Join Our WhatsApp Group

SO BAYAN RAI Complete Hausa Novel Document by SO BAYAN RAI


SO BAYAN RAI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 35192



SO BAYAN RAI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 181.52 kb

File Type: txt

Views: 847+

Download: 342+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: SO BAYAN RAI
(c) Shafi'u Dauda Giwa
Mai gidan littafi
.
Daga http://fb.com/hausaebooks



>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
.
.
Page 1
.
.
Kowacce shekara akan yi bikin shigowar sababbin dalibai
a jami'ar Ahmadu Bello dake a birnin Zazzau, duk sa'ar da
wannan lkcn yazo dalibai da dama daga jihohi daban-
daban na cikin gida da kuma na wasu qasashen qetare.
Su kan zo suyi dafifi a ko ina a cikin jami'ar wacce ta
tserewa sa'o'inta ta fannin girma, tsarin gine-gine da
kuma uwa uba bila'adadin guraben karatu, musamman
fannin kimiyya da fasaha.
.
.
Ba dalibai kadai ke murna da zuwan irin wannan lkc ba.
Su kansu sauran mutane wadanda basa karatu a
makarantar sukan zo suyi kallon yadda dalibai ke
gudanar da sha'anin murna. Samari da 'yan mata daga
garuruwa daban-daban, musamman irin wadanda ke da
abokai ko qawaye a makarantar sukan zo taya su murna,
su dauki hotuna tare da kuma yawo a cikin faffadar
makarantar wacce ke kama da babban birnin wasu
qananan jihohin.
.
.
Sau da yawa samari "'yan ido mai na ci ban baka ba" a
wajen irin wannan kallon suke yin sababbin 'yanmata.
.
ko a cikin daliban makarantar sau da yawa wasu a irin
wannan ranar suke haduwa da baqin 'yanmata har kuma
soyayya ta qullu. Wannan ba wani abin mamaki ba ne
domin kuwa idan mutum ya yi la'akari da zuqa-zuqan
'yanmatan dake jami'ar wadanda suke daukar idanu
kamar an 6aro su a leda da kuma wasu baqin 'yanmatan
dake qure adaka, su halarci bikin yaye dalibai, an san
cewar dole ne samari su garzayo kowa yazo ya za6i dai
dai qarfin shi, domin kowacce qwarya da abokiyar
zubinta.
.
.
Kyakkyawan saurayi Amir na daya daga cikin daliban
dake karatu a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma
shima yana daga cikin samarin da ke fafutikar samun
sabuwar budurwa a duk wani taro ko shagali da za'ayi na
musamman a makarantar.
.
.
Amir farin Saurayi ne mai matsakaicin tsawo. Wanda a
kowanne lokaci baya rabuwa da tabarau Kalar hadari
wanda ke bayyana qwayoyin idanun shi dake tsaye tarwai
suna kallon mutane ta cikin gilashi.
.
Amir yana kulawa da sumar shi fiye da komai na jikin shi,
domin kuwa a cewar wasu abokanshi dake a makarantar
wai duk kudin tallafin da gwamnati take baiwa dalibai
(scholarship). Amir yana 6atar dasu ne kawai wajen gyara
sumarshi. Ko daga nesa idan mutum ya hangi Amir, zai
fahimci yadda sumar shi take qyalqyali a rana, kuma ta
dan qadandane kadan.
.
.
Amir yana kyau da qananun kaya fiye da dogaye.
Fahimtar hakan ne ya sanya baya rabuwa da qananun
riguna da wanduna (jeans) masu tsada dake kama
jikinshi sosai tare da dunqulallen takalmi mai rufi dake
kama da dutsen guga na zamani.
.
.
Shekarun Amir ashirin da takwas da haihuwa. Kuma
shekarun shi uku kenan yana karatu a jami'ar ta Ahmadu
Bello dake a Zariya. Yana karatu ne a fannin adabin
turanci. Amir yana da farin jini a wurin dalibai domin
kuwa kusan kowa ya san shi.
.
Idan aka dawo 6angaren 'yan mata kuwa, anan sai dai ayi
shiru, domin kuwa a tarihin makarantar ba a ta6a samun
wani dalibi da 'yan mata suke son shi kamar su hadiye shi
ba kwatankwacin Amir. 'yanmata bila'adadin sun same
shi kai tsaye sun sanar dashi cewar suna son shi. Wasu
kuwa ta hanyar abokanshi suke bi suyi kamun qafa,
domin a shawo masu kan Amir ya amince ya ce yana son
su.
.
Abin yana bawa abokan Amir mamaki qwarai da gaske,
domin kuwa sun tsorata da wannan saurayi. Sun san
cewar kyakkyawa ne wanda ya iya saka suttura, kuma
tabbas ya iya magana. To amma duk wannan bai kai
yadda za'ace 'yanmata fiye da dari suna rububi akan shi
ba kamar wani tauraro, kowacce da zarar tazo maganar
ta bata wuce.
.
"Ina son wannan abokin naku Amir, don Allah ku fada
mashi"
.
To amma kuma inda Amir yake girgiza samari shine, duk
matsayin mace kuma duk kyanta, duk tsadar motar da
take shiga, in har tace tana son shi, to ba zai ta6a
sauraron ta ba, ya fi son ya ga mace da kan shi ya furta
mata cewar yana son ta. Kuma ya fi son mace ta riqa ja
mashi aji tana nuna mashi kamar ba ta damu dashi ba.
To amma kuma babu wata budurwa dake iya ja mashi
aji. Duk wacce ya ce yana so da wahala ta tsaya wani ja
mashi aji. Don kada tayi sakaci wani abu ya 6atawa Amir
rai har yayi fushi ya rabu da ita ya je yaso wata
budurwar. Idan har Amir ya nemi soyayya to yana sa rai
da samun nasara, kuma ko da ace ma bai nema ba yana
da tabbacin dole ne suzo wajenshi su ce suna son shi.
.
Amir baya tausayawa 'yan mata a rayuwar shi, domin
kuwa da zarar ya fara soyayya da wata budurwa, ko wata
daya ba zasu yi ba zai watsar da ita, ya canza wata
sabuwar budurwa. Idan irin haka ta faru, 'yanmata da
yawa sukan garzayo wajen abokan shi, wasu har kuka
suke yi domin kuwa basu san laifin da suka yi wa Amir ba
amma kuma ya guje su.
.
"Ni ban san laifin da nayi mashi ba haka kawai na ga ya
qurace min. Kuma na roqe shi ya fada min ya qi ya sanar
da ni komai. Ku tambaye shi idan laifi na yi mashi ya fada
min in roqe shi ya yi haquri."
.
Irin wadannan qorafi a kowanne lkc basu rabuwa da
abokan Amir, musamman wasu guda biyu da suka fi
shaquwa dashi wato Mustafha da kuma Haidar.
Wadannan samari 2n sun san halin Amir fiye da kowa,
domin kuwa daki daya suke kwana
.
Page 2
.
.
.
Wadannan samari biyu sun san halin Amir fiye da kowa,
domin kuwa daki daya suke kwana a makarantar.
.
Da yake daga su har shi Amir din duk 'ya'yan talakawa ne,
da irin wannan suke samun kudi a wurin 'yan mata. Idan
Amir ya yaudari budurwa, bayan ta kamu da
matsanancin son shi, idan tazo wajen abokanshi a rude
doin su taimake ta, sai su yi mata qaryar Amir bashi a
kusa.
.
"Dole ne sai mun sa kudi a waya mun neme shi, ko kuma
suce "yana cikin gari ya fita cikin gari tun daxun, sai dai
mu shiga taxi mu neme shi mu ji abin daya hada ku,
zamu roqe shi yayi haquri ku sasanta, amma aiki ne mai
wahala gaskiya."
.
.
Idan su Mustafha da Haidar suka fadi haka, sai 'yanmatan
su basu kudi masu yawa suce su sayi katin waya su nemo
Asmir a duk inda yake. Wani lokacin Amir yana daki a
kwance yana jin irin diramar da ake tsakanin abokanshi
da 'yanmatan. Haidar shi yafi amsar irin wadannan
'yanmatan.
.
"Amir ya tafi Kaduna, kuma gaskya indai kin matsu to sai
dai ki bishi can, domin wannan maganar ba maganar da
zan tunkare shi a waya ba ce, sai munyi "(face to face)''.
.
'Yan mata da yawa sukan bude jaka su dunqulo maqudan
kudi su bawa Haidar da Mustafha.
.
"Ku je Kaduna ku dawo dashi, zan jira ku 'please'
.
Su kuma da zarar sun amsa sai su dawo cikin daki suna
ihu, suna haurin iska riqe da kudin. Amir ya kan ce dasu
yana daga kwance.
.
"Baku da kyau mutane na, ku basu wahala sosai, babu
sassautawa".
.
Da irin wannan kudin suke rabawa su uku kowa ya sayi
kati ya zubawa wayar shi. Idan kuma an sam budurwa
mai dan sukuni, idan ta 6arar da kudi masu yawa don a
sasanta ta da Amir, sukan je kasuwa su uku su shiga
shagunan sayar da kayan sawa na manyan 'yan gayu su
sayi takalma masu tsada da riguna, kuma a ciki suke shiga
su ci abinci a manyan 'Restaurant'.
.
.
Wasu 'yanmatan kuma Amir bai fara soyayya dasu ba,
sune kawai ke haurin gidauniyar su, suke zuwa wajen su
Haidar da Mustaha domin kamun qafa. Irin wadannan
daruruwan 'yan matan sukan bawa samarin isassun kudi,
domin su ji dadin karkato masu da hankalin Amir ya so
su.
.
"Kada ki damu bebi, dole ne Amir ya so ki, ki bar wannan
a hannun mu".
.
Koda sun fadiwa budurwa haka, ba zasu ta6a cewa Amir
ya so ta ba, su ukun duk bakin su daya, kuma dukan su
mayaudara ne, kuma duk lkcn da suka zanua, ko kuma
idan dare ya yi suna daski, sukan dauki lkc mai tsawo
suna dariyar wahalallun 'yan matan da suke yaudara.
. .
Duk a cikin 'yan matan dake son Amir babu wacce Haidar
ya fi jin dadin hulda da ita, irin Shema'u domin kuwa
yarinyar akwai dasla ga motaci na kece raini. Ta ta6a
bawa Haidar chek din dubu dari.
.
Mtsew kuyi haquri, Na Katse Maku Karatu Ba tare Da Na
Tsammaci Hakanba, Sai Don Wani Uzuri Da Xan Shiga.
.
.>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 3
.
.
Duk a cikin 'yanmatan dake masifar son Amir babu
wacce Haidar yafi jin dadin hulda da ita irin wata mai
suna Shema'u, domin kuwa yarinyar akwai kudi ga
motoci na kece raini. Ta ta6a ba Haidar cek din kudi dubu
dari kyauta tace yasa kati a waya, don kawai ya shawo
mata kan Amir yaso ta. Kuma a kowanne lkc hannunta
baya gajiya da ciro rafofin dubu dai-dai a cikin jakarta.
Inda Amir ya gagari samari shi ne, yana soyayya da
'yanmatan qasashen qetare dake karatu a jami'ar,
musamman Indiyawa da larabawa, kuma abin dake qara
masa nasara da kwarjini shine yana jin turanci da larabci
sosai. Ya iya larabcine tun a karatun Islamiyya da yayyi
mai xurfi a unguwarsu dake a cikin birnin Zariya, turanci
kuwa ba a magana, domin yana a shekararsa ta uku ne a
jami'ar kuma adabin turanci yake karanta.
.
Bayan haka Amir saurayi ne dake son waqe-waqe, kuma
ya iya dadadan waqoqi na turanci da kuma larabci.
Sannan yana rera waqa da Hausa cikin taushin murya.
Wannan baiwarce ta sa idan yana tare da budurwa bata
so su rabu. 'yanmatan dake son shi idan suka samu sa'a
yazo wajensu sun sha su roqe shi.
.
"Amir ina son ka rera mani waqa mai dadi yau."
.
Idan Amir yana waqe masoyiyarshi sai tayi shiru tana
kallonshi ko qiftawa bata yi. Wata kuma sbd kalaman
soyayyar da yake fadi sai tayi ta hawayen soyayya. Ko
kuma tayi tagumi tana sauraren daddadar muryarshi. Shi
yasa da zarar ya daina kula 'yanmata duk sai su rude su
fara biyo shi. A lkcn ne kuma zasu fara 6arar da kudi a
wajen abokanshi, domin a dawo masu da Amir dan
soyayya.
.
A ranar da irin wannan bikin yaye daliban yaxo ne, Amir
yasa qananun kayanshi da yake ji dasu, sannan ya qara
gyara sumar shi ta fito sosai, tare da dan tabaron shi da
yake sakawa kadan akan dogon hancin shi. Ya shiga cikin
dubban daliban dake kaiwa da komowa domin kuwa ya
dade bai yi sabuwar budurwa ba, rabonshi daya 6are
wata budurwa a leda tun kwana sha uku da suka wuce da
yaga wata budurwa balarabiya 'yar qasar Pakistan ya ce
yana son ta.
.
Kwanansu shida kacal ya daina saurarenta, kuma ko ta
kira shi a waya baya amsawa. Sau uku tana xuwa wajen
abokanshi nemanshi, xuwa na farko suka tsara ta suks ce
bashi a kusa sai dai a nemo mata shi idan tana so. Sai a
xuwa na biyu ne ta samo kudi ta bawa su Mustafa, a xuwa
na uku suka ce ta sake dawowa ba a same shi ba. Kuma
ita ma tana nan bata haqura ba tana nan da son dan
saurayi mai farin jini Amir.
.
Amir ya riqa yawo a cikin dalibai yana waige-waige,
'yanmata suna ta kallonshi suna yabawa. Amma kuma
babu wacce ya gani da ta kwanta mashi a rai.
.
Sai bayan wani dan lkc da yaxo wucewa daidai inda wasu
'yanmatan turawa suke daukar hotuna tare da wasu
qawayensu hausawa da suka shaqu a makarantar, Amir
ya hango wata a cikinsu wacce shi a wahenshi tama fi
turawan kyau, domin kuwa fatarta irin kalar da ba a san
takamaiman yadda za a kira ta bace, duk jikinta daga
sama har qasa kalar hoda-hoda ce, kuma da ganinta haka
take a halicce, idanunta kuwa masu tsawirya ne irin
wadanda masana sirrin kyawawan mata suka ce, wai sai a
tara mata dubu ba a samu mata hudu dake da irin kalar
idon ba. Daga nesa idanun budurwar kamar ruwan toka-
toka suke, amma idan mutum ya matso kusa sai yaga
idanun kamar sun cika maqil da hawaye, suna yawo a
cikin laima.
.
Amir ya tsaya a wajensu yana murmushi, ya gaishesu kai
tsaye kamar yadda wayayyun samari ke tunkarar
budurwa kai tsaye ko wacece babu shakka ko tsoro ya ce
da budurwar cikin harshen turanci.
.
Ku biyo Iliyas dauke da
page 4
>===< "SO BAYAN RAI" >===<
.
.
Page 4
.
.
Sannan ya nuna wacce ya gani yana so da yatsa ya ce da
ita cikin turanci.
.
"Wurinki naxo 'yanmata."
.
Budurwar tayi dariya. Tana sanye da dofuwar riga baqa
marar hannu wacce ta bude da kuma baza a qasa kamar
dawisu. Ta taso ta biyo Amir, sauran 'yanmatan turawan
suna yi mata wasa. Amir ya jata suka tsaya a jikin wasu
shuke-shuke a bakin hanya.
.
"suna na Amir."
.
Ya ce da ita yana kallon xubinta da dirinta.
.
"Ni kuma suna na Ni'ima."
.
Sai a lkcn da yaji sunanta sannan ya fahimci bahaushiya
ce daga irin lafazin harshenta, idan tayi turanci akwai
jirwayen hausa a ciki. Don haka tana jin hausa. Amir yayi
mata hausa kai tsaye ya ce da ita.
.
"gaskiya Allah Ya hore maki kyau baiwar Allah, mutane
naea suke fadi maki haka a kowacce ranar duniya?"
.
Ni'ima tayi murmushin farin ciki, sannan ta ce dashi.
.
"ko a yau samari fiye da goma sun fadi min haka har ma
na gaji da saurare."
.
Suka yi dariya a lkc guda.
.
"haka ne Ni'ima."
.
Amir ya ce da ita.
.
"amma kuma masoya suna yawan fadiwa duniya cewa
kyau bashi da muhimmanci in har ba aci moriyarshi ta
fuskar soyayya ba. Ma'ana in har mace kyakkyawa ce to
yana da kyau ta amshi soyayyar wanda ya fada a tarkon
sonta, ta haka ne zata fahimci ko ita wace ce a duniyar
'yanmata."
.
Ni'ima ta ce dashi.
.
"nima ina girmama soyayya a rayuwata, kuma ina da
sauqin kai wajen amsar soyayyar wanda ke neman
soyayyata. To amma kuma na cika tsoro da kuma
fargaba, ina matuqar tsoron soyayya, in har aka ambaci
wannan kalmar na kan ji gabana ya fadi."
.
"sbd me Ni'ima?"
.
Ta dan yi tunani kadan kafin ta ce.
.
"sbd na dade ina ganin qawayena suna fadawa cikin
tarkon soyayya, kuma suna matuqar shan wahala kafin
su fita. Ina tsoron fadawa cikin irin wannan tarkon Amir.
Shi yasa mafi yawa nafi son in zauna cikin mata 'yan
uwana, ina jin tsoron in zauna da wani saurayi."
.
Amir ya yi mata murmushi kafin ya ce.
.
"lallai kin bar dadin duniya Ni'ima, ni kuma kin ga a
duniya babu wani abu da ya kai zama da masoyi dadi,
soyayya ni'ima ce daga Ubangiji Ya yiwa 'yan Adam
kyauta, ko baki da komai zaki iya zama da wanda yake
sonki, kema ki yi farin ciki irin na kowa, zaku kasance a
cikin annushuwa da begen juna. Soyayya zata iya wanke
duk wani baqin ciki dake a cikin xuciyarki komin
dadewarshi a tare dake. Kuma soyayya zata iya canza
maki halaye ki qara wayo da hikima da qwaqwalwa. Idan
kika riqe soyayya da kyau a xuciyarki, to zaki mance da
wasu wahalhalun rayuwa dake damun sauran mutane a
wannan duniyar. Me yasa zaki bar irin wannan babbar
gara6asar mai dadi Ni'imah?"
.
Budurwar taji Amir ya burgeta sosai, akwai alamun
gaskiya a maganganunshi, daga baya sai tayi ajiyar xuciya
sannan ta ce.
.
"gsky naji dadin ganinka Amir, domin kuwa babu wani
mutum daya ta6a fada min wannan sirrin dake tattare da
soyayya. Me yasa to sauran mutane basu san haka ba? Me
yasa kowa ba zai xo ya riqe soyayya ba?"
.
Amir ya ce.
.
"Sbd ba kowa ya san sirrin soyayyar ba Ni'ima. Akwai
wani abu guda daya da har ynx masoya basu gane ba.
Sau da yawa soyayyar da jini yas hada tafi soyayyar da
idanu suka hada nesa ba kusa ba, idan jinin masoyi ya
hadu dana abin son shi ko basu ta6a ganin juna ba, to da
zarar sun yi arba kuma zasu fahimci sun dace da juna,
kuma kai tsaye zasu fara soyayya ba zasu so abin da zai
nisantasu da junansu ba. Amma soyayyar da fuskoki suka
hada ita ce wacce kawai saurayi zai ga budurwa ko kuma
budurwa taga saurayi su ji wani abu dake tattare dasu ya
burge junansu, daga baya...


Read / Download SO BAYAN RAI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album