Join Our WhatsApp Group

BUDURWAR SIRRI Complete Hausa Novel Document by BUDURWAR SIRRI


BUDURWAR SIRRI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17994



BUDURWAR SIRRI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Shuraihu Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 100.12 kb

File Type: txt

Views: 919+

Download: 256+

Last download: 5 days ago

Description/Story: BUDURWAN SIRRI
Littafin Shuraih Usman
Ebook created by Shuraih Usman
Ebook publish by http://hausaebooks.cf
Publish date: 2018 at www.hausaebooks.cf

BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 1
.
Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba
.
Na fito daga gida ina sauri zan karasa wajen wani abokina domin na karbi wayata , nan na tsaya a bakin hanya ina neman lift, ban dade da tsayawa ba kuwa na samu wani dan anguwarmu yazo wucewa na tsayar da shi
.
"Abasu kala, dan Allah kabani wayana mana ya kanamin irin haka ne kaifa kasan in babu wannan waya toh fa abubuwa da yawa zasu rikirkice domin kuwa akwai document dina da yawa aciki
.
Kuma mutae da yawa suna jirana"
Na fada a lokacin dana ke tsaye a shagon su umar
shagon hada takalmane wanda wani dan cirani yazo ya bude cikin ikon Allah sai kuwa jama'a sukai ta saka yaransu cikin wannan shagon har takai yanzu wannan shago ta shahara wajen hada takalma
.
Umar wanda fuskarsa ya baci da dusar takalmi ya dubeni yace cikin muryar wasa " 99% wallahi wayanka tana gida , kuma yanzu dai kaga ina gugan takalma ne , babu yadda zanyi na saki gugan nan na je gida yanzu"
.
Kwafa kawai nayi cikin bacin rai na fice daga shagon sannan nayi natafiyata , don kuwa ba karamin haushi yabani ba,
Nan na tuna yadda ya dauki wayar ina barci da safe , inda idanuwana biyu ne a lokacin toh da babu abunda zaisa na barshi ya dauki wayar
.
Gida na nufa cikin takaici da jimamin wannan abu da umar yayi mani, kamar daga sama sai naji wata zazzakan murya tana kiran sunana
"Shuraih shuraih!! Shuraih!!!"
.
Cikin sauri na juyo don naga wacce take kirana amma cikin mamaki da zunzurutun al'ajabi sai banga kowa ba hakan ba karamin kidimani yayi ba amma sai na dauka tamkar kunnena ke yaudarana
.
Hakan na cigaba da tafiya ina isowa gida na wuce zuwa daki na , ina shiga naje na kwanta don kuwa yanzu lokacin hutu ne babu abun da nakeyi agida hakan yasa na ke dan rubutu da gajerun labarai na littatafan hausa na ringa post na su a social media,
.
Toh gashi dan iskannan ya dauke wayar kuma ya hanani,sai yawo da hankali yake yimini,kwanciya nayi bisa wata lallausar kujera dake girke a dakina, nan na kumshe idanuwa na domin kuwa barci nake bukata da nayi
. . . . . . .
.
"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UNN"
Na fada alokacin dana farka na tsinci kaina cikin dokar daji babu gida baya babu gida gaba,
.
Na mike tsaye cikin tu'ajjibin wannan lamari ina mai tsananin mamaki da Al'ajabi don a tunani na ma mutuwa nayi,
.
Toh amma da mutuwa nayi ai dole, naga mala'iku hakan ya tabbatar mani. Ba mutuwa nayi ba ,
.
Tayaya ni da na kwanta acikin dakina bisa kan shimfidata sannan na farka na ganni cikin dokar daji ai dole wannan abu ya rikita ni,
.
Babu abunda ya sake rikitani game da wannan daji face gani danayi wannan dajin sam bai yi kama da irin dajin dana saba gani ba,
Don kuwa yanayin irin wannan daji a talabijin na saba gani cikin finanan kasashen waje
.
Ni shuraihu inkiya 99% sai dana firgita ainun da yanayin wannan daji na nemi waje na zauna ina ta tunani kala kala acikin zuciyata, can sai nayi karfin hali na tashi na tunkari gabas donni a tunanina, wai kodai barayi suka shigo gidanmu suka kamani suka zo suka ajjiye anan,
.
Sai wata zuciyar tace dani yo imma barayinne suka kama ni mene ne dalilin da yasanya suka kawoni wannan waje, nan dai na cigaba da tafiya ina ganin ababen mamaki, dogayen bishiyoyine suka cika wannan daji bishiyoyin kuma zaka gansu sai kamshi suke tamkar itatunan sandal,
.
Su kansu ganyayen wannan bishiyoyin korayene ababen sha'awa, sannan kasan wannan daji wasu irin ciyayi ne wayanda ban taba ganinsu ba , su wayannan ciyayi sun kasance jajaye, kuma koda na taka su sun durkushe take zasu sake dagowa
.
Koda na kara gaba sai na hadu da wani abun mamaki wanda yai matukar tayarmun da hankali
Ba komaine na gani ba illa wata korama, wadda ruwanta yake zubowa daga saman wani katon dutse , shi wannan korama ruwansa garai garai ne dun kuwa koda na matso kusa da ruwan sai na ga hoton fuskata ya bayyana acikin ruwan tamkar an dauki hotona ne aka manna ajikin ruwan
.
Tsaban tashin hankalin dana tsinci akaina aciki a wannan lokacin yasa na kurma ihu, domin kuwa dauka nayi ko mafarki nake hakan yasa na cizi hannuna, a bisa mamaki sai naji zafi ya ziyarci hannanuna hakan ya tabbatar mani da cewa ba mafarki nake ba
.
Irin wannan koramar sam babu shi a kasar hausa, kuma na riga dana san a irin garuruwan da ake samun wayannan koramun, don kuwa na kanga hotunansu a jikin gorunan swan water da talabijin
.
Motsi naji daga bayana hakan ya tabbatar mani da a akwai wani halitta a bayana koda na waiga sai naga daga cikin wani surkukin ciyayi mitsin yake fitowa, nadai takure na matse sannan nayi na maza na daure don ganin mene ne ya ke fitowan
.
Abubuwan dana ga suna fitowa daga cikin wannan surkuki su suka saka naji cikina ya tsure, idan da ba dun ina da karfin haliba toh da babu abunda zai hana ban saki gudawa a wandona ba, amma duk da haka sai dana tsiyayo fitsari wanda ni ban ma san na tsiyayo ba
.
.
Kai friends ku taimaka ina cikin firgici
Shin ko kunsan mena gani alokacin toh ku jirani sati mai zuwa a cigaban wannan labari wanda zai runga zuwa maku duk sati Ranar Asabar da safe tare dani Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%
.
Wannan kirkirarren labarine daga 99%
Ku tsumayeni a page 2
Daga:- hausaebooks wepsite
Da keffians News Teller
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 2
.
Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin na batare da iznin wannan shafi ba
.
Ba komai nagani ba face namun daji danginsu su Alfadari, Giwa, barewa,Zaki,maciji,damisa,kura kai duk dai wani dabba da kuka san yana rayuwa acikin daji, cikin gungunsu suka nufo ni ai koda ganin haka sai na juya da nufin na fada cikin wannan kogi dayake gabana
.
Amma me zan gani wasu kyawawan kananan kifaye na gani masu zakwa zakwan hakora lokaci lokaci zakaga suna kikkirta hakwaransu, abun yabani mamaki wai ace kifaye da hakwara amma sai na tuna wani american film din dana kalla mai suna PIRANHA
.
Koda naga haka sai nayi wani gefe da gudu don na tsere ma wayannan dabbobi da suka biyo ni da mugun nufi, gudu nake iya karfina don na ceci rayuwata daga hannanun wayannan dabbobin sai dana kai wajen mintin arba'in ina tsala gudu acikin wannan jeji amma wayannan dabbobin sai bina suke duk inda na shige, abunda zai baka mamaki da wayannan dabbobin shine
.
Su ba gudu suke ba don kuwa tafiya suke amma yadda kasan suna gudu domin kuwa duk lokacin dana waigo yayinda nake tsala gudu sai na hango su a kusa dani,
Acikin wannan gudun danake yine, nazo gaban wani katon kogon dutse, batare da wani nazari ko shawaraba na afka cikin wannan kogon,
.
Ai koda shigata cikin kogon sai wani narkeken dutse ya mirgino da kanshi ya kulle bakin kogon ta yadda ko digon haske baya iya shigowa cikin wannan kogo,
.
Take duhu mai tsanani ya mamaye wannan kogon don kuwa ko tafin hannuna bana iya gani nan nacigaba da karanto addu'o'I kala kala duk wacce tazo bakina karantawa nake, har saida na karance gabadayan addu'o'in dana iya haka na runga jawo ayoyin kur'ani maigirma har zuwa wani dan lokaci
.
Koda naga an dauki dan lokaci banga komai ya faru ba sai na dan fara tafiya amma bakina babu abun daya ke furtawa face karatun kur'ani,
.
Tafiya nake ban san inda nake nufa ba, nidai nasan ina tafiya domin kuwa duhun daya mamaye wannan kogo baya bari naga maine ne agabana, na tsinci kaina tamkar wani makaho
.
Ni dai babu abunda nake furtawa face karatun kur'ani mai girma, koda na cigaba da tafiya acikin wannan kogon ina cin karo da duwatsu akalla na fadi yafi sau goma
.
Don kawai sai ina kan tafiya sai naji nayi karo da dutsi take zakaga na fadi gefe, a haka sai da hannuna na dama ya samu targade,
Kukan zuci nake sosai ina tunanin lokacin da akeyimana wa'azi a islamiya zaka ji ana cemana muyi aiki mai kyau don kuwa akwai lokacin da mutuwa zata riskemu,
.
Sam sam bana son na mutu yanzu amma kuma gani nake tamkar tsakanina da mutuwata banfi zira'I daya ba zuciyata tana ta karantomin abubuwa da yawa na cutarwa da ka iya wanzuwa a cikin wannan kogon
.
ni ma'abocin karanta littatafan yakine nasha jin labarin yadda kogo take, kuma a yadda naga dutsin nan ya mirgino da kanshi yazo ya rufe kofar fita daga wannan kogo hakan ya tabbatar mani da cewa wannan al'amari akwai TSAFI acikin sa
.
Amma haka na dake na cigaba da addu'a da karatun kur'ani a zuciyana, kai in takai takawo ma har hadisai ma karantowa nake
.
Haka na kasance a cikin wannan kogon har na tsawon wajen sa'a daya wato awa daya sannan na fara tafiya, babu abunda yake zuwa zuciyana face tunanin ALJANNU
.
Don nasan inba lamari na Aljani ba babu ta yadda za'ayi na kwanta a gida cikin dakina bisa kujera mai laushi sannan na farka na ganni cikin kungurmin daji sannan ga wasu halittu na neman su halakani
.
Haka naci gaba da tafiya kwatsam ba zato ba tsammani sai cikin kogonnan ya gauraye da wani haske wanda koda Allura ne yafadi akasa toh za'a iya ganinsa
.
Hamdala nayi sannnan na gode ma Allah daya rabani da sharrin Duhu ya Allah karemu daga sharrin DUHU,
.
Toh sai a sannan naga ashema kogon nan cikinsa tamkar wani gidan hamshakin attajiri ne ko kuma mashahurin sarki , domin kuwa ganin kogon nayi a kawace da tsarin gida,
.
Shi dai wannan kogo dana afka sam daga ciki baiyi kama da kogo ba sai dai akirashi da fada domin kuwa wani kayataccen fada ne a ciki, nan na zama dan kallo nama daina mamakin yadda akayi na zo wannan daji na koma mamakin wannan fadar wanda tafi min kama da ALjannar duniya, sai a sannan ne na lura da komai dake cikin fadar fadan ya kawatu iya kawatuwa don kuwa tun da nake a duniya ban taba ganin wani fadan dayai rabin wannan kawatuwa,
.
Duk da na kasance masoyin kallon fina finan kasa shen waje irin na su yaki, toh ko a fina finan ban taba ganin irin wannan fada ba
.
Babbar fadace katuwa wacce zata iyacin wani karamin gari akarshen fadar wata kujerace ta zinare a girke wannan kujerar an kawata ta ainun don kuwa wasu irin takubba masu tsananin walkiya da kashe idanuwa aka sossoka su ajikin kujerar
.
A saitin kujerar daga gaba wata shimfida na gani itama kalarta kalar zinari an shimfidata takai har karken fadar, kai nan dai na tsaya ina ta kalle kalle ,
.
Wani abun mamakin kuwa shine babu kowa acikin wannan fada sannan kuma ga a kowanne kusurwa na fadar an ajjiye wasu irin gumaka masu siffar mutane cikin shigan yaki,
Koda na kare masu kallo dakyau sai na gane ashe wayannan kaman sojoji suke,
.
Nayi ta yawata wa acikin fadar har kafafuwana suka fara kuka, nan na zube kasa ina mai dafe da kafafuwana, sai a sannan idanuwa na suka kai ga wata, kofa wacce sam ban lura da ita ba yayin dana shigo cikin wannan fada,
.
Koda na ga haka sai na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!!
.
Zazzakar muryace ta biyo baya "shuraih! Shuraih!! Shuraih!!!
.
SHIN A TUNANIN KU wai me nai arba da shine da har na rikice haka
BUDURWAN SIRRI
Gajeran labari
Marubuci Shuraih Usman
@hausaebooks.cf
@shuraih 99%
Page 3
.
Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin nan batare da iznin wannan shafi ba karkashin jagorancin Shuraih Usman
.

na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!!
.
Ba komai nai arba da shi ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa wacce saboda tsananin kyawunta ne nama kasa sarrafa kaina,
.
TABA RAKALLAHU AHSANUL KHALIQEEN, lallai Allah yayi halitta , ita dai wannan kyakkyawar mace wacce ta kasance bantaba ganin ta ba sai ayau, shekarunta ba za su wuce goma sha tara ba, tsananin tsabar kyawunta nema yasa har wasu dausayin fararen haskene ke bibiye da ita,
.
Na tabbata ko da cikin duhu ne mai tsanani wannan budurwa ta miko hannunta toh take duhun zai bace haske ya maye gurbinsa,
"Shuraih! "
Zazzakar muryarta wadda tafi na komai dadi aduniya ta katse mani tunanina , a irin salon yadda take kiran suna na, ji nake babu wanda ya iya kiran suna na face ita, koda wannan zazzakar muryar tata kawai mutum zai saurara toh da sai ya gwammaci ya saurara fiye da abashi kyautar makudan dukiya
.
Firgigit na dawo cikin hayyacina tamkar wanda ya farka daga barci na dubeta baki na sai kakkarwa yake amma na kasa fadan komai dakyar da sidin goshi na iya fadin "nnnna - m"
.
Murmushi tayi wanda ya kusa zautar dani don kuwa alokacin da gefen kuncinta suka lotse sai naga tama fi kyawu bisa kan da,
.
Koda taga halinda na shiga adalilin wannan murmushinn da tayi sai ta kyalkyale da dariya, ai saboda dadin sautin wannan dariya nata ban san lokacin dana sulale a kasa sumamme ba,
Iya abin da masarrafin kwalkwata ya iya dauka shine daukewar dariyar wannan budurwa daga nan kuma ban sake sanin meke faruwa ba
***
.
A hankali nafara bude idanuwana, mutane ne nafara ganinsu dishi dishi akaina, na mike na zauna sai a sannan ne...


Read / Download BUDURWAR SIRRI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album