Join Our WhatsApp Group

BAMBANCIN ƘASA Complete Hausa Novel Document by BAMBANCIN ƘASA


BAMBANCIN ƘASA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 124331



BAMBANCIN ƘASA

Reading Time: 10 Hours

Added On: 28, Jul 2023

Author: Siyama Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 615.2 kb

File Type: txt

Views: 602+

Download: 585+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [3/29, 08:37] Siyama Ibrahim: *⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION*
_-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-_        
               
   *BAMBANCIN ƘASA*
  _{Battle to reach}_

_*Book By:SIYAMAIBRAHEEM_*
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

_*بسم الله الرحمن الرحيم*_
*_Sadaukarwa zuwa ga Brilliant Writers Association one luv❤_*
*EPISODE:1&2*

   Babu abin da ke tashi a wannan dokar dajin face muryoyi da kukan tsuntsaye haɗe da dabbobin da ke keɓance a muhallin su,tun daga nesa ake sakar da maɗanni(arrows)wanda yake fitowa ta ko wani ɓangare ba tare da ya dakata ba domin kuwa zuwa suke kamar ana ruwan su ta ko wani ɓarayi na dokar dajin nan...
   Gudu yake amma tana bin sa kamar dai gudun fanfalaƙi,agaji da ceto yake nema amma ita kam burin ta shine ta cimmai dan ta ƙarasa ida ƙudirin ta a kan sa..
  Kamar ƙiftawar ido,yana juyawa da nufin fakewa a bayan wani babbar bishiya dake da wani irin dandamali kawai sai ya ji cakaf,,an kai mai damƙa mai ƙarfin gaske haɗe da matse sa da bishiyar...

  Nishi yake yi kamar wanda ran sa zai fita,so yake ya numfasa kafin ya mata bayanin inda ya fito da kuma waɗanda suka aiko sa sai dai yin hakan ya ƙagara dan kuwa bata ba sa wannan damar ba sakamakon saka mai takobin ta da tayi a wuyar sa ta yadda ta san ko hauka yayi bai isa ya musanta abin da zata tambaye sa ba...

  Idanun ta cikin nasa wararrun idanun da suka nuna alamar tsoro firgici da nadama,..
  Yana ɓari yana haki maganganun sa na ɗaukewa ya taro iya kuzarin sa ya furta
  "Kar ki kashe ni ina da iyali,ina da mata ina da yarinya ƴar ƙanƙanuwa wacce bata fi shekaru huɗu ba,ki min rai ki taimake ni,ki mayar dani masarautar da aka aiko ni ba tare da kim min lahani ba,in kika min hakan ni kuma na maki alƙawarin ba zan sake bin hanyar da maƙiyin ki ya bi ba ya mai girma sarauniyar mayaƙa"...

  Tun da ya fara jero mata jawabi take bin sa da kallo,kanzil bata ce da shi ba har sai da ya kai madakata sannan ta fara bin jikin sa da wasu irin ƙazamin kallo kafin daga bisani ta tofar da yawu ta gefen sa..
  Mayar da duban ta tayi gare sa tana son sun haɗa idanu da shi..
  "Ka ce in maka rai in bar ka ka koma inda aka turo ka"?ta mai ta tambayar tana mai ɗage giran ta biyu sama haɗe da ƙure sa da idanun ta..
  Cikin sauri da ɓarin jiki ya amsa mata da kai,ai kuwa sai ya ji saukar mari mai zafin da sai da ya saka sa ɗauke wutar wucin gadi sannan ys dawo daidai ya buɗe bakin sa ya amsa mata..
  Ƙara danne takobin tayi a wuyar sa tana kallon sa sannan ta ce
  "Ni ce doluwa"?ko ina na jikin sa na ɓari ya amsa mata ta hanyar girgiza mata kai a lokaci ɗaya kuma ya tuna abin da ta tsana kenan wato a girgiza mata kai sai yayi saurin amsa mata da
  "A'aa a'aaaa sarauniya ban ce ba"saurin tarar numfashin sa tayi tana faɗin
  "Toh ni na ce kenan"??a firgice ya girgiza kai sai ya kuma amsa mata da baki
"A'a sarauniya a'a"!!wani irin shu'umin murmushi tayi wanda ya narkar da wannan mutumin da ke hannun ta,ya sadaukar dan muddin ta riƙe ka ta maka wannan tambayar sannan ta ida da wannan munafukin murmushin toh tabbas abu na gaba da zata yi shine raba maka kan ka da jikin ka in ko bata raban ba toh zata maka lahanin da sai ka gwammaci da ma kan ta cire tun tashin farko...
  Bai gama wasi wasin sa ba ya ji abu mai kaifi ya kawo mai hari kenan ajalin sa ne ya buɗe mai ƙofa..
Fil ta gille mai wuyar,..jini ne ke bulbula kamar an ɓalle kan famfo,ƙaƙari ya shiga yi yana yin sama da ƙasa kamar an saka mai abin jijjiga jiki,matsawa gefe tayi tana kallon sa har ya faɗi ƙasa wanwas tun yana jan iska yana gwalalo idanun sa waje har dai ya ɗauke wuta ɓat ya daina juyi..

  Takowa tayi gare sa yana kwance matacce ta saka hannun ta a tsakankanin kan sa da ke lilo da wuyar sa ta riƙo jijiyar da ke reto tsakankanin wuyar da kan ta kai mai wata irin fizga wanda yayi sabadiyar rabewar wuyar nasa da kan sa..

  Miƙewa tsaye tayi tana fidda numfashi ga kan nasa riƙe a hannun ta jikin sa kwance a ƙasa,takalmin ta da ke a yanayin takalmin mahauta mai nauyi da gurabai kala kala da zai iya illata mutu da shi ta yi amfani wun take ƙirjin sa sannan ta tsallaka sa tayu wucewar ta...

  Tana tafe kamar babu abin da ta aikata har ta kawo inda take son zuwa inda nan take da tabbacin zata isar da saƙon ta kuma ya isa inda take son ya isan..
  Tun lokaci da ta danne sa harbe harben ya tsaya cak kamar ba'a yi har kawo wannan lokacin da take tafe babu rangwaji..
  Tana isowa daidai bakin mahaɗar da ya raba hanyar kashi uku ta tsaya ta kalli gabas sannan ta juya ta kalli bayan ta..
  Abin kamar a mafarki wuf ta fiddo takobin ta daga ma'adanar sa da ke gefen takalmin ta zuwa rigar ta.
Cak ta cake shi da shi sannan ta kuma murza takobin a cikin sa kafin ta hankaɗa sa da ƙafar ta ta janyo takobin ta waje..

  Juyawa ta kuma yi tana kallon hanya,daga bisani ta tsaya hannu damar ta riƙe da takobin ta hannun hagun ta riƙe da kan sa,cikin isa da gadara da nuna mulki ta buɗe baki haɗe da kaurara muryar ta cikin izza take faɗin
  "Da akwai masu son gwadawa da ni ne har yanzu cikin muhalli na"?tsit wurin ya ɗauke sai amon amshin da dajin yayi na maganar da ta kammala yi yanzu..
  Murmushi tayi sannan ta ce
"Ga saƙo na nan ina so a isar min da shi zuwa ga sarkin ottoman a sanar da shi cewa ni sarauniyar mayaƙa bana al'amura na da mata sai maza waɗanda suka amsa sunan su maza ba irin waɗanda ya aiko min ba dan haka ku zo ku karɓi tsaraba ta zuwa ga sarkin ku"tana gama faɗin haka ta mai da takobin ta ma'adanar sa ta juya da nufin soƙa kan a bishiya sai ta ji takun su..
  Takun su kaɗai ya isa ya rikitar da mutum dan siffar su ya fita daban daga siffar cikakkun mutani masu galihu,sai dai wani abu ɗaya abin mamaki,suna dumfaro ta fargabar su na daɗuwa dan kuwa ba so suke su rasa rayukan su ba.
  Juyowa tayi a tsanake ta shiga bin su da ido ɗaya bayan ɗaya sannan ta cillo masu kan ɗaya daga cikin su ya cafe kan,sai suka waro idanun su waje suna kallon kan,in basu yi kuskure ko ɓacewar basira ba wannan kamar fuskar sabon mayaƙin da aka ɗauka ne kwanaki talatin da tara da suka wuce wanda a wannan rana ake son ɗaga martabar sa zuwa mataki na biyu muddin ya kawo kan wannan mayaƙiyar dan kuwa ya bari a rubuce akan in bai kawo kan ta ba toh a yi garkuwa da iyalin sa sannan sarki ya bautar da matar sa ta hanyar mayar da ita farkar sa(mistress)..
  Wannan magana ta sa ta saka kowa ganin kamar eh zai iya aikata aikin da aka basa dan har kyautar dokin tafiya sarkin ya saka a ba sa dan yadda ya nuna yana jin aikin kuma yana da yaƙinin zai iya kawo kan cikin daren ƙarshen shekarar wanda da shi za'a yi bushashar zagayowar ranar haihuwar ɗiyar sarkin ƙasar ottman..

  Sai dai yanzu da shi aka gille masa kai sannan aka aika ma sarkin da ya aiko sa da sakon,abin ya jikkita su ya rikita su halan menene tattare da wannan mayaƙiyar da kowa in zo da nufin yaƙar ta bai iyawa sai dai shi ta yaƙe sa sannan ta haɗa da guzirin mayar da saƙon zuwa ga iyayen gidan su da suka turo su gare ta..

  "Da mai magana ne"?tambayar da ta masu kenan wanda ya saka su saurin girgiza mata kai,a ƙalla zasu kai majiya ƙarfi goma sha ɗaya dan dama a ƙirge suka su shabiyu akan in har aka yaƙe su kar su bari a ƙarasa su wani ya koma masarautar ya bada bayani dan sauran mayaƙan dake a harzuƙe ko wani lokaci su tafi su ƙarasa aikin da na farin suka kasa ƙarasawa..
  Jijjiga kai tayi sannan ta ce masu
"Ku gayawa sarkin ku,ni sarauniya na ce ya share hanya dan ina nan zuwar mai nan ba da jimawa ba sannan sai na tabbatar da na kai sa ƙasa yana kan kujerar mulkin sa sannan in ɗaga kan sa sama in nunawa halittu kan sa su tsine masa daga bisani in cilla kan sa zuwa ma'adanar kawunan dabbobin ban mamaki,ina fatar ba sai na kuma nanata maku saƙon ba"?wannam abin da rikitatwa yake,yanzu wannan mayaƙiyar har tana ganin ta kai matsayi da muƙamin da zata faɗi banza dangane da shugaban su sarkin su abin bautar su ta wuce lamin lafiya?
  A harzuƙe ɗayan ya kai hannu zai ciro takobin sa sai na kusa da shi yayi azaman dakatar da shi ta hanyar riƙe mai hannun sa da ke kan takobin ya kalle sa cikin ido haɗe da girgiza mai kai alamun kar yayi haka..
  Ba ƙaramin takaici ya ƙunsa ba dan so yayi ya kai mata yankar bazata,shi bai san ba'a iya tunkarar ta kai tsaye ba..

Wani dariyar tsoratarwa tayi sannan ta yi sama da takobin hannun ta sai saman wuyar sa ai ko ya tsure yayi tsuru tsuru ya kasa furta ko da kalma ɗaya ne sai kai kawo da idanun sa ke yi a tsakankanin fuskar ta da takobin ta da ke wuyan sa wanda yana iya ganin kan sa a takobin tsabar kaifi da hasken takobin...
"Akwai sauran bayani ne a bakin ka ko ƙorafi"?tuni ya amsa mata ta hanyar girgiza mata kai sai kuwa ta kai mai yanka ɗaya jini ya fito take sauran suka waro idanun su waje suka rinƙa yi mata kallon mamaki shi ko da takobin ke kan wuyar sa sai ya buɗi baki yana roƙan agajin ta..
  Kallon wulaƙantacce ta mai sai ta cire takobin saman wuyar sa sannan ta nuna sa da yatsa
"Kar ka sake,ko a mafarkin ka,kar ka kuskura ka yi gigin kawowa kurwa ta hari bare ya kawo har ni kai na,saboda yin hakan na nufin faruwar komai a kan ka"...

  Kaiwa nan ta cire takobin ta ta tofa mai yawu a fuskar sa tayi wucewar ta su kuma suka juya domin yin haramar komawa zuwa ga shugaban su wato sarkin masarautar Ottoman,cike da alhini suka bar dajin dan sun kai sama da kwanaki tara suna fakon ta dan ƙarasa nufin su da na shugaban su a kan ta amma abin ya ci tura gashi ƙarahe ma sai su ne suka sami illah dan ta halaka masu ɗayan su sannan ta jikita ɗaya saboda ba yankar somintaɓi ta kai mai ba....

*************
Tana tafe tana wasa da takobin ta tana gwada yadda take yaƙi da shi in ta kai nan sai ta kai can a haka ta rinƙa yi har ta kawo wani tsohoh hanya mai launi kamar yanar zuma,an rufe sa da ciyayi da juji ga wata ƙorama a gefen damar ta suna kallon juna..
  Hanyar ƙoramar ta nufa riƙe da takobin ta a hannu,tana zuwa ta tsoma takobin ciki ta jujjuya shi cikin ƙoramar sau huɗu gaba da baya sannan ta cire ta ɗaga shi sama,.
  Cak jinin da ke takobin nan sai ya ɗauke babu ɗigo ko kaɗan,tana tsaye tana kallon takobin har ya bushe sannan ta mai da cikin ma'adanar sa kafin ta juya ta kalli hanyar da ke nan kamar ta yanar zuma..
  Tana isa wurin sai ta tsuguna ƙasa ta kai hannun ta ta ɗage wannan yanar sai ga wani matsakaicin ƙofa ya bayyana..
  Tura ƙofar tayi tana mai sake yanar da ta tattare sama wanda ya koma ya rufe gidan ruf,daga ciki kuma ta saka ma ƙofar wani maƙullin sakata ta rufe sannan ta fara takawa cikin gidan dake babba ne a share kamar an share hanya..

  Sannu a hankali ta ƙarasa takawa ciki har ta iso wani ƙofar inda a nan ɗin ma,yanar zumar ce,yaye yanar tayi kamar dai na ɗazu ta shige sannan ta mayar da ƙofar ta rufe..
  Tana rufewa ta jiyo murya na tambayar ta
  "Daga ina kike"?cikin firgici ta juyo sai ta sauke idanun ta bisa kan mai tambayar..
  Mace ce da ba zata wuce shekaru arba'in da bakwai ba da haihuwa tana tsaye ta naɗe hannun ta a ƙirjin ta kan ta rufe da wani mayafi bata kasance fara sosai ba sai dai tana da haske saɓanin yarinyar da ke gaban ta wacce take fara ce ga ƙuruciya...
  Sake maimaita mata tambayar tayi
"Daga ina kike"?zuwa yanzu ta sadauƙar kame ta a gida za'a yi a hana ta fita har tsawon kwanaki ashirin da biyu ita kuwa ba haka take so ba..
  Bakin ta ya mata nauyi amma a haka ta daure ta furta
"Daga dajin al'ajabi nake"?cikin tsoro matar ta ce
"Kina da tunani kuwa?ban ce maki kar ki kuma kallon hanyar nan ba bare ma ya kai ga kin wuce har kin shige sa ba"?ita dai tana tsaye shiru fatan ta da addua'ar ta kar a hana ta fita dan akwai ƙudirin da take son isarwa washegari..
"Kin yi shiru ina tambayar ki"?ɗago kan ta tayi ta kalli matar sannan ta miƙo mata takobin hannun ta,.kallon takobin matar tayi sannan ta kalle ta kafin ta ce da ita
  "Ba zan karɓa ba dan kin san ko kin bada kina da wata amfanin me wannan zata min"?!!buɗe baki tayi tana faɗin
  "Kar ki rufe ni a gida,,ga takobin nan na bar maki kuma ba zan ɗau wata takobin ba amma kar ki hana ni fita dan babu wanda zai tsare mana gida dole sai ni"!!ajiyar zuciya matar ta sauke sannan ta janyo hannun ta ta jawo ta jikin ta kafin ta fara mata magana cikin sanyi da sigar wa'azi..
  "Kin ga dajin nan na al'ajabi ba daji ne da zaki rinƙa zuwa a kai a kai ba sakamakon mummunar tarihin da dajin ke da shi,sarsi kin san a dajin nan aka rinƙa fakon mai kula da ke har aka cim mata aka lahanta ta wanda yayi sanadiyar rasa ta da muka yi har abada,tun daga lokacin nake hana ki tunanin hanyar nan amma kullum...


Read / Download BAMBANCIN ƘASA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album