Join Our WhatsApp Group

SA MAZA GUDU 1 to 9 Complete Hausa Novel Document by SA MAZA GUDU 1 to 9


SA MAZA GUDU 1 to 9

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 90921



SA MAZA GUDU 1 to 9

Reading Time: 7 Hours

Added On: 21, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 501.3 kb

File Type: txt

Views: 1438+

Download: 1208+

Last download: 4 days ago

Description/Story: An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

SA MAZA GUDU
littafi na daya(1)
Complete book
Na Abdul Aziz sani madakin gini.
Typing Suleiman zidane kd..
Whatsapp 09064179602...

A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a
cikin daular larabawa a zamanin da babu wata
huldar kasuwanci wacce tafi cinikin batayi,anyi
wani babban birni mai suna Madinatul Zauwara.
Birnin Madinatul Zauwara na karkashin mulkin
wani gawurtaccen sarki ne ma'abocin jarumtaka
wanda ya zamo gwarzon mayaki kuma dodo ha
dukkan sarakunan dake nahiyar,ana kiran wanna
sarki da suna Sharkuf bin Aufan.
Duk wani abu najin dadin duniya Allah yabawa
sarki Sharkuf,yanada 'ya'ya guda tara amma
dukkaninsu mazane,sai mace guda daya.Babban
dansa kuwa shekararsa talatin da takwas,ana
kiransa da Lahaman.
Lahaman ya gado maifinsa a sadaukantaka da
jarumta kuma shine yake jagorantakar dakarun
sarki a duk sa'adda za'a fita FARAUTAR BAYI.
A tarihin fitarsa farautar bayi sau sittin da uku bai
taba dawowa gida cikin rashin nasara ba,kuma
duk sa'adda ya fita baya dawowa da kasa da bayi
dubu uku,sau tari idan yarima Lahaman ya fita
farautar bayi baya dawowa sai bayan wata biyu
ko wata uku.
Kasi daya cikin kaso uku na ribar bayin idan an
siyar na yarima Lahaman ne,ragowar kason biyun
kuwa na sarki Sharkuf ne.Saidai duk dakarun da
aka fita wannan farauta dasu akan basu kyautar
bayi bibbiyu.
Bisa wannan dalili ne a gaba dayan 'ya'yan sarki
Sharkuf babu mai kudin Lahaman,kuma wanda
wanda mutane ke sa ran cewa za'a bashi gadon
KARAGAR sarki to amma sho sarki Sharkuf yaki
fadat wanda zai gajeshi.
A gaba daya 'ya'yan sarki Sharkuf su tara babu
wanda yafi soyuwa a cikin zuciyarsa sama da
gimbiya Malika,duk abinda gimbiya Malika ta
furta tanaso indai akwai shi anan duniyar sai
sarki Sharkuf ya bata,kuma babu wata alfarma da
zata nema wajensa ta rasa.Kai saboda tsananin
kaunar da Sarki Sharkuf ke yiwa gimbiya Malika
ko Fada zaije tare da ita yake zuwa,su zauna tare
bisa KARAGAR MULKI,kuma duk taro mai
mahimmanci idan bazai samu damar halartar
ba,ita yake turawa ta wakilceshi.Sukan su
ragowar 'ya'yan sarki idan suna son wani abu a
wajen mahaifinsu saidai suyi kamun kafa da
Malika,in ba haka ba kuwa bazasu
samuba.Wannan dalili ne yasa dukkanninsu suke
yi mata biyayyar dole duk da cewa sun girmeta.
Yarima Lahaman ne kadai baya saurarenta kuma
sai kiyayya da hassada ta shiga tsakaninsu,sabo
da
ganin kamara sarki zai iya hanashi karagar mulki
ya bata.
In badon Yarima Lahaman yana matukar tsoron
sarki Sharkuf ba,da tuni yasa an hallaka Malika a
asirrance,domin ya huta da fargabar dake
zuciyarsa da kuma tsananin kiyayyar dake
tsakaninsu,babban abinda yake kara baiwa
Yarima Lahaman haushi shine duk abinda yake
iyayi da kudi itama Malika tanayi,har ma tana
iyayin abinda shi ba zai iyaba,saboda komai
tsadat abu tana iya sayansa,saboda tanayin
kasuwanci a boye ba tareda dashi kansa sarki ya
sani na.
Saida ya zamana cewa fiye ta rabin fataken birnin
nata ne,kuma saida ya kasance a nahiyar gaba
daya babu 'yar kasuwar da tafi Malika safarar
kayan abinci da makaman yaki
Bisa wannan dalili ne tayi sabo ainun da sarakuna
da kuma manyan attajirai,ababan misalai.Da
yawa daga cikin sarakunan da attajiran basa
ganinta sai a karshen shekara.a wannan lokacine
take kai ziyara kasa kasa tana karbat cinikin da
aka tara a hannun wakilanta dake tafiyar mata da
kasuwancinta.Sarki Sharkuf duk bai san wannan
kasuwancin da take yiba,abinda yasani kawai
shine duk karshen shekara tana shirya tafiya ta
kai ziyara izuwa manyan kasashe hudu,don
ziyartar manyan takunan bauta dake birnin
Kisra,Farisa,Yemen da kuma Misra.
A wannan lokacin ba'a barin kowa ya shiga cikin
wadannan dakunan bauta face sarakai,manyan
attajirai,manyan jarumai,da kuma kasaitattun
bokaye.Duk sa'adda gimbiya Malika zata fita
izuwa wannan gagaruman tafiya sarkin yakin
birnin Madinatul zauwara ne yake yi mata rakiya
tare da dakaru dubu uku domin tsaron
lafiyarta,dama babban boka na kasar wanda ake
kira Muzambil bin Samrad.
Wannan gawurtaccen shiri da ake yiwa Gimbiya
Malika na tsautsauran matakan tsaro,shi yasa
Yarima Lahaman ya kasa kai mata hari,saboda ya
tabbatar da cewar shi kadaine zai iya tarar sarkin
yakin nasu da kuma bokansu kuma in dai ya tare
su sai sun gane shi tunda sun san irin yanayin
yakinsa da irin sihirn tsafinsa,idan kuma yaransa
ya tuea sai asirinsa ya tonu an gane shi ya tura
su.
Burin Yarima Lahaman shine sarki ya mutu ya
gaje karagarsa,to abinda ya aiyana a ransa shine
a ranar zaisa a kama Gimbiya Malika da uwarta a
kaisu kurkuku,bisa hukuncin daurin rai batare da
sun aikata laifin komaiba,sauran kannensa kuwa
zai tursasasu suyi masa biyayya,duk wanda yaki
dole ne cikon biyu abu guda ya sameshi,kodai a
batar dashi ko kuma shima a kaishi kurkuku ya
karasa rayuwarsa a can.
A ranar da ya rage sauran kwan uku kacal
Gimbiya Malika ta tafi ziyartar da ta sabayi a
karshen shekara ne,yarima Lahaman ya dawo
daga farautar bayi.A wannan karon wata nahiya
daban suka je suka riski wata karamar kasa kawai
sai suka afkawa kasar da tsakiyar dare sukayi
mummunar barna.
A daren ne sarkin garin yayi sabon aure yana tare
da amaryasa suna shirin more amarcinsu kenan
Lahaman ya bayyana tsulum a gabansu.Nan take
aka kama sarkin aka daure shi a gaban idanunsa
yanaji yana gani kuma yana kuka Yarima
Lahaman ya yiwa matarsa Fyade kuma yana
gamawa da ita ya zare wuka ya lumamata a
ciki,take ta sulale kasa matacciya.Koda sarki
Hilairu yaga na kashe masoyiyarsa sai shima ya
sulale kasa sumamme,Lahaman ya bushe da
dariya,ya dubi yaransa yave"ku kama shi ku saka
masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai
mayar da sarki nawa.

Suleiman zidane...




Lahaman ya dubi yaransa yace "ku kamashi
kusaka masa sarka ya zama bawana,nine bakin
dare mai mayar da sarki bawa,kuma nine
GUGUWAR ANNOBA mai zuwa babu sallama.Haka
dai yarima Lahaman yayita yiwa kansa kirari,har
suka gama kama bayin dasuke bukata kimanin
dubu hudu maza da mata a cikin wannan
karamin
gari,bayan sun kone gidaje da yawa sun kwashe
dukiyoyi da yawa,nan take suka tusa keyar bayin
harda sarki Hilairu suka fice daga birnin mai suna
Baitul Laharas suka juyi suka nufi kasar Madinatul
Zauwara.
Bisa al'adar yarima Lahaman duk macen da
yayiwa fyade take yake kasheta,har a birnin
Madinatul Zaurawa kowa ya sanshi da wannan
muguwar dabi'a.Saida sarki Sharkuf ya kafawa
Yarima Lahaman doka cewa idan ya sake yiwa
wata 'ya mace fyade ko ya kasheta zai cireshi
daga matsayin yarima kuma ya yanke masa
hukuncin daurin rai da rai a kurkuki,sannan
matan birnin suka samu nutsuwa da kwanciyar
hankali.Bakomai ne yasa Yarima Lahaman ya
tsani mata ba yake yi musu fyade kuma ya kashe
su ba,sai saboda kiyayyarsa da da 'yar uwarsa
gimbuya Malika itama tasan hakan kuma yin
hakan da yake yi ne yasa taji ta dada tsanarsa
fiye da kowa a duniya.
Da yammaci ne sakaliya Yarima Lahaman ya
shigo
cikin birnin madinatul zauwara tare da
rundunarsa ta mayaka da kuma bayin daya kama
a daure cikin sarka nan bugunsu da bulala ana
ingiza su,kai da ganin bayin kasan cewa sunsja
bakar wahala,domin duksun rame akwai alamun
sunsha yunwa a wanannar doguwar tafiya da
sukayi,shi kuwa sarki Hilairu sau uku yana
yunkurun kashe kansa saboda bakin ciki amma
dakarun Lahaman na hanshi da karfin tsiya su
tattakashi cikin wulakanci da muzantawa ,duk
sa'adda sarki Hilairu ya tuna cewa an kashe
masa
matarsa Zailat wacce yake matukar SO DA
KAUNA,kuma ya tuna cewa an rabashi da
mulkinsa,dukiyarsa,kuma shi da jama'arsa da
yawa an maishe dasu nayi,dakarunsa na yaki
kuwa kusan gaba dayansu aka kashe.ko ina a
cikin birnin nasa gawarwakine da jini,sai ya fashe
da matsanancin kuka yaji ya tsani kansa da
rayuwarsa gaba daya.
Sarki Hilairu ya kasance Kyakkyawan saurayi abin
kwantance mai kwarjini da haiba irin ta sadaukai
amma ko kadan bai kasance jarumi ba,kuma bai
taba yin yakiba a rayuwarsa,sarautar ma tsintarta
yayi a sama ba gado yayi ba.Sarkinsu na da bashi
da 'da ko jika,kuma bashi da wani dan'uwa face
Hilairu.Mahaifiyar Hilairu ta kasance Kuyangar
Sarkin da ya mutu,don haka shi dan baiwane,ba
dan wata 'yantacciya ba,ta haka ne ya gaji
wannan sarauta.
A daidai wannan lokaci yarima Lahaman ya shigo
cikin birnin madinatul zauwara sai akayi akasi
gimbiya Malika ta fito rangadi zata fita izuwa
bayan gari domin yin garauta a daji.A wannan
lokaci tana tare da tsirarun dakaru wandan basu
fi su arba'in ba.A daidai kofar shiga cikin birnin
sukayi kicibus.A wannan lokaci yarima Lahaman
na cikin tsananin farinciki bisa ganin dinbin
dukiyar daya samo wacce baitaba samun
kamartaba,gami da lafiyayyun bayin da yasan
cewa zai siyar dasu da darajar gaske.Koda yarima
Lahaman da gimbiya Malika suka hadu sai
kowannensu ya murtuke fuska suka bata rai
kamar an aiko musu da sakon mutuwa,da ko
magana basayi da juna.Koda Gimbiya Malika ta
dubi tarin dukiyar da Yarima Lahaman ya samo
gami da tarin bayi,sai takaici ya kamata saboda
tasan ce Allah ne kadai yasan irin mugun zaluncin
da akayi wajen samosu,Kwatsam sai idanun
Malika suka kai kan sarki Hilairu,tana hada ido
dashi sai zuciyar ta ta buga da karfi nan take a
karon farko a rayuwarta taji ta kamu da tsananin
son 'da namiji don haka batsan sa'adda ta kura
masa idanuba har suka gifta juna tana
waigensa.Abinda ya kara mata sonsa mashi ne
shima ya kura mata idanu,cikinalamun tsananin
kaduwa da mamaki,har ya tsaya cak ya daina
tafiya sai da ka buga masa kulki aka hankadashi
gaba yana turjewa na dada bugunsa sannan ya
janye.Ashe ba wani abu ne yasa Sarki Hilairu ya
kura mata idanu ba face kamanninta yazo iri
daya sak da matarsa wacce yarima Lahaman ya
kashe tamkar an tsaga kara.Dama tun acan
birinin na sarki Hilairu yaran Lahaman suka yita
tsegumin suna cewa matar sarki Hilairu tana
kama da Gimbiya Malika.Yana daga cikin dalilin
ma da ysa Yarima Lahaman ya kasheta,tun da ya
tsani Malika,Ya tsani duk mai kama da ita.Har su
yarima Lahaman suke kule gimbiya Malika baya
daina waigensu ba,kuma zuciyarta bata daina
bugawa ba,da zafi,nan dai ta kudurci aranta
cewar ta kowanne hali sai ta mallaki wancan
bawa wanda ita yanzu ta kamu da tsananin son
sa farat daya a farkon haduwa.Babban tashin
hankalin ta shine tasan cewa ko nawa zata
siyeshi
yarima Lahaman bazai siyar mata ba,saboda
kiyayyar dake tsakaninsu.
Al'amarin Yarima Lahaman kuwa lokacin da yaga
gimbiya Malika ta fito rangadi daga cikin gari tare
da tsirarun dakaru,sai wani abu ya fado masa a
rai.Nan take yayi tunanin ya batar da
kamanninsa
ya dawo cikin dajin ya afkawa masu
tsaronta,amma sai wata zuciyar tace dashi a'a,yin
hakan abune mai matukar hadari,domin idan
asirinsa ya tonu ba zatayi masa kyauba.Domin
akwai lokacin da kwatankwacin hakan ta faru da
kyar ya samu kubuta daga zargin sarki.Al'amarin
ya faru ne wata rana sa'adda ana zaune a
fada,duk su biyun shida Gimbiya Malika suna
zaune a fadar tare da sarki,Malika na daman
Sarki shi kuwa yana hagunsa,sai ga wani mao
gadin kofar gari ya shigo cikin fadar a guje cikin
gigita,da zuwansa sai ya zube kasa gaban sarki ya
kwashi gaisuwa,muryarsa na rawa kuma kansa a
sunkuye ya bude baki yace,"Ya shugabana,kayi
sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar
gari
kawai sai muka hango.
Suleiman zidane kd
Yace,ya shugabana kayi sani cewa muna kan
aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka
hango wadansu bakin dakaru acikin shigar
bakaken kaya,bisa dawakai sun rufe fuskokinsu
sun nufo kofar gari,koda muka hango su muka
yunkura zamu busa kahon yaki,sai suka ja baya
suka nausa cikin daji suka bace bat tamkat basu
taba wanzuwa ba.Bisa wannan dalili ne yasa
muka kasa samun nutsuwa da kwanciyar
hankali,shi yasa muka ga ya dace muzo mu sanar
da kai domin kasan matakin da ya kamata a
dauka.Kodajin labarin,sai sarki Sharkuf ya bushe
da dariya,sannan yace,ai kua tasan gidan mai
babar sanda,tsoro suka ji shi yasa suka juya da
baya.To amma akwai wani boyayyan al'amari a
tare dasu,domin ko da wasa ba'a taba samun
'yan fashi ko 'yan harin da suka taba kusantar
kusa da kofar garin nan ba,saidai suyi shawagi a
can wajen gari ciki dazuzzuka,lallai ruwa baya
tsamin banza,kuma da dan gari akanci gari.Akwai
wani munafuncin da ake shiryawa tare da
waninmu.Koda gama fadin haka,sai sarki ya dubi
yarima Lahaman yace,ya kai yarima,maza ka dibi
dakari dubu kuje ku bi sawun wadannan dakarun
sumame,idan sun fice daga yankin kasata ku
kyalesu,idan kuma suna ciki ku yakesu ku kashe
su,kada kubar mutum daya ya tsira da
rayuwarsa.Koda jin wannan umarni,sai yarima
Lahaman ya mike tsaye zumbur da nufin yaje
yayi shiri,amma sai Gimbiya Malika ma ta mike
zumbur tasha Gabansa tace,ya akai da'uwana ina
rokonka ka tafi tare dani,domin idanuna suna son
ganin ko suwaye wadannan marasa kunya da
rashin tsoro har suke tunanin zasu iya kawo
mana hari.Koda jin haka,sai kowa ya cika da
mamaki a fadar musamman ma sarki Sharkuf
wanda a saninsa ko magana Yarima da Gimbiya
basayi,amma yau wai itace ke rokonsa akan ya
tafi da ita wajen gari don yakar abokan
gaba.Lokacin da yarima Lahaman yaji bukatar
gimbiya,sai ya dubi sarki domin yaji ta bakinsa ko
zai amince ya tafi ta itan,Bisa ga mamaki sai
gashi sarki ya Amince.Abin ya baiwa kowa
mamaki a fadar,soboda ansan cewa a duniya
babu abinda sarki Sharkuf ke so sama da gimbiya
Malika,kuma baya yarda taje wani wuri mai
hadari,kuma yasan irin kiyayyar dake tsakaninta
da dan'uwanta Yarima Lahaman,to amma me
yasa yanzu ya amince ya tafi tare da ita izuwa
yaki?Ita kanta Gimbiya Malikan saida ta yiwa
kanta wannan tambayar a cikin zuciyarta,nan dai
Malika tabi Yarima Lahaman a bya cikin farinciki
suke fice daga cikin fadar.Suna fita Lahaman yayi
shigar yaki ya tara dakaru dubu sukayi hawa
itama Malika sai aka kawo mata nata dokin ta hau
suka fice daga cikin gidan sarautar suka nausa
cikin dajin suna masu bin sawun dawakan da
suka gani.Koda suka iso wani wuri inda hanya ta
rabu biyu,sai Lahaman yaja limzamin dokinsa ya
tsaya cak yayi nazarin hanyoyin sannan ya juya ya
dubi gimbiya Malika yace,Daki tsaya anan ke da
rabin dakaruna dan tabbar da tsaron lafiyarki,ni
kuma da sauran dakarun zamu shiga ciki harsai
mun isa inda wadannan abokan gaba suka
buya.Kodajin wannan batu,sai Malika ta ce a'a ba
haka za'ayiba,ai yanzu baka da tabbacin cewa
hanyar da zakabi can abokan gabar suke,saidai
muma mubi daya hanyar idan muka riske su,sai
mu yakesu,in kuma kaine ka riskesu ka
yakesu.Sa'adda yarima Lahaman yaji wannan
batu,sai yayi murmushi yace ,idan wani tsautsayi
ya sameki kada kiga laifina tunda dai ni ga inda
nace...


Read / Download SA MAZA GUDU 1 to 9

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On SA MAZA GUDU 1 to 9
avatar
adamu-3

9 months ago

Reply

Masha Allah Allah ya Kara basira Aboki

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album