Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AUREN DOLE Complete Hausa Novel Document by AUREN DOLE


AUREN DOLE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 12598



AUREN DOLE

Reading Time: 1 Hours

Added On: 07, Oct 2023

Author: Ummu Maher ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ALKALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 154.87 kb

File Type: txt

Views: 2800+

Download: 716+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [1/10, 11:05 AM] Nordin: *JIRWAYE....*






*DAGA ALK'ALIMIN NABEELA DIKKO*






*AUREN DOLE!*





_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM..._


*Shimfid'a:Da farko dai Aure shi ne Alak'ar zaman tare tsakanin namiji da mace,A bisa yardar juna da Amincewar Dangi,Ta hanyar cika wasu ka'idoji,Na Al'ada da Addini.*





*Shi kuma Auren Dole:Shi ne tilasta yaro ko yarinya auren Wanda kowa acikinsu baya so,ko kuma baya kauna mafi yawa iyaye da kakanni ne ke tilasta shi."*







*SHAFI NA D'AYA*




"Zaune take a gaban kakanta, mallam Buba mak'eri,Banda k'arajin kuka ba abinda takeyi!"



"A fusace mallam Buba,Ya ce "Kinji dai na gaya maki...Wato ke gaki gagarau Ma'u!"Ni zan gindiya sharad'i kice ki shure ki wuce!"Saboda kin raina ni,Ke da muguwar uwarki!"To daga ubanki!Har uwar taki nafi karfinsu!"Aure ba fashi!Ko da ki amsa ki yarda kiyi Auren soyayya ko kuma ki karbe shi a matsayin *AUREN DOLE*"




"Cike da firgici!Ta dago kanta!Tana kallon Baba mallam(Kakanta)Hawaye ke zuba a idonta kamar an bud'a famfo!"




"Rik'e kafarsa tayi tace "Dan Allah kaka kayi min rai!Wallahi na tsani tsohon nan yafa tsofewa Babana!"Ka taimake ni!Ka had'ani da wani Kaka....!"



"Marin da Kaka ya watsawa Ma'u ne ya katse maganarta..."Tasbahar da ke hannunsa ya dinga zuba mata ta ko'ina!"Kururuwa!tah ta fito da ilahirin jama'ar gidan mai d'auke da lungage..."Suna kallon Ma'u da ke kuka!Babu halin cetontah!"Saboda gudun b'acin ran Kaka."




"Ta da muryarsa yayi sosai!"Ya ce, Yoo....Duk gidan nan akwai mai yimin musu sai ke!Ma'u to kinci gidanku kin qara tunzura ni nadawo da ranar aurenki kusa,idan yaso ki mutu agidan Alh.Kalle nafi farin cikin hakan da in barki ki auri shashashan yaron nan da kike so Kamalu!"Me yake da shi!me ya ajiye ke in kinsan asalin talaucin su baki kaunar ki aure shi!Saboda talauci n su na gadi ne!A jinin su yake..!"



"Ma'u tashi tayi cikin kunar rai!Ta nufi sashen su jikin Innarta ta fad'a tana rusa kuka!"Kamar ranta zai fitaa!"



"Kaka ahasale ya bar kofar dakinsa da ke gabas din gidan...butar da yasamu ajiye a hanyar fita waje,yayi shuri da ita,yace munafukan banza!To ku koma tsayin me kukeyi anan!?"Yana hararar sarakunan nasa da suka fito gulma.."Sum-sum kowacce ta fice sashenta domin sun San kaka sarai da masifa!!!"





"Lami ta kalli 'yartah rai!Babu dad'i!"Ta ce Kiyi hak'uri Asma'u ki yarda da zab'in Baba mallam shi ne mafita agare mu,kinsani sarai ni ko Babanki bamu isa muja da shi baah!"


"Duk gidan nan ba mai karya dokarsa!Kar ki bari zuciyarki ta rud'eki akan ki karyata,Ki barwa Allah komai!Kin sani sarai, " *AUREN DOLE* A gidan nan Ba akanki aka fara ba!Bare ak'are kanki!"





"Asma'u ta tashi zaune,Ta kalli Inna tare da kama hannayenta,Ta ce"Yanzu Inna kuna kallo Baba mallam zaiyi min *AUREN DOLE!?"* Saboda yana son cimma wata manufa tasa!"Tare da kwad'ayin Abin Duniya!"




"Wallahi na tsani!Alh.kalle,Inna bana sonsa,ba zan iya rayuwa da shi ba!Yafa tsufa!Yaransa duk sun girmeni!"Aure na zaiyi kawai, saboda budurwar zuciya!Da son zuciya!"Shi ne ya zubawa kaka kud'i domin yabashi Ni,A dole!"Shin meye haka!Addini ko Al'ada!!?"Na rasa amfanin wannan baqin aure da ake mana agidan nan......Wani Sabon kuka!Asma'u ta ke rerawa...."Inna Lami ma hawayen tausayi 'Yarta ke zuba a kyakkyawar fuskarta,Tare da cigaba da rarrashin Asma'u,da ido yayima luhu-luhu saboda kukaah!!!!"
[1/10, 11:05 AM] Nordin: *SHAFI NA BIYU*




*ALK'ALAMIN NABEELA DIKKO*








"A cikin jihar kebbi akwai wata qaramar hukumar mulki da a ke kira Argungu,"Babban gari ne,Mai cike Al'umma,Ga su da manyan yan boko maza da mata,kuma ma'aikatan gwamnati ne a kowanne fanni,Bugu da qari Albarkokin Allah sun yawaita A garin,Domin Allah ya albarkace su da manyan rafi masu dauke da Kifaye naji, na gani na fad'a,kuma mafi yawa daga cikin su asalin su D'aya ne akwai Kabawa,Lekayawa,Fulani,Zabarmawa da kuma gobirawa, noman shinkafa,da kayan lambu ne,da na masarufi sune Ayyukan su,Mutane ne masu rik'e da Al'ada ko kuma sana'ar gidan su ta gado!"Argungu gari ne na kabawan Asali wad'anda sukayi fice ciki da wajen Nigeria."Akwai cigaba mai yawa da suka samu,sunyi suna dalilin bikin kafun kifi(Fishing Festival) da akeyi aduk k'arshen shekara."Acikin wannan gari akwai wata unguwa da ake kira Gobirawa,yawancin mazauna unguwar ada caan baya zabarmawa ne,Daga baya hausawa suka yawaita acikinta."Gidan Mallam Aminu yana daga cikin unguwar layi na uku,Gabas da masallaci Sheik Bashir."Da ke Unguwar."




"Mallam Aminu,mutumen kirki ne,Wankan tarwada mai tsayi da jiki,yana cikar zati da haiba daka ganshi kaga irin malamman nan masu Da'awa,Sannan kuma ya fito daga gidan sarkin mallaman garin,Duk gidan su malammai ne kuma shi ne magajin gidan, ya kasance babban malamin da akeji da shi a jihar kebbi da kewayenta."Allah ya albarkace shi da samun ilimi mai yawa,ya na ba mutane da yawa karatun addini."Yana da mata d'aya malama juwairiyya itama tana da islamiyya ta kanta,mace ce mai kyau,ga kirki abin burgewa tana da ilimin addini,mutunci da sanin girman Dan Adam,Sai yaran su akwai Muhammad Yaseer da yaseera sai qaramin Abdul raheem."Yaran su sun taso acikin rayuwa mai kyau wato ilimin addini da na zamani."Tare da tarbiyya."Muhammad Yaseer yana karatun aikin likita,A jami'ar Danfodio Sokoto."Sai Yaseera da ta kammala karatun sakandaren mata a wannan shekarar,Abdul kuwa zai tafi aji d'aya a sakandare."Dukkan yaran kan su a had'e yake suna da zurfin ilimi mai yawa,kowannen su ya haddace Alqur'ani mai girma tare da wad'an su littafan sa ni,"Suna da kyau matuka,ga biyayyah da kamun kai da nutsuwa."




"Kamar kullum matukar mai gidan yana gari ko baya nan hakan ke faruwa agidan,wato karatu tun kafin sallah Asuba har zuwa wayewar gari, Mallam ne acikin iyalansa,Suna ta karatu ya fadiwa matarsa da yayansa,daga bisani Addu'a sukayi kowa ya shafa,Daga nan suka cigaba da fira kowa na fadin ra'ayinsa ko buqatun su da abinda suke so."Kasancewar Yaseera da Abdul ne kawai agida domin yaseer yana makaranta."




"Mallam ya tambaya Abdul na tambayeka ba ka bani amsa ba!?"



"Abdul ya ce"Abbu daman ni inason idan nagama karatuna na sakandare ka kaini jami'ar nan ta madina ina so nayi karatun likitan musulunci."




"Dariya mallam yayi tare da miqawa Abdul hannu sukayi musabaha yace masha Allah,



"Allah ya cika maka burin ka Abdul raheem,Amma kasan tufin Asirin Allah ne,muke da shi idan Allah ya kaddari hakan zanji dadi Allah yaqara tufa mana Asiri."




"Ameen ya rabbi,Umma ta itada Yaseeara suna dariyar Abdul."



"Naga bakin ki na motsi ke kuwa me kike buqata?.Umma ta tambayi yaseera tana murmushi."



"Abbu ni yaushe zan tafi makanta!?"Yaseera ta tambaya."




"Amsa ya bata na gaya maki makaranta ba yanzu ba!Ki k'ara hakuri akwai tunanin da nikeyi akai!"Inji Abbu.


"Yanayin yaseera ya sauya!Domin tana son cigaba da karatun ta wataqila Abby bazai barta ba!Tace acikin zuciyarta!"A cewa fili cewa tayi to Abbu,Nagode." tashi tayi ta nufi madafar Abinci domin hada abin Karin safe."





"Abdul ma yasan aikin falon Abbu yaje ya share tare da harabar gidan,sannan ya fara wanke motar Abbu da yake yau Assabar ba makaranta sai goma suje islamiyya su dawo sha biyu,su koma karfe biyu,su komo shidda na yamma."




"Abbu ya kalli Umma yace"Juwairiyya ina ganin kamar lokaci yayi da zan fadawa yaseera mijin da na zaba mata,saboda naga tana son karatu ni kuma sai anyi auren su nikeson ta tafi makaranta tana gidan mijinta,ba wai saboda na raina kamun kanta ba!"Wannan shi ne ra'ayi na amma me kike ganin ya race!?"



"Umma Ta numfasa tace Mallam nima,In bayanka gwara kawai tayi karatunta bayan auren,sai dai wani hanzari ba gudu ba!"Ya kamata tasan da maganar Aurenta da Najibullah shi yafi cancanta."



"Hakane In sha Allah an juma da dare zan sanarda ita!"Inji Abbu."




"To Allah ya yarda yasa mudace saboda kowacce uwa tana alfahari da samun suruki kamar n
Najibullah...Umma tace tana kokarin tashi,Bari naje na duba me ake hada mana na kari,Abbu yace to kuyi himma Ku gama Ina son nafita yanzun nan."




"In sha Allah,mallam yanzu za'a gama.."Umma tace ta nufi hanyar madafa."







*GIDAN MAK'ERA*

"Babban gida ne,Mai dauke da lungage da dama,Mallam Abubakar wanda akafi sani da (Malam Buba)shi ne shugaba agidan,Yana da mata biyu Inna Karime wato uwar gidansa wacce ta rasu shekarun baya!tanada 'ya'ya tara maza biyar,Umar,Nasiru,Aliyu,Badaru da sani sai mata,lubabatu,sahura,sai Mariya da sakina dukkan sunyi aure har da yaran su wasu kuma sunada jikoki,Sai matarsa ta biyu Amina wacce suke kira da (Anna)Da dadewa suka rabu da ita akan masifar sa,yanzu hakan shi kadai yake rayuwa sai halinsa,Anna tana da 'ya'ya shidda,Tare da Malam Buba,Mata biyar,Zainab,Ruqayya,Hassana da usaina,Aysha,sai namiji d'aya kuma shine babba acikin su wato Yusuf Mahaifin Asma'u."Tunda Anna tabar gidan malam tayi aure a kauyen felande yanzu hakan scan take rayuwa da yaranta biyu maza da ta samu Idirisu da mustafa."






"Dukkan gidan kowa na tsoron Baba mallam,Saboda mutum ne,mai akida da dokoki,Shi ke hada aure shi ke saki harkar gargajia ta yalwatu arayuwarsa Duk yaransa maza agidan suke zaune da iyalan su kowa da nashi lungu."


"Gidan mallam Buba,Babban gida ne,Wanda 'ya'yansa da jikoki har tantab'a kunne ke rayuwa acikin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AUREN DOLE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album