Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI Complete Hausa Novel Document by MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI


MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28234



MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 29, Jul 2023

Author: Maryam Yar Mama ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07030772637

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 166.49 kb

File Type: txt

Views: 4149+

Download: 1152+

Last download: 1 day ago

Description/Story: 














*💥MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI💥
(A LOVE STORY)
01
BY
MARYAM YARMAMA





*APOLOGY*
AM SO SORRY MY followers I CANT CONTINUE ,THE STORY *CAPTAIN SHAYEEDA BUT I WISH ONE DAY I WILL CONTINUED,I NEED UR PRAYER

*starring*
Adorable minal
Stubborn gal aziza
Hansome guy annur
Play boy safwan
Ummi
Saudat
Hasiya
AND OTHERS..........


*VOTE OF THANKS*
zahrah bukar
Asykhaleel
Salma ali wada
Halal dady gal
Hauwa mamee
Maman hafsy(hajara)
Lubna(lalata writter)
Miss xoxo
Raz
Aisha gana
Pretty minnah
And others friends



*KANO CITY*
Kuka minal ta saki sakamakon mafarkin datayi na mahaukacin masoyi,kuka tafara tana wai yaushe zanga mahaukacin masoyina iye,mahaukacin masoyi ka nunamin kanka,meyasa kake firgitani a mafarki,wlh ina matukar kaunarka.idan bakai bazan iya rayuwa ba pls ka cikamin burina my blue eyes

Aziza dake faman sharar bacci tashi tayi taja tsaki tace" nifa minal kina damuna,da wannan banzan mafarkinki,haba dan Allah akanki akafara soyayya mutumin ma dabaki taba ganiba amafarki kika ganshi,dan Allah kiyi mana shiru ko kuma inje inkira umma



Rufe baki minal tayi tana kuka mai tsuma zuciya tace yar uwata bazaki gane son danakewa mahaukacin masoyinnan bane,wallahi inna hadu dashi agaske wallahi kinji na rantse da Allah ko ya yake saina auresa



Razane ido aziza tayi tace yar uwa kina da hankali kuwa lalle kuwa zaki dakko ruwan dafa kanki ba kadan ba iye lalle ma,kinga kwanciyata saida safe

Minal ta doshi hanyar waje ta dauki ruwa a buta tadauki buta tayi alwala tazo tafara nafilfila tana rokan Allah ya bayyana mata mahaukacin masoyinta,



;::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Washe gari,gidansu minal ko sanwar abinci babu, kanwarsu auta da yake bata jure yunwa yarinyar shekara hudu,sai kuka take tana,wayyo cikina,zan mutu yunwa nakeji, umma ki taimakeni

Minal uwar tausayi ta fashe da kuka,ta kalli umma datayi tagumi tace umma yazamuyi ne,nifa nafi tausayin auta,kuma kinga tanada sickler karya tashi wlh ina tsoro



Umma cikin taurin zuciya tace to minal yakikeson inyi mukune,saidai inzakije gidansu hasiya wajen baffa ki tambayo mana kudin gadonmu wanda yace zai yi mana jari dashi ,in sunki subada sai mu barsu da Allah, dama mun dade muna hakuri


Hawaye yafara kwaranya a idonuwan aziza tace a a umma abarsu kawai,Meye gado,mutum ma yana mutuwa yana barin duniyar balle gado,ai kayan duniya na shedanne?a tsirara mukazo a tsirara zamu koma meye zai damemu,Allah zai sakamana kawai abar maganar gadonnan


Idon autane ya fara kakkafewa da sandarewa.

Minal ta rungumo auta tana ihun auta auta karkiyimin haka,umma mutafi asibiti,



Saka hijjabi minal tayi ta fita dagudu kan titi tana rungume da Auta da numfashinta yake sama sama,

Su umma ne suka rufa mata baya

Adaidaitasau suka tara suka shiga,nasarawa hospital suka nufa,sunashiga aka karbi auta aka shiga dakin emergency da ita.



Likitane ya kira minal yana lashe baki,umma zata bishi yace a a umma ita kadai nace zatayi signing a office dina


Aziza tace anya umma anya likitannan akwai Allah a lamarinsa ,daga ganinsa dan iskane jibifa wai minal ce kadai zata bishi office



Umma tace kul kidaina fadin zarcenan,ai Allah yana tare damu, Allah ba azzalumin bawansa bane




Minal tsayawa tayi acikin office din,



Kanne ido likitan yayi yace baiwar Allah kizauna mana


A tsorace minal ta zauna,tana kallon kyakyawan likitan,matashi tace ina
...kwana



Murmushi yamata lfy matsowa kusa da ita yayi har suna iya gogon juna,minal a tsorace tace pls yallabai kaban takardan dazanyi signing mana,



Lashe lebe ya tashi kamar zaije ya dakko takardan ,bayan minal yabi ya dafata,yana fadin gaskiya kin burgeni



Kuka tafara rusawa tana dan Allah likita banson irin wannan kuda aka sanku da taimakon al,umma, kaji tsoran Allah


Kokarin sa bakinsa yake abakin minal,yana zura hannu a hijjabinta,kuka minal tasa;tayi iya karfinta ta hankadasa gefe,tafita da gudu




Karo sukaci da aziza,da take faman sharbar kuka tace kema minal yanaga kina kuka likitan ya gaya miki auta ta rigamu gidan gaskiyane?



Cikin mamaki,minal ta kalli aziza tace da gaske,auta ta ta tafi,

Aziza tace tabbas ta mutu saidai hakuri,yanzuma gawarta zamu dauka mu koma dashi



Kukan zuci minal take tana mudai haka rayuwarmu zai kasance ina umma



Jawo hannunta aziza tayi tace tana dakin da gawar auta take,bata wani tashi hankalintaba,Allah ne ya daukewa auta karshen wahalarta naciwon sickler dinnan




Minal kukanta yafito fili dataga wannan likitan kamar mutumin kirki yanata bawa umma baki,
Mamaki ya cika minal to tawani kofa yashigo,har ya iso dakinnan




Yana ganin su minal ya kallesu da alaman tausayi a fuskarsa yace sannu yanmata sai hakuri,zaro dubu goma yayi yabasu yace gashi wannan asiya abin sadaka.

Aziza uwar son kudi ta kawo hannu da niyar ansa,minal ta amshe ta watsawa likitan kudin a fuskarsa tace munafukin Allah bama bukatar kudinka,meyasa tun wuri baku taimaki rayuwar yan uwataba sai yanzu zaka taimakemu, kaji tsoran Allah kuma ka tuna zaka mutu


Ji tayi an bata mari tas,batason lokacin da ajijiya ya kamataba tafada jikin likitan da tafi tsana aduniya


Taku kulllum
Maryam yarmama
[11/03 11:44 am] salmah💍💍: *🦁MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*02
By
Maryam yarmama
Dedicated to
All my fans



_wannan shafin nakine *aunty yar mitsila* saboda kaunar da kikewa littafina,kina karamin karfin gwiwa,you are in tha part of my heart,i wish you more happiness and beautiful life and age_





Umma ce cikin kunar rai tace ke tsabar ke shedan ce ammana kyauta kinki ansa,to kisani gidanmu bada halinnan muka tashiba,har Mahaifinki ya koma ga mahallacinsa kullum mutane kyakyawar sheda akemai,



Tashi minal tayi ta durkusa agaban umma tace umma ki share hawayenki indai akaina ne bazaki sake kukaba,zakiyi alfahari dani,zanyu biyayya agareki har karshen rayuwata,ta kalli likita tace kayi hakuri mungode da kyautar da kamana


Likita safwan nan yaji yarinyar kaunarta ya kara dilmuwa azuciyarshi yaji gaskiya bazai iya rabuwa da itaba,yace bakomai muje insa a saukeku agida


Umma tace haba dannan kai da wahala haka ashe kanada kirki haka,
Minal azuciyarta tace,tab umma dakinsan me yake shirin yiminba, Amma dai koma menene




Haka suka fito daga asibitin suna kuka,safwan ya bude musu bayan haddaden motarsa,umma da aziza suka shiga,har minal zata shiga umma tace a a minal kishiga gaba,mana,nan yayi kadan kuma ga gawar auta

Minal tanajin an ambaci gawar auta ta rushe da kuka tana ashe dagaske auta ta mutu


Safwan ya kalleta da idonsa mai narkar da yanmata yace yanmata kishiga mana sai hakuri wanda ya mutu ya riga yamutu,sai hakuri


Takasan ido,minal ta gallamai harara tace ina ruwanka da kukana,kallon kafanta tayi sai yanzu ta lura kafarta ba takalmi,buzu buzu yake,kunyane yakamata tashiga motar shima safwan yashiga yana tukawa a sannu a hankali,yana satar,kallon kyakyawar fuskar minal daya rine da hawaye

Jin kukanta yake har ransa,amma ba yanda zaiyi yahanata, yarinya mai tsoran Allah haka


Minal kallon titi take,gano wani kyakyawan mahaukacin masoyin datake mafarki tagani,gashinsa yayi luf luf kamar ns indi,a ga idonsa dara dara,yana dauke da faffadar kirji,dogo;fari kal dashi,ga hanci har baka,amma kash daga ganinsa bashi da hankali,kai duk inda ake neman namiji,in aka cire safwan to mahaukacin masoyi yakai,domin safwan ba baya bane awajen kyauba.


Kara minal tasa tace likita ka tsaya ka tsaya dan Allah,naga wani abun dana dade ina muradi da nema


Cin burki safwan yayi,da gudu minal ta bude murfin mota,ta duba hagu da dama sama da kasa bataga abin sontaba,hawayene ya fara shatata a idonta,ta dawo cikin mota jiki asanyaye

Umma dake bayan mota takalli aziza tace wai meye minal ta tsayar da motane?

Aziza tace oho ita zataki tambaya,don inaga minal takusa zaucewa
Umma tace Allah ya kyauta


;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;,;;;;,,,;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;



A kofar gidansu minal likita safwan ya tsayar da motarsa,yana kallon rubabben gidansu cikin tausayawa da jimami,duk gidan ne yafi kowa muni a layin gabaki daya,


Bude musu motar yayi,ummi suka gani a tsaye a kofar kyakyawan gidansu,tana ganinsu ta fara murmushin jin dadin ganinsu minal ta taho,ta dafa minal tace besty nashiga gidanku naga shiru lfy



Fashewa da kuka minal tayi,ta fara nunawa ummi gawar auta tana ihu da kukan auta ta mutu auta tabarmu aduniyar nan mai cike da wahala da kuncin rayuwa

Salati da ihu ummi ta zunduma ta nufi wajen umma dake rike da gawan auta,jijjiga auta take tana auta auta abokiyar kowa,auta akwai ki dashiga rai meyasa kika barmu innalillahi wa,innahilaihi raji,un

Makotane sukafara fitowa wasu nakukan rashin auta,wanda duk cikin yayan umma tafi shiga rai,da son wasa,kowa natane


Haka akafara zaman makoki

Umma da takejan chasbahana tacewa aziza taje gidansu abba ta gayamai rasuwarnan tunda yanzu shine uba,

Safwan sai hidima yake,komai shi yayi agidan mutuwarnan


Can anjima saiga aziza tashigo gidan da kuka tafada jikin umma tace umma wallahi ba Allah a zuciyar abbansu hasiya,haka yace bashi ya kashetaba balle yaxo,indai don abin sadakane wai saidai mu mutu bamuyi sadakarba,wai ahaka zamu kare ba rayuwar kwanciyar hankali


Yan gidan mutuwa suka fara jimami suna ta Allah ba tasaba saidaishi ya mutu badai kuba



Haka aka share zaman makoki ,komai safwan ne yakeyi,ya canja kamannin gidansu umma,an mai gini mai kyau,ya zuba kujeru da fridge,da t.v da jennareto,yacika store da abinci da komai.

Umma sai shimai albarka take,minal ko ajikinta ta tsani safwan,itadai burinta ta karacin karo da mahaukacin masoyinta


Abbane kanin babansu ya tako gidan ranar yazo da rashin mutuncinsa,yaga gida yayi kyau,nan ranshi ya sosu yace lallema matar nan,tafara tura yayanta duniyar karuwanci kenan



Shiga gidan yayi ba sallama,...


Read / Download MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album