Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai fiye da tunanin mai karatu...
lokacin damuna, haka ya kwashi ma aikata, su ka yi aiki sosai,  gona biyu ce d'aya ya shuka shinkafa d'aya kuma waken soya, kuma kowa ce gona ya na saran ya samu buhu saba'in ko sittin,in Allah ya yar da....
Allah sarki! rayuwa kenan," kana ta kanka,a lokacin kuma wani ta taka ya ke yi" toh hakan ce ta kasance ga Abdul, bayan amfanin gonar sa, sun isa cirewa, kwatsam sai ga wani babban al'amari ya faru....!
*****************************************
My dear Readers, wlh ku na raina a ko da yaushe, dan Allah ku yi hkr kwana2 ban yi muku post ba,hakan ya na da alaqa da rashin lfyr da na yi,amma in-sha Allah daga yanzu za ku dinga ji na akai-akai
❤️Y**A**R**MUTAN ARGUNGU``` ...✍️📚❤️




```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA?📚
marubuciyar...✍️
**Bayan wuya**
**Ashe ba so ba ne**
**Zumunta ko mugunta on typing...✍️
Writing by-Fatima Zara Alhassan ❤️ (Yar'mutan Argungu)
GARGADI!!!
Kagaggen labari ne. Sabo da haka ban yarda wani ko wata su yi amfani da kalma d'aya daga cikin wannan littafi ba, ba ta re da sanin marubuciyar littafin ba,haka kuma duka sunayen da ke ciki kagaggu ne. A KIYAYE!!!
GODIYA!
Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bisa iyawarsa da kuma yardar sa. Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna( ZUMUNTA KO MUGUNTA)lfy.
SADAUKARWA
ga yan'uwana, domin nuna mahimmancin ZUMUNTA, da kuma kaucewa rud'in zuciya domin kar ta kaimu ga yi wa yan'uwan mu MUGUNTA
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA PLS 08144066758 KO KUMA WHATSAPP NUMBER 08162058867
FREE PAGE
SHAFI NA 13
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
********************************************* Kwatsam! Sai ga wani Babban al'amari ya faru...
Tun jiya Abdul ya yi magana da ma aikatan da za su yi mishi aikin cirar amfanin gonakin sa. Yau tun da safe ma aikatan su ka iso kofar gidan su Abdul don tafiya gona,su ka yi sallama, Adamu ne ya fito ya na huhura hanci yadda kasan bututun mai haka ya ke  d'age hancin shi sama, "uban waye ya ke damun mu da sassafen nan?!!" Gaishe shi su ka yi, san nan su tsaya yi mi shi bayanin wurin wanda su ka zo nema, "oh kune ma aikatan wancan yaron koh?" a ta re su ka ce ehh ranka shi dade... Murmushi ya yi wanda ake cewa na ciki na ciki, san nan ya ce ku bari in kira mu ku shi..bayan ya shiga cikin gida ya iske inna Atika a bakin murhu san nan ya ce "inna wai ina d'an banzan yaron nan ya ke ne..kafin ya kai karshe sai ga Abdul ya fito daga cikin d'akin sa ta re da shirin zuwa gona, a hankali ya tako har gaban inna Atika ya duka " inna ina kwana" kallon shi ta yi shekeke tun daga  kai har kafa, san nan tace " da ban kwana ba za ka ganni, ka ga ka fita daga ido na in rufe!wlh da kasan yadda na tsani in bud'e idanuwana  in gan ka acikin gidan nan, na tabbata da ba za kazo ku sa da ni ba, sabo da kai kowa ya tsani ya'yana, duk wanda ya tashi Abdul kowa Abdul sai ka ce kai kad'ai ne yaro acikin garin nan...za ka tashi kaban wuri ko sai na shuka maka rashin mutunci a anan wurin!!!'
Cikin sanyi jiki ya tashi ya fita,yana mai kara jinjina kiyayyar da matar baban sa ta ke nuna mi shi,amma ya san duk wannan abun ba komai ba ne fac ce hassada...
Bayan ya wu ce,Adamu ya dubi mahaifiyar su, ya ce "inna, wallahi na tsani wannan shegen yaron, mune manya amma Abdul ya fimu masoya, wani lokacin kuma wallahi ya na ba ni tausayi...kai dallah tafi can sakaran banza wanda bai san ciwon kansa ba!!
tausayi, wallahi yanzu ya fara gani indai ni ce Atika, ba yana takama ya samu gonaki har yayi shuka ba? Toh yau zai je ya girbe shukar sa mai kyau, dan wallahi mud din ina cikin duniyar nan toh Abdul da shi da arziki sai alahira acan d'in ma dan ban da yadda zanyi ne da na yi wallahi!!! amma da ni ya ke wasa, zaman garin sai ya gagare sa, da kafarsa zai fece kuma ina zaune ka ce ni na fad'a ma ka!!" Shewa sukayi san nan su ka tafa(kunji wani zance na  inna Atika,sai ka ce a hannun ta kaddarar Abdul ta ke?  Amma muje zuwa duk zakaran da Allah ya nufa da caara...?)
******Bayan fitowar Abdul daga gida, su ka kama hanyar gona, isar su  ke da wuya
Abdul ya yi tozali da gonakin sa duk  sun k'one bakikirin,har ta kasar wurin za a sha fama kafin a iya sake  noma  awurin, ba bu abun da ya  fito  daga bakin shi sai kalmar. " Innalilllahi wa inna ilaihir raji'un×3
mamaki da al'ajabi su ka kama ma' aikatansa, sabo da ganin yadda gonar ta koma, wannan ko rantsuwa mutum ya yi ba zai yi kaffara ba, saka wutar aka yi... rike shi su ka yi ganin cewa ya yi suman tsaye. A haka su ka dauke shi sai gida...ko kafin ka ce kwabo! labari ya cika gari, wa su ma har kara gishiri su ke yi a labarin
Ma su yi mishi jaje na yi, suma yan'Allah kara na yin na su...
Wasa-wasa sai da zaman garin JADA ya gagare shi, haka ya tattara komatsen sa ya fice daga garin, bai zame ko ina ba sai tasha wajen shiga mota, shi kan shi a lokacin idan ka tambaye sa inda zai je bai sa ni ba, kwatsam! ya ji conductor na cewa "katsina...katsina, hakan ya samu kansa da cewa katsina zai tafi(wannan shi ne farkon zanen kaddarar Abdul).
Bayan motar su ta cika,san nan su ka kama hanya sai birnin katsinan dikko...
LITTAFIN ZUMUNTA KO MUGUNTA, YA NA IYA KASANCEWA NA KUDI, A KO WANE LOKACI KU ZAMA CIKIN SHIRI, AMMA IDAN NA GA RUWAN COMMENTS,KILA INA IYA CANZA RA'AYI BA SAI NA SAYAR BA📚
COMMENTS AND SHARE```
YAR'MUTAN ARGUNGU 📚❤️💙❤️
` ````````






















ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
marubuciyar...✍️
**bayan wuya**
**ashe ba so ba ne**
**zumunta ko mugunta? on typing...✍️
writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
❤️ARGUNGU WRITER'S ASSOCIATION ✍️
Gargadi!!!
kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free page ne, zai iya zama na kudi ako yaushe,  akiyaye!!!
Jinjina 👌
ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen❤️💙💚
Godiya:
ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode❤️
Ban manta da ke ba fatima iman Ibrahim ❤️
ta re da Abubakar Birnin tsaba👌
godiya ta musamman ga USMAN RIO👍
FREE PAGE📚
k/wata 3/10/2022
SHAFI NA 14
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
*********************************************************San nan su ka kama hanya sai birnin katsinan dikko...
Motar su ba ta tsaya a ko ina ba sai a Tashar NATO.  Bayan sun sauka driver ya sauke mu su kayan su, kowa ya kama gaban sa, amma ban da Abdul. Samun wuri ya yi anan cikin tashar ya na tunanin rayuwa, duk wanda ya ce mi shi rayuwa za ta sauya mi shi haka wallahi ba zai yadda ba,  amma ya san cewa dukkan tsanani ya na ta re da sauki, kukan yunwar da cikinsa ke yi ne ya dawo da shi daga duniyar tunani...Hannu ya sa ka acikin aljihun sa domin dauko sauran kudin da su ka rage mi shi, aka ce ya dauka in ya gansu ( watoh an sace kudin), kara dubawa yayi, da mamaki ya ke kallon kasan aljihun na sa, wanda aka yanke... murmushi ya yi wanda ya fi kuka ciwo, ya na aikin me hakan ta  faru?  zuciyar shi ce ta ba shi amsa "ka man ta mai son abun ka ya fi ka dubara?" Dogon numfashi ya ja...ya na mai jinjina al'amarin mutane, wato kowa kansa ya sa ni, ba bu wanda ya damu da halin da ka ke ciki. Tunawa ya yi kamar ya saka wa su canji acikin aljihun gaban rigar sa, ai kuwa ya na sa ka hannu sai ga wata tsohuwar d'ari biyu. Tun d'azu ya ke wannan tunanin ya kira ta ko kar ya kira? Sabo da rabon da su yi waya tun rasuwar mahaifiyar sa, a lokacin da ta kira shi ta yi mi shi ta'aziyya, sai kuma ya zo ya sayar  da wayar sa  sabo da bukatar yau da kullum...
Haka dai ya bi zabin zuciyar sa, ya ari wayar driver ya sayi  katin naira dari(100) ya saka aciki...
Zaune ta ke akan makeken gadon ta, kallo d'aya za kayi ma ta kasan cewa akwai damuwa a tattare da ita, amma ta na kokarin boyewa...Da Sallama sister  ta, ta shigo cikin d'akin san nan ta ce "yaya Lima mommy na kiran ki sabo da haka ta ke ce ma ta."  A hankali ta bi bayan sister  ta. A parlo su ka tarar da mommy zaune ta na kallon TV, zama su ka yi san nan Halima ta ce "Mommy gani"
"Halima ya kamata yanzu ace kin cire maganar Abdul'aziz ,acikin zuciyar ki, tun da ya zo gidan nan sau d'aya, har yanzu bai dawo ba, kullum sai kice ayi mi shi uzuri zai zo,Ha ba Halima! ya kamata ace yanzu ki yi wa kanki karatun ta natsu, ki fitar da miji cikin mane ma Auren ki, tun da ba ra sa su ki ka yi ba, toh magana dai ta karshe ita ce mahaifin ku ya ce in fada mi ki ya ba ki nan da wata daya,muddin ba ki tsayar da wanda ki ke so ba a cikin manemanki, toh wallahi za ki ga bacin ransa sosai! Sabo da haka ki cire wani Abdul daga ranki, ki rungumi   kaddarar ki hannu biyu, amma idan kuma har Allah ya sa Shi Abdul din mijin ki ne, toh za ki ga kafin wa'adin da aka d'ibar mi ki ya cika zai zo, sabo da matar mutum kabarin sa."
"Insha Allah mommy ta, zan kasance mai biyayya a ga re ku, amma dan Allah ki ta ya ni da addua kin ji mommy?"
"kar ki damu Halima kullum cikin yi muku addua mu ke yi, Allah ya yi mu ku zabi na alkhairi ke da yar' uwarki"
Amin mommy, su ka rungume ta a ta re...
Haka su ka zauna su na firar su ...karar wayar Halima ce ta cika parlon, tun d'azu ake kira amma ba ta dauka ba, kasan cewar number ce ba bu suna, "Halima ba ki ji ana kiran wayar ki ba ne? ki dauka ma na". mommy ba suna number ce , toh idan number ce shine ba za ki dauka ba? kubar yin hakanan!.  sa ke kira aka yi akaro na uku...Dauka tayi ta na jin muryar mai yi ma ta sallama, cikin kaduwar jiki ta furta Abdul! a bangaren Abdul kuwa murmushi ya yi san ya ce ma ta ya shigo katsina amma yanzu zai zo gidan su, cikin murna ta ce toh sai ka zo...
Bayan sun gama waya ta juyo ido biyu su ka yi da mommy, nan ta ke kunya ta kamata, murmushi mommy ta yi san nan ta ce addua ta, ta karbu kenan ta na dariya.
Bayan daddy ya dawo, mommy ta fada mi shi Abdul'aziz zai shigo zuwa anjima, ya yi farin ciki sosai, ya kuma yi  fatar Allah ya sanya alkhairi.
Da kyar Abdul ya samu mai mashin ya dauke shi akan naira d'ari zuwa Barhim estate.  Bayan ya isa gidan su Halima, da mamaki ta ke kallon shi, kamar ba Abdul dinta mai gayu ba, ko kadan ba ya wasa da tsafta, amma kuma idan ka dube shi da kyau za ka ga akwai damuwa a tattare da shi, wanda idan ba kallon tsaf ka yi mi shi ba, toh ba za ka ga ne ba...
Haka ta yi mi shi jagora zuwa cikin gidan su, daddy da kansa ya tarbe shi hannu bibbiyu, sabo da akwai shi da son mutane, ballan ta na wanda ke son yar' sa, bayan sun gaisa aka gabatar mi shi da abinci ta re da abun sha,bayan ya gama su ka kara yi mi shi gaisuwa akan rashin iyayen sa...
San nan daddy ya nemi karin bayani akan Abdul, duk da yana jin labarin Abdul d'in amma bai san shi ba, sabo da wancan zuwan na sa ba ya gari, amma duk da haka ya na son takaitaccen tarihin sa, kun san waka a bakin mai ita tafi dadi...
Sunana Abdul'aziz Abubakar mai Noma...
haka ya kwashe labarin sa ya fadawa su daddy,kowa ya tausaya mi shi, shiyasa aka ce ku tausayin mai mulki idan ya rasa ko mai dukiya, su din abun tausayi ne.
Wannan shi ne farkon zaman Abdul a karkashin daddy, duk wasu gonakin daddy ba bu wadda Abdul bai san da zaman su ba, arzikin daddy ya ninka na da,  shiyasa ya ware wa Abdul gonakin sa na shuka AYA,  ko kafin ka ce kwabo! katsina tafi ko wace   jaha noma AYA a cikin Arewa.
Shima Abdul'aziz arzikin sa ba a cewa komai. Haka akayi bikin Abdul da Halima,  su na zaman su cikin kwanciyar hankali da kuma kaunar juna...Bayan shekara daya Allah ya azurta su da samun k'aruwa, yarinya ta ci sunan mahaifiyar sa, amma su na kiran ta da Aneesa.
Duk ranar asabar Abdul na zuwa da iyalan shi gidan gonar sa, wadda ta ke a malumfashi, domin shakatawa, yauma hakan ce ta kasance, su ka shirya su ka tafi, gona ce babba sosai, gefe daya anyi ginin zamani, mai kyau kamar ba daji ba, sai kuma d'ayan gefen  wanda d'akin mai gadi ya ke a wurin, a gefen haggu kuma itatuwa ne daban-daban na kayan marmari( Ya'yan itatuwa)..
Aneesa ce ke rarrafe  a farfajiyar wajen, idon ta ne ya kyalla akan wani Zomo fari fat mai d'aukar ido ,  gefe d'aya kuma ga wani katon maciji na son sarar wannan zomon, abun ka da k'urciya, don a lokacin watan ta 7,  kamar ance iyayen su kalla, aikuwa su ka yi ido biyu da wannan macijin wanda ke son sarar zomon da ke hannun Aneesa...
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA
PLS
08144066758
KAR KU MAN TA DA:
COMMENTS    AND SHARE
      TA KU HAR KULLUM...
❤️YAR MUTAN ARGUNGU``` 📚❤️





















```ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?📚
MARUBUCIYAR...✍️
***Ashe ba so ba ne***
***Bayan wuya...***
***zumunta ko mugunta? On typing...✍️
GARGADI!!!
ƙagaggen labari ne,sabo da haka ban yadda wani ko wata su juya min littafi  ba, ba ta re da izinina ba,akiyaye!!!
JINJINA 👌

Ga yan'uwa na, Allah ya barmu ta re, ya kuma haɗa kanmu,muyi zumunta❤️💙
GODIYA
Ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai da ya ba ni ikon rubuta wannan littafi bi sa iyawar sa, da kuma yardarsa.Allah ya ba ni ikon kammala wannan littafi mai suna (ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺?)
MATAIMAKA
**Abubakar Shu'aibu birnin tsaba**
**Usman isah Rio**
**iman fatima Ibrahim*
GAREKU MA SU BIBIYAR LITTAFAI NA.
Ni mai neman gyaran ku ce, sabo da duk mutum mai kuskure ne, idan har kunga wani gyara toh kofata a buɗe ta ke(08144066758).
13/10/2022
Free Page
SHAFI NA 15
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
*************************************************Cikin tashin hankali iyayen Aneesa, su ka nufi wajen,  domin kaiwa tilon ƴar su ɗauki. Zuwan su ne ya sa  macijin saurin buɗe kansa da nufin ya kai wa ZOMON nan sara.   Abdul bai san lokacin da ya yi tsalle ta re da sandar da ke riƙe a hannun sa ba, ta re da kiran sunan Allah, ya bugawa macijin akansa. Wani irin tsalle macijin ya yi da nufin ya koma kan  Abdul,  amma Allah bai ba shi sa'a ba. Da sauri su ka ɗauke Aneesa,  wadda sam sam hankalin ta bai tashi ba, sabo da  ba ta ma san abun da ke faruwa ba..
A haka ma su gadin gonar  su ka bazama wurin neman wannan macijin, amma ƙasa ko sama ba su gan shi ba...
wannan abun da ya faru, shiyasa su ka tattara kayan su za su wuce gida. Bayan sunyi sallama da ma su gadi.
Sun fito kenan za su wuce sai ga wasu zomaye su biyu macce da namiji, ɗaya babba ɗayan kuma bai kai shi ba, can kuma sai ga wancan zomon da Maciji ya tashi cizo, shi ma ya zo ku sa da wanɗan nan ya tsaya, sai su ka taru su na kallon su Aneesa har su ka ɓacewa ganin su...
Bayan shekaru huɗu,  abubuwa da yawa sun faru, ciki har da rasuwar iyayen Halima, bayan sun yi haɗarin mota, da kuma zuwan Abdul JADA, sabo da jin hukuncin duk mai yanke ZUMUNTA da kuma falalar da ke cikin sada ZUMUNTA
ganin yadda yan'uwansa su ke rayuwar ƙasƙanci da kuma zallar talauci, sai a lokacin ne ya ke jin labarin, Inna Atika ta haukace kuma an neme ta  ba a ganta ba...
Kun san ance zuciya ba ta da kashi, haka ya sa, Abdul ya ji tausayin su, ta re da yi mu su alƙawarin zai samo mu su mafita.
Bayan ya koma katsina ya yi shawara da matar shi, Halima akan halin da ƴan uwan sa su ke ciki, ya na kuma neman shawarar ta...
Ta na jindadi duk lokacin da mijin ta ya zo neman shawarwari awurin ta, da wuya ya zartar da hukunci ba ta re da ya nemi jin ta bakinta ba, hakan na yi ma ta dadi sosai, shiyasa ta ke natsuwa ta ba shi shawara mai kyau,   toh hakan ce ta kasance a yanzu ma...
Ta nu na mishi cewa ya samar mu su gonaki acikin garin JADA, san nan ya saya musu gida ko ya gina mu su wani, sabo da wancan tsohon gidan na su  na Da,  sisi ma albarka. sabo da ita har ga Allah tafi son ya bar su acan JADA ɗin, ba wai don ba ta son su ba ko kuma don su na dangin mijin ta ba, a'a sai dan ganin cewa duk mutumin da ya ce baya son ka, daga baya kuma ya dawo ya ce yana sonka toh wallahi karyane...
amma ga mamakin ta, sam Abdul bai yi na'am da zancen ta ba, abun da kuwa bai taɓa faruwa a tsakanin su ba.Ta nu na mishi illar ɗauko su, amm sam ya yi kunnen uwar shegu da zancen ta. A haka ta koma gefe ta zubawa  sarautar Allah ido.
Alokacin da ya ɗauko ƴan uwa shi, Aneesa ta gama primary school going to secondary school. Bayan ya nu na mu su wuraren da za su yi na su aikin, ya kuma haɗa su da  ƙwararrun maaikatan sa, domin su nu  na musu abubuwan da ba su sa ni ba...
**************
           Rayuwa kenan, ance kasha daɗi kasha wahala.  ko kafin kace kwabo, su Adamu sun zarce yadda ku ke tunani. Amma kun san mai hali ba ya fasa halin sa, sabo da har yau da na ke faɗa mu ku , su na nan da ƙudirin su a cikin zuciyar su...
A ranar da Aneesa ta kammala secondary school ɗin ta, da wata biyu, wanda ya yi dai-dai ga ranar da ba za ta taɓa mantawa ba, shi ne lokacin da aka kashe  ma ta iyaye...
Sabo da a lokacin idan har ba ta manta ba, akwai ranar da ta dawo daga islamiyya, ta iske ran Baffan ta a ɓace, ummanta kuma ta na zaune ku sa da shi, ta na ba shi haƙuri.  "cikin nuna abun da aka yi mi shi ya ɓata mishi rai sosai! Halima har yaushe ne ni kam zanji daɗin ƴan uwana? yanzu abun da su Yaya  su ke yi min dai-dai ne fisabilillahi!?  su sa yar min da gonaki biyu, san nan su ce ban isa inyi mu su magana ba akan me! toh wallahi nagaji, su tattara inasu-inasu su wuce, tun da su ba za su taɓa canza hali ba, dama tun farko sai da ki ka gargaɗe ni, amma na yi kunnen uwar shegu da zancen ki, Halima wannan wane irin ZUMUNTA ne  ko ince MUGUNTA?
A jiyar zuciya Halima ta  yi, san nan ta ce " Abban Aneesa dan Allah ka kwantar da hankalin ka, duk abun  da zaman lafiya bai ba da ba, wallahi tashin hankali ba zai ba da shi ba, duk abun da ya yi tsanani maganin sa Allah, amma kam tabbas ba su kyauta ba, kuma ba bu inda ake sayar da abun wani ba ta re da izinin mai shi ba, kuskure dai ne sun ri ga sun yi shi ayi haƙuri a ta ri gaba." 
Sun yi wannan maganar da sati ɗaya. Kwatsam! Sai ga su kawu Adamu, da daddare ta re da ƴan fashi, abun da ya tada hankalin mu ainun, bayan sun nemi Baffa na da ya saka mu su hannu akan  takardun dukiyar shi, waɗanda su ke mallakin sa, amma yaƙi, sabo da a cewar sa, ba zai yi yu kura da shan bugu gardi da karbe kudi ba, ba zai yarda a ce duk gwagwarmayar da ya sha a rayuwa, amma wai lokaci ɗaya ace ya bayar da dukiyar sa, wallahi sai dai duk abun da zai faru ya faru.Hakan ne ya fusata wa su ƴan fashi biyu dake can gefe ɗaya harbin mahaifina a ƙirjin sa, mahaifiya ta kuma akai, hakan ya sa na gigice ta re da ɗimaucewa,  duk da a lokacin ba na cikin hayyaci na, amma ba zan taɓa manta muryoyin da ke magana a gaba na ba. Ɗagowar da zanyi, ya yi dai-dai da cire baƙin ƙyallen da ke ɗaure a fuskar su, kawu Tukur da Adamu... harbin da aka yi min ne a ƙafar hagu,   shiyasa na sume a wurin,ban sa ke sanin inda kai na ya ke ba.
A ɓangaren su kawu Adamu, bayan Aneesa ta sume a wurin, tabbas sauran ɓarayin da su ka zo da su, sun so abar Aneesa a wurin su wuce kawai. Amma kawu Tukur ya ce sam, ba za a bar ta ba, sabo da ba ta mutu ba, idan su ka bar ta asirin su zai tonu, kawai su kashe ta su huta. Har ya ɗana kunamar bindigar sa, sai ɗan fashin  ya ce kar su kashe ta, sabo da jin jiniyar motar ƴan sanda. Amma sabo da ƙarfin haki irin na Tukur sai da ya ɗauki Aneesa, su ka wuce da ita.  Haka ya jefar da ita a cikin daji. Duk wannan abun bai isheshi ba, sai da  ya koma wajen malamin sa na tsibbu, ya sa aka haukatar da Aneesa.
Wannan shi ne labarin rayuwar Aneesa...
GODIYA TA MUSAMMAN GA MASOYA NA MA SU BIBIYAR LITTAFAI NA. ❤ALLAH YA BAR MU TA RE DA KU
INA MAI FARIN CIKIN SANAR DA KU CEWA, DAGA YANZU ZA KU IYA SAMUN LITTADI NA A @WATTPAD
sai na ji ku
DOMIN SHAWARWARI KO GUDUNMUWA
        PLS
          👇
08144066758
KAR KU MAN TA KU YI MIN
***VOTE***
***SHARE***
***COMMENT***
Ta ku akullum
ƳAR MUTAN ARGUNGU``` ❤📚











ZUMUNTA 🤝 KO MUGUNTA 👺...✍️
marubuciyar...✍️
**bayan wuya**
**ashe ba so ba ne**
**zumunta ko mugunta? on typing...✍️
writing-by Fatima Zara Alhassan ❤️
Gargadi!!!
kagaggen labari ne. idan ya yi dai-dai da rayuwar ku, toh akasi ne. kuma wallahi ban yadda a juya min littafi ba ta re da izini na ba! Free page  ne,ban ya fe ba, duk wanda ya sayar da shi,akiye!!!
Jinjina 👌
ga yan'uwa na Allah ya bar zumunci, ameen❤️💙💚
Godiya:
ga ma su bibiyar littafai na, Allah ya sa ka muku da alkhairi nagode❤️
Ban manta da ke ba, fatima iman Ibrahim 😘
K/wata: 20/10/2022
Free Page📚
SHAFI NA 16
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
**********************************************************A jiyar zuciya su ka yi, ya yin da ita kuma Aneesa ta sa ka tafin hannun ta domin share ƙwallar da ke zubowa a fuskar ta, ta re da son yi mi shi magana. Du ban ta ya yi da kyau ya na mai ƙara jin tausayin ta, san nan ya ce "ki tashi mu tafi, na san yanzu haka sarauniya tana can ta na dubin hanyar mu. A'a Aneesa ba sai kince komai ba, ki aje duk wa su tambayoyin ki har mu isa masarauta, na tabbata sarauniya ba za ta ƙi amsa mi ki duk wa su tambayoyi da ke cikin zuciyar ki ba."
Ba ta re da ta yi mi shi gardama ba ta ce " toh".
Hakan ya sa shi miƙewa tsaye, ta re da girgiza jikin sa, ya na wa su irin surutai...
gefe ɗaya ta koma ta na kallon ikon ubangiji, ganin abun ta ke tamkar a majigi, ganin ta ke yi kamar mafarki ne, wanda ako wane lokaci ta na iya farkawa...
A tsorace ta ke kallon sa, ganin ya koma wata halitta ta daban.  Ya lura ta na son sume mishi ne, shiyasa ya su re ta( ya ɗauke ta) da hannun sa, sai akan fukafikin sa, nan ta ke su ka lula sararin samaniya, yau ga Aneesa a cikin gajimare. Tun ta na ɗarɗar har tafiyar ta yi ma ta

Please Login or Register in order to submit comment