Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

RUBUTACCIYAR QADDARAH Complete Hausa Novel Document by RUBUTACCIYAR QADDARAH


RUBUTACCIYAR QADDARAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 141438



RUBUTACCIYAR QADDARAH

Reading Time: 11 Hours

Added On: 14, Nov 2024

Author: Maryamah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 758.26 kb

File Type: txt

Views: 1265+

Download: 3076+

Last download: 3 days ago

Description/Story:
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
*By Maryamah* ๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
ยฉ2020

PAGE 01
Qarar wayarta ceta ta yarda ita daga daddadan baccin safen da ta koma tunbayan data idar da sallar asubah. Idonta arufe ta laluba bedside drower din tareda daukan wayan, akunnenta kawai tasaka Kaman yanda tayi tunani muryar kawarta taji Afeeya. Cike da karadi take cewa "ah this girl so u dey even sleep u forget say na Guru lecture we get today koh?" ae tun Afeeya bata karasaba tai tsalle ta diro daga kan gadon tareda kallon agogo.9:10am yanuna lecture dazasu shiga 10:00am sanin halin Guru Kaman yanda suke kiran lecturan medaukansu Biol315 dabaya tolerating late coming koda karin minti daya yasa dasauri sauri tai wanka kasancewarta ba ma'abociyar kwalliya ba yasa doguwar riga kadai ta zira tareda daukan jakanta tayi waje bata ko saurari Mama Uwani daketa faman kwala mata kira Akan ta tsaya ko Tea ne tasha tayi waje.
Kiris ya rage ta fasa kuka ganin parking space din babu ko mota daya. Se alokacin ta tunada motarta na wurin gyara sannan kowa na gidan yafita bata da zabi illa ta taka da kafa zuwa titi ko Allah zesa ta samu abin hawa. Tafiya kawai takeyi tanajin wayarta na kara alaman kira Amma taki kulata abin haushi har seda tazo kabuga daga cikin unguwar tasu ta Tudun yola sannan tasamu adaidaita sahu. BUK old site yakaita, Sanda ta isa kofar Lecture Hall din a gajiye take liqis, tsayawa tayi sannan ta duba agogon wayarta karfe 10:20am ta gani ido ta zaro dan ko giyar wake tasha bata isa ta ratsa masa class ba, rashin mafita ya sakata kawai ta nemi guri akan varander dake wurin ta zauna tana sauraron yanda yake gabatar da lecture din tashi cikeda kwarewa dasanin abinda yakeyi. Tabbas ya amsa sunan nasa na Guru Dan da ka yake bada lecture batareda ya duba littafi ba haka idan yana dictation baya manta ko full stop akan abinda yafada. Tayi nisa cikin tunanin tajiyo muryarsa yana fadin "Tear a sheet of paper and write your name".
Ko ba afadaba tasan short gun zebayar nan sauran daliban yan uwanta da suka yi latti suka hau hayaniya suna fadin "we are sorry sir" Dan sunsan tabbas inhar akayi test dinnan babu kae tokuwa rubutacciyar carryover ce Dan shi baya fixing date na test haka in kayi missing baya make up . Banzan kallon daya watsa musune yasasu yin shirun dole se asannan idonsa ya sauka akanta, hankaki kwance tana danna wayarta kamar ma batasan abinda yake faruwa ba. Murmushin da iyakarsa lebe yayi Idonsa still akan ta yafurta "You can come in but indicate on ur papers as late comers I'm going to subtract 5 marks from ur score" dasauri suka ringa shiga dukda sunsan balallai suyi wani abin kirkiba Dan inkai missing lecture dinsa sau daya ba lallai kagane class din gaba ba.
Yi tayi Kaman bata batajiba seda wata yarinya dake kusada ita ta kara maimaita mata dacewa "kitashi tun bechanza ra'ayiba". Tura bakinta daya zame mata dabi'a tayi tana kunkuni tareda harar Afeeya dake mata dariya kasa kasa sannan ta shiga, duk abinda takeyi akan idon Guru Dan murmushi kawai yayi Sannan yashiga dictating musu test question din daya basu minti 20 kachal. Kamar yanda ka'idar sa take kuwa ko minti daya be kara musuba ya tattara takaddunsa yayi waje dan shi haka yake baya shiga lokacin wani shima ba'a shigar masa nasa.
Bayan da suka fito Afeeya na mata tsiyar wae me ta tsaya yi harta makara yanzu da bebarsu sun shigaba yaya kenan, ita dae bata tankataba har suka shiga wata lecture. Kasancewar chain classes ne dasu yasaka basu samu break ba se karfe daya. Suna zaune a cafteria suna cin abinci ita Afeeya, Maryam se Aysha,hira sukeyi jefi jefi har ta gama, ganin basu gama ba kuma da dan sauran lokaci ya sakata ciro wayarta dake cikin jaka tafara duba missed calls din kai murmushi tayi ganin kiran sahibinta har 5 missed call batareda bata lokaciba tae dialing number kaman dama yana jiranta yae saurin katsewa ya kirata.
" HAMDAH" ya kira sunanta cikin wata irin murya datake sakata manta kowanne saurayi inbashiba."na'am ABDUL" ta amsa masa.
"I missed you so badly babe wallahi i feel like flaying to Nigeria to come and see that beautiful face of yours". wani killer smile ta saki kamar yana gabanta tareda cewa "I missed you too My Jaan can't wait to see you". Tuni ta manta da wanzuwar su Aysha dake kallonta, ko ba'a fada ba sunsan Abdulmalik ne Dan aduniya in kanaso kaga fara'ar HAMDAH to kakira sunan ABDULMALIK.
Abin har mamaki yake basu insuka tuna haduwar HAMDAH da ABDULMALIK din lokacin suna 100l alokacin shikuma yana service dinsa a Chemical engineering department nan BUK. Ba irin wulakancin da beganiba a wurin HAMDAH Amma ya jure Dan acewarsa samun mace kamarta she an sha wahala. Naci da kuma iya soyayyah irin nasa ne ya ribato masa zuciyarta dukda daga baya sun yita samun sabani lokacin data fuskanci tarin yammata daya ke dasu, hakan ba wani Abu bane musamman awurin samari irin Abdulmalik da ya mallaki abubuwa da damage inkayi la'akari da kyau, gayu, ilimi ga uwa uba kuma kudi daya ke dashi Dan haka mata kebinsa ako ina.
A haka dae sukayi sabo tun abin yana kamar wasa harya zama da gaske yakeyi dan zancen Abdulmalik a wurin Hamdah hatta dame bawa flowers ruwa a gidansu ya sanshi. "To Juliet se kitashi mu tafi in kuma anan zakiyi taki lecture din se mu barki muyi gaba". Seda ta hararesu sannan sukayi sallama tana ta zuba masa shagwabarta dake kara masa sonta, se wurin karfe biyar suka tashi gaba daya sukae sallama inda suka fita tareda Maryam daya ke unguwar su daya.
A Get 4 sukayi sallama da Maryam din tashiga gida. Tun daga get take aikawa Khaleefa kaninta da sakon harara dan shi yaja Mata da motarta na nan da duk bata makara har hakaba. "Yi hakuri auntyna wallahi tun 7am nake gurin mechanic dinnan ashe beyiba seda na tasashi agaba tukunna". Se kuma tadan saki fusaka ganin motar tata fes Dan har wankewa yasa akayi "Allah ya taimakeka dayau nida Kaine agidannan" ta fada tana cilla masa bandir na 100N,cafkewa yayi Dan yasan metake nufi tareda cewa "Se Aunty Allah yasa kifi haka "murmushi tayi tareda amsawa da "Amin" takarasa cikin palour.
Zaune ta tarar da mahaifiyarsu wadda base angaya makaba saboda tsananin kama da sukayi, kwalliya tayi ta alfarma cikin wani danyan Boyel dayasha stone work me kyau da tsari yayinda palour ya bade da kanshin turarenta da kuma air freshener da akasaka. "Se Mumcy duk wannan kwalliyar taron Abbah ce haka" cikin sigar tsokana tayi maganar.
"Ungo wannan ja'ira wato kun mayarda ni kamar kakarku ko yanzu su khaleefa suka gama shine kema zaki dora naki". Seda ta kwankwadi ruwan da kareema me aikinsu tamiko mata kafin tace "Ai Mummy kwalliyar yau dince tafi takullum wae duk dan ki hana Abbah karo mana Aunty to tunda tsoranki yakeyi bari muzamu hada kae munemo masa sedai kiji yan kawo Amarya". Pillow dake gefenta ta chilla mata tana cewa "Dan gidanku sedai Abdilmalik yai miki badai Abbah ba nikadice ba kari" dariya ragowar yan uwannata ke kwasa Dan dramer mummy da Hamdah ba fashi kullum se anyi.
Seda tayi sallar magriba sannan ta suko kasan ta tarar da gaba daya yan gidannasu a palour in kacire Anty Zahra datayi aure da Yaya Abubakar da ke aiki a Lagos. Kallonsu tayi tsaf sannan tace"Tab lallai Abbah anmaka wayo kalli wadannan zaratan samarin Duk yayan tane Amma taringa kwaskwarima da powder Duk dan karkaga ta tsufa kayo Amarya".
Harararta Mumcy tayi sannan tace "Wlh Hamdah zanci gidanku haka kawai zakibi kidamu mutane" ta hade rae.kallonta Abbah yayi yaga yanda ta kule yai murmushi yace "Haba An Maririna aikinsan kekadaice ki kyale Hamdah" she a sannan ta saki ranta Dan tasan tsakanin Hamdah da Abbah tana iya sakashi yayi auran ma kuma yayi.
Cin abincinsu sukeyi cike da kauna sam babu wani takura a tsarin rayuwarsu inkaga yanda iyayen ke wasa da yayansu haka babba da karami Amma kuma hakan besa wani ya raina nagaba dashiba komai nasu yanada limit.
Zuri'ar Professor Ahmad Muhammad Ammani kenan da Dr Maryam Aliyu yola. Aurene na soyayya tsakanin jikakken Dan Bokon dakuma farar bafillatanar ta yola, sun hadune lokacin da aka turashi bautar kasa Yola yana koyarwa a makarantarsu har Allah ya kaddarah aure a tsakaninsu alokacin Maryam din nada shekaru 13 ya taho da ita nan kano inda iyayensa suke. Auransu ba dadewa suka koma kasar Germany dazama inda yaci gaba da karatunsa na Masters asannane kuma tayi Haihuwar farko ta haifi Yah
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download RUBUTACCIYAR QADDARAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album