Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

CIN AMANA KO FANSA Complete Hausa Novel Document by CIN AMANA KO FANSA


CIN AMANA KO FANSA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39410



CIN AMANA KO FANSA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 08, Sep 2023

Author: Zahra Muhammad Mahmud Surbajo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 241.24 kb

File Type: txt

Views: 1046+

Download: 760+

Last download: 14 hours ago

Description/Story: ๏ปฟCIN AMANA KO FANSA
Zahra muhammad Mahmud
Made by:- Shuraih Usman
Ku shiga nan kuyi like na shafinmu http://fb.com/hausaebooks

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: ๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““

*CIN AMANA*

*KO*

*FANSA*

๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““

*(TRUE LIFE STORY )*





Zahra Muhammad Mahmud





ยฎ *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*PML*



*Godiya ga Allah mad'aukakin Sarki, tsira da Aminci sutabbata ga annabinmu Muhammad sallallahu ala'ihi wasallam.*



*Wannan labari ba k'agagge bane yafaru dagaske,duk abinda ke ciki anyine da gaske, suna kawai na wa'inda abun yashafa Nasauya,da d'an abinda ba'a rasaba.baya ga haka babu abinda Nasauya*



Ya Allah, yadda nafara rubuta littafinnan lfy,Allah kasa nagamashi lfy.





*page 1*





Y'anmatane su biyu, y'an kimanin shekara goma sha shida da haihuwa,suka rugo da gudu zuwa Cikin d'akin kakarsu suna ta kiranta, uniform ne ajikinsu, alamar daga makaranta suke,



"Grany!!! Grany!!! where are you? we miss you so much,mekika tanadarmana yau."

A zaune suka ganta tana Kallonsu, k'arasawa jikinta sukayi, suka rungumeta, kowacce tamata kiss a gefen kumatunta.



"Kai ni banason iskancinnan naku, ace gird'a gird'a daku Amman har yanzu baku girmaba,wato abinnaku gaba yakeyi,yau kuma harda sumbatata ko?".



Dariya sukayi suka K'ara rungumeta,Khairat ce tace,



"Haba Grany, danma kinsamu munzo gidanki yau shine harda yimana wulak'anci,ni dama wlh banso zuwa ba,Fatima ce da shegen naci tace muzo gidanki,gashi daga zuwanmu kinfara halinnaki."sakin Grany tayi takoma gefe tazauna,



Fatima tace, "Wayyo Sis kiyiwa Grany uzuri, bakiga se kallonmu takeyiba, alamun taji dad'in ganinmu, hala taji haushin bamuyi sallama bane, ko Grany?",tawaiga Tana kallon kakar tasu.



Grany dariya tayi sannan taruk'osu dukansu tace ,



"Haba kha'iriyya ta fushi kikeyi danine?, nicefa babbar k'awarki ranar bikinki,"dariyace takwacemusu dukansu,khairat tace,





"Wai,dagwargwajiya kenan Grany ansha gwargwaro ranar aurena,"cigaba sukayi da dariyar.



Ranar wuni sukayi agidan Grany,seda la'asar suka mata sallama suka wuce gida.





Khairat da Fatima sa'annin junane, dan anhaifi Fatima da Sati biyu aka haifi Khairat.



Iyayensu mata ya da k'anwane,haka zalika, Iyayensu maza suma wa da k'anine.





Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Fatima,suna kiranshi da Abba,mahaifiyarta Mesuna Hajiya Salamatu suna kiranta da Umma.yaran Alhaji Nasir hud'u biyu maza biyu mata,Yaya Jameel shine babba, se Yaya Umar mebimasa,se Fatima, da autarsu Yasmeen.



Alhaji Mukhtar Abubakar shine mahaifin Khairat,suna kiranshi da Daddy, Wanda wa yake agurin Alhaji Nasir,uwa d'aya uba d'aya,

Matarshi d'aya Hajiya Binta,wacce take yaya ga mahaifiyar Fatima, yaransu guda shida,hud'u mata biyu maza,Aunty Fareeda Itace babba ,se Yaya Kamal mebimata,se Aunty Khadija,se Kha'irat, se Fa'eeza,da autansu Yusuf.



Gidan Alhaji Nasir dana Alhaji Mukhtar ahad'e suke sede katanga data rabasu,

Suna zaune da iyalansu agarin Kaduna awata anguwa Mesuna Tudunwada dede layin k'osai kan katagum road,



kansu ahad'e yake haka na iyalansu komai nasu tarene ko kasuwancin suma a tare sukeyi inda suke Saida kayan sawa kama daga na maza zuwa na mata, da yara, komai suna saidarwa a kasuwar checheniya dake Kaduna.



Zumunci ne me k'arfi a tsakaninsu inda ahalin yanzu babban d'an Alhaji Nasir yana auran Y'ar gidan Alhaji Mukhtar Khadija, harda yaransu guda biyu suna zaune a kinkinau dake Kaduna,ita kuma Farida wani ma'aikacin nepa take aure harda yaranta guda uku.



Rayuwar wannan family rayuwace mecike daso da k'aunar juna.



Grany,wacce sunanta na aynihi Hajiya Asiya amman jikokinta nace mata Grany,yayinda y'ay'anta da sirikanta kecemata Hajiya, Itace tahaifi Iyayensu maza,kuma a kakanninsu ita kad'aice tarage musu sauran duk sunmutu



Kha'irat da Fatima kansu ahad'e yake ko bacci tare sukeyinsa babu abinda ke rabasu suna matuk'ar k'aunar junansu ko kad'an ba'ajin kansu,ajinsu d'aya Boko da Islamiyya, suna da k'ok'ari sosai dan sotari twins ake cemusu,dan duk jarabawa sede suyi bracket, kowa cikinsu beson b'acin ran d'an uwansa.





Maman Yusuf

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: ๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““

*CIN AMANA*

*KO*

*FANSA*

๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““





Zahra Muhammad mahmud





*LOSING SOMEONE WHO DOESN'T RESPECT OR APPRECIATE YOU IS ACTUALLY A GAIN, NOT A LOSS.*





*pure moment of life writers*

*p.m.l*





*page 2*





Rayuwar Fatima da Khairat rayuwace mecike da son juna.



Khairat irin matannanne masu azababen kyau don ko daga nesa ka hangota kasan me kyauce,farace me hanci ga yalwar gashi tamkar indiya, komai da akeso ajikin mace Allah yabata,wannan baiwa da Allah yay matane yasa ta d'auki dogon buri akanta tanaji da wannan kyau da Allah yay mata shiyasa ko saurayi take burin me kud'i,in talaka yazo gurinta seyasha wulak'ancin dako a hanya yaganta baze sake marmarin kulataba,

har k'awayensu na makaranta sunsani shiyasa yanzu kirarin dasuke mata shine matar Manya,jin dad'i take insuka kirata da sunan.



Fatima nada kyau dede misali Amman bata Kama k'afar khairat ba,sede dirin halitta na y'a mace itama Allah yabata,batada da wulak'anci ga kowane ne yanuna yana sonta burinta de Allah yabata miji nagari.



Akan wannan halin na Khairat sunsha yin fad'a da Fatima sabida hakan,inkaji fad'ansu to akan wannan halin na Khairat ne Sam Fatima batason halin.





Yau ba makaranta dan haka su Fatima suka tsefe kansu sukaje Kitso,ahanyarsu ta dawowane wani me liffan yatsaresu,saurayine matashi ba laifi akwai natsuwa da kamala atattare dashi sallama yamusu,



"yan mata barkankude," yafad'i yana kallon Khairat da alamun ita yabiyo.



Khairat bata amsaba sema wata uwar harara data watsa mishi.Fatima ce ta amsa,



"barka kadai malam".



murmushi yayi sannan yace,





"Don Allah kuyi hak'uri da tsaidaku da nayi wlh son yar uwarkine yakamani tunda na hangota duk danaga ita ranta kamar beyi na'am daniba Don Allah kubani number d'inku da Address dannazo har gida nasameta,"yafad'i yana kallon Khairat.



"Dank'ari mune zamu baka address d'inmu harda number waya,to wlh bakaji da kyauba gwara tun wuri kanemi dede kai danmu ba sa'anninka bane dahar zaka wani ce kana sona Allah yakyauta wlh farashin gold beyi karyewar da za'ayiwa jaki mangala dashi ba,"tafad'i rai abace taja hannun Fatima da niyar suwuce subarshi, kwace hannunta Fatima tayi ta tsaya,itako Khairat gaba tayi abunta,cikin sigar tausayawa Fatima tace mishi,



"Don Allah malam kayi hak'uri wlh banji dad'in abinda tayi maka ba, kuma in zan baka shawara ka hak'ura da ita wlh tunda tanuna bata sonka banajin akwai abinda zesa tasoka kayi hak'uri kanemi wata don katsira da mutuncinka kaji,don Allah kuma kayafemata pls,"tafad'i cikin sigar rarrashi.





Murmushi yayi Yace, "bakomai baiwar Allah nagode dake kika saurareni, Amman kinsan sharrin so wlh jinake bazan iya hak'ura da ita ba kitaimaka kibani address d'inku da sunanku pls banak'i shawarar ki bane zuciyata ce bazata iya hak'uraba ki taimakamin pls",yafad'i kamar zeyi kuka.



Ba musu Fatima tabashi abinda ya buk'ata dan ta tausaya mishi daga k'arshe tamishi fatan alkha'iri, dazasu rabu yafad'a mata sunanshi Ahmad.



A hanya tasamu Khairat se cika take tana batsewa kotakanta bata biba sabida inda sabo tasaba da halinta, ahaka suka ci gaba da tafiya bamecewa kowa uffan.



Suna shiga gida d'akinsu suka wuce dan ajiye hijabansu ananne Khairat tacewa Fatima,



"Wai don girman Allah sis se yaushene zaki gane darajata tafi k'arfin irin wa'innan samarin? kina zubarmin da ajina wlh ni matar manyan mutanece,yakamata kigane har yanzu ban samu kalar mijin daya dace daniba, amman ke da Kare da doki kowama address d'inmu kike basu suzo su tak'uramin dan Wlh wannan ma nasan kinbashi address d'in watak'ila ma harda rakiyar phone number mitsss,"tayi tsaki ranta ab'ace.



murmushin takaici Fatima tayi ta dubeta tace,



"Sis kenan wani lokacin inkikayi wani abun senaga kamar ba'a family d'aya mukeba,dan de tarbiyya dede gwargwado iyayenmu suna bamu kuma sunsamu a makarantun da ake koyar damu sanin darajar d'an Adam.Haba Sis kituna fa Allah dakanshi yace yakarrama bani adam kewacece dazaki dunga wulak'anta mutane?,kituna Allahn daya baki kyaun dakike wulakanta mutane sabida shi shine yayi kuma wainda kike wulak'antawar bayan yahanemu dayin hakan, tabbas nabashi address sede inyazo shima ki koreshi kamar yadda kika saba,ni narasa mekike nema aduniyar da watarana ko labarinki baza'aji acikintaba, haba Sis yakamata ki farka daga wannan banzan mafarkin dakikeyi."



"Mafarki fa kikace Sis to wlh kece kike mafarki ni reality show nake yi, koma mezakice naji amman wlh babu yadda za'ayi nakai kaina gidan talauci sede kita fad'in abinda kika dama,kuma wlh shima wannan dakanshi ze kama kansa dan bade niba sede wata wlh."kiran da Umman Fatima tai musune yasa suka bar maganar suka tafi gurin kiran.





Maman Yusuf

[4/26, 10:10] Zahra Surbajo: ๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““

*CIN AMANA*

*KO*

*FANSA*

๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““๐Ÿ““





Zahra Muhammad mahmud





*Pure moment of life writers*


Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download CIN AMANA KO FANSA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album