Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

FALALA DA MARTABAR SAHABBAI Complete Hausa Novel Document by FALALA DA MARTABAR SAHABBAI


FALALA DA MARTABAR SAHABBAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 5471



FALALA DA MARTABAR SAHABBAI

Reading Time: 0 Hours

Added On: 03, Jul 2024

Author: Aliyyu Abdullahi 'Dan Malam ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08067396502

Book License : Free

Category: Documentation

File Size: 29.2 kb

File Type: txt

Views: 473+

Download: 198+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [14/11 10:11] 'Dan Malam: FALALA DA MARTABAR SAHABBAI
#Shimfiďa: Da sunan ALLAH mai rahma mai jin 'kai, tsira da amincin ALLAH su 'kara tabbata akan Manzon ALLAH S.A.W cikamakin Annabawa shugaban manzonni. ALLAH yace:
An tsinewa waďanda suka kafirta daga Bani isra'ila (zuriyar Annabi Yakub A.S) da harshen Annabi Dawood A.S da na Annabi Isa ďan Maryam; saboda sun kafirce kuma sun wuce gona da iri. Sai ALLAH ya cigaba da cewa:
(Saboda) sun kasance basa hani ga juna akan munanan ayyuka idan aka aikata, lallai makoma tayi muni akan waďannan abubuwan da suka kasance suna aikatawa (ma'ana dukkanin su da masu aikata waďannan ayyukan da waďanda basa hani ga aikata su) a duba ko wane littafin tafsirin waďannan ayoyi wato Sura ta biyar (Suratul Mai'da) daga aya ta saba'in da takwas zuwa ta tamanin da ďaya (Q5:78-81). Waďanda ayoyi dasu na kwana don jiya nayi muqabala da wasu ýan uwa akan son zuciyoyin su dangane da abunda ya shafi bid'o'i waďanda ake 'kir'kirowa a addini. Dalilin da suke bayarwa su da maluman su shine: Mai yasa bamu ta6a fitowa mun soki birthday wanda kullum ake kan aikatawa ba? Dalilin mu anan shine: Birthday yahudanci ne kuma ai a matsayinka na musulmi mai imani, idan kana karatu baka bu'katar sai an fito an ce maka wannan kafirci ne wanda bashi da asali a musulunci. Manzon ALLAH S.A.W yace: Mumini madubin mumini ne, idan yaga aibu a gurin ďan uwansa, ya gyara. Idan don ALLAH muke yin addinin, dole mu dinga kar6an gyara daga gurin juna. Da dalili ake addini ba da son zuciya ba. Ka karanta kuma ka ďauki sakon da yake 'kunshe a cikin wannan rubutun don idan baka karanta ba, nayi imani cewa waďanda suka fika zasu karanta kuma su amfana. Duk da cewa 'Karshen duniya ne kuma duk iya salo na da'awar mutum ba yanda zaiyi idan ALLAH bai shiryi mutum ba, wannan ba hujjace ta 'kin kira ga gaskiya ba. ALLAH ya koyar da ManzonninSA ciki har da Manzon ALLAH S.A.W akan cewa: Ba zaka iya shiryar da wanda ALLAH baiyi niyar shiryar dashi ba. Misali: Mu duba 'Dan Annabi Nuhu A.S, matar Annabi Luď A.S da baffan Annabi S.A.W wato abu 'Dalib. Kuma mu dawo ta ďayan 6angaren mu duba rayuwar matar Fir'auna (kafirin da yafi ko wane kafiri kafirci a tarihi). ALLAH ya buga misalai dasu a gurare daban daban a Qur'ani kuma Manzon ALLAH S.A.W ya bada labarin su a hadisai daban. A musulunci, mun yarda bayan Annabawa, babu masu darajar sahabban Manzon ALLAH S.A.W kuma wajibi ne duk mai imani ya yarda da hakan. Idan muna karanta tarihin su kuma muna amfani da abubuwan da muka karanta, zamu ci riba duniya da lahira. ALLAH da KANSA ya yabe su da cewa: Mazaje ne waďanda kasuwanci da siye da siyarwa baya shagaltar dasu daga ambaton ALLAH; suna cike da tsoron ranar da zuciyoyi da da idanuwa zasu raunana (Ranar Qiyama) to dayake ba Tafsiri nake ba, bana son in ja da yawa tunda dama shimfiďa ce duk da akwai abubuwa masu yawa da nake son kawowa amma a hankali inshaa ALLAH zan isar da sa'kon. ALLAH ya san zuciyata na dalilin wannan rubutun kuma ina ro'kon ALLAH ya bani ikon 'karasawa lafiya kamar yanda na fara da sunan ALLAH, ALLAH ya bani ladan tare daku. ALLAH KA rabamu da riya da ribatar Shaiďan..
(1) MUS'AB BIN UMAIR (Farkon jakadan Musulunci)
Mus'ab ďan Umair ya taso a gidan wadata da jin daďi don mahaifiyarsa ta kasance daga cikin mutane mafi kuďi a Makkah. Ya kasance ďan gayu wato babu matashi a Makkah wanda mata suke labarinsa kamar Mus'ab bin Umair saboda ga kyau, ka kuďi ga mulki don mahaifiyarsa ta kasance daga cikin masu faďa aji na wancan lokacin. A lokacin, farkon Manzoncin Manzon ALLAH SAW ne kuma a lokacin, musulunci bai fara 'karfi ba don Manzon ALLAH SAW da sauran sahabbai farkon musulunta suna zaune ne a "Daru Arqam bin Arqam" suna ibadah a 6oye. Wata rana, Mus'ab bin Umair ya ji labarinsu inda yazo don cin mutuncin Manzon ALLAH da sahabbansa inda ALLAH ya shiryar dashi ya kar6i musulunci a maimakon haka. Ya fara yi a 6oye har wata rana yazo shiga wani mai suna Uthman bin Taiha ya gansa yaje ya gayawa maman Mus'ab wato Khunais bint Malik wanda dama tayi fice ne a mugunta don kusan duk makkah ana tsoron sharrinta amma tare da haka, ALLAH ya jarebeta da son ďanta 'kwaya ďaya wato shi Mus'ab. Bayan an kai mata labari, ya dawo gida sai yaga duk manyam mutanen makkah an taru ga mahaifiyarsa a cikin su. Suka zazzage shi suka ci mutuncinsa wanda har sai da maman nashi tayi masa wani naushin da sai da yaga taurari. Bayan wannan, an kulle shi amma sai da ya san yanda yayi ya bar gidan ya koma Daru Arqam wanda wannan yayi daidai da lokacin da Manzon ALLAH SAW ya tura sahabbai 'kasar sarki najjashi wanda ba musulmi bane amma baya bari a takurawa musulmai a 'kasar. A lokacin sai suka tafi tare dashi har zuwa wani lokaci wanda bayan sun dawo, ya 'kara zuwa gurin mahaifiyarsa inda yace mata: Kinga wannan takobin, Na rantse da ALLAH duk wanda kika sa ya kamo ni saina raba kansa dashi. To dama tasan halin shi tsaf zai iya. Daga 'karshe yace: Yake mahaifiyata! Ki kar6i wannan addinin da yake na gaskiya lallai ni ina sonki da rahamar ALLAH. Sai tace: Na rantse da taurari ba zan kar6a ba. Haka kawai girma na ya zube a banza?! Tana ji tana gani haka suka rabu da hawaye. Mus'ab bin Umar ya gwammaci rayuwar wahala akan wanda jin daďi duk don ya samu yardar ALLAH. Wata rana, sahabbai suna ganinsa sai suka fashe da kuka suka ce: Kalli yanda Mus'ab ya dawo wanda da kowa yasan irin jin daďin da yake ciki amma yanzu kalli kayan da yake sakawa!. Manzon ALLAH SAW yace: Ni naga Mus'ab a Makkah a lokacin ba wani matashi wanda yake jin daďi kamar sa. Manzon ALLAH SAW ya tura shi Madina don yayi kira ga musulunci kuma ya koyar da addini inda anan ya samu ďumbin nasarori don manya-manyan mutane a madina sun musulunta a sanadiyyar shi inda kusan duka mutanen Madina suka musulunta a wancan lokacin. Ya samu gaggarumar nasarar da ba'a kwatantata da wata a wancan lokacin. Ha'ki'ka ya isar da sa'kon ALLAH wanda Manzon ALLAH SAW ya aiki shi dashi tare da gaggarumar rinjaye. Lokacin ya'kin Uhud, bayan shaiďan ya samu rinjaye akan musulmai inda bayan sun bar kan dutsen uhud, kafirai dalilin da yasa kafirai suka samu galaba a kansu. Lokacin da Mus'ab ibn Umair ya fahimci cewa ya'ki ya canja kuma akwai matsala, sai yayi kukan kura yayi kabbara ya 'kara himma har takai ga sun zama ýan tsiraru daga cikin waďanda suke kare Manzon ALLAH daga harin kafirai waďanda basu da wani buri da ya wuce na ganin bayan Manzon ALLAH S.A.W a wannan lokacin. An sare masa duka hannuwa biyu inda daga karshe yayi shahada tare da sauran manyan jarumai waďanda sukayi shahada a ya'kin uhud wanda hatta Hamza anan yayi shahada. Bayan an gama ya'kin, Annabi SAW tare da sauran sahabbai sun zo ďaukan gawawwaki don binnewa da yiwa shahidai ban kwana inda aka tsince shi a cikin su sai Manzon ALLAH SAW yayi hawaye inda yace: Munyi hijra tare don ďaukaka kalmar ALLAH, lallai sakamakon mu yana ga ALLAH. Annabi S.A.W ya cigaba da cewa: Daga cikin mu akwai waďanda suka bada gudunmawa iyakar 'karfin su amma sun koma ga ALLAH ba tare da sun ci gajiyar wahalar ba (ma'a basu riski lokacin da addinin yayi 'karfi ba) yace: A cikin su akwai Mus'ab bin Umair. Aya ta 23 ta cikin sura ta 33 (Q33:23) ta sauka ta dalilin wannan. ALLAH yasa mu dace.
Daga 'karshe wannan kamar sharen fage ne na tarihin sahabbai shiryayyu wanda gudunmawa ta ce, duk mai son sanin cikakken tarihin, ya duba waďannan littattafan: Albidaya wan nihaya na Al-hafiz ibn Kathir, Qasasus sahaba da sauran ingantattun littattafan sira na manyan malamai. Zamu cigaba da tarihin sahabi na gaba a cikin jerin rubutun inshaa ALLAH ko gobe idan na samu lokaci. Ayi sharing don Manzon ALLAH SAW yace: Duk wanda yayi nuni ga aikin alkhairi yana da lada kamar wanda yayi. ALLAH KA sanar damu abunda zai amfane mu! ALLAH KASA addinin nan ya zamo hujja gare mu ba hujja a kanmu ba!!
Don gyara ko jan hankali ko tambaya, ga nombobi nan kamar haka:
08067396502 (WhatsApp).
08169965350 (Kira kawai).
©Aliyu Abdullahi 'Dan Malam
[14/11 10:11] 'Dan Malam: FALALA DA MARTABAR SAHABBAI (2)
Wani ya tambayi Manzon ALLAH SAW alamomin tashin Qiyama inda bayan ya bayyana alamomin ta, sai sahabbai suka tambaye
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download FALALA DA MARTABAR SAHABBAI

START READING

OR

DOWNLOAD TXT NOW
This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album