Join Our WhatsApp Group

KUKAN KURCIYA Complete Hausa Novel Document by KUKAN KURCIYA


KUKAN KURCIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14891



KUKAN KURCIYA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 08, May 2023

Author: Abba Gana ,Bilkisu Ibrahim ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 91.47 kb

File Type: txt

Views: 1199+

Download: 332+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: maida kallonmu gareta, tacika hannu dak'asa ta watsa jikinta, tasake kwala ihu saini Ameeda,  d'iyar malam dauda da iya Abu, d'iya d'aya tilo agurin iyayenna, nice tafari nice auta,  yarinya mai farin jinin tallah.


   Bansan sanda hawaye suka zubo bisa kumatunaba, takuma kaikaicewa ta rabga ihu, na girgiza kai dan tabani tausayi matuk'a.
   Mai adaidaita sahu ta tare, cikin muryar 'yan maye ta ce, "gidanmu zaka kaini.
    Mai adaidaita ya yatsine fuska, toni nasan gidan kunne? kifad'i anguwar dazaki malama.
   Tayi shiru alamar tunani, can tađ'ago tana kallonsa da rinannun idanunta, ta ce, "kaga namanta sunan anguwarmu amma muje zan dinga nuna maka hanya.
   Mai adaidaita yaja dogon tsaki yana fad'in saboda nima makakkene irinki ko??, yaja adaidaitarsa yayi gaba.
   Ta tuntsure da dariya tana nuna babur d'in tasa, kaga mahaukacin mutum, amfad'a maka dan ina a bige kwakwalwata bata aiki ne?, jiri ya jata kamar  zata fad'i, tayi saurin dafe wata mota dake bayanta.
  Indai tak'aice muku ta tsaida adaidaita kusan uku amma basu d'auketaba dan jin tamance sunan anguwarsu, da k'yar wani yad'auketa, tako ringa nuna masa hanya dalla dalla har kofan gida, ta zaro d'ari biyu acikin d'ankwalin ta tamik'a masa, yakarb'a yana fad'in toga canjin malama.
   Ta juyo tana kallonsa dan harta fara tafiya, ta ce, " sunana ba malamaba, kuma canji kaje nabar maka duka, tafad'a dad'an k'arfi.
   Mai adaidaita ya jinjina kai yana godiya ya ce, "ya ALLAH yashiryeki kinji.
   Muda muka biyosu abaya mukace amin ya RABBI.
  Cikin gidan tashiga tana tangad'i, iya Abu dake a tsakar gida tana aiki tabita da kallo cikin bacin rai.
   Ameeda tazube agabanta tana fad'in iya taimaka mini da abinci wallahi cikina kamar b'arayin duniya sunmin sata.
    Iya abu ta balla mata harara ke  tsinanniya kada ki bata min rai in abinci kikeso ki koma ki ciwo daga inda kika fito , idan kuma kinje kibar tunawa dani, inkuma bahakaba wlhy yanzu jikinki zaya gaya miki.
   ameeda ta tuntsure da dariya harda bugun k'asa ta ce, "iya aii tsinannun nada yawa dankema tsinanniyarce, na tabbata kafin iyayenki su mutu saida suka tsitstsine miki albarka..
   Kafin ta k'arasa iya abu tashiga jibgar ta tamkar ALLAH ya aikota, itako sai ihu take da kururuwa harda zagi, makwafta suna jinsu, babu wanda ya leko balle a shigo ceto, dan idan da sabo sun saba, babu wayewan gari dabaza'a daki ameeda ba, saidai idan bata kwana a gidanba, dan wata sa'in bata kwana agida,
         duka sosai iya abu tayi mata, saida taga  ko  yatsun hannunta baya motsi sannan tabarta tana cigaba da kalaman tsinuwa da d'ebe albarka ga d'iyar tata.
   Ahaka malam dauda yashigo yasamesu, azatonmu za'a samu rangwame daga garesa, amma saimukaji yana ambatar wannan shegiyar sai yanzu tadawo gida??.
   iya abu dake cin rai ta huro hanci ta ce, "yanzu tadawo zatamin iskanci nazane shegiya.
    Yayi dai dai,yasa k'afa ya shuri ameeda dake kwance A kasa matsiyaciya tashi kibawa mutane wuri, sai kaurin taba kikeyi asararriyan yarinya.
   Na rintse ido nabud'e danjin irin munanan kalami da iyaye ke yima d'iyarsu, lallai dole ameeda ta lalace indai har haka iyayenta suke mata tun tana karama.
   Itako ameeda tana kwance ko motsi batayiba bare ta amsa kalaman baban nata kota bi umarnin sa, ruwa ya d'ebo ya watsa mata, tabud'e idanunta dak'yar,  ya ce, "bacewa nayi kitashi anan ba me kika tsaya kina kallona, ameeda ta mika masa hannu tana fad'in taimaka ka kaini d'aki baba wlhy duk jikina yayi tsami, waccan tsohuwar ta dakeni sosai, kafa yasa ya shureta da karfi yana zagi da tsine mata, ta maida hannunta tana fad'in bakaso natashi kenan, dan nikam bazan iya tashiba, duk cikin yanayin maganar bugaggu take maganar.
   Banza sukai mata suka cigaba da harkokinsu, saida taji rana tafara dukanta taja jikinta da k'yar tashiga dakinta a kofar dakin ta kwanta abinta.................

Ku biyomu.



Hikayarmu!!!
Abba gana
            &
     Bily

www.muhdabbagana.blogspot.com
[10/02 20:06] Abba Gana: KUKAN KURUCIYA.......



                 NA
MUH'D ABBA GANA
                  &
BILKISA IBRAHIM {Bily}
    (Mrs Abdus'salam)


Page3⃣&4⃣


WACECE AMEEDA???.

     Ameeda diyace ga malam Dauda, iya Abu itace mahaifiyarta, ita kad'ai Allah ya mallaka musu, sun dade suna neman haifuwa a kwana a tashi Allah ya albarkacesu da Ameeda, sun nuna mata so da kauna da ya wuce misali wanda hakan ya jawo ta tashi a sangarce, tayi karatu har zuwa secondary kuma tanada kokari, ta samu tarbiyya dai dai gwargwado a wajen iyayen nata.
    Ameeda tun tana 'yar karama take talla, saboda tsantsan son kudi irin na mahaifiyarta tun mahaifinta malam dauda baya jin dadin tallar da ake d'oramata  har ya zamana baya iya cewa komai  dan iya abu ta mallakeshi sai abinda tace.
    AMEEDA k'yak'yk'yawace sosai, ga dogon hanci, tanada hak'uri sosai, dakuma tsoro.
   Duk da gatan da iyayenta suke mata wannan baihana mahaifiyarta duka da aibanta d'iyar ta taba, abu kadan ameeda zatayi sai mahaifiyarta ta hauta da duka da zagi, balle taje bata sayar mata da kayan sana'ar taba, aii ranar ta banu.
   K'yawun ameeda yasa takasance mai farin jini awajen samari, talakawa damasu kud'i, idan kaga motoci na layi a k'ofar gidansu saika d'auka wani taro akeyi, duk wanda yazo kuma dole taje balle idan yanada mota, inko tak'i zuwa mahaifiyarta  tafara tsinemata kenan dayi mata gori, wai babanta talaka itama taje ta auri talaka, saisu dawwama a talauci.
    Wannan maganganu suna k'ona zuciyar ameeda, amma babu yanda zatayi tunda mahaifiyarta ce.
  
Akwana a tashi wani saurayi mai suna Naseer yashigo rayuwar ameeda, Naseer d'an mai kud'ine sosai, gashi shima an sangartashi, dan shikadaine awajen  iyayensa, kwata-kwata bashida tarbiyya ko kad'an, ya kware a fagen shaye-shaye da neman mata, tunda ya k'yalla ido akan Ameeda yaji yana buk'atar yayi tarayya da ita, amma saidai ameeda tak'i bashi had'in kai, yaja ra'ayinta da kud'i, amma ta bijirewa buk'atarsa.
   wani abokinsa Badaru shiyya bashi shawarar yakama k'afa da mahaifiyarta mana, yasan dole tasa  ta kulashi , yakoji dad'in wannan shawarar tasa, dan haka sukayi shiga ta mutunci sukaje har gidansu ameeda, yanemi izinin zuwa wajenta zance, dafarko mahaifiyarta tak'i amincewa, dan ta ce, "baza'a kashewa d'iyarta kasuwaba tana tashenta, amma da Naseer ya ajiye mata d'aurin kud'i saita amince da sauri, harda alk'awarin mallaka masa ameeda.
   Tun daga nan Naseer yasamu damar zuwa wajen Ameeda, saidai tak'i bashi hadin kai, ganin wannan yasa yafara zuba mata benelyn acikin lemo, tun bata sha harta fara saboda tana ganin nan gaba shi zai kasance mijinta,
    Ahankali lemon dayake kawomata yafara tasiri a rayuwarta, har takanji idan bata shaba bata jin dad'i.
   Da Naseer ya kula tazo hannu, saiya koma kawo mata zallar benelyn, da sauran kayan saka maye, akwana atashi harta fishi kwarewa wajen iya shaye-shaye, ya kuma koya mata zuwa club, takanje ta kwana acan, ba tare da wani fargaba ba, Ameeda tayi suna a club saboda iya rawa, da d'ibar kayan maye, idan tana rawa dolene abata fili a club.
    Saidai abin sha'awa ga rayuwar ameeda, duk iskancin nata bata tab'a aikata zina ba, babu lallab'ar da Naseer bai mataba amma tak'i, bayanshi wasu dayawa su kan sha kawo mata hari amma tak'i, duk buguwar datayi baka isa kaja ra'ayin taba, bare kace zaka nuna mata k'arfi.
    Wasu samarin kuma suna tsoron Naseer ne saboda zarransa,  yanzu Ameeda tazama cikakkiyar 'yar maye.
   Gashi iyayen nata sun tsaneta, suna kuma tofin ala tsine da k'addarar rayuwar data da baibaye d'iyar tasu.
   

        Yauma kamar yanda ta saba ta tashi tayi wankanta, tad'au kwalliya cikin wando da riga na fakistan, tayi matukar kyau, tafito tana goge takalmi, iya abu tafito daga kicin hannunta rikeda kwarya da gari, Ameeda ta ce, "iya yau babu abincine??.
   Iya abu ta watsa mata harara, tana fad'in tunda kin bani kud'in yi abinci basai ki danne ni ki kwataba.
   Ameeda tayi murmushi tareda jawo jakkarta, tazaro 'yan dubu dubu guda biyar ta mik"a mata, ga wannan kuyi cefane kafin nadawo.
   Jikin iya abu na rawa takarb'a tana washe baki, yauwa 'yar albarka, idan kina bada irin wannan mai zai sa muringa fada, kedai ALLAH yabaki miji nagari mai kud'i da mota.
    Ameeda tayi murmushi domin jin furucin mahaifiyar nata, tana mamakin kwadayi irin na mahaifiyarta, itadai indai kanada kud'i to komai mugun halinka zata zauna dakai, ahankali ta furta ya ALLAH ka shirye iyayena, kakawo mini canjin rayuwa mai albarka.......

Ku biyomu.


           ©2017


Hikayarmu!!!.
Abba gana
            &
     Bily
[10/02 20:09] Abba Gana: KUKAN  KURUCIYA..........




                  NA
MUH'MD ABBA GANA
                    &
BILKISA IBRAHIM {Bily}
      (Mrs Abdus'salam)



Page5⃣&6⃣



AMEEDA tamik'e tana fad'in iya bari naje saina dawo, iya tajuyo tana kallonta ta ce, "to Yau kuma sai ina??.
    AMEEDA tad'an gyara tsayuwarta ta ce, "iya zanje wajen falmata ne, amma zuwa yamma zan dawo, zanbawa hashimu sako yakawo muku yanzu idan nafita.
   Iya ta washe baki tana fad'in to madallah, Ameedan baba, amma dan ALLAH yau kar a dawo a buge d'innan.
    Ameeda ta fice tana fad'in to inna, a zaure ta tsaya tana share hawaye, da alamun tana cikin damuwa, tad'an dad'e tana zubar da hawaye, daga baya tagyara fuskarta sannan ta fice.
    Gidan wata k'awarta taje falmata, itama dai falmata irinta ce, dan a club suka had'u, saidai falmata tana zaman kantane, wannan halinne ya banbantata da Ameeda, a hankali suka shaku har suka zama k'awaye mafi...


Read / Download KUKAN KURCIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album