Join Our WhatsApp Group

GOJE Complete Hausa Novel Document by GOJE


GOJE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 44971GOJE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 15, May 2024

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 07084653262

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 254.2 kb

File Type: txt

Views: 156+

Download: 167+

Last download: 25 minutes ago

Description/Story: [3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE
*3&4*
Tuntun'be tayi da wani girkakken icce tayi mummunar faduwa kanta ya bugu da tsinin iccen, lokaci guda jini ya fara tsartuwa, hannu tasa ta dafe gurin, murya ta bud'e sosai ta kwarma ihu! wanda ya tashi dabbobin dake dajin. lokaci guda suka fara koke-koke, wasu daga ciki har sun fara fitowa daga ramukansu.

Hakan ya sanyasu tsayawa a gurin kwakkwaran motsi babu wanda yayi a cikinsu, da ido yayi musu magana cewa suyi lamfu a kada wanda yayi motsi wanda zai dauki hankalin dabbobin da suka fara fitowa, hakan sukayi, dajin! yayi tsit! sai kukan dabbobin ne kawai ke tashi.

Wani irin juwa da hajijiya ta dinga yi a gurin kafin ta yanke jiki ta fad'i kan ciyayi, jini kuwa duk ya jika mata fuska da gaban rigarta.

Cike da jarumta ya daidaita kwari da bakar dake hannunsa, yanayi yana waiwayen bayansa yana hasashen ta inda wata dabbar zata fito, da baya da baya ya dinga tafiya har ya cimma inda take kwance, yana yunk'urin d'aukarta yaji hucin wucewarsa zurrrrrrr! cikin zafin nama yayi wani irin tsalle ya zaro kaifaffar wukar dake rataye a bayansa ya fille masa kai! tsayin macijin ya kai in taha.!

Fitilar dake hannunsa ya kunna ya haske mata fuska yana kallonta, yayi mamakin yanda akayi ma har ya dawo da baya domin taimaka mata, wai kamarshi, *GOJE!* yarinya 'kank'anuwa irin wannan tayi yunkurin marin fuskarsa.

Tsaki! yaja yana gyada kanshi, da alama hakan ya zame masa jiki, tsumman dake d'aure a k'ugunta ya fizge, ya yagi rabi ya daure mata kan dashi, tsam ya matse jinin ya daina zuba, ya dauketa kacokan ya goya a bayansa yasa tsumman ya daureta, yanayin tafiyarsa sam be sanja ba cike da jarumta yake taka itacuwan gurin tunda ya fahimci a sume take burinshi ya samu inda ruwa yake domin ceton rayuwarta.

Yaran ya kira suka fito, daga mab'oyarsu da yawa daga cikinsu sun farauci k'ananun dabbobi irin wanda suka firfito, ya basu umarnin zuwa su nannad'o macijin da ya sare masa kai, yana gama basu umarni yayi gaba bai tsaya ba har sai da ya cimma inda ruwa yake,
Kwantar da ita yayi kan rairaiyi, yasa hannunsa cikin ruwan yana debowa yana watsa mata a ko'ina na jikinta.

Sai da jikinta ya jike jagab da ruwa sannan Allah ya bata ikon sauke ajiyar zuciya, gashin idonta ya fara motsi tana so ta bude idon amma sunyi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta yake mata, hannu ta dora saman kanta bakinta sai motsi yake, Tashi yayi ya bar gurin.


Ta jima tana ganin dishi-dishi a idonta kafin su bude sosai, da yake garin ya soma haske can nesa ta hangoshi tsaye amma bayanshi kawai take gani, cikin mugun tsamin jiki da azabar qunar data tashi tai jawur! ta mike zaune tana bin ilahirin jikinta da kallo, wasu zafafan hawaye suka kwace mata, lebe ta ciza tana furzar da wani irin huci! wai kamar ita Gimbiya gaba da baya itace a wulakance a yashe a bakin kogi, wani kazami bagidaje yana ganin sassan jikinta, wannan abun yayi mata mugun ciwo a rai.

Yana daga inda yake tsaye ya dinga jin shashshekar kukanta na tashi. Ya juyo tare da da zuba mata jajayen idanuwansa.

Itama shi take kallo tana kisma irin hukuncin da za tayi masa mutukar ya kusanto inda take.

Be saurareta ba, bakin kogin ya nufa ya tsuguna yana daura alwala.

Jin sawun tafiya da haushin karnuka yasa da sauri ta waiwaya, yaran shi ne tare da karnukansu da kuma abunda suka farauto.

Suka samu wani fili suka zube kayansu da yake duk inda zasu shiga sukan tafi da guzurinsu, wata katuwar dadduma suka shimfida, kafin su hura wuta, sannan suka nufi bakin kogin domin daura alwala kamar yanda suka ga ogansu yayi
Shine ya jasu jam'i, duk tana zaune tana kallonsu, suka idar ya daga hannu sama yana addua suna amsawa mamaki sosai ya lullubeta ganin yanda yake azkar masu zafi da adduoin da takasa tantance mai yake fada tunda wasu da labarci yake, tayi mamakin hakan daga gurinsa a ganinta rikakken *d'an daba* *d'an ta'addah!* irinsa bai kamata a samu ilimin addini a tare dashi ba.

A nutse ya juyo yayi wani irin zama tamkar basarake! ya kashingida tare da tankwashe kafa daya ya dogare dayar tare da dora hannunsa akai.

A maimakon musabaha kamar yanda Annabi ya koyar sai kawai suka dinga dukan hannunwasu da sunan gaisuwa a gareshi, wasu daga cikinsu suka fara bushe-bushe irin nasu suka hada baki gurin fadin." *A lafiya Goje!* *Cauuu!!* Uban mafarauta! *Sa'a dai* mai maganin *wuka da kaho* *Dawa dai!! Umarul-Faruku* muna mika gaisuwa a gareka."

Ya dinga girgiza kansa yana jin tsigar jikinsa na wani irin tashi, numfashi ya shiga saukewa yana furzar da wani irin huci, Shisha ya kaiwa raruma yasa a baki ya fara tada hayaki a gurin.

Ganin haka sai suka tashi suka bar gurin, rabuwa sukayi wasu suka fara aikin gashe-gashen irin dabbobin da suke farauto, wasu kuma suka kutsa cikin dajika domin samun abun da zasu ci.

Tana nan zaune a inda take k'aik'ayi duk ya isheta, rana ta kwalle a gurin, so take ta tashi ta sauya guri kunya da tarin takaici sunyi mata dabaibayi, yanda Allah ya taimake ta ma ta lura sam ita din bata gaba gabansu, domin dik wanda yazo wucewa ta kusa da ita ba yayi mata kyakykyawan kallo.

Kafafunta ta motsa, domin mikewa tsaye, aikuwa qunar ta kwaile ta fara fitar da ruwa da jini, tsananin azabar zafi ya sanyata tayi saurin mikar da kafar cikin tsautsayi ta danne kunama! lokacin ta d'ana! wani irin 'kara tayi jikinta ya dinga rawa! da rarrafe ta matsa daga gurin, idonta kan kunamar tana kokarin bin gefen kogin domin shiga wani rami...........Kafarsa yasa ya murjeta! yana cire kafar taga yanda tabi kasa tayi daga-daga a gurin!!

Inuwarsa ta dinga kallo yayi mata rumfa gata tayi goho tamkar mai shirin haihuwa, gabadaya duwawunta a waje wando ne kawai ya taimaketa.

Duk da tana jin tsoron sake zama a gurin hakan nan ta hakura ta zauna jikinta har yanzu rawa yake ga zufa sai ketowa take da sassan jikinta.


Tsugunawa yayi kusa da ita har tana jin hucin numfashinsa, ta kalleshi, beyi aune ba yaji saukar kakkauran yawun bakinta a fuskarsa, yasa hannu ya sharce yawun yana me cigaba da watsa mata kwala-kwalan idanuwansa,


Cikin zafin nama ta ciko hannunta da kasar gurin zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, kasar ta zube a jikinsa, hannu yasa ya buge, ya kalleta fuskarsa a murtuke yace." Meye sunanki a wane gari kike."?

Tana kuka me cike da azabar data rasa wace iri ce tace." Ni kake tambaya garinmu kaje ka daukoni a gaban iyayenta amma saboda rainin hankali kazo kana tambayata."

Ya girgiza kai da fadin." Ni taimaka miki zanyi amma ban san abinda ya shafeki b.........."Karya kake."! ta katse shi da karfin gaske sai huci take! tana jira ya sake wata magana ta kaiwa fuskarsa mari!

Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta, tunda ya taso a lokacin yarinta da girma babu wanda ya ta'ba karyatashi cikin abokai da sauran jama'ar gari sai wannan karamar yarinyar, Sa'arta ta sameshi mai tsananin tausayin mace amma ba don hakaba da yau ta gane kuranta a hannunsa.

Cinyoyinta ya zubawa ido yana kallon yanda qunar ta ruruce! tana ruwa da jini gashi har ta fara cin jikinta, ba tare da tayi aune ba taji saukar hannunsa, fittt ya d'aye fatar data qone! jiki na karkarwa ta rike hannunsa, tana aika masa da Allah ya isa.

Be saurareta ba ya hade duka hannuwanta ya rike da hannunsa daya, ya sake bin d'aya cinyar ya d'aye fatar qunar! kawai sai ta zube a gurin tana makyarkyata.

Tsallaketa yayi yaje ya dauko wata 'yar roba cike da gishiri yazo ya tsuguna yana kokarin bude robar gishirin.
Ta dinga girgiza masa kai tana kokarin tashi zaune, ya mayar da ita ya kwantar, cikin rashin tausayi, ya barbade qunar da gishiri! ya tashi ya bata gurin..........Sandarewa tayi a gurin kamar matacciya yanzu kukan zucci take mai mutukar zafi, tsabar azaba hawaye ya bushe a idonta, yana daga inda yake ya hango yanda ta wargaje a gurin ta daina boye komai, ya bude wata jaka wani yadi mai kauri ya dauko, ya nufeta dashi, bata iya ce masa komai ba tana kallo ya cicibeta ya dora kan zanin ya nannade mata jiki, can inda shimfidar daddumar take ya nufa da ita ya samu gefe guda ya kwantar da ita.
Sannan ya tashi daga gurin, ido kawai ta rufe tana sakin wani irin nishi irin na wahala....


*Ga wa 'yanda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu, wato Sadauki Omar tare da Goje! Sadauki Omar return*


*#500 via......0542382124....Binta Umar gtbank, idan kati zaki turo #600 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262......Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number...... 22796074090*
[3/29, 8:15 AM] Surayya Dee.: *GOJE!*🏹
🐕‍🦺🐕‍🦺🐕‍🦺
_(SADAUKI OMAR RETURN👑💫_)

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION🖊️📚_*
_____________________


FREE PEGE
*1&2*
"A zahiri kamar cikkaken namiji amma abun kunya kamar ka shekara talatin da uku ba aure ace namiji kamarka mara tsoro mafarauci a dajika! amma a gida malalaci gauro tuzuru wanda ya gaza samawa kansa nutsuwa wannan jarumtar taka a banza tunda baka da aure har yanzu baka cika cikakken namiji ba." Wata 'yar tsohuwa ce take wannan maganar,

idona na kai kan wanda takewa surutun ya juya baya jikinsa sanye da kayan farauta ba'kin yadi mai kaurin gaske rigar mai fadi ce iya kafadarsa, ta tsaya iya kacin gwiwarsa sai yayi amfani da wandon jens kafarsa sanye da takalmi mai igiyoyi, bayansa kawai na kalla na gazgata maganar tsohowar, hakika duk inda cikakken namiji yake mai zati da kirar mazantaka to za a sanya guy a ciki dogo ne mai fadin kirji jikinsa a cike a murde babu rama ko ta kwabo a tare dashi, har yanzu be juyo ba da alama akwai abinda yake.

Tsaki taja tace." *UMARU* ina magana amma dai yau a gida zaka kwana ko."?

Ba tare da ya juyo ba yace." A'a bah! zan kwana a gida ba"!! yanayin yanda yake magana a ciccije sai dana tsorata!. sake 'buya nayi ina gyara biro da takardar dake hannuna.

Tace."To koda naji ai gwara dana tambayeka saboda ana magariba zan rufe kofata kaje ka 'karata."

Uffan bece mata ba, na hangoshi yana d'aura wasu tafka-tafkan layu a damtsan hannunsa.

Ya dauki wata hula mai kunnuwa ya kwafa akansa kafin ya juyo, saurin sunkuyar da kaina nayi gabana na dukan uku-uku! yana da manyan idanuwa sosai amma sunyi wani mugun jaa! lebansa bakikirin, alamu sun nuna farin mutum ne amma tsabar busa hayaki gami da shaye-shayen magungunan tauri! fatarshi tayi wata irin dabbara-dabbara!

Kafin nayi aune! naji ya kurma uban ihu! ya dunkule! hannu kafin ya kalli gabas yamma kudu arewa ya fara yiwa kansa kirari kamar haka.

"Nine *Umaru!* Namijin duniya! mai tarwatsa namun daji! Na d'aya 'kwal! a gurin uwa da uba! dubu jiran mutum dubu!! naci uwar d'an iska! naci uwar duk wani dan tauri! Ihuuuu!!! Nine Umaru! wanda wuka komai kaifinta bata ratsani! Nine dai Umaru! mai karnuka dari ba d'aya, mai masoya gabas! yamma! kudu! arewa! An buga an barni! naci dubu sai ceto! nayi tawa nayi ta wasu!! Umaru nake d'aga Tanimu jika gurin Uwale! Idan da wanda yake da yaja ya fito don uwarsa."!!!
Yana maganar yana zazzare ido da ciccije baki sai rarume-rarume yake a dakin. Uwale na ganin ya zaro labceceyar wukar dake rataye a kafadarsa taje gurin tana rirrikeshi, ya tureta gefe, fito da wukar yayi sai sheki take ya fara gurzawa a jikinsa.

Gabadaya jikina in banda kyarma babu abunda yake, yau garin neman labarai na kawo kaina mahallaka, da gudu! na fito daga bayan kyauren nayi waje! ba zan iya ganin wannnan tashin hankalin ba😂

A maimakon na kama hanya na gudu,sai na b'uya a bayan wata bishiya ina jiran fitowarsa, kimanin mintina goma ya fito, kallo guda nai masa na sunkuyar da kaina, gabadaya jikinsa kayan farauta ne, kwari da baka, wukake a soke a kowane sassa na jikinsa. Tirkashi ashirye yake na sheda cewa babana Umaru jarumi ne.

Wani irin fito yayi fit-fit! kawai sai ganin karnunka nayi suna fitowa ta bayan gidan, kafin wasu zaratan matasa kamarsa suka biyo bayan karnukan suna sanye da kwatankwacin kayan dake jikinsa.
Sun kai su goma suka zageyeshi kafin su farayi masa kirari! kamar haka, *GOJE!* jarumi a gida jarumi a waje! *UMARUL-FARUK!* ba ka san wargi ba, baka san tsoro ba! baka san wasa ba! kayi taka kayi ta wasu! Namijin duniya tarwatsa namun daji! *Zaki!* uban mafarauta! kaine jagora *GOJE!* Ja muje! Mudubi mai nuna mana hanya."

Kallonsu kawai yake yana tattauna lebensa kafin ya gyada kansa, A ciccije yace." Zamu kai sati muna gwagwarmaya ina fatan kowa ya sallami iyalinsa."

Suka bashi amsa da fadin "Eh ranka ya dade munyi yanda ka umarcemu."

Hanya kawai ya kama suka rufa masa baya tare da karnukansu dake faman haushi!! duk sun cika unguwar. sawun tafiyarsu kawai kake ji da sautin kukan karnukansu.


A daddaure suka shiga da ita motar suka sanyata a tsakiyarsu, kafin direban ya shiga ya zauna, a gaggauce ya figi motar suka fita daga masarautar, yau suna cikin farin ciki bukatarsu ta biya gurin kidnaping din yarinyar da suke sanya ran samun makudan kudi daga gurin iyayenta.

Wani irin nishi! take gumi duk ya jika mata jiki sun daure mata fuska da kyar take jan numfashi, kawai sai ta shiga nanata kalmar shahada watakila ajalinta ne ya sauka a cikin wannan dare.

Da yake dare ya tsala shiyasa motar ta samu sararin sharara gudu yanda ranta yake so,

Wani irin wawan burki motar taci! ji kake kuuuuuuu!! kafin ta gangara can gefe guda tana watangaririya!

Da azama! ya isa gurin jama'arsa na tare dashi, yayin da gurin ya cika da kukan karnuka abunka da dare!

Motar dake watangaririya ya durfafa! babu tsoro a tare dashi yasa kafarsa ya daki murfin motar, cikin ikon Allah ta bude, a take suka fara rige-rigen fitowa, lokacin da sukayi arba dashi suka tabbatar *Makashinsu* ne sai gudu! radada! direban kuwa kafin ma ya samu nasarar fitowa motar ta kama da wuta!
Tana kwance! magashiyan! ko ina na jikinta a daure! wucin wutar ya kama gefen zaninta! ta rasa yanda za tayi sai ta fara jan jiki tana gurnani!

Allah yayi masa ji! da sauri ya juyo yana haska gurin da wata...


Read / Download GOJE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album