Join Our WhatsApp Group

GURBIN IDO Complete Hausa Novel Document by GURBIN IDO


GURBIN IDO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 97468



GURBIN IDO

Reading Time: 8 Hours

Added On: 04, Apr 2023

Author: Safiyya Abdullahi Huguma ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 9134848107

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 540.97 kb

File Type: txt

Views: 10542+

Download: 5686+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: iya ganinka,wanda ya wadatu da korayen tsirrai da kuma shukoki nau'i daban daban,masu tsaho da kuma gajeru,ciyawa tafasa da sauran tsirrai da ubangiji ya huwace musu su wanzu a wajen,wanda wasu ma dan adam bai san meye ba,wasunsu kuma magani ne da garkuwa ga jikkunan dan adam.

Yadda sararin yayi kore shar da nau'in tsirran da kuma yawaitarsu kadai xai bayyana maka cewa muna lokacine na yawaitar saukar ruwan sama wato lokaci na damina,duk da da cewa gurin waje ne mai cike da ni'ima da kuma albarka,albarka data sanya mawuyacine ka samu wajen a bushe ko kuma a qafe.....wannan dalili ya kawo wanzuwar fulani wajen a muhallin,suka kafa bukkokinsu suka kuma tashi gagarumar ruga a wajen....saboda waje ne daya dace da muradinsu da kuma buqatar dabbobinsu,wanda buqatar dabbobin nasu sama take da tasu buqatar.

Yammaci ne lis,wanda daqiqu kadanne ne zasu ratsa magariba ta shiga,lokacine da kowanne makiyayi yake qoqarin kada kan dabbobinsu zuwa gida inda zai turkesu saboda gabatowar dare,daga cikin wannan dajin mabanbantan tawagar shanu wani lokaci harda raguna da akuyoyi ke kutsowa cikin ainihin wajen da suke kira da gari a wajensu,kowanne tawaga na tafe ne da masu kula da ita,mutum biyu uku hudu har zuwa biyar idan sunyi yawa,yawancinsu maza ne,matan dake ciki daidaiku ne.

Da sannu sannu wadan nan dabbobi ke wucewa zuwa guraben da muhallinsu yake,kamar sun gama wucewa.....saiga wani garken na daban na bullowa a hankali.

Kyawawan shanu ne tunkiyoyi raguna da kuma awaki masu tarin yawa da daukar hankali,ba komaine ya kawo haka ba sai yanayin qoshi da kuma tsaft da garken keda yashi,kusan duk dabbar dake ciki fara ce.....sai wasu daga ciki dake da ratsin ruwan qasa......duka ba wannan ne abun mamakin ba,abu mafi daukar hankali shine Kyakkyawar matashiyar dake kara kaina daga hagu tsakiya xuwa daman dabbobin tana saita su,da fari zaka zaci ba ita daya ke wannan aikin ba,amma idan ka tsawaita dubanka a kanta zaka fahimci ita kadai dince,dauke da sanda guda daya tak.

Kyakkyawa kyau na musamman kuma na asali koda cikin fulanin,irin kyan da zaka tsammaci half case ce,maimunatu nada wani irin kyau na daban wanda ke sanya duk wanda yake baqon gani a gareta ke bata lokacinsa wajen binta da kallo,saidai kuma.....duk da wannan kyau nata babu mutum daya daya aboceta wajen tahowa gida,kusan kowa ya kado dabbobinsa ya barta,babu koda mutum daya ma cikin wadanda sukayi gaba dake waiwayota ko duba halin da take ciki bare yayi niyyar tayata ta samu ta iso gida da wuri.

Kusan itama hakan bai dameta ba,duk da tanashan wahala,amma ya zamar mata jiki,ta kuma saba da yanayin......sanye take da baqin saqi maimakon farin saqi da akasan mafi akasarin fulani na tu'ammali dashi,zaka iya hangen yadda kayan suka dangale mata sosai fiye da dangalewa ta al'ada da aka saba gani tattare da fulanin,don kuwa koda rigar maimunatu tayi dagewar da banda baqar rigar yadi data saka daga ciki,babu abinda zai hana mutum ya hango albarkatun qirjinta da suka fara tasawa,sai kuma yalolon baqin mayafin data sake rufe qirjin nata dashi,duk kuwa da cewa ba wani kauri ne dashi ba,bashi da maraba da abun tace koko,hakanan bashi da tsaho,don ko mazaunanta baikai ba,tun abun yana da girma da kuma kaurinsa take amfani dashi,amma har kwanan gobe ta kasa rabuwa dashi,saboda dumbin tarihin da mayanin yake dashi a gareta da kuma rayuwarta gaba daya.

Zanin jikinta shima a dage yake sasai,kanta na sanye da Hular kaba irin wadda fulani ke yawaita amfani da ita da suke kira da(malafare)sakamakon yawaitar zafin rana ko kuma tunanin saukar ruwan sama,wadda ta baiwa doguwar jelar gashin tsohon kitson dake kanta bayyana sosai,kitson DOKA inji hausawa,su kuma suce dashi(BIƊEJI)(mai tudu daga tsakiya)shine a kanta,don haka jelar ga sauko dama da hagu na fuskarta da kuma bayanta,abinda ya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau da kuma bayyana asalin yarenta.

Kunnenta babu dan kunne,saboda bata dashi,bata ma ta'ammali dashi,amma hannayenta cike suke cankas da duwatsu kalar kore shar da kuma ja,irin shirin duwatsun da akasan fulani dashi,hagu da damanta gaba daya,masu yawan gaske,wasu daga ciki ma sun girme mata,amma dai wasu abubuwane da bata iya rabo dasu,tana jinsu ne tamkar fitar numfashinta.

Daga qugunta salkar ruwa ce ta duma da aka fafe daure tam,abu guda daya da take da damar tafiya dashi zuwa wajen kiwo,qafafunta kuwa wasu takalman roba ne rufaffu wanda baka rasa bafulatani dashi saboda yanayin shiga daji qayoyi da sauransu,shi kadaine fari a jikinta,duk da tsufar da yayi amma fes yake,da alama ya samu kulawa.

Cikin matuqar juriya da kuma jajircewa take wulga sandar tata tana maida dabbobin hanya,duk kuwa da cewa numfashinta baya sauka zuwa cikin cikinta saboda uwar yunwar dake sakadar hanjinta kamar zata tsinka mata su,cikin matuqar kulawa take kada sandar,saboda ko kadan batasan ta samu kowacce dabba a cikinsu,wannan kusan al'adarta ne,bata dukansu,saidai duk umarnin da zata basu suna ji suna kuma biye da ita,hakan ya haifar da shaquwa mai ban mamaki tsakaninsu,idan tana magana dasu wani lokaci,kai kace tana magana ne da mutane 'ya uwanta.

Har mantawa take cewa ba bil'adama bane kamarta,sau tari takanji sunfi mata mutanen dake kewaye da ita take kuma rayuwa a cikinsu,idan tana tare dasu,tana jin kamar bata da wata sauran damuwa,tana daukansu ne kamar wasu 'yan uwanta.

Sannu a hankali take ci gaba da kadasu cikin juriya da qarfin hali zuwa hayar da zata sadasu da gida.

Tafiya me matsakaicin nisa suka bayyana a rugar ummaru,faffadan riga mai dauke da bukkoki masu yawa,ga wadanda suka zaunu kuma sun fara gini na jar qasa da kara wanda suka tasheshi a matsayin katanga.

Ta bayan dakunan da suke mallakin wasu suka keta,jimawa kadan sai gasu a haggo(wajen daure dabbobi),ta waiwaya a hankali tana duban sararin gidan,babu matar daya zame mata wajibi duk sanda fa dawo ta shaida mata dawowarta,wannan qa'ida ce,wadda tsallaketa ko saba mata dai dai yake da saima kanta tashin hankali da rashin nutsuwa tsahon wasu kwanaki,idan ma batayi sa'a ba,cikin duka kwanakin da zasu biyo.....za'a yita kiranta da sunan da duk duniya babu sunan data tsana sama dashi

"Miwarti inna!" Ta bude dukka kaifi muryar da Allah ya bata tana qwalawa innar kira tare da shaida mata ta dawo,saidai yanayin zaqin da muryarta ke dashi,sam bata da amsa amo ko kuwwar da kiran xai isa inda takeso

"Inna miwarti!" Ta sake fadi,saidai da alama ko kusa da inda innar take basu jita ba.

Waiwaya tayi gefe guda,yarone dan kimanin shekara takwas,zaune yana wasa abinsa,yayi fututu,kai zaka ce daga sansanin gudun hijira aka tsamoshi,kai ta jinjina,tanason tace dashi wani abu amma tana tsoro kada cibi ya zama qari,bata da zabi illa ta aikeshi ya kira innar

"Laulo,yanoddanan inna" daga kai yayi ya dubeta yana yamutse fuskarsa dake harmutse da qasa

"Owalad'o(bata nan)" ya amsa mata a tsiwace yana maida kansa ga wasansa.

Kanta ta daga sama tana kallon sararin samaniya,hadari ne yake hadowa wanda bisa dukkan alamu ba zai dadeba zai bada ruwa daga yanzu zuwa kowanne lokaci,bata qaunar yanayi irin wannan,lokacin da take dawowa daga kiwo.....cike da gajiya qishi da yunwa,take fara ta turke dabbobin a muhallinsu....ta sanar da inna ta kuma shaida dawowar tata,ta wuce zuwa cikin gida,duk da cewa koda ta wuce din bata da tabbacin samun hutun da dukka jiki irin nata daya wuni yana kara kaina tsakanin jeji da jeji a tsakiyar dabbobi,ba shakka da biyu inna ke aikata hakan a gareta,sai taja da baya kadan ta jingina da wani turke tana ci gaba da duban sama,zuciyarta cike da addu'ar dawowar inna a wannan lokacin.

Cikin matuqar d'ar d'ar take a wajen,duk da ba karatu ne da ita ba mai yawa....amma ta sani xama a wannan lokacin cikin turakun dabbobi abune mai hatsari,bugu da qari ma,a al'adarsu tasan yadda suke taka tsantsan da wajen a lokaci irin wannan.

Sosai ta lula cikin duniyar tunani a dan zaman da tayi a waje,wanda har batasan laulo yabar wajen ba,hakanan batasan hadarin ya gama hade jikinsa ba waje guda,ya kuma fara busa iska dake hade da qura,saida qurar ta gifta ta gaban idanunta,daidai sanda ruwa ya fara sauka.....dai dai kuma lokacin da idanunta suka kai mata ga dabbobin da suka tarwatse a wajen.

Da sauri ta miqe cike da fargaba guda biyu,na farko ruwan saman da zai taba jikinta duk yadda taketa qoqarin kauce masa,na biyu kuma warwatsewar dabbobin data tabbatar da cewa saita sake wani aikin kan ta hade kansu.

Tana miqewa dai dai bullowar wata mata,doguwa ce sambal,farar bafulatana ta usul,sanye da fararen kayan saqi,ta yane kanta da babban mayafi kore shar da shi,a gurguje matar take,da alama itama tana gudun tabatan da ruwan saman zaiyi

"Maimunatu!"ta qwala mata kira bayan taja birki tana hangota tsakiyar dabbobin cikin dan ragowar hasken da duhun hadari dana dare ya fara hadiyeshi

"Na'am inna"

"Muguwa!......saboda bana nan ne shine kika barmana dabbobi su wulaqanta......seto me wanna nima ɓerde(sai na bata miki rai),ki kamasu ki kallaceminsu" daga haka ta sanya kai zuwa shiyyar da dakunansu suke ganin ruwan na sake qarfi.

Abinda ya daga hankalin maimunatu kenan,ta riga data saddaqar yau din mawuyacine ta samu barci matuqar ruwan yaci gaba da taba jikinta,wani irin jiki Allah yayi mata da baya qaunar ruwan sama,indai zai tabata to lallai zata kwana da zazzafan zazzabi,amma sai gashi innar ta wuce abinta ko a jikinta,nata burin dai kawai ta tattala mata dukiyarta.

Duk da yadda ruwan yake dukanta hakata dinga kamasu tana killacewa,ta daure wata saniya tana laluben danta da aka haifa wancan satin,santsin tabon dake wajen ya debeta,ta tafi suuuuu idanunta a rufe tana jiran ta jita a qasa,amma sai taji wani abu ya cake gaban qafafunta,abinda ya hanata faduwa kenan,ya kuma sanyata bude idanunta d asauri wanda tun kan ta bude din haske ya cika idanun nata.

Tarwai ta bude manyan idanun nata da ruwa ya jiqe gashin idanun nata,kamar yadda ya jiqe na girarta da kanta yasa suka hade gaba daya,fuskarta ta sake haske ta kumayi tarwai da wani irin kyau.

Idan har idanunta dai dai suka nuna mata mutum ne tsaye a gabanta,matashin saurayi dauke da lema da kuma fitilar torch light mai tsananin haske.

Da sauri taja da baya cike da tsananin tsoro,saboda tunda take kaf kafin rugarsu bata taba sanin wannan fuskar ba,abune kuma mawuyaci indai kaidin haifaffen rugarne ka tashi bakasan dan wani gidan ba"tsaya mana" ya fadi da dan qarfin murya amma a tausashe,abinda ya dan bata nutsuwar tsaiwar,yadda take dubansa ya tabbatar masa data gamsu dashi ba,don haka yace

"Me kike a ruwa a daidai wanna lokacin a haggo?" Qas tayi da kanta saboda wadatuwar hasken da walqiya ta bayar a lokacin ya haska mata fuskarshi sosai,ta kuma so ta ganeshi

"Ina daure dabbobi ne" kamar xaiyi magana sai kuma taji baice komai ba,ya ajjiye lemar kansa gefe,ha saqale fitilar a jikinsa,ya fara kama mata dabbobin yana tayata dauresu.

Tsai tayi tana dubansa,sai kuma ta taka a hankali itama ta fara kama wadanda zaa daure din tana tayashi sunayi tare,lokaci lokaci tana satar kallonsa,kamar yadda shima yake satar kallon nata lokaci bayan lokaci,ta gaza gasgata idanunta,wani yau a rugar yasa hannunsa yana taimakonta?,abinda ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya faru ba,rashin sabo da ganin hakan ya sanyata dari dari dashi,har zuwa sanda suka gama tas,ya qarasa wajen lemar ya dauketa yana rufeta,saboda bata da wani sauran amfani a wajensa,saboda abinda zatayi masa rigakafi dashi ya riga daya faru.

*ZAFAFA BIYAR*

*_Kundi kuma dausayin zaqaqa kuma da d'ad'an litattafan hausa masu cike da nishadi soyayya darasin rayuwa dana zamantakewa,tsantsar ilimantarwa da kuma fadakarwa_*

*Wannan karon ma gasu tafe da wasu taskirar tsararrun litattafan guda biyar*

SANADIN LABARINA
Hafsat rano

BABU SO
Billyn abdul

GURBIN IDO
Huguma

FARHATUL K'ALB
Miss Xoxo

INAYAH
Mamuhghee

Dukka guda biyar din akan

1k

Guda hudu:::700
Guda uku:::500
Guda biyu:::400
Guda daya:::300

*_Garzaya ki biya naki a fara a kan idanunki ta wannan account din_*

Hafsat Kabir Umar
2270637070
Zenith bank

*Saiki tura shaidar biyanki*
07040727902

*MASU KATIN WAYA ZASU TURAWA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYA*

09134848107

*_KARKU MANTA.....HAR KULLUM,SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA NE_*

*GURBIN IDO*👀👀👀

*Free page 02*


"Migodake" ta fada a hankali tana sharce ruwan fuskarta,dubanta yayi,ya sakar mata murmushi,wani abu me suna nutsuwa da sanyin halin daya karanta tattare da ita na dan qaramin lokaci yana burgeshi

"Karki damu,ba komai" kai ta jinjina,saita juya tana nufar cikin gidan tana qudundune jikinta waje daya saboda yadda sanyi ya fara ratsata,da alama akwai damuwa kenan,yayin da shi kuma ya juya ya dauki torch dinsa ya fara gangrawa yana barin wajen,saidai sau kusan uku yana waiwayarta kafin ta qule masa yabar ganinta,ya sauke ajiyar zuciya yana maida hankalinsa sosai ga hanya,zuciyarsa na qissima masa ita,tsahon wanzuwarsa a rugar bau taba kula da ita ba,hakanan bai taba ganin macen da Allah ya zubawa kyau me sanyi da tsari irinta ba,ko wacece ita?,da wannan tunanin ya isa kofar wani gida,wanda shi dayane kaf kafin wajen dake dauke da ginin qasa da bulo.

Babban tsakar gidane daya kasance wayam babu kowa saboda ruwan daketa sauka,yakai dubansa ga dakunan dake jere a tsakar gidan,har ya nufi wani daki daga ciki,sai kuma ya dakata ya juya akalarsa zuwa wani daki dake daura dashi,muqullin ya taba,a rufe dakin yake dole dai ya karbo muqullin,abinda yasa ya juya da dan sassarfa ya nufi daya dakin,yasa hannu ya dage asabarin da aka saukema qofar dakin saboda kaucema shigar ruwa.

Dumine ya fara dukan fuskarsa kafin hasken fitilar aci bal bal dake dakin ya cika masa idanu,matasan mata ne guda biyu da yaro namiji guda...


Read / Download GURBIN IDO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On GURBIN IDO
avatar
salima

11 months ago

Reply

Nice story

avatar
ibrahim-6-8

9 months ago

Reply

That's so amazing

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album