Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DA BAN SANSHI BA BOOK 3 Complete Hausa Novel Document by DA BAN SANSHI BA BOOK 3


DA BAN SANSHI BA BOOK 3

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36330



DA BAN SANSHI BA BOOK 3

Reading Time: 3 Hours

Added On: 11, Jul 2024

Author: Fauziya D Suleiman ,

Ebook Compiler : Zeinab Abdoul-karim

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 194.25 kb

File Type: txt

Views: 1098+

Download: 758+

Last download: 2 days ago

Description/Story: 锘縖10/28, 2:16 PM] H Inna馃馃徏: DA BAN SAN SHIBA

kashi na 3
Zeinab Abdoul-karim
(1)
BAYA TA HAIHU
Alhaji Musa yana zaune a falo shi d'aya yana kallo, sai dai rabin hankalinsa ba shi ga kallon da yake yi, akwai wani abu dake damunsa cikin rai, musamman na bore da iyalinsa suke yi masa, da can baya ne da yanzu yana nan zaune da yaransa da matarsa, amman yau babu ko d'aya. Ya kalli 6angaran d'akin Hanan kamar yana tina wani abu sai ya mik'e tsam ya nufi shashinta, ya isa k'ofar d'akin ya fara k'ok'arin bugawa, sai yaga k'ofar ta bud'e ya lek'a da kansa yana kiran sunanta.
"Hanan! Hanan! Baiji motsinta ba ballle ta amsa, sai ya k'ara lek'a d'akin ya tabbatar babu kowa aciki, yayi d'an jim yana tinani, sai ransa ya bash tana tare da mahaifiyarta, ya kamata ya gansu tare, don haka kai tsaye can ya nufi, sai dai nan d'in ma bai ga Hanan ba, Haj. Bilkisu kawai ya gani tana kallo, ya shiga d'akin da sallama, ta amsa batare da ta kalli inda yake ba, ya tsaya yana k'are mata kallo daga inda yake tsaye a bakin k'ofa sannan ya fara magana.
"Banga Hanan ba, ina son yin magana da ita."
Taci gaba da abinda take yi amma tana masa masa maga "kaduba d'akinta mana, zaka ganta. Can na fara dubawa ban ganta ba shi yasa nazo na tambayeki, ko kuma ta fita ne? Ya k'ara tambayarta. "Nifa ban sani ba, idan har baka ganta ba ya tabbata bata gidan kenan. Ta bashi amsa cikin gadara da 6acin rai, ya d'an ji haushin yanda take bashi amsa, don haka cikin 6acin rai shima ya fara magana. "Amman kin san bana son hanan ta fita da daddare, ki duba agogo yanzu karfe tara na dare, ina mace zata fita cikin wannan daran, ba kuma tare da sanin mahaifiyar ta ba? "Gaskiya alh. Ka fara kai ni mak'ura, shin hanan karamar yarinya ce da dole sai na san ina tayi? Taja dogo tsaki ta kawar da kai, ransa ya 6aci da abin da ta aikata, kamar zai k'ara yin magana amman sai ya fasa, ya gyad'a kai ya fice daga d'akin, ta bishi da harara cike da tsananin bak'in ciki da takaici. Na kusa maganin taurin kan ka wallahi" ta fad'i a zahiri cikin takaici.
Bayan ya koma falo abu d'aya yazo ransa kiran wayar Hanan. Domin babu abinda bai
1 路 Like 路 React 路 Reply 路 Report 路 10 February 2017
Zeinab Abdoul-karim
(2) babu abinda bai so illah ace d'iyarsa na fita cikin dare irin haka, ba kuma tare da ya san inda take ba, ya daddana wayar ya kara a kunnensa, cikin sa'a kiran ya shiga wayarta ta fara ringing. Duk wani mataki na yaudara da neman isar buri Mansur ya kai ga Hanan, sai dai yana gab da yin abin da zai zamto na k'arshe gareta kiran wayarta ya shigo, firgigit hanan tayi gami da k'ok'arin ture mansur daga gareta, hakan bai masa dad'i ba, ya bita da kallo cikin tsananin damuwa, abin data fara yi ya fara bashi mamaki, domin rigarta da ya kusa rabata da ita ta mayar cikin rawar jiki da tsoro. Ya kalleta cikin wani irin maye da bai ta6a shiga ba ta begenta, ya kai k'ololuwa yau a neman cimma burinsa ga hanan, amman ta aikata masa haka. Cilin wata irin murya mai kama da ta wanda ya sha giya ya bugu ya fara magana "yaya haka hanan? Bata kalleshi ba tayi shiru cikin damuwa, ta sanya hannu ta toshe bakinta tana kallon wayarta da ke ci gaba da kira, idan ta katse sai wani ya k'ara shigowa ta kasa ta6awa, mansu yataso
Mansur ya taso daga inda yake yana layi ya nufeta ya tsaya daga bayan ta, ta waiga ta kalleshi har lokacin jikinta rawa yake yi. "waye ya kira ki hanan? Mansur ya tambaya kamar zai k'ara janta jikinsa, amma sai ta kauce da sauri tana nuna masa wayar, cikin rawar murya ta fara magana.
"Babana ne ya kira man...shine ya kara..." tana cikin rawar baki, ya kalli wayar sai ya mik'a hannu da nufin zai d'auki, sai ta rik'e hannun da sauri alamar bata son ya d'auki wayar, ya juya ya kalleta cikin idonta. "Me zaka yi man? Ta wurga masa tambaya, cikin 6acin rai ya bata amsa. "zan kashe ne, watak'ila da bakiji kiran ba, daba zaki damu haka.
Ta girgiza kai alamar a'a tana cigaba da kallon sa "kar ka kashe, kar ka kashe kiran babana man...
Cikin fushi ya fusge hannunsa daga rikon dayi masa ya nufi gefen gado ya zauna ya dafe kansa, ta juya ta kalleshi a yanda yake zaune, babu komai a jikinsa sai gajeran wando, hawaye suka zubo daga idonta. Tabbas tana son mansur tana son yin duk abinda yake so, amman bazata iya sa6awa
(3) amman ba zata iya sa6awa mahaifinta ba zata iya tsallake maganarsa ba, hawaye ya zubo daga idonta mai ciwo, sai ta d'auki wayar da sauri ta rik'eta a hannunta, sannan ta janyo k'aramin gyalenta da sauri wanda ya fad'i a k'asa ta fara kokarin yafawa, mansur ya d'aga ido da sauri ya kalleta cikin mamakin abin da take k'ok'arin yi, cikin d'aga murya ya fara magana. "Hanan me kike shirin aikatawa? Kina nufin baki k'aunata kenan? Yanayin yanda yake maganar kamar zai fasa kuka, hanan ta kalleshi sai ta fashe da kuka tana gyad'a kai. Kayi hak'uri man, bazan iya karya alk'awarin da na yiwa mahaifina ba, bazan iya ba... Ta k'ara rushewa da kuka, ta yi hanyar fita da gaggawa, ya mik'e da sauri ya nufeta yana magana cikin d'aga murya. "Haman ki tsaya...kar ki cutar da rayuwarki da tawa, ima son ki hanan... Bata kula shi ba ta fice da sauri, sai ya nufi kofar zai fita, sai kuma ya tuna yanayin da yake ciki, ya koma da gaggawa ya d'auko riga doguwa ya sanya ya bita da hanzari. Hanan tana tafe cikin sauri tafice daga
Gidan, maigadin gidan ya bita da kallo cikin mamaki, dai-dai lokacin mansur ya fito da gaggawa, yayi kamar zai bita da k'afa sai kuma ya fasa ya nufi motarsa cikin sauri.
Tana tafiya a hanya tana goge idonta yazo yayi parking ya fito da sauri ya sha gabanta ta kalleshi cikin damuwa idonta yana zubar da hawaye. Me yasa haka hanan? Me yasa? Ya wurga mata tambayar data kara tayar da hankalinta, ta kwar da kanta gefe ta kasa bashi amsa. "Wannan ba shine abinda ya kamata ki min ba, yanzu ina kike son saka raina? Ta kalleshi cikin idonta wanda ke zubar da hawaye "ina sonka mansur, amman bazan iya yin abinda kake so ba, na jima ina adana kaina, na yiwa mahaifina alkawari bazan sa6a ba, na yi maka alk'awarin samuna a yanda nake, na maka alk'awarin auran ka, bazan sa6a ba, ba zan yadda na auri kowa ba sai kai, ka yadda da hakan. Yanda take maganar cikin kuka ya sanya shi kasa cewa komai, duk da ba hakan ya so ba, amman babu yanda zai yi, cikin k'ok'arin rarrashin kansa ya fara magana. Shike nan na yadda,
(4) zan bi abin da kike so ba don ina so ba hanan, amma ki tabbatar soyayyarki tana gab da hakani. Ta k'ara kawar da kanta, ba tason maganar shi tayi tasiri a cikin ranta, ya kamo hannunta yana magana. Kizo muje na kaiki gida. Babu musu ta bishi zugwi-zugwi, ya bud'e motar ta zauna, sannan ya zagaya 6angaran direba, ya jima yana kallonta ko zatace musa wani abu amma ta kasa magana, sai ajiyar zuciya da goge idanu kawai datake yi, ya tayar da motar ya fara tafiya. Aliyu bayan tashin sa daga jiont din su kai tsaye gidan alh. Musa ya wuce, a cikin ransa yaga dacewar yaje ya gaisheshi, domin ya kwana biyu basu had'u ba, sanda yake shiga ofis bai shiga yanzu shi kwana biyu, duk da a k'asan ransa yana jin kamar akwai wata buk'atar da zata kai shi gidan bayan haka, amman yak'i yadda da hakan, yafi bari, ya sak'a abu guda cikin ransa kawai. Yana tafe akan hanya bayan ya shiga cikin layin gidan, bai san dalilin daya sanya yake tafiya a hankali ba, kawai dai ya san ba shi da karsashi, kamar ance ya kalli wani 6angare
Na layin sai ya hango mota a tsaye, abin da ya bashi damar k'arewa motar kallo gami da k'ara rage gudu bai gane motar ba, domin cikin mansur yana da motoci kala-kala shi kuma bai san wannan ba. Kawai sai yaji ya kasa amincewa da tsayuwar motar a gurin, yana zargin ta mansur ce, ya matsa can gaba ya tsayar da motarsa amma yana iya hangen motar, bai ganin komai na cikin motar domin gilasan motar bak'ak'e, don
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DA BAN SANSHI BA BOOK 3

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album