Join Our WhatsApp Group

MURMUSHIN ALKAWARI Complete Hausa Novel Document by MURMUSHIN ALKAWARI


MURMUSHIN ALKAWARI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 29026



MURMUSHIN ALKAWARI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 159.23 kb

File Type: txt

Views: 920+

Download: 259+

Last download: 2 days ago

Description/Story: MURMUSHIN ALKAWARI complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih

.
BUDEWA
Akwai lokacin da rayuwa ke dauke da abubuwan ban sha'awa masu dauke kewa da nishadantarwa kamar irin su shudin launin sararin samaniya kyakkyawan gajimare fari fat mai tafiya ahankali kamar Dusan kankara wata sa'ar har dasu bakan gizo mai launi launi wanda kan yi babakere akan farin gajimare kalolin sa gwanin ban sha'awa sakamakon hasken rana da kan ratsa ta tsakanin girgijen ruwa. Haka nan har kullum rayuwa dauke take da mutane masu baiwa ta iya nishadantarwa ta hanyar hikima mai ban mamaki acikin su har da su dattijo SIDI MAI JAKA.
.
Acikin irin wadannan lokutan ne masu dadi da dadada zuciya ina zaune ni kadai a kofar gida kamar kullum Ina dauke da dan alkalamin rubutuna da littattafaina a hannu kaina asama ina kallon gajimaren dake tafiya a hankali sakamakon aassanyar iskar dake tura shi. Mukuwa ta Bi'adama dake zaune akan doron kasa tana fifita mu ko wanne lokaci daga yanzu ruwan sama na iya sauka.
Duk wannan daddadan iskar dake fifitani haryanzu Allah bi bani ikon dora alkalami na akan takardar ba domin babu wani kwakkwaran zare na labari acikin kwakwalwarta adaidai lokacin ne wani murmushi ya subuce min ni kadai ga wanda ke wucewa ma idan ya dubeni saiyayi zargin gamo nayi ni ko ba wani abu ne ya sani dariya ba sai tunanin cewa koda kwakwalwata babu wani kwakkwaran labari.
Baza'a rasa a kwakwalwar dan tsoho sidi mai jaka ba.
Shekaru uku da suka wuce wannan dattijon sidi mai jaka Yabani labarai masu dadin gaske har guda biyu nakuma karu dashi matuka ta wajen dada koyon hanyoyin da ake iya tsara labari mai bada ma'ana batareda ya gudurar da makaranci ba.
Wannan ita tasa a yanzu dana zurawa gajimaren idanu sainaga banida wata mafita sai sidi mai jaka. Dan tsoho mai jakar labarai barkatai. Cikin sauri na nufi cikin gida domin na sa ayi min TUBANI in yaso ko daga baya ne kanina ya bini dashi zuwa gurin sidi mai jaka.
Ba'a Dade ba na fito sannan cikin sauri sai na nufi gidan sidi mai jaka zuciyata cikin damuwa Ina mai Addu'ar Allah yasa Yabani labari mai dadi kamar na TANI DA BARAYI ko na ANAS MIJIN MABARUKA GURGUWA bugu da kari kuma gashi kullum sai dada samun korafe korafe Nakeyi daga gurin makaranta na suna cewa wai kwana biyu Na kasa rubuta musu komai wai basira ta kare min.
Wannan abu na damuna matuka domin idan har akwai abunda naki jini a duniya toh shine na bakantawa makaranta na rai. Nariga nasani cewa ni mutum ne kamar kowa dole ne wata rana na nemi labari na rasa to dan ma na yi sa'a Allah ya hadani da dan tsoho mai buhun labari ni kaina wannan dattijo na bani mamaki domin ban taba tsammanin labarin MABARUKA gurguwa zai burge ni ba sai daya fara yau kuma ko wanne iri zai bani? Allah masani Saidai naje gare shi din Nace cikin zuciyata.
.
Karfe tara na safiyar wannan ni'imtacciyar Lahadi na isa kofar tsohon gidan sidi mai jaka tun daga nesa na hange shi tsaye a kofar gidan yana gugar hakori da wani dogon asuwaki reshe guda yana muzurai ko shakka banayi Shima fitowa yayi domin ya sami rabonsa na daga daddadar iskar dake busawa.
Murmushin sa yafadada sa'ar dana karasa gare shi ya dubi littattafan dake hannuna sainaga murmushinsa ya subuce daga fuskar sa lokaci guda sannan batareda yayi min sannu da zuwa ba sai yace.
NAS. Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani!
Ameen baba nace dashi cikin mamaki sannan na dada da cewa me kake nufi da mugun ji da mugun gani? Sidi mai jaka ya zare zungureren asuwakin daga bakin sa kana ya dada kallon littattafan dake hannuna cikin takaici yace
Abinda nake nufi da mugun ji da mugun gani shine mutum kamar ka yazo guna neman labari dauke da littafin rubutun sa kadai babu Tubani! Na fashe da dariya.
Haba baba sidi kaima kasan ai bazan fara zuwa gurin ka babu tubani ba yanzu haka din nan yana gida akan wuta da zarar an gama kanina zai kawo nan nan da nan naga fuskar sa ta washe cikin farin ciki yayi kaki ya tofar gefe guda sannan yace.
Haba nas ko kaifa yanzu naji kyakkyawan labari to ai Daman mugun jin da nake nufi shine ace dani babu tubanin baki daya amma yanzu tun da yana tafe shiga cikin Zaure ka dauko min kujera ta kazo mu fara da wuri don wannan karon labarin da zan baka yanada tsayin gaske don yafi na MABARUKA gurguwa tsayi ya dubi katon agogon sa OMEGA mai kamar ankwa.
Kaga har tara ta dan wuce me yiwuwa tunda muna da dan lokaci me tsayi ma iya gamawa kafin Sallar azahar.
Hakane nace dashi sannan cikin sauri na shiga zauren na kinkimo tsohuwar kujerar mai kamar makara na girka masa ita ajikin katuwar bishiyar durumin dake kofar gidan sannan cikin sauri na koma cikin zauren na dauko wani tsohon buzu duk ya jeme kamar fatar ganga ban damu ba nazo na shimfida shi agaban kujerar sannan muka zauna lokaci guda. SIDI mai jaka ya dubeni da busasshen murmushi Nima na dube shi har yanzu sanye yake da tsohuwar rigar nan dai dana nasan shi da ita tun tsahon shekaru uku har yanzun dai itace a jikinsa bai sake wata ba kamar bawon dankali.
NAS wannan labari da nake son na baka dauke yake da dogayen zararruka har guda uku wadanda sai na saka ma su sannan zan hada na kulle ma su guri guda me yiwuwa labarin ya baka dariya me yiwuwa ya baka haushi ko tausayi ko ma ya saka kuka yadai danganta da irin tunanin ka da fahimtar ka.
.
Hakane Nace dashi sannan ya dada da cewa shi ma wanan labarin barayi ne irin na TANI? Kokuwa labarin gurguwa ne Shima? Sidi mai jaka ya girgiza kai yace.
Wannan Labarin na wasu jaruman fim ne na Hausa. Na dube shi cikin kaduwa nace.
Labarin yan fim fa kace Anya kuwa zaiyi dadi? Sidi mai jaka ya fashe da dariya yace
Zan baka daya daga cikin zararrukan idan kaji babu dadi sai mu tsinke zaren mu jefar sai mu sake saka wani sabon zaren Labarin. Amma ina tabbatar maka da cewa ban taba baka labarin matasan zamani kamar wannan ba.
Ya dan yi shiru sannan ya karyi Goro ya jefa abakinsa.
NAS. Kafin a kawo tubanin Inason ka bani Aron zuciyar ka mu koma can cikin birnin Borno.
.
BABI NA DAYA 1
.
GARIN BORNO
.
A RANAR LAHADI 2 SATUMBA 2004
.
Nas acikin duk kyawawan matan dana taba baka labarinsu abaya irin su tani da kyakkyawa ummi kawar mabaruka gurguwa babu wacce takai koda rabin kyawun FALMATA. Sidi mai jaka yace dani yana dubana.
Wacece kuma Falmata?
Itace mace ta farko da nake son saka maka zaren labarinta yanzun nan idan Allah yaso. Sidi mai jaka ya amsa min kai tsaye. Nikuwa sai na girgiza kai cikin tsananin shakkar jin abinda yace kana nace dashi a tausashe.
Yanzu ashe baba sidi har akwai wata mace wai ita falmata da za'ace wai tafi ummin nan kawar mabaruka kyawu? Haba baba jifa sunanta wai falmata saikace wata hula. Ni sunanta ma baiyi kama da sunayen kyawawa ba. Baba sidi ya kalleni cikin murmushi kana ya dada karyar goro ya jefa bakinsa yace.
Nas kenan to ai abinda nake so ka gane shine kyawun fuska daban kyawun suna daban kuma abinda nake so ka sani shine falmata tana daya daga cikin kyawawan mata na wannan zamani. Ayadda na sami labari ita kanta falmata tana kiran kanta da kyakkyaw haka nan alokacin da take budurwa kafin ta auri SAIFULLAHI wani saurayinta ya taba cewa da ita.
Kai falmata wallahi kyawunki yafi kyawun kudi akan doron kasa. Gashi idan kika bata rai sainaga kin kara kyawu idan ko kikayi murmushi Wallahi numfashina har daukewa yakeyi saboda shauki...
Kana nufin kasa dani ita falmatan matar aure ce? Na katse shi da wannan tambayar. Baba sidi ya gyara zama akan tsohuwar kujerar kana yayi gyaran murya yace.
Haba Nas me kake ci na baka na zuba kaidai bani aron kunnuwanka kasha labari.
Na gyara zama nace Naba Ka.
Yauwa to kamar yadda nace dakai tun farko inason ka dauki zuciyarka cancak ka mayar da ita cikin wani kayataccen dakin shakatawa wanda ke dauke da kayan alatu acikin garin Borno.
Na mayar da zuciyar tawa. Nace dashi ina mai tunanin irin zaren da wannan tsoho zai saka min awannan rana. Sidi mai jaka ya dada gyara zama sannan yafara cewa.
.
Karfe biyar da biyar na yammacin wannan lahadi wata farar kofa ta bude sannan wata kyakkyawar halitta tafito daga cikin bandaki sannu ahankali tana rausaya kamar bishiyar turare ta ratso kan tattausan kilishin dake lullube da dandasheshen dakin shakatawar tana tafe tana wakar wani fitaccen fim na hausa. Alokacin data kawo tsakiyar dakin shakatawar tana wake tana rausaya ji takeyi kamar itace ainihin yarinyar dake wannan waka acikin fim din data Gani.
Wannan kyakykyawar halittar sunanta Falmata fadin kyawunta kauyanci ne kokuma bata lokaci domin za'a iya asarar takardu da ruwan alkamali masu yawan gaske kafin a zayyane surar wannan kyakkyawa.
Kamar yadda ta saba yau ma falmata daga ita sai daurin kirji da wani tattausan shudin kyalle mai taushi haka ta shigo falon in ka dauke wannan daurin kirjin jikinta tik take kamar dankali. Kanta babu dan kwali sai gashin kana yalo yalo baki sidik yana sheki ya kwanto mata har gadon baya. Tun da take ba'a tabayi mata kitso ba domin koda anyi ma anyi a abanza don ko rabin sa'a bayayi zai warware saboda tsabar santsin gashinta.
Sannu ahankali falmata ta nufi jikin katon madubin sannan ta janyo wata yar kujera mai doron baya ta zauna sannan ta dubi kyakkyawar halittarta ajikin madubin tayi murmushi.
Sannunki yarinya falmata... Kyawu dai kam Allah yabaki.... Saidai kuma bakiyi dacen miji ba. Tace da kanta lokaci guda kuma tana kokarin goge ruwan dake diga daga cikin lallausan gashinta falmata ta dubi fararen idanunta sannan sai jajajaja bakake bakaken lebben bakinta suka fadada da murmushin alkawari ga wanda yayi dace take kaunarsa sannan saitaci gaba da rera wakar fim dinta tana kwalliya abinta. Alokacin babu wani mahaluki aduniya daya isa yace wai acikin bakin ciki mara misaltuwa take domin na farko dai fuskarta a washe take lebbanta dauke da murmushi gashi kuma tana rera waka abinda harda rausayawa.
Tsahon kusan sa'a guda ta share tana shafe shafe da goge goge daga karshe dai ta dubi kanta duba na karshe ajikin madubi saitayiwa kanta murmushi domin tayi farin ciki da abindata gani takuma riga tasan cewa ko iblishi ne shi bai isa yaganta ya dauke kai ba. Dole ne hankalinsa ya kwanta da ita. Dolene ya amince da ita ayammacin wannan rana mai kunshe da manufarta ta aiwatar da boyayyen sirrin dake zuciyarta yana ci ganga-ganga kamar wutar makera.
Falmata ta shige wani dan daki ba'a dade ba sai gata ta fito da wasu shudayen kaya riga da wando dinkin fakistan wadanda sukayi matukar matse jikinta gamgam. Suka kuma fito da boyayyiyar halittar da Allah yayi mata afili wannan shiyasa falmata kurawa jikin katon madubin idanu akaro na biyu ta sake nazarin kanta.
Falmata tariga tasan ita kyakkyawa ce domin tun tana yar kankanuwa mahaifinta ke kiranta da kyakkyawa uwarta ma kyakykyawa Take kiranta dashi yan ajinsu ma yan uwanta mata a fimare sun sha cewa da ita kyakykyawa ce amma a fakaice. Domin wata sa'ar sai daya daga cikin daliban mata ta dubi falmata tace kai Allah yaban gashi irin na falmata wata babbar kawar falmata ta taba cewaWata babbar kawar falmata ta taba cewa ba abinda take son falmata dashi sai tsayinta.
Irin wadannan batutuwa su saka sa tun falmata bata kula har dai ta ankara da cewa ashe dai itama kyakkyawa ce.
Dan haka ayanzu data dada kallon kanta jikin madubin saita dauki turare ta fesa ta dada daukar wata kalar daban ta fesa sannu ahankali saida ta fesa sama da kala bakwai sannan saita wuce kai tsaye ta zauna akujerar dake kallon kofar katon dakin shakatawar ta fara zaman jiran maigidanta saifullahi.
Karfe shida saura kwata na yamma saifullahi ya karaso gida tun kafin ya shigo dakin shakatawar yaji kamshin turare ye bugi hancinsa abin yabashi mamaki domin ya riga yasan ayadda matar tasa ta tsane shi batayin kwalliya don shi sai in zata fita unguwa wannan duk bata dame shi ba domin ya riga yasan ko matarsa tayi wanka ko kada tayi ko tayi kwalliya ko kada tayi ko tayi direshin ko kada tayi kai aduk halin datake ciki kyawunya bai taba gushewa ba kamar yadda kaunarta bata gushewa cikin zuciyarsa ada.... Dacan kafin idanunsa su kai kan babbar aminiyarta INYAMI.
Cikin tsananin mamaki saifullahi ya shigo cikin dakin sanye da babbar riga da yar ciki da wandonta kansa matse da rantsatstsiyar hula tangaran hannun na dauke da bakar jaka wacce awani lokaci daya wuce babban direbansa MUDI ne ke rako shi da jakar har cikin dakin amma tun daga ranar daya auri falmata sai ya haramtawa direban shigowa musamman ma dayake direban ya fishi dan kyawun gani. Afuska nesa ba kusa ba. Saifullahi baki ne dogo kakkaura yana sheki kamar an shafa masa shuni saboda baki yanada tarin gashin baki kamar tsohon soja hakanan yanada tarin gashin kai duguzunzum kamar shekar ungulu adan sa'ar dayake saurayi sosai ashekarun alif tari tara da tamanin cinyewar kenan da burgewa ka ajiye suma duguzunzum babu ko tajewa wannan tsohuwar al'ada ita ke biye da saifullahi har zuwa wannan lokaci dayake dan shekara arba'in da biyu kaida ka dube shi ka dubi falmata saika ga kamar hasken fitilar kwai ne da na hasken rana. Dayawa daga cikin mutane sunyi ittafakin cewa in banda al'amari na masu gidan rana saifullahi bai isa debowo falmata ruwa wanka ba ballantana na sha.
.
Falmata ta...


Read / Download MURMUSHIN ALKAWARI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album