba kashe ki zan yi ba ko? Ta re da yi ma ta dariya...
Kunya ta ji ta sunkuyar da kan ta ƙasa, ta na wasa da yatsun hannun ta. San nan ya kwashe duk abun da ya faru tsakanin sa da Aneesa ya faɗa mu su...

Ta'aziya su ka yi ma ta, san nan sarauniya ta ce, " Aneesa nasan za ki yi mamaki ta yadda aka yi mu ka san ku ko?  Amma wannan ba abun mamaki ba ne, du ba da cewa kowa ne Bawa da tashi ƙaddara, duk wanda ka ga ya shigo rayuwar ka,  toh akwai dalilin sa na shigowa ciki,  sabo da haka duk rintsi kar ka wulaƙanta kowa,  ba kasan manufar ubangiji na yin hakan ba. Aneesa na ji daɗi akan yadda iyayen ki, su ka kuɓutar min da ƴata gimbiya Hoor, ba ta re da sun san ko wacece ba, Allah ya ƙaddara Hoor ta na da rabon sa ke shaƙar iskan duniya, hakan ya sa ubangiji ya kaɗo mahaifinki wajen kuɓutar da ɗiyar sa, ta re kuma da tawa ɗiyar. A wancan lokacin watannin ki bakwai zuwa takwas aduniya, amma ki na zuwa ko ina, hakan ne ya sa ki ka shaƙu da ZOMOn da ke cikin gonar mahaifinki,. Akwai wata rana, kun tafi gona, ki ka fita cikin farfajiyar wurin, ki na wasa ta re da zomon ki, sai ga maciji ya zo zai sareku, idanuwan iyayen ki ya kai wajen, nan ta ke mahaifinki ya yi bismillah ya kwaɗeshi akai,  amma aka nemi shi aka rasa. Toh ba maciji ba ne, Aljani ne, ya na kuma cikin manyan Dakarun sarauniya SAMEE . Bayan na kore ta daga cikin masarauta, shine ta haɗa ba ki da wasu Bayina da ke cikin masarauta aka sace gimbiya Hoor, sun so su kashe ta amma Allah bai ba su sa 'a ba,   ba yadda su ka iya, sabo da sun gano cewa akwai kafi sosai ajikin Hoor, hakan ya sa su ka jefar da ita, ta yi ƙoƙari ta ga ta koma gida amma abu ya ci tura,. A lokacin da ta shigo cikin gonar,  kamar za ta halaka sakamakon mai gadin gonar ba a banza ya ke zaune wurin ba, ganin haka ne yasa ta koma siffar zomo don ta samu ta zauna ƙalau ajejin. A lokacin ba bu inda ba mu duba ta ba, amma ba mu ganta ba, hakan ya sa mahaifina ya yi na sa bincike sosai, san nan ya gano ma na wajen da Hoor ta ke, ta re da gargaɗin mu da cewa mu yi sauri sabo da ta na cikin haɗari, amma kuma ya ga wani haske a ta re da ita.
A lokacin da mu ka isa, ni da yarima Fu'ad mun iske iyayen ki za subar gonar, sabo da tsorata da ganin macijin. Ga nin haka ne ya sa ba mu baiyana mu su ko mu suwaye ba, gudun kar su ƙara firgicewa, mu na nan wajen har su ka ɓace wa ganin mu, shiyasa kawai mu ka ɗauki  Hoor, mu  ka tafi,  ba ta re da munyi mu su godiya ba, shi kuma wancan Aljanin na sarauniya Samee, mahaifinki ya hallaka shi. Shiyasa idan za ka kashe ko wane irin ƙwaro, toh ka tabbatar ka kira sunan Allah,  toh a wannan lokacin duk MUGUNTAr dabba, ba zai yi tasiri a wajen ka ba insha Allah.
Bayan mun koma gida, na ƙudurta cewa, insha Allah nima wata rana zan ramawa ABDUL-AZIZ ABUBAKAR MAI NOMA alkhairin da ya yi min, duk da a wancan lokacin bai san ya taimake ni ba....
Wata rana kwatsam! sai na yi makarkin iyayenki, su na cikin mawuya cin hali. Bayan gari ya waye, Sarki Fu'ad ya zo gaishe ni, sabo da alokacin annaɗa shi sarkin farisa, ya iskeni cikin damuwa, cikin tashin hankali ya tambaye ni "Sarauniya me ke faruwa na gan ki cikin damuwa?"  A jiyar zuciya na sauke, san nan na faɗa mishi mafarkin da na yi, san nan na ce kuma ina son zuwa inga halin da ku ke ciki,  sabo da alkhairin su gareni..Cikin kwantar da hankali ya ce, shi zai tafi, ba sai na je ba, ba bu yadda ban yi da shi ba, akan ya ba ri ni na je, amma ya ce shi zai tafi...
Cikin saa'a ɗaya, ya isa najeriya, bayan ya sauka a gidan ku, ya iske wannan tashin hankalin, iyayenki kwance ba bu rai. Abun mamaki kuma bai ganki ba, ya duba ko ina a cikin gidan ba ki ciki, bai bar gidan ba ya ji maƙwabta sun shigo, ta re da jami'an tsaro. Anan ya bar su ya wuce...
Bayan ya zomin da labarin, tabbas abun bai yi min daɗi ba, shiyasa mu ka duƙufa wajen neman ki,  anan mahaifina ya sanar  da mu, dajin da ki ke, ta re da cewa anyi mi ki sihiri. A lokacin da  Sarauniya Ayra ta zo nan, a zancen ta, Aneesa kuka ta ke yi sosai, ta na tambayar kan ta wannan zumunta ce ko mugunta aka yi wa  iyaye na!!!???
Gimbiya Hoor ce ta jawo ta jikinta ta na rarrashi,  san nan su ka yiwa sarauniya sallama. Bayan tafiyar su Aneesa, parlon ya koma daga sarauniya sai sarki Fu'ad.  " Sarauniya dan Allah ki ba ni dama, in aiwatar da aikin da na fara?" Fu'ad ba ka da matsala, na ba ka dama ɗari bisa ɗari,  dama ance kyawun ɗan ƙwarai, ya gaji ubansa" na shaida cewa lallai ka gaji mahaifinka sarki Baqeer, wajen wanzar da adalci, ya kore MUGUNTA...
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA👇
08144066758
      DAN ALLAH KAR KU GAJI DA YIMIN
       ***COMMENT***
      ***SHARE***
       ***FOLLOW***
               and
      ***vote***
KU NA IYA SAMUN LITTAFI NA
#Wattpad#
       KO KUMA KU JE    #Arewa Books#
GA WAƊANDA BA SU KARANTA( ASHE BA SO  BA NE) toh kar ku damu, za ku iya samun shi a,  www.dlhausanovels.com
TA KU HAR KULLUM
******ƴar mutan Argungu```****





```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**
Zumunta ko mugunta on typing...✍️
                   NA
Fatima Zara Alhassan ❤️
                (ƴar mutan Argungu)
ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚
GARGADI!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️
K/wata/9/11/2022
FREE  BOOK📚
SHAFI NA 18
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
*******************************************************  "Na shaida cewa lallai ka gaji mahaifinka sarki Baqeer, wajen wanzar da adalci, ya kore MUGUNTA...
****************                 ************
****************   ❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤               ************
****************                   ************
  Murmushi Fu'ad ya yi, san nan ya ce "Sarauniya ya maganar karatun Aneesa?"
Ninfasawa sarauniya ta yi, kafin ta ce "kar ka damu, insha Allah za ta yi karatu har sai ta ce ya ishe ta, matuƙar ina raye, amma yanzu mu bar duk wani har kan  karatun ta har a gama bikin Hoor, san nan ta zaɓi duk makarantar da ta ke so. kai ma ina son ka aje duk wa su ƙudurorin ka har bayan bikin nan, san nan mu ga abun da ya kamata mu yi akai." Cikin girmamawa yarima fu'ad ya ce toh sarauniya, duk abun da ki ka ce shi za ayi. "
Har ya yi ma ta sallama ya miƙe zai tafi...
"Fu'ad ina kuma za  ka tafi, ba mu ga ma maganar shirye-shiryen bikin nan ba? ka fa san yau saura sati biyu,  kuma kasan ranar asabar mu na da shirin bikin al'ada."
"Haka ne sarauniya, da ma ina son sanar da ke cewa, Salman ya ɗauki nauyin duk wa su abubuwa da za a gudanar a ranar bikin  al'ada,  ya ce ita ce ta shi gudunmuwa..."
"Toh masha Allah! abu ya yi kyau, Allah ya yi albarka ya bar ZUMUNTAR ku har abada." "Amin ya Allah"
A haka dai su ka rufe shafin zancen su, yarima fu'ad ya yi gaba...
Salman abokin yarima fu'ad ne, makarantar su ɗaya, anan su ka haɗu da juna.
Salman ya na da barkwanci ga kuma ɗan banzan shiga rai, tun da ya ƙyalla ido ya ga fu'ad shikenan ya dinga binsa ya na son su zama abokai, tun fu'ad na ba sar da shi,  kasancewar sa marar son hayaniya, har ya  biyewa salman su ka zama abokanan juna. Salman asalin su ƴan Saudiyya ne, shima iyayen sa ƴan gidan sarauta ne,amma sam, mahaifinsa bai da mu da sarauta ba , shi ya sa ya faɗa har kar kasuwanci, wanda yanzu haka ya na cikin manyan ƴan kasuwar da ake damawa da su a duniyar aljanu. Wannan kenan...
"Haba Aneesa, ashe haka ki ke, ba ki jin lallashi?  tun ɗa zu ki na kan yin abu ɗaya, wa ya ce mi ki kuka na magani...shigowar sarauniya ne ya katsewa gimbiya Hoor zancen ta, yauwa sarauniya ga ra da ki ka zo, ta re da miƙewa su dukan su...A hankali sarauniya ta ƙaraso inda Aneesa ta ke tsaye ta shafa kan ta, san nan ta ce "wa ya taɓamin gimbiya Aneesa ta?  ta re da zaunar da ita a  gefen ta,  san nan ta ce "Aneesa har ga Allah na so ace kin zauna ta re damu har abada, duk da nasan ke ba jinsin mu ba ce, du ba ga yadda dangin mahaifin ki su ke azzalumai, ba su duba halaccin da mahaifin ki ya yi mu su ba,Aneesa ni ba zan tilasta mi ki cewa dole sai kin zauna da mu ba, zan iya mai da ke dangin mahaifiyar ki,sai dai kuma ina jiye mi ki shiga halin rayuwa, uwa uba,  ba lallai ne su ma su kula da ke yadda ya kamata ba, duniyar nan cike ta ke da mugayen mutane, tun daga jinsin mu har zuwa na ku, san nan ta ƙara riƙe hannun Aneesa ta  ce, ina son ki samu ilmi,  sabo da ki sa mu ɗan jagoran da zai dinga nu na mi ki hanya,  amma ba zan matsa mi ki ba,  zan ba ki lokaci ki yi tunani."
Cikin kuka Aneesa ke cewa " dan Allah sarauniya ki yi haƙuri idan na ɓata mi ki rai, wallahi ba da gangan na ke yin kukan nan ba, kukan na zuwa min ne, idan na tuna abin da ƴan uwan mahaifina su ka yi ma na, ba zan taɓa man ce karamcin ku a ga re ni ba, nagode akan hidimar da ku ke   yi mi ni, Allah kaɗai zai iya biyan ku, wani ɗaci ta ke ji ya na taso ma ta, sabo da baƙin cikin dangin mahaifin ta...
"Ajiyar zuciya sarauniya ta yi, san nan   ta ce, "ba bu godiya a tsakanin mu, ni na ɗauke ki tamkar ɗiya ta Hoor, kin ga da ma na ku sa korar Hoor sai mu yi zaman mu ta re da Autata."
Kun ya Aneesa ta ji, ta na ɓoye fuskar ta a jikin sarauniya. Hoor da ke zaune a gefe ta na kallon su, sai yanzu ta yi magana...
"Sarauniya ina fa zaune, amma ku ke haɗemin kai, ki na ce ma ta kora ta za ki yi fisabilillah, ta na maganar cikin shagwaɓa..."
Muryar fu'ad su ka ji ba ta re da ya tsaya buɗe ƙofa ba..."kar ki da mu Hoor, ni kam ina ta re da ke tun da sarauniya ta juya mi ki baya, ta re da ƙawata fuskar shi da murmushi"
Ita ma Hoor murmushi ta yi, "gaskiya ne yaya yarima, kuma fa sarauniya ta san cewa da tsohuwar zuma ake magani..."
Dariya sarauniya ta yi, kafin ta ce  " ku zo dai ba din halin ku ba, kar ku yi min kuka, har dai su 0'0 ban faɗi suna ba, ta na kallon gefen Hoor" dariya su ka yi su dukan su, san nan su ka isa wurin sarauniya su ka rungume ta su du ka...
Akwana a tashi a sarar mai rai. Ga shi har satin bikin gimbiya Hoor ya shigo. Sarauniya ce zaune ta re da Aneesa, ta na yi ma ta bayanin yadda su ke gudanar da bikin Al'adar su. san nan ta ƙara da cewa..."Aneesa kin ga gobe ne ranar bikin al'adar gimbiya Hoor, kuma gobe za ki haɗu da halittu nau'i daban-daban cikin masarautar nan, sabo da haka ina son ki natsu ki cire tsoro daga cikin ranki, ba bu abun da za su yi mi ki, ba ri in ba ki kaɗan daga cikin tarihin aljanu...
"Duniyar Aljanu  wata irin duniya ce wacce ta bamban ta sosai da ta ku duniyar. Ta wajen kamannin ta, da yanayin ta, da kuma abubuwan da ta ƙunsa. Allah ya halicci aljanu bisa  siffofi nau'i uku kamar yadda Manzon Allah (s.A.w) ya faɗa a cikin wani hadisi.
A cikin su akwai waɗanda su ke da jikin su shigen irin na ku, sai dai bambancin yanayin ƙirar jikin da kuma girman halittan. Akwai kuma waɗanda Allah ya halicce su ne a bisa siffar karnuka da macizai.(waɗan nan su ne waɗan da idan su na jikin mutum zai riƙa yawan mafarkin karnuka ko macizai, ko ƙadangaru, da sauran su).
Akwai kuma waɗan da su acikin dazuzzuka su ke yin rayuwar su, sai dai ba su zama waje guda.
Duk wannan labarin da na ke ba ki, sun samo asali ne daga Al'ƙur'ani  da Hadisan manzon Allah(S.A.W) kuma sahihan labaruka sun tabbatar da haka.
Acikin nau'i na  na biyu akwai ma su ido ɗaya RAK a tsakiyar kan su, akwai kuma waɗan da idanuwan su ya tsaga ne daga sama zuwa ƙasa.Akwai ma su bindi(jela)
da komai irin na halittar Birrai(monkey).
Wani kuma bakin sa ya fara ne tun daga jikin kunnen sa zuwa ɗayan kunnen. Wani kuma haƙora ne da shi kamar na Damisa ko zaki. Dariya ce ta kufcewa Aneesa jin  sarauniya ta ce bakin su kamar na zaki...
Dingure ma ta kai sarauniya ta yi, san nan ta ce "ina magana ki na dariya ko? Allah ya kaimu gobe ki sha mamaki, zan ga yadda za ki yi idan su ka zo wannan taron, ballan ta na ace ki ga ma su bakin kada(crocodile)."
Cikin tsoro Aneesa ke kallon sarauniya "yanzu duk waɗan nan halittun zan gan su gobe a wajen bikin gimbiya Hoor?!!"
"ƙwarai da gaske, ai shiyasa na zaunar da ke ina faɗa mi ki nau'o'in su don kar ki gan su ki rikice . kuma na tabbata duk kan su za su shigo wannan masarautar ,sabo da sarki fu'ad ya aika mu su da goron gaiyata."
A jiyar zuciya Aneesa ta yi, ta na mai ƙara jinjina girman ubangiji, ko akan waɗan nan halittun  dole imani ya ƙara shigar mutum....
Sarauniya ce ta katse ta daga zancen zucin da ta ke yi, ta hanyar cewa.....
HIMMM, MASOYA NA, GA FA ANEESA CIKIN ALJANU, KO ME KU KE GANIN ZAI FA RU IDAN ANEESA TA YI IDO BIYU DA WAƊAN NAN ALJANUN DA SARAUNIYA TA LISSAFO MA TA?
MASOYA NA, SHIN KO KUN TAƁA SANIN YADDA ALJANU SU KE GUDANAR DA BIKIN AL'ADAR SU?
AMMA KAR KU DAMU, KU BAR MI NI WUƘA DA NAMA A HANNU NA, DOMIN ZUWA ƊAUKO MU KU RAHOTO😜
KU DAI KU CI GABA DA SUBURBUƊAMIN
***COMMENT***
***SHARE***
***VOTE***
***LIKE***
ZA KU IYA SAMUN WANNAN LITTAFIN A #WATTPAD#
KO KUMA KU ZIYAR CI SHAFIN
(AREWA BOOKS)
GA DUK WAƊAN DA BA SU KARANTA
(ASHE BA SO BA NE) MA ZA KU GARZAYA www.dlhausanovels.com.ng  
KAR KU MAN TA, ƘOFA TA A BUƊE TA KE, DOMIN BA DA SHAWARWARI KO GUDUNMUWA👏
TA KU HAR KULLUM, MAI SON FARIN CIKIN KU....
💖ƴar mutan Argungu``` 💖
























```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
MARUBUCIYAR...✍️
**Ashe ba so ba ne
**Bayan wuya**

**Zumunta ko mugunta on typing...✍️
                   NA
Fatima Zara Alhassan ❤️
                (ƴar mutan Argungu)
ARGUNGU WRITER's ASSOCIATION...📚
GARGADI!
ƙagaggen labari ne. Ban yadda wani ko wata su juya shi,ba tare da izinina ba, akiyaye. Idan kuma ya zo dai-dai da rayuwar wa su, toh akasi ne!.
GODIYA
Ga mabiya littafai na, Allah ya barmu ta re,ya kuma ƙara danƙon zumunci 💙❤️
K/wata/18/11/2022
FREE  BOOK📚
SHAFI NA 19
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
******************************************************* Sarauniya ce ta katse ta daga zancen zucin da ta ke yi, ta hanyar cewa..."wa su kuma su na da yanayin halitta irin na Halittun cikin ruwa. Wa su kuma kamar halittun kan tudu su ke. wato su na da ƙofato, fukafukai, ƙaho, da sauran su. ( su ne waɗan da idan  sun shiga  jikin Ɗan Adam zai riƙa yawan mafarkin shanu su na binsa  a guje, ko kuma mafarkin faɗuwa daga tsauni mai nisa).
Allah ya hore mu su chanza  launi, ko siffar jikin su zuwa ga wata halittar daban.
Shiyasa akan sa mu waɗanda su ke riki ɗa su shigo  cikin Bil'Adama har a riƙa yin harkokin kasuwanci ko wata hulɗa da su, ba ta re da an gane su ba .
Musamman a lokacin aikin Hajji, da yawa daga cikin su, su kan zo su yi cuɗanya da Bil'Adama domin gudanar da ibadar su.(waɗannan muminai ne ba sa cutar da mutane).
Akwai kuma wawayen cikin su waɗanda su kan shigo duniyar  Bil'Adama domin gudanar da MUGUNTA da ayyukan saɓon Allah. kamar zina, sata, tsafi, har ka da bokaye da sauran su...
Amma abun da ke tsare duk kan wani Bil'Adama daga sharrin su shi ne ALƘUR'ANI mai girma. muddin  su na lazimtar yin azkar na safe, rana da yamma,toh duk MUGUNTAR  Aljani bai isa ya je  inda  su ke ba, da izinin Allah."
wani ƙaho sarauniya ta miƙawa Aneesa, san nan ta ce "ki riƙe shi da kyau Aneesa, zai yi miki amfani sosai a wasu lokutan, ni ma na gajeshi ne a wajen mahaifina, ya na da ɗumbin tarihi... amma sarauniya ni me zan yi da ƙaho? kuma na  tabbata ya na da matuƙar mahimmanci a wajen ki,  amma meyasa ki ka zaɓi ki bar min shi?"
Murmushi sarauniya ta yi, ta na mai fuskantar Aneesa..." Na ba ki shi ne sabo da abubuwa guda biyu, na ɗaya za ki iya komawa ko wace irin kalar halitta idan ki ka busashi, na biyu za ki iya zuwa duk inda ki ke so a faɗin duniyar nan, san nan ta sake kallon Aneesa ta ce, amma ki guji yin zalunci da mugunta a duk inda ki ke, kuma da zarar an gama bikin gimbiya Hoor zan sa ka ki makaranta, za ki zaɓi duk school ɗin da ta yi mi ki, ni kuma na

Please Login or Register in order to submit comment