Join Our WhatsApp Group

SADIYA cigaban SO BAYAN RAI Complete Hausa Novel Document by SADIYA cigaban SO BAYAN RAI


SADIYA cigaban SO BAYAN RAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 49777



SADIYA cigaban SO BAYAN RAI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 257.57 kb

File Type: txt

Views: 503+

Download: 279+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
01
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
Madugun Taska
¤
¤
A ranar da Sadiya ta rasa Amir masoyinta ta gudu cikin daji tana kuka. A ranar ne kuma ta hadu da masoyinta Khalifa, wanda ya maye mata gurbin tsoho masoyin ta Amir.
Ga yadda al'amarin ya faru.
¤
¤
**~**
¤
¤
A duk bayan wata uku, wani lkcn wata hudu Hafsatu matar Dakta Hamza ta kan xo qauyen Gazari ta kawowa 'yan uwanta xiyara, dangin mahaifinta da suka rage mata a duniya idan zata xo yawanci mijinta ke kawo ta a motarsa, idan zata yi kwana biyu sai ya barta a nan, ya koma Abuja inda suke zaune, sai lkcn da ta shirya komawa sai ta yi masa waya ya xo ya dauke ta.
¤
Dakta Hamza babban likita ne, wanda yake da asibitinsa mai zaman kansa, bayan nan yana aiki a asibitocin gwamnati jefi-jefi. Musamman idan wani aikin gaggawa ya taso wanda ake da buqatar qwarewa, sai a kirawo shi yaxo ya yi.
¤
Dakta Jamza ba zai wuce shekaru arba'in ba a duniya, kodayaushe ana dangantashi da mutumin da ya samu nasara a rayuwar shi, yana da manyan kadarori wadanda suka hada da filaye da manyan gidaje da kuma uwa uba katafaren asibitinsa wanda mutane suke turuwar xuwa sbd qwararrun ma'aikatan da ya xuba da kum isassun kayan aiki na zamani dke a cikin asibitin.
¤
Dakta Hamza mutum ne da yake dora rayuwarsa kullum daidai da zamani, idan har akwai abin da yafi tsana a rayuwar sa, bai wuce hanyoyin rayuwa na gargajiya ba. Duk qarshen shekara ya kan dauki hutun kwana uku xuwa hudu, kuma yawanci baya tsayawa a Najeriya, ya fi tafiya qasashen waje ya shaqata. Motocin da Dakta Hamza yake amfani dasu duk wadanda ake yayi ne, komai tsadar mota idan har yayinta ya wuce, ya kan yi sauri ya rabu da ita.
¤
Dakta Hamza yana fita filin qwallon qafa da sassafe kafin ya fita wajen aiki. Da yamma idan ya dawo da wuri kuma, ya kan sa kayan qwallon kwando ya tafi wajen wasanninsu na manyan mutane tare da abokansa. Ga wanda bai san Dakta Hamza ba idan ya yi abin sai ka ji kunya, don kuwa ya kan yi rayuwarsa kamar ta yaro dan shekara goma ba tare da ya damu ba.
¤
matarsa Hafsatu da qanin sa Khalifa wanda yake karatu a Jami'a. Dakta Hamza yana da 'ya'yansa biyu Alfat da Abba, yaran biyu sun saba da ganin yadda mahaifinsu yake gudanar da rayuwarsa. Dakta Hamza kan yi wasan qwallon teburi shi da qanin shi Khalifa, su yi ta jayayya akan makin da kowa yake iqirarin ya samu, duk kuwa da yake Khalifa qanin sa ne na biyar. Shekarunsa ashirin da bakwai a duniya.
¤
Sannan kuma ya kan yi wasan dambe shi da babban danshi Alfat dan shekara bakwai a duniya, wanda suke raba rana kowa yana kaiwa kowa duka, wani lkcn Hafsatu ta kan fito harabar wasannin su tayi kallo. Idan kuma ta ga zai cuci danta sai ta xo ta janye shi ta ce.
¤
"wasan ya isa haka nan, lkcn cin abinci ya yi."
¤
Idan za a lissafo abubuwan da Dakta Hamza ya fi so a rayuwarsa fiya da komai, in har za a yi la'akari da yadda ya kan nuna ne a zahiri, to ya fi son qaninsa Khalifa, daga nan a iya sako 'ya'yansa a mataki na biyu, matarsa kuma ta qarshe.
¤
A farkon auren su sa'ar da Hafsatu tana amarya, da ta ga Dakta yafi son qannin sa, sai ta fara nuna qyashi da kishi. Da Dakta Hamza ya fahimci haka sai ya zaunar da ita suka yi magana.
¤
Khalifa shine kadai dan uwansa da ya rage masa a duniya. Iyayensu biyu sun rasu tun suna qanana, a sannan Khalifa shekarunsa hudu a duniya, shi kuma Dakta Hamza yana da shekara goma sha bakwai. Mahaifinsu soja ne wanda ya rasu a wajen fadan kwantar da tarxoma. Bayan shekara biyu kuma mahaifiyarsu ta rasu. Kafin ta rasu ne ta kamo hannun Hamza ta hada da hannun qaninsa Khalifa ta ce dashi.
¤
"Wannan ciwon ba zai bar ni ba Hamza, ina son kayi mani alqawarin ko bayan raina zaka riqe qaninka Khalifa, ka kyautata masa fiye da kowa a duniya, ynx baka da wanda ya fishi."
¤
Hamza wanda shima yake kuka, ya ce da mahaifiyarsa ya yi mata alqawarin zai kula da qaninsa, kuma zai kyautata masa.
.
A haka da fadi-tashi Hamza ya kammala karatun shi na likita a Jami'a, ya kuma ci gaba da kulawa da Khalifa wanda yake zaune a wurin wani abokin aikin mahaifinsu da suka yi aikin soja tare.
¤
Basu da dangi a kusa, mahaifinsu mutumin Taraba ne, wanda har ya rasu bai nunawa 'ya'yansa biyu inda danginsa suke ba. Ita kuma Mahaifiyarsu bafillatanar Adamawa ce, wacce ya aureta a wani qauye shima ya dade da tashi, sai dai tarihi,wannan ne dalilin da yasa Dakta Hamza da qanin shi Khalifa basu da wasu 'yan uwa da zasu nuna. Sai dai abokan arziqi da suke zaune tare. Ynx idan ba Dakta Hamza ba Khalifa bashi da kowa a duniya, sannan idan ba Khalifa ba Dakta Hamza bashi da kowa a duniya.
¤
Wannan shine asbin da Dakta Hamza ya fadiwa matarsa Hafsatu a taqaice, kuma tun daga lkcn da ta san haka ta daina damuwa.
¤
Idan Dakta Hamza baya nan Khalifa ne yake gudanar da komai na gidan.
¤
¤
Lp=02¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
02
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba.
¤
¤
Ida Dakta Hamza baya nan Khalifa ne yake gudanar duk wasu aikace-aikace dake gidan, shi yake kai yara makaranta, sannan kuma idan Hafsatu zata je wani wuri shi zai kai ta a mota.
¤
A daidai wannan lkc ynx, Dakta Hamza yana qasar Jamani, zai yi kwana shida, ynx kwanan shi biyu da tafiya, saura kwana hudu ya dawo, tun kafin ya tafi Hafsatu ta fadi mashi cewa an yi wata rasuwa a qauye, zata je tayi gaisuwa, amma ba zata kwana ba, a ranar da ta je zata dawo, Dakta Hamza ya ce da ita idan ta tashi tafiyar ga Khalifa nan ya kai ta, tunda dai shi baya nan.
¤
Da yake tafiyar ta kama ranar Asabar ce, Khalifa bai damu ba, tunda ba ranar Karatu ba ce, ya shirya Hafsat ta fito tare da 'ya'yanta Alfat da Abba suka shiga mota suka dauki hanyar xuwa Zariya daga Abuja. Daga Zaria xuwa qauyen Gazari kilomita hamsin ne idan sun bi ta doguwar hanya, idan kuma sun bi ta yanke, sun bi ta garin Galadimawa, kilomita arba'in da biyu ne. Da zasu xo ta doguwar hanya suka bi, sai a dawowa ne da suka ga sun yi yamma, don tafiyar tayi masu sauri, sai suka yanke shawarar su bi ta yanke su shiga qauyuka, har su hau kan titin Kaduna ba tare da sun bi ta Zariya ba.
¤
Da qarfe shida na yamma su ka xo wani qauye mai suna Gogi, a nan ne kuma motarsu ta lalace, Khalifa ya fito ya bude murfin injin ya fara duba inda matsalar ta faru. Hafsatu ta fito tare da 'ya'yanta suka zauna a dakalin qofar wani gida kusa da inda motarsu take. Suna jiran Khalifa ya gyara su tafi.
¤
A qauyen Gogi suka yi sallar Maghrib da Isha'i, har qarfe takea tayi Khalifa bai gano matsalar da ta samu motar ba, kuma gashi babu mai gyara a qauyen, dole sai da aka taimaka masu aka hau Babur aka je wani gari dake a gaba aka nemo masu mai gyara ya xo da kayan aiki. Hafsatu da 'ya'yanta suka shiga wani gida suka zauna a cikin damuwa, don kuwa basu ta6a fuskantar irin wannan matsalar ba a duk tafiye-tafiyen da suka dade suna yi.
¤
Sai da qarfe goma na dare makaniken ya gyara masu motar, ya ce dasu hanyar da suka biyo ce akwai ruwa da ta6o, shi ne ya shiga cikin kafireton motar, sai da aka wanke. Khalifa ya sallami mai gyaran, mutanen qauyen suka yi masu tayin wajen kwana, da suka ga dare ya yi, bai kamata su keta daji da wannan xundumemiyar motar tasu ba.
¤
Khalifa ya yi masu gdy, ya ce zasu tafi haka nan suna so ne su kwana a gida, ya kira matar yayansa ya ce ta fito su tafi an gyara motar. A lkcn tuni 'ya'yanta sun yi barci, ta dauki Abba shi kuma Khalifa ya dauki Alfat suka shiga mota, Khalifa ya tayar da motar suka tafi, shi kadai zaune a gaba, Hafsatu ta zauna a baya tare da 'ya'yanta, suka tafi a hankali don kada su sake samun matsala a hanya, farin watan dake ci kamar rana a sararin samaniya tare da manyan fitilun motar sun taimakawa Khalifa wajen ganin hanyar da suke bi a cikin dajin. Duk da haka sun yi nadamar rashin bin doguwar hanyar da titi yake, don kuwa saurin da suke yi ya jawo masu sun haifi nawa, sun wuce qauyen Turunkawa da kadan motar ta sake lalacewa a rami. Khalifa ya 6ata kusan minti talatin yana ba motar wuta, yana fitowa yana qwaqule qasar data toshe tayoyin motar, lkcn da Khalifa ya fitar da motar sha daya da kusan rabi.
¤
Hafsat ta shawarci Khalifa dasu samu wani qauye su kwana tunda dare ya yi, washe gari sai su tafi hasnkalinsu a kwance. Khalifa wanda ranshi ya 6aci sosai, yayi kamar zai fashe da kuka, ya ce da ita kada ta dau komin dare a gida zasu kwana in Allah Ya yarda, matsalarsu kafin su hau titi ne, ta yi haquri.
¤
Suka wuce wasu qauyukan guda biyu, da kuma wata tsangayar fulani wadanda suka yada zango a wata faffadar gona. A sannan qarfe goma sha biyu ta wuce tuni, sun fara tunkarar daya na dare. Hafsatu wacce take matuqar jin tsoro, ta kifa kanta a bango motar tana addu'a, 'ya'yanta kuwa tuni sun yi barci a jikinta.
¤
Lkcn da suka bar tsangayar fulanin ne a baya, sun xo inda wani Jar gargari yake, babu yawan bishiyu da itatuwa, sai dai tsakuwa da duwarwatsu akan hanyar. A sannan ne fitilun motar suka haskowa Khalifa wata kyakkyawar matashiyar yarinya a kwance a bakin hanyar, da kuma wasu qunshin kayan a cikin zani a gefe guda.
¤
Khalifa wanda shi ya fara ganinta ya ji gabanshi ya fadi, yayi saurin yin salati a bayyane, don kuwa jikinshi ya bashi cewar aljana ce taxo ta kwanta masu a bakin hanyar. Ya dade da jin labarin yadda aljanu ke xuwa bakin hanya su zauna in dare yayi nisa. Salatin da yayi yasa Hafsat tayi sauri farkawa daga gyangyadin da ya fara daukarta. Ta tambaye shi cikin sauri.
"Khalifa....mene...ne?"
ya kasa magana, qafarshi ta fara kyarma, ya kasa taka motar, wanda hakan yasa suka tsaya dab da inda budurwar take. Hafsatu wacce ita ma taga abin da Khalifa ya gani. Ta yi saurin dauke numfashi da taga budurwar wacce take a kwance ko gezau bata yi ba a cikin hasken fitilun motar. Khalifa da Hafsatu suka yi ta karanta addu'o'in su na tsammanin zasu kori aljanar.
¤
¤
Lp=03¤<>¤<>¤<>¤ $@DI¥@ ¤<>¤<>¤<>¤
¤
page
03
with
Iliyas Ishak Gundutse
Abu Ihsan
madugun taska
¤
¤
Khalifa da Hafsatu suna ta karanta addu'o'i, suna tsamanin aljanar zata 6ace ta basu hanya su wuce.
¤
Suna nan a haka a tsorace cikin motar, sai suka ga kamar tana motsawa tana qoqarin tashi zaune. Budurwar ta tashi zaune ta kalli fitilun motar wadanda suka kashe mata idanu ta sa hannu ta kashe mata idanu, tasa hannu ta kare fuskarta wacce take sharkaf da hawaye. Sannan akwai alamar tsoro da razana a fuskar tata, a lkcn ne Hafsat tace da Khalifa.
¤
"Ina jin wannan baiwar Allah mutum ce ba aljana ba ce, wataqila wani abin ne ya same ta na tashin hankali yasa ta shiga cikin wannan halin, amma yadda muka haskata haka da aljanace da ynx ta 6ace, ba zata tsaya muna haskata ba tun daxu."
¤
Khalifa wanda har xuwa ynx bai warware ba daga tsoratar da yayi, ya ce da Hafsatu.
¤
"Anti ba mutum ba ce, idan kuma mutum, idan mutum ce me zai kawo ta nan cikin wannan uban daren ta xo ta fadi ita kadai. Aljana ce Anti, mu ci gaba da addu'a, in Allah Ya so sai ki ga ta 6ace. Ta bmu hanya mu wuce."
¤
Budurwar ta ci gaba da kukan da take yi tana share hawaye, a lkc guda kuma tana tarbe fuskarta daga hasken fitilun. Hafsatu ta sake qarfafawa Khalifa guiwa ta ce dashi. "na fadi maka wannan yarinyar mutum ce Khalifa, bude ka fita ka je ka same ta, ka ji me yake faruwa da ita? Wataqila akwai wani taimako da zamu iya yi mata, kada ka mance, duk wanda ya taimaki wani, to shima Allah Zai taimake shi."
¤
Khalifa ya juya baya ya dubi Hafsatu cikin tsoro. "Anti na san da haka, amma gsky ba zan iya xuwa wajenta ba, ta xo ta kama ni mu 6ace tare? In dai kin san ba aljana ba ce, kina ganin ba zata cuce mu ba to mu rufawa kanmu asiri kawai mu wuce ta, bakinmu qanin qafarmu, kada mu jawowa kanmu masifa muna zaune lfy."
¤
Hafsatu ta ce dashi.
¤
"ni bari in fita komai zai same ni ya same ni tunda mace ce 'yar uwata, in har akwai taimakon da zan iya yi mata, to zan yi, 'ciwon 'yan mace na 'ya mace ne'."
¤
Hafsatu ta bude qofar motar tasa qafarta waje ta gyarawa 'ya'yanta kwanciyarsu, wadanda suke ta sharar barci basu san wainar da ake toyawa ba. Da Khalifa ya tabbatar da gaske matar yayansa fita zata yi wajen aljanar, sai shima ya yi qarfin hali ya kashe motar, amma bai kashe fitilun ba, ya ja burkin hannu ya bude tasa qofar ya ce da ita a lkcn da ta fito daga cikin motar.
¤
"Mu je mu gani tunda kin matsa sai mun je Anti, amma ki tsaya tukuna mu karanta 'Ayatul kursiyyu' qafa uku-uku, sannan mu je wajenta, ba gaggawa zamu yi ba."
¤
Hafsatu tawuce gaba abin ta ta ce dashi.
¤
"In Allah Ya yarda babu abin da zata yi mana koda aljana ce, ka kuntar da hankalinka Khalifa."
¤
Hafsatu ta tafi kai tsaye ta tunkari budurwar, Khalifa ya biyo ta a baya yana ta taka-tsan-tsan kamar wanda zai shiga ramin maciji, jira kawai yake yi yaga wani abu wanda bai amince dashi ba, ya juya baya aguje ya koma cikin mota.
¤
Da Hafsatu ta isa kusa da yarinyar tayi mata sallama da qarfi, yarinyar ta amsa ba tare da ta daina kukan da take yi ba. Hafsatu ta tambayeta.
¤
"Baiwar Allah ke mutum ce ko aljana?"
Yarinyar ta ce.
"ni mutum ce."
¤
"Me ya faru ki ka xo wannan dajin a cikin dare haka kika zauna a nan? Baki jin tsoron kada wani abu ya same ki a nan?"
¤
Yarinyar ta bude baki zata yi magana kuka ya qwace mata, ta kasa cewa komai, Khalifa ya matso dab da Hafsatu da ya tabbatar yarinyar ba aljana ba ce, mutum ce, ya tambayeta.
¤
"ina za ki je ynx? Muna a hanya ne. Ko akwai wani taimako da zamu iya yi maki?"
¤
Yarinyar ta girgiza kai alamar babu wani taimako da zasu iya yi mata a halin...


Read / Download SADIYA cigaban SO BAYAN RAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album