Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

A GIDA DAYA Complete Hausa Novel Document by A GIDA DAYA


A GIDA DAYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 75608



A GIDA DAYA

Reading Time: 6 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Maman Fareesa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 445.92 kb

File Type: txt

Views: 637+

Download: 1415+

Last download: 3 days ago

Description/Story: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story& written by mmn fareesa


*GODIYA*
Alhmdllh ala kulli halin🙏tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (S W A) da ahlayensa da sahabbansa. ALLAH nagode maka daka bani ikon Fara wannan book. Yadda nafara lfy Allah kasa na idar lafiya.


*Gargad'i*
Banyarda wani ko wata ba su canza mun novel ta kowace siga ba. In kunne yaji jiki ya tsira.

*Abin lura*
Ya kamata ace muna d'aukar abinda ya dace muna yin amfani dashi, muna yin watsi dana banza.


BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

🅿️1&2

Kyawawan y'an mata ne zaune su ukku acikin mota a back sit, yayin da wata guda ke zaune a front sit kusa da driver, kasancewar sun dawo daga skul zasu koma gida ne.
Budurwar dake atsakkiyar su ce tayi ajiyar zuciya had'e da kallon ta kusa da ita tace. "Hmmmm! Wallahi *Khadija* fargabar dawowar Yaya *mahmud* na keyi, sabo da nasan mun shiga ukku agida, sai mun zama bamu da wani sukuni wallahi."
Ummi ta karb'e zancen da cewar. "Kin san fa ko ƙarshen wata inya dawo yayi two days walllahi jinina akan akaifa yake, balle kuma ace anmai doshi aiki nan gaba d'aya."

*Khadija* ba tace komai ba, tayi dai shiru kawai tana ta sauraron su. sabo da ita wanda ma suke zancen akansa bata san shi ba.

Zee dake front sit ta tab'e baki ba tare da tace komai ba, sai dai ak'asan ranta murnar dawowar shi take yi.. Cikin isa da raini ta cewa driver d'in. "Kai dallah yi parking."

Bai ce komai ba yayi parking agefen hanya.
Ummi ta kalli Maryam suka tab'e baki sbd ganin zee ta fita sun tsaya da wani boy friend d'in ta ibbi suna magana.
Ahankali khadija ta d'ago dara daren Golden eyes ɗin ta ta azasu afuskar ummi, tukun ta buɗe baki cikin siririyar muryar ta tace. "Ko dai asauke ni na shiga adai-dai ta ne? Dan wallahi inada uzuri agida in mun koma."

Ummi tace. "Ah ah wlh Abba ba zaiji dad'i ba, ya ga mun fito tare wani ya koma daban bari na mata magana." Tana fad'in hakan ta bud'e k'ofar ta fice zuwa gurin da zee suke atsaye
Rumntse idanunwan ta Khadija tayi sabo da fitsari ne sosai ya kama ta tun a skul, amma sabo da tana da k'yan-k'yami yasa bata shiga toilet d'in skul d'in ba.
Maryam ta dube ta tace. "Lafiya dai ko?"
Khadija tace. "Lafiya lau fitsari ne nake ji sosai..." kafin Maryam tace wani abu ummi da zee sun shigo cikin motar.
Maryam tace. "Dan Allah isah muje khadija ce keda uzuri wallahi." Mitss! Zee ta doka tsaki had'e da cewa. "Aikin banza da wofi, dama akan wannan *agolar* ce aka matsa mun? Wato uzurin ta yafi nawa kenan?" Banza sukai Mata, yayin da isah yaja motar suka nufi gida, dama duk cikin yaran gidan ya tsani zee sabo da ba tada mutunci da girmama manya, ko gemun ka najan k'asa indai kana ak'ark'ashin gidan su to ba zata girmama ka ba daga ita har mama *jummai* (mahaifiyarta).

Suna shigowa get isah yayi parking suka fito.
Zee tayi hanyar sashen su yayin da ummi, Maryam, Khadija suka nufi suma nasu sashen atare.
Khadija dake ta sauri sabo da fitsarin daya kama ta,l ko sallama batayi ba ta shiga waiting parlour tana mai wucewa k'ofar sashen su.
Hajiya hakimah dake zaune kan kujera taja tsaki had'e da cewa. "Ke zonan dan uwar ki baki iya sallama ba?"
Jikin Khadija har rawa yake yi ta nufo gurin ta. Cike da tausayawa ummi da suke k'ok'arin zama tace. "Ayya hajiya tayifa sallama k'arar TV ce tasa bakiji ba." Wata uwar harara hajiya ta watsowa ummi, hakan yasa ummi Jan bakin ta tayi shiru suka zauna ita da maryam akan kujerun dake parlourn.
Ahankali Khadija ta duk'a nesa da ita tana cewa. "Kiyi haƙuri hajiya dan Allah." Hakan ko yayi dai dai da fitowar Aunty (mahaifiyar Khadija). Kallon ta anty keyi cike da mamaki sabo da ganin ta tsigunne agaban hajiya hakimah kuma tasan yanzun taji k'arar anbuɗe get sun dawo daga skul.
Cikin shan k'amshi hajiya hakimah tace. "Ki kiyaye rashin k'in yin sallama aguri ga mutum, domin ko hakan na nuna bashi da tarbiyya, dan haka tashi kije." Jiki babu laka Khadija ta tashi ta kalli anty ba tare da tace komai ba ta nufi wata k'ofa. Anty bata ce komai ba ta dubi su ummi tace. "Kun dawo daga skul d'in?"
Atare gaba ɗaya suka amsa mata da. "Eh anty sannu da gida."
Tace. "Yauwa." Tana barin parlourn.

Tab'e baki hajiya hakimah tayi had'e da cewa. "Kilibabbun banza, zaku tashi kuje ku had'a kayan guga da aka kawo kujeran ko gulmar zaku tsaya yi ne? Ai gara wannan yaron ya dawo koya gyara muku zama! (mahmud).
Tashi sukayi ummi tace. "Dan Allah hajiya da gaske gobe Yaya zai dawo?" Banza ta musu basu kuma cewa komai ba suka bar parlourn.
Hajiya kuwa Sai da aka Kira magrib tukun ta tashi ta shiga ciki.

***********
Khadija na nufar shashen anty toilet ta wuce tayi buk'atar ta, kafin ta fito anty dake zaune kan bed ta dube ta had'e da cewa. "Laifin me kikayiwa hajiya?"
Sun kuyarda kanta tayi had'e da cewa. "Na shigo banyi sallama ba!"
"Daga yau karki kuma hakan sabo da ba dai-dai bane kina jina?" Ahankali tace. "Eh."
Anty tace. "Khadija bana son fitina ko kad'an, wllahi inba cin alhaji yace ki dawo nan da zama tunda umma ta rasu naso ace gidan yaya Abbas kika koma, bazan iya matsa musu ba tunda ya damu da ke k'in amincewa ta ba dai-dai bane zaiji bbu dad'i, dan haka Allah ki zauna da kowa lfy agidan nan babu ruwan ki da kowa." Ahankali tace. "To insha ALLAH."

Anty tace Kin ga gobe yayan su zai dawo daga Abuja acan yake aiki, amma yanzun anmai doshi nan. Nasan halinshi baya shiga harkar kowa agidan nan, tunda nazo Yana bani girma inhar yazo ƙarshen wata yayi week end, sabo da haka ki girmama shi shima yayan ki ne." Ahankali tace. "To" kawai.
Anty tace. "Yaya karatun naki to, kina dai ganewa ko?"
Cikin sanyayyar muryar ta tace. "Eh anty alhmdllh Ina ganewa, kinga yaune zuwa na na ukku a skul d'in amma alhmdllh wlh."

Anty tace. "Masha Allah! Ai haka akeso."
Kiran Sallar magrib ya saka su yin shiru, khadija ta wuce toilet sabo da tayi alwallah..

*Asalin labarin*

Alhaji Adam d'an asalin k'auyen shema ne dake jihar katsina. Su ukku ne agurin iyayen su. Adamu sai bello da k'anwar su binta.
Sun taso da tarbiyya tare da ilimin addini dana zamani.
Binta primary skul tayi aka mata aure a kano. Yayin da Adam da bello suka cigaba da karatu had'e da kasuwancin su na siyar da kayan gwanjo. Bayan Adam yyi diploma mahaifinsu ya rasu, hakan yasa suka siyar da gidan su da gonakin su suka dawo kaduna da zama tare da mahaifiyar su (inno).

Cikin hukuncin Allah Adam ya had'u da hakimah sukayi aure, kasancewar babban gida ne ya sata agidan su aka jamusu ƙofar su daban.
Ahankali kasuwancin su ya fara haɓɓaka har suna zuwa garuruwa sarin kaya.
Bayan wani lokaci hakimah ta haifi mahmod, alokacin Kuma bello ya had'u da jimmai. Itama dai anan aka kawo ta bayan auren su aka ja musu katanga.
Babu laifi suna zaune lfy da juna duk inno Bata shiga harkan su sai dai agaisa amutunce. Sai dai kuma Allah yayiwa jummai hassada duk abinda mazajen su zasuyi musu indai taga na hakimah yafi nata sai taji haushi aranta, amma afili bata nunawa. Ana ahaka hakima ta haifi d'anta na biyu yusuf, akuma lokacin jummai ke kwaikwan cikin ta na fari.
Zuwa lokacin data haifi kamal duk mazajen su sun Sami aikin gwamnati.
Acikin wasu shekaru aka canza ginin gidan zuwa na zamani, akayiwa kowa sashen sa daban, itama inno sashen ta daban.
Ayanzun haka alhaji Adam (Abba) yana da ƴaƴa Mahmoud, yusuf, kabir, ummi, maryam, sai auta salim....

*Mahmoud*
Saurayi ne d'an kimanin 35yrs. Ya kammala karatun sa na mass com (d'an jarida) har an d'auke shi aiki a Abuja duk karshen month yake zuwa kaduna yayi 2 days kafin ya koma.
Mahmoud kyakykyawane ajin farko, akwai class da miskilanci had'e da shank'amshi. Dogo ne wankan tarwad'a, yana da k'atuwar sallaya atsakkiyar goshin sa dake k'aramishi kyau, bai cika dariya ba saita Kama, murmushin sa kuwa sai ya ga dama yake yi, inya had'e rai saika d'auka besan meye dariya ba.
gaba d'aya yaran gidan najin shakkar sa da tsoron sa sosai, sabo da baya wasa da yaro ko ya sakar
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download A GIDA DAYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album