Join Our WhatsApp Group

GIDAN MULKI Complete Hausa Novel Document by GIDAN MULKI


GIDAN MULKI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 121163



GIDAN MULKI

Reading Time: 10 Hours

Added On: 03, Jan 2024

Author: Asmeetar Haidar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08082589590

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 616.96 kb

File Type: txt

Views: 956+

Download: 756+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: GIDAN MULKI

Story and writing

By

Asmeetar Hydar






Ban yarda a sarrafa min labari ta kowacce siga ba, balle har a ɗora shi a website ko You Tube ba tare da izinina ba, wannan babbar matsala ce ga wanda duk ya yi ƙoƙarin yin hakan, dan haka a kiyaye. Haƙƙin mallaka nawa ne ni Asmeetar Hydar




I salute this group of writer's cox of your courage and ingenuity, the great writer's oganization of wisdom and technology, Mikiya writer's association, dignity and skill are in your blood i really appreciate being one of the member of this group



BISMILLAHIR RAHMANIN RAHIM

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ubangijin taliƙƙai, Allah ya daɗa tsira bisa ga shugabanmu Annabi Muh'd (s a w) Littafin GIDAN MULKI, ƙagaggen labari ne kuma mai gajeren zango, littafi ne wanda ya ƙunshi abubuwa kamar haka, Girman kai, Mulki, Gadara da kuma taƙama, ban yi wannan littafin dan na ci zarafin wani/wata ba, duk wanda yaga ya yi daidai da rayuwarsa to akasi ne, ku dai ku bibiyeni cikin littafin GIDAN MULKI, domin jin yanda zata kasance, na sadaukar da wannan littafin kacokan ga ƴaƴan sarauta da ke faɗin duniya, ni ce taku har kullum Asmeey ta Hydar marubuciyar littafin MAYAUDARI, ku dai ku bini kai tsaye cikin labarin tare da alƙalamina

08082589590






P.1
















*ƘASAR SUDAN........*



Da ƙarfin tsiya ya tura ta kan bed ɗin cikin zafin nama ya dannawa ƙofar key yana ƙara haɗe fuska kamar wanda tun da Allah ya haliccesa bai taɓa dariya ba, Afnan na ganin haka ta miƙe fuska ba bu walwala cikin taƙama da nuna isa ta ce "How dare you, do i look like your type? wallahi sai ka san ka taɓa jikina"

Jin abin da ta ce ne ya ƙara harzuƙa Muby da fuskarsa ta gama rinewa.

Gashin kanta da ke cikin alƙibba ya damƙe da ƙarfin tsiya ya haɗe bakinsu guri ɗaya, cikin salon mugunta ya cigaba da sarrafa bakinsa cikin nata yana kaɗa harshensa a ciki, wani zugi da raɗaɗi ne ke ratsa lips ɗinta kamar ana tsatstsaga shi, duk iya ƙoƙarinta na ganin ta ƙwace kanta amma hakan ya gagara, alƙibbar da ke jikinta ya fara kiciniyar cirewa, ganin abin da yake ƙoƙarin yi ne yasa Afnan saka dukkanin ƙarfinta da niyar ƙwace jikinta amma sai taji tamkar dutse take turawa dan ko motsawa be yi ba, a fusace ya yi jifa da alƙibbar nan take wata arniyar rigar bacci ta bayyana kwance kan kyakykyawar surar jikinta kalar sararin samaniya, gashin kanta da ya sauka kan wist ɗinta ne ya tattare ta bayanta yana mai damƙe wist ɗin nata cikin salon mugunta.

"Ashhhhhhhhh, wayyo Allah Fulani"

Murmushin mugunta ya saki a karo na farko, wanda hasken haƙoransa ya ƙara dallare room ɗin, cikin wata murya mai ɗan karen daɗi kamar ana busa sarewa ya matsar da bakinsa daidai kunnenta a hankali ya ce "Yau Fulani baza ta kwaceki ba, tun da ke ki ka kawo kanki, kin kasa zama inda ku ka sauka kin zo rashin kunya ko?".

Be jira amsar da zata bashi ba ya ƙara jefata kan bed, kafin ta mike ya yi saurin faɗawa kanta.

Afnan na ganin tabbas yau Muby ba zai saurara mata ba ne yasa ta ƙara haɗe fuska tana faɗin "You will pay for it, sai na saka an kulleka har tsawon rayuwarka, sai kayi nadama marar iyaka, ni wallahi ka sauka a kaina tun kafin fushina ya tabbata a kanka".

Ko sauraron abin da take faɗa be yi ba ya cigaba da murzata kamar ya samu fulawa, kayan jikin nata ya yaga da ƙarfi tare da cillasu gefe, nan take na shanunta su ka haske gurin masu masifar kyau da tsantsi, sun cicciko kamar zasu tsone masa ido, da sauri ya kai bakinsa a kai, wani zugi ne ya shigeta ta ƙwalla ihu tana ture kansa amma ina Muby ko jinta baya yi, ita kuwa Afnan ba bu alamun nadama a fuskarta balle arziƙin hawaye, idanunta a bushe taƙi yarda ta yi kuka dan ganin take rainata zai yi, dan a rayuwarta ta tsani raini.


Ƙara ta sake ƙwalawa jin wani raɗaɗin ya ƙara shigarta, kuyanginta da ke parloun ƙasa ne su ka ji ihun nata, da sauri su ka haura saman steps ɗin dan ganin abin da ke faruwa.

Tsayuwa su ka yi gaba ɗayansu aka rasa wadda zata buɗe ƙofar, sarai sun san halin Prince Muby baya ɗaukar shirme, tabbas idan su ka buɗe ƙofar sai sun fuskanci mummunan hukunci, idan kuma su ka kasa ceton Princess Afnan to yau me raba ta da su sai Allah, gaba ɗaya jikinsu rawa yake tsabagen tsorata, sun kasa yanke shawarar da zata ƙwace su.


Muby kuwa ya gama ficewa a hayyacinsa dan ganin surar jikinta, bai taɓa tsammin yanda take siririyarnan zata yi kayan marmari haka ba. Duk idanunta sun yi jajir tsabagen ɓacin rai, jikinta sai rawa yake kuma taƙi yarda saƙonninsa su shigeta, bata taɓa samun namijin da ya wulaƙanta ta irin Yarima Muby ba.

Shi ko gaba ɗaya ya mance cewar horata yake dan laushin jikinta da ke tsarfar masa, kayan jikinsa ya fara cirewa dan ganin zasu takura masa, Afnan na ganin haka ta tashi da ƙyar tana ƙoƙarin arcewa, hannu ɗaya yasa ya maidata tare da sakar mata nauyinsa, ƙara ta sake saki a karo na uku ganin yanda namiji kamar Muby ya danneta da dukkan ƙarfinsa, ga jikinsa duk na majiya ƙarfi fatar jikinsa a murɗe, gashin ƙirjinsa kuwa a kwance luf-luf mai masifar laushin tsiya, kamar zata yi kuka ta kallesa a hasale ta ce "Ka sauka a kaina haka wannan zalunci ne, duk abin da ka yi mun sai na faɗawa mai martaba, ba zai raga maka ba"

"Allah ko? ai nayi tsammin ke ce za ki ɗauki mataki, kamar yanda ki ka kawo kanki ba tare da an rakoki kamar yanda ake rako kowacce amarya ba, ni kuma haka zan yi abin da naga dama da ke, tun da abin da ki ke so kenan"

Ya ƙarashe maganar yana jifa da pant ɗinta gefe, subhanallah ya furta a ransa, tare da sauke doguwar ajiyar zuciya ganin shape ɗinta tamkar ita ta tsarawa kanta, har ya kai bakinsa kan na shanunta sai kuma ya tsaya cakkk, jin yanda ake dukan ƙofar kamar za'a karya, ganin hakan yasa Afnan ta samu damar janye jikinta, da sauri ta mayar da kayanta tare da saka alƙibba tana watsa masa harara, kwanciya ya yi ruffff da ciki ya dafe mararsa da ke barazanar barin jikinsa.

"Yareema ka buɗe ƙofarnan tun kafin ranka ya ɓaci, a yau ne na tabbatar baka da zuciya kuma baka gajeni ba, ina mulkin naka da taƙamarka su ka tafi ne?"


Cewar wani Dattijo da ke bakin ƙofar cikin shigar sarakuna duk jikinsa gold ne masu masifar tsada da sheƙi, dukan ƙofar ya cigaba da yi yana kiran sunansa, kallonsa ya mayar kan kuyangin da ke gurin cikin tsawa ya ce musu "Ku sauka daga nan kafin na hukunta ku"

Jiki na rawa su ka bar gurin har suna neman faɗuwa, daidai lokacin da Afnan ta buɗe ƙofar cikin isa da gadara, wani kallo ta yiwa Dattijon wanda za'a iya kiransa da kallon raini, kamar wata zinariya haka ta fara tafiya taku take cikin taƙama gami da nuna isa, har ta sauka down steps, shi kuma dattijon ya shige daga cikin ɗakin, a kwance ya same shi yana murƙususu dafe da cikinsa, amma wannan karon ya maida kayansa.


Gefen bed ɗin Dattijon ya tsaya yana kallonsa fuska a haɗe ya ce "Ka kyauta ai tun da ka yi abin da ranka yake so, yanzu kalli abin da ka jawa kanka na farko ka zubar da girmanka a kan wannan ƴar gadara, bayan haka ka jawa kanka ciyon da baka da maginsa a halin yanzu"

Lumshe idanunsa ya yi masu firgitattun kyau a hankali kuma ya buɗe su, cikin cool voice ɗinsa me kashewa mata masu cikakkun aji jiki ya ce "I'm sorry Abbu wallahi nima bada niyar wani abun na aikata ba, ni kaina sai yanzu nake jin haushin abin da na yi, amma hakan ba zata sake faruwa ba ayi min afuwa mai martaba"

Ya ƙarasa maganar yana mai rusunawa ƙasa.

"Shikenan ka sameni a fada yanzu"

"An gama Abbu yanzu zan shiga wanka na fito"

"A fito lafiya" Mai martaba ya faɗa yana fita daga ɗakin.




.......
A gafen Afnan kuwa a fusace ta fice daga babban parlourn gidan wanda ya fi girman manyan ɗakuna goma, ba bu abin da ke ciki face kayan sarauta da kuma gold-gold iya ganin wanda ya gani, gaba ɗaya parlourn ya tsaru kamar baza'a mutu ba, ko'ina kuyangi ne tsaye suna tsaron parlourn.



Da sauri kuyanginta su ka bi bayanta suna tattara alƙibbar da ke sauka har ƙasa, motoci ɗari ne ke jiranta a babban gate ɗin da ke waje, tun daga harabar gidan sarautan take taka wani carpet wanda aka shimfiɗa me ɗan karen laushi da haɗuwa kalar ruwan ganye, dogarai kuwa sai faɗuwa suke suna kwasar gaisuwa har ta fita daga gidan, wanda haɗuwarsa ma ya wuce shugaban ƙasan SUDAN ya iya zama cikinsa, gida ne wanda yake da hawa sama da uku kowanne hawa ɗaya yana ɗauke da dogarai masu tsaronsa guda ɗari, gaba ɗaya gidan zagaye yake da masu kula da shige da fice, ta ko'ina CC camera ne kama daga fadar me martaba har wajen gidan sarautar, ba bu inda zaka shiga a gidan wanda bazai baka sha'awa ba, hatta masu aikin gidan abun burgewa ne yanda su ke komai nasu cikin tsari, duk aikin gidan da na'ura su ke yinsa, hatta bawa flowers ruwa da na'ura ake yi.



Dogarai da kuyangin da su ka yi mata rakiya ne ke take mata baya, har ta shiga wata arniyar mota fara sol ƙirar Lexus jeep me masifar tsada, ita ce fara kawai a ciki amma duk sauran motocin baƙaƙe iri ɗaya ƙirar, Lamborghini.



Tana shiga ta zauna cikin taƙama da jin kai, ɗaya daga cikin dogaran ne ya rufe ƙofar motar nan take su ka bar unguwar cikin busa algaita, duk mutanen da ke unguwar sun san kalar algaitar da ake busa mata idan ta shigo unguwar, daga zaran sun ji wannan ƙarar busar kowa ke ɓoyewa cikin gida idan ba haka ba a wulaƙanta duk wanda ya fito kallonsu, duk da cewar babbar unguwace me tattare da attajirai da kuma manya-manyan ƴan kasuwa masu ji da kuɗi, amma ko kaɗan basu kai dukiyar sarki Ahmad ba, shine mai faɗa a ji a garin duk da cewar akwai shugaban ƙasa.



Babban hotel ɗin garin da su ka sauka ne motocin su ka fara shiga, kana ganin hotel ɗin ka san daga shugaban ƙasa sai masu masifar dukiya ke iya zuwa, ko jiran a gama pearking bata yi ba ta fice daga motar, ma'aikatan hotel ɗin na ganinta kowa ya rusuna ƙasa suna kwasar gaisuwa, amma ko kallon banza basu samu ba.


Taka steps ɗin ta fara har ɗakin da Fulani ke ciki, sanin halin Fulani ne yasa Afnan yin sallama murya a daƙile cike da miskilanci ta ce "Barka da wannan lokacin Fulani"

Kallon tuhuma Fulani ta yi mata kamar zata tambayeta sai kuma ta share zancen tana faɗin "Barka Gimbiya"


Wata matashiyar yarinya ce a gefe zaune kan sofa tana latsa waya, kamar daga sama matashiyar da zata kai shekaru ashin da uku ta ji muryar Gimbiya na faɗin "Ke baki iya gaisuwa ba ne? ko rashin girmama ɗan adam ne".


Jin abin da Afnan ɗin ta faɗa ne yasa matashiyar kallonta tana faɗin "Are you okay ni sa'arki ce? Fulani kina jin abin da wannan yarinyar ke faɗa min, yau kuma mulkin a kaina ya dawo".

Kallon Afnan da ke tsaye Fulani ta yi kafin ta ce "Gimbiya bata haƙuri kafin ranki ya ɓace, bana son rashin kunya" Jin abin da Fulani ta faɗa ne yasa Afnan ɗaure fuska ta ce "I should apologize to her, are you serious?"

Ta faɗa tana mai kallon Fulani da itama Afnan ɗin take kallo.

"Gimbiya ki bata haƙuri na ce"

"Fulani amma kinsan cewa ita ɗin ƴar kishiya ce ba asalin uwa ɗaya ba....."

A fusace matashiyar me suna Halima ta miƙe tare da ɗaga hannu da niyar kwara mata mari, cikin zafin nama Afnan ta damƙe hannun fuskarta a haɗe alamun baza ta ɗaukar mata ba ta ce "Don't try it next time dan ba zan saurara miki ba, ki tsaya a matsayinki na ƴar kishiya, na fi ƙarfinki na wuce saninki kuma na girmewa tunaninki"

Tsawa Fulani ta daka mata ganin abin na neman wuce misali, "Gimbiya koma ɗakin da ki ka zaɓa please, kar ki tayar mana da hankali anan, ke ki ka ce kin fi son naki ɗakin ke ɗaya, meyesa za ki kawo mana wannan taƙamar taki? dan Allah ki tafi"

Fulani ta faɗa tana dafe kanta wanda har ya fara yi mata zafi.

Kallon Fulani Afnan ta yi tare da marairaice fuska ta ce "Yanzu kina nufin ƴar kishiya ta fi ƴarki ta cikinki?"


"Ya isa haka Gimbiya wallahi zan ɓata miki rai, tun da har ban isa da ke ba shikenan".

"Haba Fulani wallahi gaskiya Gimbiya ke faɗi yanzu kin fi son Aunty Halima akan ƴarki" Cewar wata yarinya da ta shigo ɗakin, sanye cikin kayan sarauta shekarunta baza su wuce sha huɗu ba.

Har Afnan ta buɗe baki da niyar magana sai ta fasa ganin mai martaba ya shigo, nan take ta sha jinin jikinta, har ƙasa su ka rusuna suna gaishe shi, fuska cike da fara'a ya amsa yana mai tambayar Afnan inda ta tafi tun ɗazu, jin ta yi shuru ne yasa shi daka mata tsawa "Am asking you for the last time Gimbiya, where did you go?"

"Amm...amm....., Baffa dama gidansu...


Read / Download GIDAN MULKI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album