Join Our WhatsApp Group

BUSA A MUTU Book 6 Complete Hausa Novel Document by BUSA A MUTU Book 6


BUSA A MUTU Book 6

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14164



BUSA A MUTU Book 6

Reading Time: 1 Hours

Added On: 18, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu usman, Alamin Ahmed Misau

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 76.39 kb

File Type: txt

Views: 577+

Download: 265+

Last download: 1 day ago

Description/Story: BUSA A MUTU
Littafi Na Shida (6)
Part A
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana
WANNAN
muguwar dabi'a ta Sarki
ta addabi
Wannan
mutanen kauyensu da sauran mutanen da ke zaune a
garuruwan makoftaka kuma ya zame musu alakakat,
domin ya shafe shekaru talatin yana yi musu wannan
mulkin zalunci.
An sha hada Dakaru azo a yakcshi domin a kawar
da shi a kashe Dodon nasa, amma abu ya faskara.
Bisa dole mutane suka rungumi kaddara suka zuba
Ido suna jiran ranar da mutuwa za ta riski Sarki Labarazu
domin su huta da wannan abin takaici.
Da isar Sarkin kasuwa Rubiyan izuwa cikin fadar
Sarki Labaruza sai ya zubc kasa ya kwashi gaisuwa
sannan ya dago kai ya dubeshi cikin tsananin damuwa da
fargaba ya ce, "Ya Shugabana yau fa wadansu bakin
mutane sun shigo garin nan wadanda ga dukkan alamu
sun shigo da cikakken shirinsu kuma tamkar sun san
sirrin garin namu.
Abu na farko dai sun ki su ci ko su sha komai na
cikin garin nan, bare mu sami damar da zamu kamasu a
hannu mu kaisu can kogon Dodo.
Abu na biyu shi ne, basu yarda sun sauka a ko ina
ba sai a kasuwa inda suka bukaci na basu hanyar gida.
Nan takc na tsuga musu kudi a tunanina za su
hakura su koma cikin gari inda zamu gama da su nan da
nan amma sai suka ki yarda suka biya kudin da na iuula
musu.
Bayan an kaisu masaukin nasu sai na bukaci su
bani kwangilar kai musu abinda za su rinka ci da sha nan
ma suka ki amincewa.
Koda Rubiyan yazo nan a zancensa sai Sarki
LabaraZu ya daga musu hannu yana mai dakatar da shi.
Ribiyan ya tsuke bakinsa yai shiru, a sannan ne Sarkı
Labarazu ya dauko wani farin kyalle ya shafeshi da
hannun hagu yana mai karanta wadunsu dalasiman tsali.
Nan take hoton su Gimbiya Suzaila ya baiyana
akan kyallen, boka Labarazu ya yi arba da su gaba
dayansu.
Koda ya ga jaruma Suzaila a cikin tawagar sai
ransa ya baci ya takarkare ya kwarara uban ihu mai
tsananin firgitarwa wanda yasa Rubiyan ya firgita, ya
dimauce bai san sa'adda ya saki fitsari ba a wando.
Sarki Labarazu ya kasance narkeken kato mai kirar
Sadaukai da siffa irin ta mutanen farko.
Kallo daya zaka yi masa ka san cewa sadauki nc
mai dakawa maza gumba a hannu.
Cikin tsananin fishi Sarki Labarazu ya cakumi
kwalar rigar Rubiyan ya dagashi sama da hannu daya
tamkar sillan kara ya ce, "Saboda me tun da farko baka
aiko da gaggawa an gaya mini zuwan wadannan baki
ba?"
Cikin tsananin tsoro da kyarmar jiki Rubiyan ya ce,
"Ka gafarceni ya Shugabana na yi zaton zan iya kamasu
nc a hannuna ba sai na zo na sanar da kai ba."
Labarazu yai wurgi da Rubiyan ya fadi can gefe
daya tamkar ya yi wurgi da tsumma sannan ya ce,
"Hakika wadannan baki su ne mafi hadari daga cikin
dukkan bakin da suke zuwa mana. Idan ba mu yi da
gaske ba su nc za su kawo karshen mulkinmnu anan
garin".
Yanzu dai muna da mutanen da zamu yankawa
Dodo har na tsawon kwana shida, dole ne kafin rana ta
bakwai mu fara sato wasu daga cikin wadannan baki
wadanda zamu yankawa Dodon namu".
Koda jin wannan batu sai tsoro ya kama Rubiyan
ya ce, "Ya Shugabana ta ya ya zamnu iya sato wadannan
mutanc alhalin ko yaushe suna tare a waje daya. Duk
hanyar da zamu bi mun bi, amima mnun kasa samun
nasara".
Labarazu ya ce, "Kar ka damu a daren yau zan san
abinda zan yi. Yanzu ka tashi ka tafi na sallameka".
Nan take Rubiyan ya mike tsaye ya fice daga cikin
fadar da sauri.
Shi kuma Sarki Labarazu ya sake kurawa wannan
farin kyalle da ke hannunsa idanu ya shiga nazari yana
karanta wadansu dalasimai na tsafi.
A CAN masaukin su Gimbiya Suzails kuwa da
Yarima Hasralu da Ginsbiva Lushaira suka shig cikin
dakin su sai suka zauna suka yi shiru kowannensu ya
fada cikin kogn tunani.
Abinda Hasnalu yake ta tunowa da shi shi niu,
lokacin da ya gana da Gimbiva SulaiZa a cikin lambun
gidan sarautar mahaifinta, lokacin da ta gindaya masa
yana son ya sami soyayyata dole ne
dokar cewar in dai yana
yaje dajin Kirzufa ya kamo Jarumi nai kahon BUSA A
MUTU yuzo ma ta da shi."
Koda Hasnalu yzo dai-dai nan a tunaninsa sai
kwallar takaici a cika masa idanu, domin ya san cewa
tabbas wutsiyar rakumi layi nesa da kasa. Idan har
Jarumi Imran ne ya kamo Muraisu mai kahon Busa a
mutu shŁi ke nan dama ta wuceshi.
A bangaren Gimbiya Suzaila kuwa, ba wani abu ta
fara tunowa da shi ba face lokacin da ta kaiwa Ainiirin
nan abinci.
Nan take ta tuna cewa abincin da ta kai masa kala
biyu ne.
Daya gasasshen nama ne, daya kuma 'ya'yan
itatuwa ne na tuffa da ayaba, sai kuma ruwa a tulu.
Ita dai ta ga ya dauki tuffar ya gutsura sau biyu ya
ci, sannan ya ajiye ya dauki Ayaba ya gutsureta sau daya
ya ci, sannan ya dauki tulun ruwan ya yi masa kur6a
uku.
A dai-dai wannan lokaci nc ta tuno da kalar fatar
Almajirin wacce ta kasance wankan tarwada. Duk da
cewa fuskarsa ta cika da gashi akwai alamun ccwa
kyakkyawa ne shi na gaban kwatance domin idanunsa
dara-dara nw masu tsananin fari da haske kuma hancinsa
dogo ne siriri, a kasansa akwai dan karamin baki tamkar
yankan wuka.
Lushaira ta tuna cewa yadda ta ga kamannin
wannan Almajiri haka boka Kirishna ya siffanta Jarumi
Imran. Nan take taji ta gamsu a cikin zuciyarta dari bisa
dari cewar wannan almajiri shi ne Jarumi Imran.
Kawai sai kuma taji ta kamu da tsananin sonsa a
cikin zuciyarta yadda babu abinda take so sama da ta
sake saduwa da shi.
Nan take itama ta dilmiya a cikin kogin tunaninsa
da begensa, al'amarin da ya sanya lakaici ke nan a cikin
zuciyarta saboda bata taba tsintar kanta a cikin irin
wannan yanayi ba.
A dai-dai wannan lokaci ne Yarima Hasnalu ya
dawo cikin haiyacinsa, koda ya dubi Lushara ya ga ta
shiga cikin irin halin da ya tsinci kansa a ciki, al'amarin
da yai matukar bashi mamaki ke nan ya dubeta cikin
damuwa ya ce, "Ya ke yar uwata, tunanin me kike yi ne
AA Misau ke Magana
Madakin Gint
haka wanda har Va dauke miki hankali kika manta cewa
muna tare?"
Koda jin wannan lambaya sai Lushaira ta bushe da
dariya ta ci gaba da dariyar kamar ba za ta daina ba.
Al'amarin da yai matukar baiwa Hasnalu mamaki ke nan
ya zuba ma ta idanu kawai.
Daga can sai Lushaira ta nutsu ta ce, "Ya kai dan
uwana kayi sani cewa ba wani abu bane yasa ka ga ina
yin wannan dariya ba face yanin nima na shiga irin halin
da ka tsinci kanka a ciki.
Abinda nake nufi shi ne., nima yanzu na fada tarkon
soyayya kamar yadda kaima ka tsinci kanka a ciki".
Koda jin haka sai Yarima Hasnalu ya gyara ZaIma
cikin firgici ya dubcta ya ce, "Ya ke 'yar uwata ni a
sanina da ke ban taba ganin kin so wani da narriji ba,
kuma ba kya sauraron 'ya'yan Sarakai da Attajirai masu
ZUwa neman aurenki ba.
Wane nc wannan gawurtaccen saurayi mai sa'ar
gaske wanda har ya sami matsugunni a cikin zucivarki
farat daya haka?"
Sa'adda Gimbiva Iushaira laji wannan tambaya sai
tayi ajivar numfashi sannan ta cc, "Ya kai fan uwana ka
yi sani cewa a iya rayuwata da duk irin tafiyc-tafiyen da
na yi ban laba ganin da namiji mai kwarjini, haiba da
kyau ba kamar wannanAImajir da ya Z0 mana heman
laimako aka wulakantashi."
Koda jin wannan batu sai Yarima Hasnrlu ya kara
irgita ainun ya ce, "Haba kanwala wanc tsautsatyI ne ya
kaiki son Jarumi Imran alhalin kin san cewa Gimbiya
Suzaila ma tana sonsa?"
Lushaira lavi murmushi sannan ta ce, "Ai da ni da
Suzaila duk muna son mutumin da bai ma san halin da
muke ciki ba ne.
Duk da cewa ita ta fara sonsa ne tun daga ranar da ta
fara jin labarinsa ni kuwa sai da na fara ganinshi ido da
ido sannan na kamu da sonsa, tawa soyayyar lafi ta ta karfi.
Dalilina anan ita ce, tana sonsa nw kawai saboda
jarumtakarsa ni kuwa ina sonsa ne saboda ganin irin
mu'arnalarsa da halayyarsa ba wai kyansa ko
jarumtakarsa ce ba ta fauke mini hankali tunda sa'adda
ma na ganshi.bai yi wata jarumtaka ba sannan kuma ban
ga kyawunsa ba s(isai kasancewar gashi ya cika fuskarsa
gaba daya kuma bai yi wata shiga mai kyau ba wacCe za
ta bayyana kyansa ba".
Koda jin wannan batu sai Lushaira ta yi murmushi
ta ce, "Ai konai na rayuwa akwai sa'a da rabo. LLokaci
zai bambance konmai".
Koda gaina fadin hakan sai Gimbiya ILushaira ta
mike tsaye ta tafi izuwa kan shimfidarta ta kishingida
domin ta huta a lokacin ne kuyanginsa suka shigo dauke
da farantan ahinci da 'ya'yan itatuwa suka zube a gaban
Yarima da gaban Lushaira sannan babbar cikinsu ta dubi
Lushaira cikin biyayya ta ce, "Ya Shuabata shin akwat
Wani aiki da kike buralar mu yi muku a yanzu?"
Lushaira ta ce, "A'a babu komai. idan akwai bukatar
hakan zamu sanar da ku, ku tashi ku tafi na sallamcku".
Nan take kuwa kuyangin suka mikc tsaye suka ficc
daga cikin dakin.
Lokacin da yamma tayi ya Zamana cewa babu
sauran zalın rana sai Gimbiva Suzaila ta fito cikin
harabar gidan ta kama kewaye tana Zagaya gidan tana
nishadi.
ne sauran abokan taliyara la suka rinka
A lokacin
wajcn Swaila
firlitowa daga cikin dakunarsu suna zuwa
suna gaishcta a lokacin da ta zauna a cikin lambun gidan.
A wannan lokaci ne, Suzaila ta lura ccwa ba la ga
lawarcn Sadaukai ba Jarumi Shalaru da Jarumi Halaru,
sannan kuma a cikin kuyangin su Gimbiya Lushaira ba la
ga wala baiwa ha mai suna IKILIMA.
Nan take hankalinta ya dugunzuma ta dubi Sarkin
yakin mahaifinta ta ce, "Ya kai Sarkin yaki shin ko ka
san inda tagwayen Sadaukai suka talī?"
Koda jin wannan tambaya sai hankalin Sarkin yaki
ya dugunzuma ya kama kalle-kalle da waige-waige ya
shiga binciken ko wani ya ga sa'adda su Jarumi Ililaru
suka fita amma sai kowa ya ce bai gani ba.
A dai dai wannan lokaci ne Yarima Hasnalu da
Gimbiya lushaira ma suka fito daga cikin dakinsu. Koda
suka hango laro an yi cincirindo an zagaye Gimbiya
Suzaila sai hankalinsu ya dugunzuma suka karaso wajcn
da gudu.
Da zuwansu sai Suzaila ta dubcsu cikin damuwa ta
ce, "Dakaruna guda biyu da baiwarku daya sun karya
dokarmu ta cewar kada kowa ya fita daga cikin gidan
nan, lallai sun sulale sun fice daga cikin gidan, saboda
haka bamu da sauran kwanciyar hankali dole nc yanzu
mu lafi neman wadannan 'yan uwa namu, amma ni kadai
nake so na fita bana son kowa ya bini domin ina ji a
jikina cewar akwai mugun tanadi da mutancn kauycn
nan suka yi mana mai hadarin gaske".
Koda gama fadin hakan sai Gimbiya Suzaila ta mike
tsaye da sauri ta juya za ta nufi inda dokinta kc daure
cikin hanzari Sarkin yakinta ya sha gabanta ya ce,
"Ranki ya dade ba zan iya barinki ki tafi ke kadai ba
domin idan wani abu ya samcki ba tare da na gani ba,
idan na koma Birnin Lairuf ban san abinda zan gayawa
mahaifinki ba.
Zai iya fusata ma ya sa a hallakani saboda ya
gargadeni kafin mu baro gida ccwar duk inda za ki
fuskanci wata masifa na tabbatar da cewa ina tare da ke."
Lokacin da Gimbiya Suzaila taji wannan batu sai
jikinta ya yi sanyi domin ba ta da ikon ta hana Sarkın
yaki binta. shi kansa Yarima Hasnalu hankalinsa ya
dugunzuma ainun da yaji ccwa Suzaila za ta fita neman
Dakarunta nan take yaji cewar ba zai iya zama ba ya jira
lokacin da zata dawo ba, saboda zai kasance a cikin
fargaba da zullumi saboda rashin sanin balin da takc ciki
Kawai sai ya budi baki ya cc, "Ai ina ya kamata
na bika mu tafi tare tunda baiwarmu guda daya ta bace."
Koda jin wannan batu sai Suzaila ta dubcshi tayi
murmushi ta ce, "Shin kara son ka fita farautar ajalinka
ne? Ka sani cewa kai ba Jarumi banc saboda me za ka
siyar da rayuwarka a banza?"
Hasnalu ya maidawa Suzaila nartanin murmushia
muguntar da tayI Inasa yà cc, "Dalilin da ya sa ita baro
gida na biyoku iZuwa wannan taliva mai hadari shi ne
zai sa na biku a yarzu tunda duk a cikin aiki muke".
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Suzaia ta
kyalkyale da dariya ta ce, "Hakika duk abinda ka fada
gaskiya ne don haka duk wanda ma yake ganin zai ya
binmu ya biyomu ban hana kowa ba".
Nan take Suzaila ta ruga izuwa irida dokinta yake ta
kwanceshi ta hau.
A guje Sarkin yakinta, Hasnalu da Lushaira ma suka
ruga izuwa inda nasu dawakan sukc suka hau.
Nan da nan aka bude musu kofar gidan suka fice
cikin azababben gudu tamkar za su tashi sama.
Abin tambayar anan shi ne, "Ina suka dosa, ina za su
Je sU ga tagwayen Sadaukai su Jarumi Shalaru da baiwar
da ta bata "
AA Misau ke Magana
Da yake Suzaila ce akan gaba kawai sai ta zamo 'yar
Jagorarsu duk inda dokinta ya dauke
Sanya nasu.
dauke sawu anan suke
Kamar Suzaila ta san înda ya kamata su je kawai sai
Ta durfafi hanyar fadar Sarki Labarazu duk da cewar bata
taba zuwa ba kuma ba, kuma bata san a inda takc ba.
Abinka da wanda ya taso a cikin gidan saraua,
Suzaila tana la'akari ne da irin yanayin alamomi na
hanyar da zata kaisu izuwa fada.
Ai kuwa suna cikin tsala gudu ne suka hango gidan
sarautar.
Tun daga ncsa suka hango Dakaru sama da mutum
dubu zaratan mazaje a tsaitsaye. rike da muggan
makamai suna gadin gidan.
Nan take Lushaira da Yarima Hasnalu suka firgicc
suka tsorata ainun da ganin wadannan zaratan Dakaru
masu kwarjini da ban tsoro.
Suzaila da Sarkin yakinta kuwa ko gezau ba su yi
ba. Maimakon ma su rage karfin gudun dokinsu sai suka
kara kaimi.
Koda ya rage saura bai fi taku goma ba tsakanin su
da kofar gidan sai wasu daga cikin Dakarun da ke tsaron
gidan suka taso rikc da dogaycn masu suka tare hanya.
Bisa dole su jaruma Suzaila suka ja linzamin
dawakansu suka yi turjiya.
A sannan ne Shugaban Dakarun gidan sarautar ya
ratso ta cikin 'yan uwansa yazo gaban su jaruma Suzaila
Ya yi tsayuwar takama irin ta manyan jarumat ya đubesu
va ce, "Su waye ku? Mene ne yake tafe da ku ga Sark i
aihalin ba a san da zuwanku ba?"
Koda jin wannan tambaya sai Suzaila ta dubi
Shugaban Dakarun ta ce, "Ka jc ka gayawa Sarkinku
cewar ya bani mutanena guda uku da suka bace Ka
shaida masa cewa ni ce jarurma Suzaila Sarkin yakın
Bimin Lairuf.
Idan bai bani mutancia ba ty va sani cewa ran
dayansu dai-da: yake da ran gaba dayan jama'arsa. Idan
daya daga cikin mutanen ya rasa rayuwarsa to sai na
share mulkinsa daga doron kasa".
Koda jin wannan batu sai gaba dayan Dakarun gidan
sarautär suka fusata ainun suka yunkuro za su afkawa su
Jaruma Suzaila da vaki amma sai Shugaban nasu ya daka
Imusu tsawa suka fasa.
dubi
Dakarun ya
Shugaban
Suzaila cikin
girmamawa ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki ki saurara
na jc na shaidawa Sarki wannan sako naki"
Koda garma fadin hakan sai ya juya ya koma da baya
ya shige izuwa cikin gidan sarautar. Jim kadán bavan
shudewar wadansu 'yan dakiku nasu yawa sai kawai
suka ji kasa ta kama girgiza, nan take kuma suka ji wani
irin takun sawu mai karfi da kara mai ban tsoro tamkar
giwa ce ke tahowa.
Cikin hanzari Dakarun gidansarautar gaba daya
suka dare suka samar da hanya.
Koda jaruma Suzaila tayi arba da abinda ke shirin
tunkarOSu sai tà razana ainun duk da ccwa ta kasancc
gawurtacciyar jaruma waccc ta yaki bakar macijiya ta
kogo da kuma sihirtacciyar halittar kogi sai da zuciyarta
ta buga da karfi ta razana ainun saboda tayi arba ne da
wani irin mutumn mai kira ta matukar ban tsoro.
Mutumin ya kasance dogo zan kalele tamkar bishiyar
dabino, sannan kaurin hannayensa tamkar na katon
reshen bishiyarr...


Read / Download BUSA A MUTU Book 6

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album