Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka yi wa inna murja sallama, su ka wuce gona.
Malam kabiru asalinsa ɗan garin KAITA ne wadda ke cikin jahar katsina.
Ya na zaune ta re da matar shi Murja, kusan shekarar su ashirin amma Allah bai ba su haihuwa ba.
Ba ya da wata sana'a wadda ta wuce Noma.
Kuma kunsan noma ga mai ɗan karamin ƙarfi akwai wuya.
Shiyasa aminin sa malam sale, ya zo mishi da shawarar su je birni ko Allah zai sa, adace su samu wani aiki wanda zai fi noma samu.
Amma malam kabiru ya ce shi sam, ba bu inda zai tafi,  sabo da ance mishi ƴan birni sun fiye walaƙalanci, gara ya yi zaman shi, ya ci gaba da noman sa zai fi mi shi sauƙi.
Bayan kwana biyu malam sale ya zo mishi da zancen cewa ya samu aikin tsaron maƙabarta a cikin garin katsina.
Malam kabiru ya yi mishi murna sosai, da kuma fatar alkhairi
Haka rayuwa ke tafiya, da daɗi da ba bu  daɗi...
Kwatsam sai ga malam sale ya zo mi shi da wani zance , na  cewa su taimaki wannan bawan Allah.san nan  ya kwashe duk iya abun da ya sani game da wannan mutumin ya faɗawa abokin sa.
Wannan shi ne mafarin zaman malam Baƙo a gidan malam kabiru...
"ƳAR MUTAN ARGUNGU MUN JI SHIRU?
DAN ALLAH A CI GABA."
HAKA JAMA'A KE TA KIRA NA SU NA FAƊAMIN.
SHIYASA NI KUMA NA  TATTAKE NA ZUBA MU KU RUBUTU MAI YAWA😜😍
MA SU KIRA NA A WAYA SU NA ƘARA ƘARFAFAMIN GUIWA WALLE NA JI DAƊI, KUMA ALLAH YA SA KA MU KU DA ALKHAIRIN SA❤  
KAR KU MANTA ƘOFA TA A BUƊE TA KE DOMIN BA DA GUDUNMUWA KO SHAWARWARI👇
08144066758 KO KU TUNTUƁE NI AKAN LAYIN WHATSAPP 👇
       08162058867
KU DAI KU CI GABA DA SUBURBUƊAMIN
***COMMENT***
***SHARE***
***VOTE***
***LIKE***
ZA KU IYA SAMUN WANNAN LITTAFIN A #WATTPAD#
KO KUMA KU ZIYAR CI SHAFIN
(AREWA BOOKS)
GA DUK WAƊAN DA BA SU KARANTA
(ASHE BA SO BA NE) MA ZA KU GARZAYA www.dlhausanovels.com.ng  
TA KU HAR KULLUM, MAI SON FARIN CIKIN KU....
💖ƴar mutan Argungu``` 💝





``ZUMUNTA KO MUGUNTA??📚                       NA
FATIMA ZARA ALHASSAN
                   (ƴar mutan Argungu💖)
INA MIƘA ƊUNBIN GODIYA TA GA MASOYA NA, SABO DA JAJIRCEWAR SU, WAJEN BIBIYAR LITTAFAI NA, ALLAH YA SAKA MU KU DA ALKHAIRI😘
INA MAI ƘARA BA  KU HAƘURI, AKAN RASHIN JI NA, DA BA KU YI BA KWANA 2👏
INA GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA, DA YA BA NI IKON CI GABA DA RUBUTA WANNAN LITTAFI BI SA IYAWAR SA. ALLAH YA SA IN KAMMALA CIKIN AMINCI!
4/2/2023
SHAFI NA 22
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
***
Wannan shi ne mafarin zaman malam Baƙo a gidan malam Kabiru....
**
Kammalawar cin abincin su ke da wuya, malam kabiru ya shiga cikin gida da kwanukan abincin da su ka cinye...
Inna Murja ce ke ta  kai  kawo wajen gyara tsakar gidan ta. Macece mai tsafta ƙwarai d gaske.
Da sallama ɗauke a bakin su, su ka shigo cikin gida, malam kabiru ya nufi  wajen wanke-waken su, don  ya ajiye kwanikan abinci, ya bar malam Baƙo su na gaisawa da Inna Murja.
Bayan ya aje kwanikan
Ya miƙa ma ta keson (Tabarma) ya na magana  " Har mun kammala, yanzu za mu wuce"
"To malam Allah ya tsare ya kai ku lafiya,ya kuma ba ku ikon aiki sosai, sannan ku dawo cikin amincin sa"
Murmushi malam kabiru ya yi, ya na mai ƙara ƙaunar matar sa, duk shekarun da su ka yi tare, bai sa murja ta gaji da kula da shi ba.Ba bu ranar da zai fita ba tare da ta jero mishi addu'o'i ba. kullum ya kalli matar shi, sai ya ce" da ace murja ta samu ilmin zamani, yadda ta samu na addini, tabbas da  za ta riƙe muƙamai kala-kala.
Tun ɗazu malam Baƙo ke kallon su ya na murmushi, ya na kuma mamakin cewa, dama akwai irin wannan soyayyar a ƙauye? A tunanin shi, wayayyu ka ɗai ke soyayya? ( kun fa ji, tunanin malam Baƙo😅?)
Da fa kafaɗun sa, malam Baƙo ya yi. Firgigit  ya dawo hayyacin sa, ya na cewa
"Amin amin Murjanatu na"
Ai malam Baƙo mai zai yi inba dariya ba...
Shi ma malam kabiru, kunya ya ji, ganin dariyar da Abokin na  sa ke yi mi shi.
Sannan ya ce "zo mu tafi, dariyar ta isa haka nan, a rage dariyan,lokacin yin ta na nan zuwa"
Tsit ka ke ji, malam Baƙo ya bar dariyar, ya zubawa malam kabiru idanuwan sa, waɗan da su ka rine, da alama kukan zuci, ya ke yi...
"me ya sa, ko yaushe malam kabiru ke cewa ya adana dariyar sa, lokacin yin ta na nan zuwa?  shi kan sa ya san cewa, idan ya ce ya na da sauran farin ciki, to ya yaudari kansa.
Amma har gobe, ya na ƙara godiya ga Allah da ya kaɗo shi, cikin rayuwar malam kabiru.
Sabo da mutum ne mai barkwanci, da son jama'a, uwa uba ya na da ibada sosai...
Ganin irin kallon da ya ke jefo mi shi, ya sa malam kabiru jan hannun shi, su ka fita...
Zaune su ke su uku a office ɗin Barrister  Aminu Bello ɗan tsoho, babban lawyer a fannin shari'a, kuma ya yi ƙaurin suna sosai a najeria, wajen iya sharia
Sarki Fu'ad ne, zaune da shiga irin ta Aneesa, ba za ka taɓa cewa ba Aneesa ba ce.San nan ya koro wa Barrister Aminu duk bayanan sa, kasan cewar, yau kwana goma shaa biyar kenan, da aka buɗe kes(case) ɗin mutuwar iyayen Aneesa, magana har ta kai katu.
kuma katu ta ba da damar su ɗauki lawyer.
Tun last week sarki fu'ad ya zo wajen Barrister Aminu, (Aneesa) su ka tattauna akan waɗanda ta ke zargin su ne su ka kashe mata iyaye...
"Malama Aneesa, me ya sa ki ke zargin su?
"Sabo da a gaba na, abun ya faru"
"ko a gaban ki, abun ya faru, idan ba shaida, to ina mai tabbatar miki aikin banza ne. ƙwararrun hujjoji, su ne cin nasara a kotu.
Sabo da haka, dole mu dage wajen bincike, ba zamu sakarwa ƴan sanda komai ba,  kuma in sha Allah zan saka ido akan su kawu."
"Toh shikenan  Barrister, nagode, sai na ji ka,Jazakallahu khairan"
"Amin-amin Aneesa, duk yadda muka yi da ƴan sanda zan kira ki"
Su kawu ba su san cewa Aneesa ta yi magana da  alƙali ba.
Cikin sauri Barrister Aminu, ya shigo cikin office ɗin, ya na cewa:
"Dan Allah ku yi haƙuri na sa ka ku jira, wlh wani uzuri ne, ya tsayar dani"
"Ba damuwa Barrister,  take your time"
Cewar Aneesa(sarki fu'ad)
Su kawu sai hararar barister su ke, ƙasa-ƙasa, sarai ya gan su, su na hararar shi.
Gyaran murya Barister ya yi, ya na mai kallon su kawu, don ba zai iya haɗa ido da Aneesa ba, sabo da ɗan banzan kwarjinine da ita sosai, san nan ya ce
" Abun da ya sa na ce muku mu haɗu, sabo da in sanar mu ku cewa,  za ayi zaman kotu ranar litinin mai zuwa in sha Allah,kamar yadda alƙali ya sanar da mu,
shi ya sa na ce, ba ri inji ta bakin ku, me ake ciki game da shaidu? sabo da shaidun da mu ke dauke da  shi yanzu ba zai isa ba, dole sai mun kawo wasu."
"Barrister na ji kana maganar shaidu? duka-duka yaushe aka fara binciken, da har za a samu shaidu? cewar kawu Bala"
Murmushi Barrister ya yi, " A tunani na za ku yi farin ciki  kuma ku ƙara ba ni ƙwarin guiwa?"
"mun yi farin ciki, amma ka faɗa ma na, wane shaidu ne ka ke cewa ba zai isa a gabatar da shi a katu ba? Cewa kawu Tukur...
Murmushi Barrister ya yi, ta re da gyara zaman shi, "ku yi haƙuri akan rashin faɗa mu ku da ban yi ba, tuntuni. Akwai wasu ƴan fashi biyu da aka kama, da laifin kisan kai, bayan binciken da rundunar ƴan sanda su ka yi, an gano cewa waɗan nan ɓarayin su na ɗaya daga cikin mutanan da su ka je gidan Alh. Mai Noma, su ka kashe shi ta re da mai ɗakin sa.
Amma kuma sun shaida ma na ba su, su ka yi  halbi ba, da sa hannun wasu mutane...
Amma kar ku damu, wannan shaidun ya nu na min cewa akwai babbar nasara a cikin wannan shari'ar."
Mutuwar zaune su kawu su ka yi,sai uban zufan da ke karyo mu su...
"Mu na godiya Barrister, kuma in sha Allah, nima zan yi ƙoƙari na ga na samo na wa shaidun, sabo da aiki mutum ɗaya ya raina" Cewar Aneesa (Sarki Fu'ad).
" kar ka damu Barrister dole mu ma mu tashi tsaye don ganin an hukunta waɗan da su ka kashe ma na ɗan uwan mu," cikin kuka kawu Tukur ke wannan maganar...
A gajiye ta shigo cikin ɗakin, ta yar da jakarta a kan gadon ta, san nan ta mai da kallon ta ɓangare ɗaya inda roomate ɗin ta ke kwance ta na bacci.
Dundu ta naɗa ma ta a bayan ta, ai ba bu arziki  Feenat ta tashi a firgice ta na kwaɓe fuskar ta.
"Dama wallahi nasan ke ce,  saboda  mugunta mutum na bacci za ki zo ki tashe ni!?"
"Cikin taikaci ta ke kallon ƙawar ta ta, "idan har ba ki son muguntar, to ki tabbatar da kin gama aikin ki kafin ki yi bacci, idan kuma ba haka ba wlh ko gobe sai na yi mi ki dundun da ya fi wannan ciwo.  Ke ki ka raba mana duty, in yi gyaran ɗaki da safe ki yi  na rana, amma sabo da zaman ki lazy ko tsinke ba ki ɗauke ba? Ta re da ɗaukar filo ta ƙara ma kawa feenat.
Feenat  asalin ta ƴar jahar kano ce, ta na cikin ɗaliban da kwankwaso ya ba wa scholarship, wannan kenan
Rigimar su ba ta wuce Aneesa ta gyara wuri, feenat kuma ta ɓata wajen.
Ita ma ɗauko na ta tayi ta na ramawa, kafin ka ce kwabo duk sun ya mutse ɗakin...
Ƙwanƙwasa ƙwafar da aka yi ne ya hana su ciki gaba. Buɗe ƙofar ke da wuya ta   san ya ihu sabo da murnar ganin wadda ba  ta yi tunani ba.
Rungume juna su kayi, su na farin cikin ganin junan su...
"Murmushi Sarauniya ta yi, ta na mai cewa: Auta Aneesa  wurin zaman ma sai na roƙa? tare da murmushi akan fuskar ta"
"Dariya  Aneesa ke yi, "tsabar murnar ganin ki ne ya sa ka ni rashin ganin   ba a zaune mu ke ba"
Bayan sun zauna feenat ta gaishe da sarauniya san nan ta fita
" Sarauniya tun da ki ka kawo ni, ba ki sa ke zuwa ba, kuma kin san ban da kowa sai ke, ta re da fashe wa da kuka!"
"Auta Aneesa ba dai rigima ba, toh ke in ban da abunki,  don mi na ba ki ƙaho? kuma kin san na faɗa mi ki ,cewa duk ranar da ki ka yi kewata,  da zarar kin busa shi, za ki je duk inda ki ke son zuwa.
Amma duk da haka ki yi wa maman ki uzuri kin ji?"
"Cikin jin kunya Aneesa ta ce " na yi mi ki uzuri  mamata, ni ma dan Allah ki yi haƙuri , wlh na manta da ƙahon sam"
Murmushi sarauniya ta yi " Ba ki yi min komi  ba Aneesa, da fatar ba bu wata matsala dai ko? kuma ki na karatu da kyau?"
Cikin jin kunya Aneesa ta ce, " ina karatu sosai sarauniya.Yanzu haka mun fara rubuta Test, shigowa ta kenan...
Sallamar feenat ne ya katse Aneesa
Ta na ɗauke da table water a hannun ta,
"mama ga ruwa" cewar feenat
Murmushi sarauniya  ta yi ,san nan ta shafa kan feenat ta ce, " Allah ya yi mi ki albarka feenat"
"Sarauniya me ya sa yaya Fu'ad be biyo ki ba?"
"Kar ki damu Auta, yayan ki aiki ya yi mishi yawa, amma da zarar ya kammala aiyukan shi, zai kawo miki ziyara in sha Allah."
"Allah sarki  yaya fu'ad! Allah ya ba shi sa'a. Sarauniya ba ri in dafa ma na abinci"
"Auta ki na nufin kullum sai kin yi girki?! To miye amfanin ƙahon da na ba ki? ma za tashi ɗauko min ƙahon in ga ni."
Cikin sauri Aneesa ta ɗauko shi, ta ba sarauniya, sai ƙyalli ya ke yi kamar zinari
Ƙahon sarauniya ta  kai ga bakin ta, ta busa shi cikin ƙwarewa, nan ta ke abinci iri-iri su ka bayyana a gaban su...
Cike da mamaki Aneesa ta ce, "yanzu ina da wannan abun na tsaya ɓatawa kaina lokaci?"
Murmushi sarauniya ta yi, san nan ta ce "Ai sabo da ba ki ɗauke shi da mahimmanci ba ne, shi ya sa ba ki kwantar da hankalin ki wajen koyon aiki da shi ba. Amma duk abun da ki ka sawa ranki, da zarar kin busa shi shikenan."
Haka dai su ka kwashe a wanni su na fira,daga baya sarauniya ta yi ma ta sallama san nan ta tafi...
Sai yamma su malam kabiru su ka dawo daga gona, ko wannan su ya gaji.
Bayan magrib malam kabiru ya zo kiran malam bako ya zo su ci abinci. Sai dai me ze   gani a bakin ƙofar? Tashin hankali...!!!
Ƴar mutan Argungu```





```ZUMUNTA KO MUGUNTA?
                          NA
   💖FATIMA ZARA ALHASSAN💖
             (ƴar mutan Argungu)
SHAFI NA 23
BISMILLAHIR  RAHMANIR RAHIM
**********************************
Tashin hankali...
Murmushi ta yi wa malam kabiru. Shi ma ya mayar ma ta da murmushin...
Gaisawa su ka yi, san nan su ka shiga tattaunawa a tsakanin su. Hakan zai nu na ma ka cewa, dama can sun san juna...
Bayan ta faɗa mishi buƙatar ta, shi kuwa malam kabiru ya yi ma ta alƙawarin cika ma ta shi.
Fu'ad ne zaune a ɗaki ya na jiran isowar sarauniya, tun jiya ta sanar da shi za ta kawo mishi ziyara, kuma ta na son ayi zaman kotu ta re da ita.
Iskane mai ƙarfin gaske ya tashi a tsakar gidan su kawu, irin guguwar nan ce me shegen ƙara ,wadda kan iya tafiya da mutum sukutum idan bai yi hankali ba.
Hakan ya sa mutanan gidan kowa ya yi ta kan sa,  ma su rufe windows na yi, ma su ɓoyewa na yi...
Murmushi Fu'ad ya yi, sabo da ya san cewa, sarauniya ce ta shigo gidan.
Haske ne ya fara fitowa daga bangon ɗakin, a hankali har ya mamaye ɗakin baki ɗaya
Sarauniya ce ta bayyana a gaban Fu'ad, rungume juna su ka yi su na murmushi
San nan su ka shiga gaisuwar yaushe gamo...
Abinci mai rai da lafiya ya gabatar ma ta da shi.
Bayan ta gama cin abinci, su ka shiga tattaunawa akan yadda zaman kotu zai kasance.  San nan ta faɗa mishi  na ta shirye-shiryen.
Murmushi Fu'ad ya yi, san nan ya ce "sarauniya, me zai hana mu rufe wannan  kes(case) ɗin, sai mu kama su kawu, mu tafi da su masarauta in hukunta su da hannu na, ya fi duk wannan abun da zamu tsaya yi?"
"ka manta tun farko, kai ka kawo ma na wannan shawarar na cewa, mu fito mu su a mutum, kuma a matsayin Aneesa?  Sabo da haka, maganar jayewa duk bai ta so ba, a yadda ka fara, ina son ka kammala kawai.ƴan uwansu  Bil'adama su kawa laifi ba mu ba, shiyasa  mu ma za mu sanya ƴan uwansu Bil'adama su yanke mu su hukunci dai-dai da abun da su ka aikata. in sha Allah komai ya zo ƙarshe. Ita kan ta Aneesa zan so ayi zaman kotun nan gobe  ta re da ita."
Jinjina kai Fu'ad ya yi, ta re da  kallon sarauniya, san nan ya ce, " Amma wa zai  ɗauko ma na Aneesa?"
"Murmushi sarauniya ta yi, "har ka manta  Aneesa ba ita ka ɗai  ba ce?  yayar ta fa, na ƙasar, Hoor..."
Shi ma murmushi ya yi, "Na man ta, Hoor rigima na nan... dangware mishi kai sarauniya ta yi, "ba ri dai ta ji ka, ba ruwa na"  a ta re su ka yi dariya...
Su kawu  ne zaune a gaban Boka tsimmirarre, su na ma su duƙar da kan su ƙasa, " ya bokan mu, mu na son a sa ke haukatar ma na  Aneesa, ta bi duniya ta halaka ba ta re da an sake jin ɗuriyar ta ba!
Idan ma ya kamata a kashe ta, mun fi son hakan" cewar kawu Tukur...
Tuntsirewa da dariya boka ya yi, nan ta ke kuma ya ɗaure fuskan shi, kamar wani dodoBige-bigen sa ya fara yi, ya na  wa aljanun sa kirari: ya marmazuƙeeee...ya baburuntsetseeee...haka ya ke ta shirmen sa, faɗi banza faɗi wofi.
Tun kafin ya  gama surkullen shi, wata irin walƙiya ta gifta ta wajen kayan tsafin shi, nan take kayan su ka kama da wuta...
Cikin tashin hankali su kawu su ka ce, ƙafa me na ci  ban baki ba? ai kafin ace kwabo, ko bujen su kawu ba a gani...
Haka wutan nan ta haɗa har boka ta ƙone  shi ƙurmus, wuri ya dawo baƙi ƙirin, wan nan shi ne ƙarshen boka tsimmirarre(  Allah ka karemu daga yin shirka, ma su yi kuma Allah ka shirye su idan ma su shiryuwa ne).
Yau ake zaman kotu, mutane sun cika maƙil, kasancewar akwai shari'ar da ake yi yanzu kafin a yi ta su Aneesa...
"Adamu ka na ganin ba za mu sa ka su Duna ba, wajen kashe yarinyar nan?  duk yadda za su yi, kar su ba ri ta isa kotu, kawai su kashe ma na ita!"
kai tsaye ya ce, Tukur ni fa na bar ma ka wuƙa da nama a hannun ka,  sabo da ka fi ni sanin duk wasu makirci irin na arnan farko, don haka duk abun da ka ga ya fi kawai a yi." cewar kawu Adamu...
***************************************************************
Shiri malam kabiru ke yi, ta re da  ba wa murja labari akan malam baƙo. sallallami murja ke yi ta na cewa,  lallai ka ji tsoron Allah ka ji tsoron mugun mutum, toh yanzu malam birnin za ku je ta re da malam baƙo?"
"Eh, daga nan can zamu wuce, sabo da kar mu makara, yanzu haka malam idi ya na bakin hanya ta re da direba, mu ka ɗai su ke jira. Idan har Allah bai bamu ikon dawowa  a yau ba,  to lalle kar ki kwana a gidan nan ke kaɗai, ki kira Asame ɗiyar karima ta taya ki kwana.'"
"In sha Allah, zan kira ta. Allah ya tsare hanya ku je lfy, ku dawo lfy"
"Amin-Amin Murja nagode..."
Ya na fitowa ƙofar gida ya tarar har malam baƙo ya shirya cikin yadi ruwan ƙasa-ƙasa, ya yi mi shi kyau sosai, sabo da malam kabiru ce mi shi ya yi, ɗaurin Auren  ɗiyar abokin su ne za ayi, shi ya sa zai raka su. wannan kenan...
***********************************************
Zaune Aneesa ta ke a ɗaki, ta na rubutu a diary ɗin ta, (littafi ne mai ɗauke da sirrikan ta)
Motsi ta ji  cikin kicin( kitchen ) ɗin su, ta san kuma tun ɗazu feena ta fita,  balle ta ce ita ce...
A hankali ta tashi zuwa dubowa,  leƙawa ta yi kaɗan, ba ta ga komai ba,  cike da mamaki ta faɗa kicin ɗin gaba ɗaya, ta dudduba ko ina, duk da ba wa su kaya ne a cikin kicin ɗin ba, har za ta fita, sai kuma taji motsi a bayan ta...
Juyowar da za ta yi su ka yi ido huɗu  da  gimbiya Hoor.  Cikin tsananin murna  ta daka tsalle ta rumgume ta. gimbiya Hoor na ganin haka, ita ma ta buɗe hannun ta, ta rumgume  Aneesa, su na dariya...
"oha ni, su Aneesar sarauniya an girma?"
Murmushi Aneesa ta yi,  da sauri Aneesa ta ɗago ta na kallon  fuskar gimbiya Hoor, "yaya Hoor ciki na ke gani? kafin ma gimbiya  Hoor ta yi magana,  Aneesa ta fara rawa ta na waƙa "am going to be a mother....am going to be...
Riƙe ta Gimbiya ta yi, ta na murmushi, san nan ta ce  "Aneesa ba mu da lokaci,  yi sauri ki zo mu tafi,  su sarauniya na can su na jiran mu...
"Zuwa ina?" cike da mamaki Aneesa ta tambaye ta, tsoron ta kar ace wani abu ne ya faru da sarauniya.
"Kar ki damu, kowa lafiyalau ya ke.yi  sauri ki ɗauko  min ƙohon da sarauniya ta ba ki,  wannan cikin ya sa ƙarfi na ya yi ƙasa, ba zan iya  kaimu ba.(Kun san cikin aljanu girma ne da shi sosai,  ba irin na bil'adama ba.)
miƙa ma ta ƙahon Aneesa ta yi, san nan gimbiya ta ce ta ɗauko mayafin ta, su tafiBayan Aneesa ta shirya, gimbiya Hoor ta riƙe hannun ta, su ka zauna a ta re.
Kamar ƙiftawa da bisimilla, sai ga su Aneesa a cikin Nigeria.
Saƙo su ka turawa sarauniya cewa sun iso nigeria.
Bayani ta yi mu su yadda za su mayar da ƙaho ya zama abun hawa,  ita kuma za ta dinga kula da motar.Haka su bi duk wani bayanin da sarauniya
ta yi mu su.
Sai ga mota haɗaɗɗa a gaban  su ta re da buɗe mu su ƙofofi. Haka motar ke tuƙa kan ta, ba ta re da sun yi komai ba
**********************************************************
Bayan alƙali ya yankewa ma su laifi hukunci, aka wuce da su gidan gyaran hali, san nan alƙali ya ba da hutun rabin sa'a( 30mnt) kafin a gabatar da ƙara ta gaba, wato shari'ar su kawu...
Burin su kawu ɗaya, Allah ya sa lokaci ya cika, kafin Aneesa ta zo, sabo da su na son a kori ƙarar...
Fu'ad ne shi da sarauniya a cikin mota,  ya na sauri su isa kotu kafin lokacin da aka ɗiban mu su ya yi. Amma sai dai me, jin kawai su ka yi taya ta fashe, cike da mamaki fu'ad ya  fita ya duba...
Cin karo ya yi da su DUNA shi da yaran sa, sun zagaye motar. murmushi fu'ad ya yi, sabo da gano dalilin da ya sa su DUNA su ka  ta re shi, a tunanin su Aneesa ce.
Magana ya yi musu " me ku ke so?"
Cike da maganar iskanci DUNA  ya ce "  kashe ki a ka ce mu yi,  kuma har an biya mu"
"Ina son ku koma wajen wanda ya turo ku, ku ce mu su ni maccece mai kamar maza,  kashe ni kuma sai manyan mazaje..."
Cikin fushi ta re da fusata, Duna ya  ce, "kanbur*** ni za ki kalla ki ce, sai manyan mazaje  za su iya kashe ki!!!
Mai da kallon sa ya yi  wajen yaran sa,  ya na mai daka musu tsawo "me ku ke jira ba ku kawo min kan shegiya ba?!"
Jikin su na rawa, su  ka yi kan  Aneesa ɗauke da makaman su...
Ganin hakan ya sa  sarauniya fitowa daga cikin mota a zafafe!!!
Tsawa ta daka mu su..."kaiiiii...nan ta ke iska  ya dinga jifa da su,  wa su sun some wa su kuma sun samu raunuka a jikin su...
Duna na can gefe tsaye ya na kallon ikon Allah, duk da zuciyar sa, ta razana, amma hakan bai sa ya fasa tunkaro inda su sarauniya su ke ba. A cewar sa, ba a taɓa ba shi aiki ya ka sa  ba!!
Cike da mamaki fu'ad ke kallon ƙarfin hali irin na Duna.
Wuƙa ya zaro daga ƙugun shi,  zai sokawa fu'ad....amma wuƙar ta ƙi shigar fu'ad. shi kuma ba komai ya sa ya ƙyale duna ba, sai dan ya ga iya gudun ruwan sa
cikin tashin hankali duna ya kalli cikin idanuwan fu'ad ya ga wasu irin macizai ƙana-ƙana su na yawo, wasu kuma sun fara fitowa daga ciki...
Wuƙar hannun shi, ya sake ya na makarkata zai zube a ƙasa, da alama sume wa ya ke son yi.  Amma fu'ad bai bar hakan ta faru ba...
Ta ro shi ya yi, ya miƙar  da shi tsaye, san nan ya huura mi shi iskan bakin sa, nan ta ke Duna ya miƙe ya na "sai oga...choii!choii! irin yadda ƴan daba ke yi.
Murmushi fu'ad ya yi, ya na mai da fa kan duna san nan ya ce  " ka faɗi iya abun da ka sa ni"
"in sha Allahu oga zan faɗi komai" cewar duna
Wajen yaran duna sarauniya taje, ta warkar da su, abu kamar haɗin baki, duk wanda ya farka sai ya ce, "Choiii...choiii oga, zamu faɗi gaskiya"
Umarni ya ba su duna, su wuce kotu, su za su zo daga baya
Bayan su wuce sarauniya ta kalli fu'ad ta ce, " me ya sa ka canza mu su tunani?"
"Na sauya mu  su tunani ne na ɗan lokaci kaɗan, ana gama shari'a a yau tunanin su zai dawo, amma ba za su iya tuna kwangilar da su kawu su ka ba su ba., abu ɗaye ne za su iya yi da ƙwaƙwalwar su, shi ne su ba da shaida a kotu akan cewa turo su aka yi domin  su kashe ni. Kuma da zarar sun yi ido huɗu da su kawu, za su nuna su...
******************************************
Bayan hutun da alƙali ya ɗiba ya cika, jama'a su ka dinga shigowa dan ganin yadda shari'ar za ta kaya...
Alƙali ya

Please Login or Register in order to submit comment