Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DR HAJAR Complete Hausa Novel Document by DR HAJAR


DR HAJAR

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 73627



DR HAJAR

Reading Time: 6 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Dija Wazeeri ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 412.46 kb

File Type: txt

Views: 762+

Download: 802+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: ο»Ώ[18/12 7:31 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰




GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Mai kowa mai komai muna neman gafaransa. Ya Allah ka azurta mana tsoranka wanda zai iya hana mu sab'a maka. Ina kodiya a gareka Allah daka bani ikon fara wannan littafi lfy Allah kasa na kareshi lfy Allah ka bani daman isar da sak'on da nakeson isarwa ga Al'umma Allah kasa kuma ya amfanesu Allah ka ganar damu abunda bamu ganeba Allah karabamu da sharrin duk wani me sharri Allah ka biya mana buk'atunmu ......


*TSOKACI*

Wannan labarin ba gsky bane be faruba k'irk'iranshi nayi kawai don nisha d'antar da masu karatu ,Allah ka bani ikon isar da sak'on da nake fatan ze amfaneku insha Allah duk wani wanda ze karanta labarin don haka ina rokon yan uwana da duk yanda kukaga littafin ya kasance karku ce komai cox haka na riga na tsara...


*SADAUKARWA*

Na sadaukar da wannan Littafin gareki yar uwata HAJARA HUM'D BUBA Allah ubangiji ya cika miki burinki Allah yaji k'an mahaifinki yasa haske kabarinshi Allah ya Albarkaci ruyuwanki Allah ya rayaki muga har auren ki ,Ameen......


KUNA RAINA YAN MUTUNCI

Neeratluv my Besty
jannat (k'awar arziki)
My zee yabour
First lady
Husna Bauchi
Zara Bukar
Mss Xoxo
Yar ficika
Sajna
Aisha Abbakar
Khadija Candy
Maryam S Bello
Anty Khadee
Mummy Sultan
Maman ihsan
Beebei dee
Zara B-B
Action baby
Ayusha Ilyasu

Da sauran wanda ban lissafoba duk kuna raina ina muku fatan Alkairi Allah ya k'ara muku basira da, daukaka Allah ya rabaku da sharrin mak'iya😍

Ban manta dakuba yan group d'ina (D&W Novels) Nagode ,da irin son da kuke nuna min Allah ya barmu tare ya k'ara had'a kanmu, ya biya muku buk'atunku Ameen...


LITTAFIN MARUBUCIYAR

FANSA (RIVENG)
BURIN MINAL
NADIYA
ZURI'A D'AYA
K'IYAYYAR NAMIJI


KANO


"Kaga Malam pls live me alon na fad'a maka wai ana soyayya dolene? Kafa takura ma rayuwa ta".

"Baiwar Allah don girman Allah kiyi hak'uri ko sunanki ki fad'a min pls I'm begging u," sai kuma kayi ae, khadija zomu tafi " kije ina zuwa" khadija ta fad'a ranta 'a b'ace ...

Wucewa tayi tabar khadija wurin kallon mutumin khadija tayi tace "bawan Allah kayi hakuri da 'akwai dalilin dayasa kaga tak'i sauraron ka 'amma kar kayi fushi insha 'Allah zan shawo maka ,kanta ga number na, za muyi waya dakai duk yanda mukayi da ita"..

"Ok na gode (god bless you) " murmushi khadija tayi tace "Ameen sai anjima", har zata wuce ya tsaidata da cewa , pls baki fad'an sunan kiba da kuma sunan k'awar taki "ohhh sorry sunana khadija ita kuma Hajo " wow ashe sunan mamana gareta", Allah sarki tow barin wuce kar tayi ta jirana " ok tow thank you very much Nana Khadija am captain murad by the way" ur wlcm captain sunan babana gareka so bazan iya fad'a ba" Allah sarki ,kice zaki dinga gaisheni har k'asa kenan duk sanda muka hadu" murmush tayi tace "maizai hana barin tafi kar tayi ta jirana" ok tow ki gaida mun ita kow bye"....

Tawuce ta , tafi da Sauri don tasan ba k'aramin aikin Hajara bane tatafi ta barta..

"Dallah yar rainin wayo kin sani sai jiranki nake , kuma kinsan nace miki zan d'auki Jawahir a school" fuskar Khadija 'a d'aure tace sorry tow muje"..

Tunda suka fara tafiya babu wanda yawa wani magana cikin su, Hajar ta fahimci khadee haushinta ,take ji , murmushi tayi tace "Khadee wai yanaga sai wani 6ata rai kike?".

"Hmmm Hajar kenan ba dole na 6ata rai ba wlh abunda kike baya dacewa sam" rayuwan duniya tana kunshe da abubuwa da yawa, na d'aya farin ciki, bak'in ciki, haduwa, rabuwa ,samu, rashi lafiya, ciwo,mutuwa, Annabi ya horemu da muyi hakuri da duk wanda mukayi karo dashi domin ba zai dauwama ba, zai wuce.

Amma ke sam kink'i mance abun daya riga ya wuce she karu biyar da suka wuce, haba Hajar wlh kiwa kanki fad'a, shi kenan haka zak k'are rayuwanki bazakiyi aure ba 'ina gudun ranar da Jawahir zata buk'aci ki ,kaita gurin mahaifinta, mezaki ce mata ?wacce amsar kike da ita da zaki fad'a mata? I hope kin tanadesu?".

"Hmmm Khadee wlh bazan ta6a iya mancewa da abun daya faru ba 'a kullum na kalli Jawahir sabo yake zamamin Khadee namiji bad'an goyo bane Bazan kuma yarda dawani d'anamiji a rayuwata ba, namiji mugune Allah ya isa min"ta k'arashe tana kuka ,

Kiyi hakuri Hajar nasan abune mai wuyar mancewa a gareki bake kad'ai ba har muma bazamu mance ba Amma idan kinyi la'akari bafa duka maza bane masu mugun hali kuma keba yarinya bace yanzu Dr Hajar"...

"Duk nayarda da abunda kika fad'a Khadee Amma mubar zance kawai, don kina tayar min da ciwan dake damun zuciyata ne kawai". da haka suka isa school d'in su Jawahir suka d'auko ta sannan suka d'auki hanyar d'anladi nasidi

A hotoro Dr Hajar ta ajje Khadee ita kuma suka, k'arasa cikin estate d'in Ibrahim kunya wani k'aton gida suka shiga mention wanda ya gaji da haduwa daga gete din gidan, anrubuta wlcm to Doctor galadanci house da wani abu me kelli...

Cikin gidan kuwa abun kallone don komai da tsari aka yishi ginin gidan sama ne, wanda 'akwai wurin da zaka iya ganin mutanen waje wurin da glass akayi shi, wasu furanine a zagaye a gidan masu bada wani kamshi me kwantar da hankali cen gefe guda kuwa wurin shak'atawa ne wanda yasha kujeru na alfarma sai kuma wurin parking spaces wato gurin (ajje motoce) motoci guda bakwaine a gidan ferari da BMW lemozin CRV Lombagini Land rovar sai 406 wanda ake kai yara school...

Daga ,gefe guda kuwa akwai k'aton masalaci had'ade ,sai kuma d'akin me gadi kusa da get din gidan ,get din kofee brow ne me remot da an danna ze bud'e kansa, sai kuma k'asan gidan dayasha intalock masu kyau kalan ja da ruwan toka,

Karnuka ne kwance wurin guda shida masu kama dana surawa sai harkan gabansu suke kala kala...

Fitowa tayi ta kama hannun jawahir suka nufi wata kofa me kyau ,dannan bell tayi wata yar budurwa tazo ta bud'e mata ga dukan 'alamu yar aikin gidan ce , da murmushi ta kar6i jakar dake hannun Dr Hajar da kuma lunch boxs din dake hannun Jawahir ,

Shiga sukayi suna shiga k'amshin abinci ya daki hancin su , wuri coredor ne haka sai kitchen ta gefe sai kuma wani k'ofa transperant ana iya ganin nawaje amma nawaje bazai iya ganin na ciki ba, falow ne wurin yasha royar chairs ruwan madara da goldin masu masifar kyau da laushi cen gefe guda kuwa daining aire ne shima royal ruwan madara da goldin sai kuna wani drowar da aka ajje cups dasu madara confals da sauran su zubi da tsarin falon yayi ga wani taf keken tv tare da stand dinshi na gani a fad'a gefe guda kuma stairs ne me hannun k'arfe yasha carpet gefen wurin anjera wasu cendulls masu bada wuta different colos sai kuma wani shoglass wanda yasha humurori da turarukan wuta masu k'amshi

Hawa saman sukayi nan ma wani falow ne wanda taci uwar na k'asa a haduwa ,kujerun ciki royal ne suma amman ruwan toka hannun kuma sky blue da carpet dinma haka sai santa tabel kalan jikin hannun kujeran ,sai katon tibin bango wanda sai wane da wane ake ganin irunsu a gidan su gefe guda kuma wani standard a.c ne, had'ad'e gefe da gefen gurin t.v kuma wasu manya manyan sufiku ne tare da hufan su,falon ba k'arya yayi k'amshin turaren wutane kawai ke tashi sai sanyi ac dake bugawa gidan shiru babu hayaniyar kowa sai tv dake aiki sai kuma na'urorin gidan na more rayuwa ,cikin falon akwai daki daya sai kuma da'an fito akwai dakuna guda uku daya na kalifa daya na Dr Hajar d'ayan kuma ciki da falo ne shima na 'alfarma shi kuma na mahaifin sune...

Zama tayi kan lalausar kujeran dake falon tana ,maida numfashi irin ta gaji dinnan, kuma kowa yaga fuskarta yasan bata, da walwala kuma tana cikin damuwa, "Alawuya ina Mami" ta fad'a tana cirewa Jawahir doguwar rigan school din ta" tana d'aki bata jima da shigaba yanzu bak'inta suka tafi" ok maybe ta shiga sallar la'asar ne ,yau me kike dafa mana?" Sakwara miyar igusi sai kuma marfesun naman kai sai gashe -shen kifi da ,dankali," wow my best food yau zanci abinci kenan na koshi kin kusa gamawa?" Eh miyar igusi da farfesu suna wuta sakwara da kifi da dankali kuma nagama su"...

"Yawwa tow kiyi sauri ki gama kafunnan nayi wanka sai naci, yanzu tafi da Jawahir ki hada mata
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DR HAJAR

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album