Join Our WhatsApp Group

BAN DACE DASHI BA Complete Hausa Novel Document by BAN DACE DASHI BA


BAN DACE DASHI BA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10367BAN DACE DASHI BA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 09, Jan 2024

Author: Aysher Angel ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 09169472057

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 59.68 kb

File Type: txt

Views: 812+

Download: 211+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 💨 *BAN DACE DASHI BA* 💨
By Hafsat Hisham
*(AYSHER ANGEL)*


Page 1 and 2
Free page

Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057


Abroad,
Sanye take da dogon wando da rigar sanyi mai hood, ta rufe kanta da hular rigar wanda ya rufe rabin fuskarta tareda kitso da aka yi mata kirar kalaba wanda ya bazu, kanta a kasa take tafiya tana sauri, kafin ta ankara taci karo da mutum, under her breath tace,
"Sorry....".
Maheer ya bita da kallo cike da mamaki, Kasim ya tab'oshi saying,
"Let go...".
Maheer yace, "Wait... Wannan yarinyar da nayi karo da ita muryarta da kammanin fuskarta sak irin na abokina ne wanda nike nema tsayin shakaru...".
Kasim yace, "Kana nufin Mujahid, yaron nan da ya kasa fita daga tunaninka...".
Maheer yace, "Yeah... Duk da sau daya na tab'a haduwa da yaron nan amma ya kasa fita daga tunanina, kallo daya zakayi mashi ka fahimci yana cikin damuwa, har zuwa yanzu ina jimamin halin da zai kasance a ciki...".
Kasim yace, "Wannan kuma kai da bakinka kace min macece...".
Maheer yace, "Ehhhh macece saidai muryarta da kammanin fuskarta sak irin nashi ne, but ita wannan tafi kama da black Americans, bata yanayi da en Nigeria... Saidai zuciyata tana ayyana min cewa zata iya kasancewa tsanin da zai sadani dashi...".
Kasim yace, "Ta ina zaka iya samota a kasar nan?".
Maheer yace, "Wait and See...".
Kafin Kasim ya ankara Maheer ya b'ace babu shi babu alamarsa, under his breath yace,
"What's so special about that boy da har Maheer ya kasa mantawa dashi...".
Direct ta wuce inda locker take ta bude ta dauki abun da yake a ciki sannan ta juyo, Maheer yayi nemanta har ya gaji yayi tsaye yana bin wajen da kallo wanda yake dauke da floors da yawa, samunta abu ne mai matuk'ar wahala a gareshi, idan ya sameta miye zaice mata, ji yayi an taboshi yana juyawa yaci karo da ita, da turanci wanda yake zaune akan harshenta tace,
"Ka tare min hanya...".
Da sauri ya matsa ta wuce tana tafiya da sauri-sauri, ya bita da kallo fuskarsa dauke da mamaki the more yake hango fuskarta the more yake ganin Kammanin da takeyi da Mujahid, abokinsa....
Kafin ya ankara har ta b'acewa ganinsa, ya dafe kai saying,
"Shit...".
Kasim ya k'araso saying,
"Ka ganta ne...".
Maheer yace, "Na ganta saidai na kasa mata magana...".
Kasim yace, "Dama meyyy zaka ce mata? Ka manta da wannan abun...".
Maheer yace, "I can't... Momcy kullum cikin maganarsa take kamar yadda na damu hakanan itama ta damu...".
Kasim yace, "Let go...".
Direct suka wuce Villa dinsa da suke a zaune, tun daga wannan lokacin tunaninta ya addabi zuciyarsa, yana rufe idanu zai hango fuskarta a lokacin da tayi crossing dinsa ta wuce, sai tunaninsa ya koma kacokan a kanta, wayarsa ce tayi ringing ya duba yace,
"Momcy ce...".
Kasim yace, "Allah sarki Momcy, idan kun gama ka bani mu gaisa...".
Maheer yayi picking call din saying,
"Momcy... Mujaheed...".
Momcy tace, "Did you see him?".
Maheer yace, "No, na hadu ne da wata black American, fuskarta da muryarta sak irin nashi ne kuma zuciyata tana ayyana min cewa zata kasance hanyar da zan hadu dashi...".
"Da kuwa nayi murna, yaron nan a kullum dashi nike kwana dashi nike tashi, idan na tuna yadda yake bleeding, Allah ya kareshi a duk inda yake... Kayi magana da ita...".
Maheer yace, "No amma zanyi k'ok'arin ganin na sameta... Kasim yana ta hararena domin ban bashi ba kamar ba ya da wayar kiranki...".
"Ba yarona mu gaisa...".
Maheer ya lumshe idanu tareda mik'a wayar wa Kasim, yayi zurfi a tunani yana k'ok'arin nemo hanyar da kai k'ara haduwa da ita a wannan kasar mai girma....
Tun daga wannan ranar tunaninsa ya koma a kanta, kwata-kwata ya daina tunawa da abokinsa Mujaheed, abun har tsoro yake bashi....
************
Maheer yana rangadi a daya daga cikin wurarensa dake a kasar, yayinda bodyguard dinsa suke mara masa baya, still yayi a sanadin hangota da yayi zaune tana sirfing coffee, tana sanye ne da dogon wando da riga wacce ta tsaya mata a daidai kugunta, kitson dake a saman kanta yayi baya ya bazu a gadon bayanta, kitson yafi mashi kama da zane amma yana ganinsa akan en boxing, smile ne yayi escaping akan lips dinsa yayi taking steps tareda jan kujerar dake opposite da ita ya zauna yana mata murmurshi saying,
"Hi...".
A hankali ta d'ago tana kallonshi da dara-dara idanunta, tace,
"What? Did you want to sleep with me... You speak hausa, Right?... Ba haka nike ba, kaje inda suke, har wawasonka zasuyi sai ka zab'a ka darje sannan...".
Maheer kallonta yake cike da mamaki idanunsa a ware, jin hausar Nigeria tar a bakinta, saida ta watsa mashi wani mugun kallo sannan ta zaro kudi daga pocket din wandonta ta ajiye akan table ta mike tareda taking step daya zata wuce, Maheer ya mike da sauri tareda kama hannunta saying,
"Please...".
Kamar walkiya ta juyowa tareda sakar mashi masu nausi (punch) a fuska saida wutar kansa ta dauke na wasu seconds, ya tafi hutun rabin lokaci, yayi still yana kallonta cike da mamaki jin nausinta ya zarce na wasu mazan, cikin ransa yace,
"Karfi ne da ita...".
Bodyguard dinsa suka yo kanta, gani yayi ta dunkule hannu tareda fuskantarsu babu tsoro ko dar a ranta, duk da yawansu kuma kartai ne sosai, ta bashi mamaki sosai duba da yawansu kuma kartai ne sosai....
Maheer ya d'aga masu hannu, suka tsaya cak, tayi wani shegen murmurshi saying,
"Kayi tunani mai kyau otherwise zaka kashe kudadenka ne a asibiti, basu san abun da suke tunkara bane...".
Maheer yace, "Please...".
Tace, "Name your price and I will beat you black and blue until you pay for it... Damn it... Don't you ever show your face infront of me again otherwise you will regret it... Don't mess with the wrong #... I'm no match for you...".
Ta juya ta fice, ji yayi ruwa yana bin kasan hancinsa yana tab'awa da hannunsa, ya ware idanu ganin jini, kenan hab'o tayi mashi, ya zauna akan sofa yayinda aka soma bashi taimakon gaggawa....
Daya daga cikin bodyguard dinsa yace,
"Sir, we have to sue her, look at what she did to you, she have to know her limit...".
Maheer yace, "There is no need for that... It's my fault...".
Wayarsa ce tayi ringing ya ware idanu tareda kallon daya daga cikinsu under his breath yace,
"Har Momcy ta sani kenan...".
Yayi picking tareda kangawa a kunne saying,
"Momcy kadda ki damu ba wani babban abu bane, hab'o ne kawai...".
Cike da damuwa Momcy tace,
"Who did this to you?".
Maheer ya kwantar da kai tareda sakin murmurshi while saying,
"Mai KAMANNI da Mujaheed ce, na ganta na mata magana tayi ignoring dina na rik'e mata hannu ta bani naushi...".
Momcy tace, "Ayyerh... Shine har da hab'o...".
Maheer ya soma shafa beard dinsa yana hango yadda ta juyo kamar walkiya ta bashi nausi, yace,
"Karfi gareta kamar meyy, nausinta ya zarce tunani...".
Momcy tace, "Allah ya tsare... Sai ka kiyaye gaba and kayi ka gama ka dawo Nigeria domin uncles dinka sun isheni da mitar ka tafi kaki dawowa kasarka ta haihuwa...".
A take yanayin fuskarsa ya sauya, maganar da yayi a zuciya ta fito...
"Kamar idan na koma wata uwar zasuyi min... They hate me and I knew it...".
Momcy tace, "Subhanallahi... Maheer wannan ba tarbiyyar da nayi maka bace...".
Maheer ya ware idanu ankara da katob'arar da yayi, yace,
"I'm sorry, bazan sake ba...".
"Allah yayi maka albarka...".
"Amin...".
*************
A duk lokacin da ya tuna karonsa da ita sai yayi murmurshi, yana mamakin wacece ita? miye tarihin rayuwarta? miye dalilin da ya saka ta baro kasarta ta haihuwa ta shigo kasar nan tana yawo babu kallabi babu jilbab, Kasim ya tab'oshi, Maheer yayi firgigit, Kasim yace,
"Tunaninta kakeyi?".
Maheer ya lumshe idanu saying,
"Itace dalilin da ya saka har yanzu nike a kasar nan...".
Kasim yace, "That means ka daina damuwa akan abokinka Mujaheed, ka koma damuwa a kanta...".
Maheer ya bud'e idanu tareda waresu, yace,
"Na damu da ita ne saboda zata iya kasance hanyar da zan hadu da abokina Mujaheed... Kasim ka saka ai min bincike a kanta?".
Kasim yace, "Alright, I will do that koda ka bari mu koma Nigeria...".
Maheer ya maida idanunsa ya lumshe ba tareda yace mashi komai ba....
Tun daga wannan ranar Kasim ya saka ake yi mashi bincike a kanta amma babu wani cigaba....
***********
Some Days later,
Maheer ne tareda Kasim zaune a parlor suna kallon kwallon kafa, Kasim ya turo baki saying,
"Yaushe wannan mai delivery din nan zai iso ne... Yunwa, i swear...".
Maheer yace, "Ruge... Acici uwayen tauna...".
Kasim yace, "Oho... Da lafiya ake ci idan babu lafiya sai an matsawa mutum sannan yake ci...".
Maheer yace, "Whatever, da alama yau zaku sha kashi ne...".
Kasim yace, "Ba bakinka ba, miye na kallon kwallon bayan ba da team dinku ake yi ba...".
Maheer yayi wani shegen murmurshi saying,
"Saboda idan aka ciku in ji dadin dariya maku...".
Kasim ya tab'e baki saying,
"Idan kuma mukayi winning ka koma da er kunyarka...".
Maheer yace, "Whatever...".
Bell aka danna Maheer ya mike heading to the door, ya ware idanu ganinta a tsaye sanye da kayan masu delivery, da mamaki yake kallonta, tace,
"Your pizza...".
Maheer yace, "You...".
Tayi banza dashi tareda mik'a mashi saying,
"Here you go... Sign here...".
Maheer ya amshi takardar ya soma signing while saying,
"Wacece ke? Shin miye ya sakaki a wannan halin? Shin wanne dalili ne ya saka kika baro kasarki ta haihuwa kika dawo nan kina yawo babu veil babu jilbab...".
Tayi banza dashi, juyawa tayi ya riko hannunta, kamar walkiya ta juyo tareda fizge hannunta ta kama hannunsa ta murd'ashi baya saida ya saki k'ara saboda azabar zafi da ya ratsashi, yayi yayi amma ya kasa kwacewa saboda karfin ba daya ba, yana mamakin karfinta sosai....
Kasim ne ya fito da sauri ya k'araso jin ihun maheer, ya ware idanu ganin yadda ta murde mashi hannu, da karfinsa zai fizge hannun, ta janyeshi tareda wurgashi gefe saida ya saki k'ara yana mamakin mugun karfin da take dashi, bai k'ara yunkurin komawa inda suke ba, wasa wuri gareshi....

Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

*For those of you da zasuyi payment, zaku tura 600 ta wannan account....*

*9169472057*
*Aisha*
*OPAY BANK*

*Sai a turo evidence of payment via WhatsApp 09169472057...*

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057...*Hafsat Hisham *(AYSHER ANGEL)* 🥰🥰
💨 *BAN DACE DASHI BA* 💨
By Hafsat Hisham
*(AYSHER ANGEL)*


Page 3 and 4
Free page

Littafin Ban Dace Dashi Ba na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

Tana mashi wani mugun kallo still bata saki hannunsa tace,
"Didn't I warn you... Na kyaleka ne a fari saboda ba kai bane ka kawo kanka wajena ba, nice na bayyana a gareka, kayi babban kuskure daka k'ara gigin tab'a hannuna, sai na tabbatar da hannunka yasha bandage ta yadda duk lokacin da kayi tozali dashi zaka ji shaklar tab'a min jiki...".
Ta k'ara murd'a hannun saida yayi k'ara, ta wurgar dashi gefe ta wuce tareda hawa bike da tazo dashi, ta murza key tareda bashi wuta tayi gaba abunta....
A sanadin murd'a mashi hannu da tayi har saida ya samu karaya, aka gyara mashi hannun har da saka mashi bandage, Kasim yace,
"Yarinyar can karfi gareta kamar meyy, da tayi wurgi dani saida naga walkiya...".
Maheer yace, "She's amazing...".
Kasim ya ware idanu saying,
"Kanka daya kuwa, yarinyar nan ta k'arya maka hannu and you are saying she's amazing...".
Maheer ya wurga mashi harara sannan yace,
"Ina ruwanka, hannunka ko hannuna...".
Kasim yayi mashi banza, ya dauki waya yana dubawa, cak ya tsaya tareda ware idanu fuskarsa dauke da mamaki, yace,
"What? Ashe er boxing ce... Shiyasa take da mugun karfin nan...".
Maheer yace, "Wacece er boxing?".
Kasim yace, "Wannan yarinyar wadda tayi maka hab'o kuma ta k'arya maka hannu...".
Maheer yace, "What? Y'ar boxing kuma?".
Kasim ya mik'a mashi wayar, Maheer ya ware idanu ganinta sanye da kayan en boxing, under his breath yace,
"She's really amazing, shiyasa take da wannan karfin wanda ya zarce hankali, tana da abun ban mamaki...".
Momcy ce ta ajiye mashi call, yayi picking saying,
"Momcy, ashe er boxing ce shiyasa take da mugun karfin nan...".
Momcy tace, "Wacece?".
Maheer yace, "Wacce take KAMANNI da Mujaheed abokina...".
Momcy tace, "Y'ar boxing kuma?".
Maheer yace, "Ehhh yanzu naci karo da hotonta a waya akwai boxing da zatayi a gobe, zamuje kallo...".
Momcy tace, "Okay, ya hannun?".
Maheer yace, "Da sauki, zan kawo maki ita ki rama min tunda tayi wa d'anki hab'o har da k'arya mashi hannu...".
Momcy tayi murmurshi saying,
"Kai ka janyowa da kake rik'e mata hannu...".
Maheer ya b'ata fuska saying,
"Na daina...".
Momcy tace, "Dole kace ka daina tunda kaji a jikinka... Allah ya k'ara sauki...".
Maheer yace, "Aameen...".
Sun jima akan waya kafin sukayi sallama yayi hanging call din....
***********
Washegari tun kafin lokacin suka wuce, Maheer da mamaki yake kallon wajen fili ne, mutane sun zagaye wajen ana ihu yayinda dayar wadda za'a kwafza da ita take tsalle tana kai wa iska naushi, itace ta fito tana sanye da riga mai hannun vest tareda wando, ihu wajen ya dauka yayinda masoyanta suke kiran sunanta suna ihu, d'aga masu hannu kawai take kanta a kasa har ta isa tsakiyar wajen....
Tun Maheer yana hangota har ya daina hangota kasancewar a baya-baya suke, dakyar ya kutsa ta cikin mutane ya k'arasa gaba wanda yayi daidai da farawa, aka kawo mata farmaki ta goce tareda farmakarta da kafafu saida tayi taga-taga, waccen ta zuciya ta kai mata naushi saida tayi taga-taga, ji yayi har cikin ransa, tausayinta yake har a zuciyarsa, ba ya jin dadin ganin an naushi fuskar dake KAMANNI da ta abokinsa Mujaheed, sun fafata sosai, idan ta kai naushi har dashi cikin masu jinjina mata amma duk lokacin da aka naushi fuskarta ji yake har cikin ransa, tausayinta yake, tausayi take bashi, wani naushi ta kaiwa waccen tayi warwas a kasa, a take wajen ya kaure da ihu yayinda fad'a ya cakame a tsakanin masoyan waccen da kuma masoyanta, saida kaga an dauki mutum an nana da kasa, waje ya kacame da fad'a, Maheer k'ok'arin ta inda zai kub'utar da kansa yake, dakyar yake gocewa abubuwan da ake jefowa, wani katon abu aka jefo a inda yake, kamar daga sama yaji an janyeshi, ana ture mutane tareda kutsawa dashi ta cikinsu, saida ta fitar dashi waje sannan tayi wurgi dashi a gefe saying,
"What is this? What brought you here? Meyy ya kawoka?".
Maheer ya ware idanu ganin itace, smile yayi saying,
"Na zo ne saboda ke, and you save me, kin ceci rayuwata...".
Saida tayi mashi wani mugun kallo kamar zata kai mashi naushi har saida ya razana yayi baya, tace,
"If you come here again at your own risk, babu abun da ya shafeni, idan saboda ni ne thou ka sani abun da kake nema ba zaka tab'a samu ba domin kuwa ba haka nike ba, kaje ka nema a wajen wasu... Stand up and get the hell out of here...".
Ta janyo hular rigar dake a jikinta ta saka ta wuce tana tafiya da sauri-sauri, Maheer ya d'aga murya saying,
"Heyyy...".
Ta tsaya cak tareda...


Read / Download BAN DACE DASHI BA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album