Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

UMMI Complete Hausa Novel Document by UMMI


UMMI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33495



UMMI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 18, Oct 2024

Author: Ahlam Yusuf ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 07046861910

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 169.83 kb

File Type: txt

Views: 527+

Download: 317+

Last download: 10 hours ago

Description/Story: BISMILLAH AR-RAHMAN AR-RAHIM🙏

This is my first novel, and wannan litaffin ba na kudi bane, nayi shi ne at my own free will, sabida haka, ku Kwantar da hankalin ku, kuyi karatu cikin walwala sanan a dinga min zafafan comments and reviews via this number: 07046861910. Idan comments dinku ya bani karfin guiwa, toh sai a cigaba da yi muku update, Idan kuwa ba haka ba, toh sai a fasa novel dinma gaba daya. And please ban yarda ayi min kari ko ragi a novel dinnan ba, so a kiyaye hakki na dan Allah da Annabi. This novel is dedicated to you, a karanta lafiya.
🚫No CALLS please just comments.

Ahlam Yusuf💕

✏📖

Suna zaune su uku a cikin school cafeteria suna cin doya da egg sauce. Daka gansu, kasan cewa money lives here. Sun saka wasu tsadadun abaya wanda yayi musu bala'in kyau ga kuma ko wace da waya wanda bai yi kasa da iPhone 12 pro max ba. Ummi ce take bawa Zahra da Iftihal labarin tafiyan ta zuwa Abuja "ai wlh naji dadin Abuja this time around" dukan su suna shewa, sai Iftihal tace "ae lalai an samu duniya". Suna cikin hirar su, sai ga wasu guys, suma da ka gansu ka gan ajebotas, kaiiii sun hadu ne ba wasa.Shigowa suka yi cikin cafeteria din suka samu wajen zama. Daya daga cikin su ne ya kwalla ma mai cafeteria kira "Aunty gamu fah munzo, pls bring us our regular" suma suna hirar su irin ta maza.....Ummi wace ta bisu da kallo tun da suka shigo ta rage muryar ta na cewa friends dinta "Kaiiiii kun ga wani kuwa sai kace shi yayi kanshi" Zahrah ko ta harare ta Iftihal kuma ta hada da cewa "toh mabaruka sannu, ke bansan meye hadin ki da maza masu haske ba" murmishi Ummi tayi. Su Ummi sun gama cin abincin su, duk sun mike zasu tafi wajen biyan kudi a dai dai lokacin daya daga cikin samarin da suka shigo dazu wanda ake kira Farid ya mike Shima ya nufi wurin biyan wanda Ummi take yima auntyn magana "aunty, nawa kudin mu"? aunty ta fada mata. Dai dai Ummi zata fito da ATM sai ga Farid yazo cike da iyayi da zakewa yace "aunty ki sallame mu pls" Ummi ko ta daga manyan idanuwan ta tana yimai kallon tara saura uku. Sai tace "Malam sai ka dan dakata ta gama damu ai". Farid ya kalle ta, ya daga mata gira daya cike da iskanci yace "excuse me" abin ya ba Ummi haushi, ta ja tsaki ta fita tare da su Iftihal da Zahra bayan ta biya kudin. Suna tafiya inda suka yi parking tsadadun motocin su, Ummi fuska a hade tace "ku ji min wannan dan rainin wayon da yake ji ba wani shege sai shi" Zahra cike da tsokana tace "I thought he's your crush" Ummi tace "crush din wahala" su ko suka fashe da dariya. wurin motocin su duka tsaya yi ma juna sallama da hug, kafin kowa ya wuce.

Gaban wani katon gate ne haddadiya Ummi tayi parking tana horn. Wani tsoho da ya saka farin kaya daya ji guga kasancewa ran juma'a ce ranan ya leko domin ya san wa ke buga wanan uban horn din. Ganin cewa yar gidan ce yasa ya koma da sauri dan ya bude gate din. Ummi ko ta saka speed ta shiga compound din, ta fito daga motan tana kalon mai gadin sai tace "Baba Salisu ina yini, ya aiki" Baba ya amsa mata da cewa "Alhamdullilah, sannu da zuwa Hajiya Karama" tace Yauwa ta karasa cikin gidan. Wani makeken gida ne mai uban kyau...kai ka ce ba Za'a mutu a bar duniya ba. Cikin gidan kuma wani katon parlor ne well decorated da foreign interiors. Zaune ta ga maman ta wace take matsayin Hajiya babba, ta saka wata getzna mai uban kyau ga gwala gwalai. Ummi ta nufe inda take taje tayi hugging dinta tare da cewa "mummy ina wuni" mummy tace "how're you sweetheart and how's school"? Ummi ta amsa mata Kafin ta hau sama taje dakinta. Dakin ta hadu....kai ka ce dakin amare ne, komai tsap tsap harda yar show glass din da ta cika da kwalaben tsadadun turaren wuta kala kala. Ajiye jakanta tayi akan gado tare da ijiyan zuciya taje bathroom domain tayi alwala. Ta idar da sallah, sai ga group call din Zahra da Iftihal, ta dauka suka dinga hiran su har suka gaji. Washe gari, Ummi ta fito cikin wani simple gown taje dakin maman ta ta gaishe ta, daga nan ta sauka domin tayi breakfast kafin taje school. Tana zaune akan dining tana dana wayan ta, sai wata mai aikin su ta shigo rike da tray kato a hannun ta, ta ajiye akan dining din. Zata juya ta tafi sai Ummi tace mata "Samira dawo" Samira ta tsaya tana kallon Ummi. Ummi ahankali tace "mai yasa kike tsami da sasaffen nan, ba kiyi wanka bane"? Samirah tace "nayi amman turare na ya kare ne" Ummi tace "idan kin gama aiki Kizo in baki" Samirah ta gode mata ta wuce. Ummi ta kamala breakfast dinta ta hau sama dan ta shirya zuwa school. Ta shiga bathroom tayi wanka, ta yi shafe shafen ta, taje ta bude wardrobe wanda yake a gyare ta fito da wata atampa blue black da ash mai embellish a jiki, ta hada da Gyale da hula to match with it domin ummi ba mai son daura dankwali bace sai dai idan zata biki. Ta saka kayan ta, style din simple A shape gown ne mai ajihu da kuma bead work a wuyan da hanun wanda yayi mata kyau Sosai kuma ya shiga da skin color dinga. Gata Ita dark chocolate ce,da dan tsayi, not slim and not fat, kuma ga gashi mai cika da tsawo har gaban goshi, ga Manyan idanuwa da karamin baki, Tabarkallah, Ummi is beautiful. Ta dauka jakan ta to match da flat shoe, ta dau car key dinta na Mecedes Benz ta fita daga dakin. Ganin babu alaman maman ta na gida yasa ta fita daga gida ta nufi wurin motan ta tare da fada wa mai gadi ya bude gate. Ta kama hanyar zuwa school.

WACECE UMMI?
Amina Aminu shine cikaken sunan ta. Ita budurwa ce da bata wuce shekara ashirin ba kuma a garin Kano take zama tare da iyayen ta. Ummi, Ita kadai ce ya tilo da Allah ya ba iyayen ta wato Alhaji Aminu da kuma Hajiya Hadiza. Kasancewa Iyayen ta duka suna da kudin kansu yasa ummi bata rasa komai da kudi zai iya siya, amman hakan bai sanya Ummi ta zama lallataciya ba. Toh jama'a da duk daular da Ummi take ciki, shin meye kuke ganin makiyan buduruwar nan mai suna Ummi zasu harba mata nan gaba?? Toh muje zuwa domin jin cikakken labarin.


✏📖

Ta shiga cikin school recreational center dinsu dan ta jira Zahra da Iftihal, sai baza kamshi takeyi na turaren wuta da kuma na kanti. Kawai ta yi ido hudu dashi, ya sa wata shada mai kyau, mai tsada, gashi kaman balarabe, Masha Allah Farid akwai kyau kam. Tare dashi ta ga wata siririya wace itama tana ajin su Ummi ne ana kiran ta yellow kamar ba ta cin abinci, gashi da ka ganta ta ji bleaching har ta kone,ta dage sai nanake mai take yi kaman dole shi ko kulata bai yi. Ummi a ranta tace "duk iyayin ka, da wannan bone din kake yawo". Ummi ta hada rai, Farid ya bita da kallo har ta nemi wuri ta zauna a wani gefe. Sai kallon ta yake yi without blinking...... Chan sai gasu Iftihal da Zahra sun shigo suka Nufi wurin Ummi, suma sun sha kyau, sai baza kamshi suke yi. Atare suka fita suka je aji domin za'a fara lectures. Sai kallon su ake tayi dan suna burge mutane, gashi they're nice but basu bari a shishige musu. Sun shiga aji suka zauna suna hira, Ummi tayi ido hudu da yellow wace tuntini take ta watsa mata uban harara dan taji haushin yanda Farid ya ke ta kallon ta dazu. Sun kammala lectures dinsu na first period wanda ya dauka 1:45 minutes. Ana fita daga aji, su Ummi ma suka fita waje....Anan ko yellow wace take tare da kawayenta ta je inda su Ummi suke tsaye. Yellow tana kallon Ummi cike da raini tace "ke wurin ki nazo dan ubanki, ki fita daga sabgar Farid, dan kinga Yaro mai kudi mai kyau, kina so ki fara iyayi dan ya biyo ki, toh ba zai......" Taaas Iftihal ta tsinka wa yellow
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download UMMI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album