Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

ASIRINSA YA TONU Complete Hausa Novel Document by ASIRINSA YA TONU


ASIRINSA YA TONU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51187



ASIRINSA YA TONU

Reading Time: 4 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Fadeela Lamido ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 305.44 kb

File Type: txt

Views: 450+

Download: 566+

Last download: 2 days ago

Description/Story: β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦
*ASIRINSA YA TONU*
β„πŸ’¦β„πŸ’¦β„πŸ’¦


β„β„β„β„πŸ’¦
*By*
β„β„β„πŸ’¦
*Fadeela Lamido*
β„β„πŸ’¦

β„πŸ’¦


*Bismillahir Rahamanir Rahim*



β„β„πŸ’¦
*Page 1 to 3*
β„β„πŸ’¦



Yara ne yan kimanin shekara 14 su uku suke buga ball duk kansu mata ne kuma kamarsu daya farare tas, idan ba sanin su kayi sosai ba baka iya banbance su"

Wasan su suke hani,an sai faman ihu suke, inda kasan wasu garadan maza, shiga sukayi kamar yadda cikakun yan ball keyi saidai na yariya 1 da ya babban ta domin kuwa duk cibiyanta waje yake, kirjinta kawai guntuwar rigar ta rufe"

Zuwa cen daya daga ciki ta tsaya cak tare da zunboro baki tana fadin"

Nidai gsky *Nehilah* manayi dan kinga kin fimu iyawa saikita mamayan mu"

Tsalle wadda aka kira da suna *Nehilah* tayi sannan ta buga ball din tare da fadin kada Allah yasa kiyi bari yaya ya dawo mayi tar....


Daidai lokacin wata dadtijuwar mata ta futo,tai tsaye asaman bene cikin fada tace"

*khadi sadiya* kuzo Ku wuce ciki, nagaya muku ku daina beyewa wannan shashashar yariyar, ku barta taitayi, tunda ita kunnenta na kashi ne"

Tunin khadi da sadiya suka nufi shiga gida, yayin da *Nehilah* tayi tsaye ta turo baki"

Harara matar ta zuba mata sannan tace"

Zakizo ki shige gida ko sai na sameki agurin"

Cikin sauri ta fara takawa tare da buga kafafuwanta akasa tana kunkunai"

Koda ta shiga babban falon gidan bata bi takan kowa ba kai tsaye dakin su tashige"

Matar ce ta bita da kallo sannan tace lallai akwai aiki"

Daidai lokacin Wata mata ta fito daga daki sanye da gyale, ga dukkan alama fita zatayi, dan murmushi tayi sannan tace"

Aini duk tabaran da *Nehilah* zatayi bana ganin lefinta, *Yaroh* shine babban me laifi, shine ya shagwabata ki duba fah duk kannesa ba wanda yake sakin ma fuska sai *Nehilah* sabo da yana ganin cikin su guda, sauran ko uba suka hada, karashe mgr tayi cikin haushi"

Cikin mamaki matar tace *hajiya babba* wannan wacce irin mgn ce banda abinki ai kinsan halin *yaroh* basan mgn ne dashi ba"

Hmmm *Antyn su* kisan Allah *Yaroh* yan ubanci yake nunawa, dan duk wani dadaure fuskan shi akan yaran dakina yake sauka, *Nehilah* ko tunda yaga shine yasha nono ya rage mata tattalin ta kawai yake, aini tuni nagano manufar shi, dan haka nagayawa yaran dakina su kiyaye shi"

Ajiyan zuciya *antyn su*ta sauke cikin rashin jin dadin zancen tace"

Aini bansan da wani takun saka tsakanin *yaroh* da kannen saba, amman zanyiwa tufkar hanci"

Tafiya *hajiya babba* ta fara tana fadin nidai saina dawo"


Itako *Nehilah* gado ta fada cikin haushi ta fara neman no yayanta
Sai dai wayar kashe take"


Misalin karfe 4:30pm ne *Nehilah* taji tsawar motar yayan ta, wani zilo tayi ta doro daga gadon har yanzun tana nan cikin shigarta ta dazon, waje ta nufa cikin murna bata damu da yanayin jikinta ba"


Tana isowa matashin saurayin na fitowa daga cikin motar dogo ne fari tas daka kalli fuskar *Nehilah* ka kalli ta wannan saurayin kasan ciki daya suka fito, sabo da tsananin kama da suke, koda duk familyn kama suke da juna, amman ta *Nehilah*da yayanta tayi yawa"

Jikin shi ta fada tare da lumshe ido, shima cikin kulawa ya kara mannata ajiki, tare da sun kuyo da kanshi yana leken fuskanta, zuwacen yace"

*Neehila* meya same ki? daga ganin idon nan naki kinyi kuka"

Wani hawayen ta sake matsuwa sannan tace"

Ba Anty bace.....

Katseta yayi da fadin tace kin cika wasa?

Cikin sauri ta daga kai"

Dagata yayi cak ya sakata awuya, sannan ya kwantar da murya yace"

Rabu dasu share hawayenki"

Dariya ta fara sannan ta zagayo da hannun ta ta rike fuskar shi"

Ahaka suka ratsa ta falon gidan inda khadi da sadiya ke zaune kauda idon su,sukayi dan da sun kallesu yana iya zagin su"

Dakin Anty suka shiga, tare da sallama, jin dariyan nehilah ya sata saurin dagowa Ido ta zuba musu cikin takaici tace"

Yaro gsky bana son irin wannna yaya zaka dauki yariya sangwamemiya kamar *nehilah*ka mata maka wuya banda lalacewa shekaranta nawa?

Dariya yayi tare da sakkota, kan kujara ya daura ta sannan yace"

Anty nifah bana ganin girmanta, har yanzun neehila yariya ce 14 fah gareta, haba anty yaushe aka haifeta?

Daidai lokacin *nehilah* ke fadin yaya yau fa nayi ball kafah fuwana zafe suke zokayimin tausa

Cikin sauri ya nufeta ya fara dannan mata kafah yana matsawa"

Tsaye Anty tayi tana kare masu kallo hakika tana son dakatar da wannan dabi,a ta *yaroh* da *nehilah*, saidai duk ta inda ta bullu musu kyaucewa suke, tana cikin wannan tunanin taji muryan shi yana fadin *neehila* da kk gama ball din kinyi wanka kuwa?

A,a toh ai Anty ce tayi min fada"

Oyya maza tashi kije kiyi wanka"

Cikin shagwaba tace"

Yaya nifah agajiye nake anjima zanyi"

Girgiza kai yayi domin yafi kowa sanin taurin kai irin na kanwar sa, hankalin shi ya maida gurin anty suka cigaba da hira"

Zuwa can ta sauko jikin shi ta sake darewa tare da kamo hannun shi ta daura akan kafarta"

Matsa kafar ya fara ba tare da ya waigo ya kalleta ba,

Yayin da antyn su ta zuba musu ido, azuciyarta take fadin Ikon Allah "

zuwa can ta fara lumshe ido alamar tanajin bacci, dan haka ya dan girgizata"

Zabura tayi atsorace cikin rarrashi yace "

Tashi ki koma dakin ki"

Ba musu ta mike dukkan su bayanta sukabi da kallo, harta kule"

Shima mikewa yayi yana fadin anty bari naje na watsa ruwa neehila ta shafamin warin zufah"

Har yakai kofa yaji Anty tace ah ah Yaro, aiko inason mgn da kai"

Tsayawa yayi cek sannan ya dawo ya zauna"

Kara tamke fuska Anty tayi sannan tace"

Meya faru tsakanin ka dasu khadi ?

Mamaki ne ya kama shi Anty meko? ance miki wani abu ya farune?,

Shiru anty tayi domin ita kanta tasan babu abin da ya faru, dan haka tace"

Yaro ka natsu sosai kaji abinda zan fada maka,

Kwata2 banajin dadin abin da kake yi, yaran nan dukka kannin ka ne, dan me zaka ware nehilah ?, koko so kake kajamin zagi dan kasan ba abu me wahala bane ace ni nake kitsa muku"

Shiru yayi kansa akasa zuwa can yace"

Anty nifah ba wani abu dasuka min, kanninane fah, ai idan ina sakar musu fuska
rainani zasuyi"

Hmmm *yaro* nidai nagaya maka ka bari kawai banaso wani irin wasa ne bakayi da nehilah me yasa bata rainaka ba?

Anty ai ita nehilah tasan darajata da mutuncina, kuma batason baccin raina, dan haka nima nake kokarin faranta mata"

Toh ni dai na gaya maka kabari banaso dukkan su kannan kane banason kana nuna banbaci atsakanin su"

Shiru yayi zuwa can ya bude baki ahankali yace"

Anty wai ke yanxun har kin manta lokacin da hajiya babba takemin gori cewa tunda kika haifeni ko bari baki sakeyi ba, nasha zuwa daukan salma gurinta amman ta hanani daukan ta, har cemin tayi 'ya'yata ba kanni na bane, ni ahaka zan kare banda abukin shawara, shiyasa Allah ya tausaya min ya bani nehilah, shiyasa tun tana karama nake neman shawara agurinta"


Kallon shi kawai anty take,
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download ASIRINSA YA TONU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album