Join Our WhatsApp Group

DA IMAN Complete Hausa Novel Document by DA IMAN


DA IMAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 38073



DA IMAN

Reading Time: 3 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Mamuh Gee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 223.62 kb

File Type: txt

Views: 962+

Download: 450+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ๏ปฟDAIMAN
Na Mamuh geeh
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
DAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE
โ˜†dedicated toโ˜† Husnah bbchoudiallo BISMILLAHIR-
RAHMANR-RAHEEM. Ina mika dukkanin godiata ga
masoyana masu son novels dina, Kuma akoyaushe ina
samun sakon fatar alkhairanku...ngd allah yabar kauna.
1โ†’5 Sallama take kwadowa tun akofar gidan harta shigo
dan karamin tsakar gidan. Sanye takeda atampha `yar
leda kalar kore shar wato kalar asalin `dan `kauye..sai
wani gyale fari data yafo mai bakin lesi da `yar jakar
hannunta `baka data farfashe alamar tsufa duk da itace
tafi kowa wayewa akauyen tunda itake zuwa birni.
Shekarunta xasu kai talatin da takwas zuwa da arba'in
zuwa da sama. Wata sallamar takuma kwadawa tana
fadin, Wai duka gidan bakowane nake sallama ba'a
amsawa? Daga bayanta taji an amsa mata cikin wata yar
siririyar murya. Juyowa tayi adan tsorace tana ganinta ta
hade fuska tareda watsa mata harara tace, Lallai na
yarda da kinsamu sake a wurin ladingo. Munafuka mai
kamada mayyar uwarta ace kina cikin gidan nan naketa
rangada sallama amma kikayi lukus a daki. Toma wai
uwar me kike adakin ne. Sunkuyar da kanta tayi
muryarta na `dan rawa tace, Kiyi hkr iya jummai wlh
kainane yake ciwo banjiba. To dama ina zakiji ladingo ta
daure miki gindin iya shege. Ladingon ce tafito daki cikin
sauri tana daurawa guiguyayen kanta dankwali murya
cikeda masifa tace, Wai hayaniyar me nakejine a gidan?
Washe jajayen hakoranta tayi dasuka dafe tana fadin, Aa
jummai lfy daga zuwanki kike fada,badai wannan mai
kamada muciyarce ta tabakiba yanxu nasa buba ya yayi
mata dukan shanu ba. Aa kyaleta ai dagayau kuma
andaina dukanta dan nazo mana da mafita akanta kuma
wllh ba karamin samu zamuyiba ke wlh har makka sai
munje. Washe baki ladingo tayi cikeda farin ciki tace,
Haba jummai yanxu naji zanje, Nidai idan xamu samu
kudin aiko gidan cire kaine xan bada ita na huta da ganin
wannan shegiyar fuskar tata mai kama da jariran aljanu.
`Dakin ladingo suka shige. Tadan leko tace, Kuma wlh
kafin nafito ki tabbatarda kinyi wanke wanke kin dora
mun abincin saidawata na rana.munafuka dangin ifiritu.
Sum sum tawuce tafara hada kayan wanke wanke dan
ita tarigada tasaba da xagi,cin zarafi,duka da wahalar
babah ladingo da `yayanta buba da idi dakuma babbar
aminiyarta wato iya jummai. โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹โ—‹ Gyara zama tayi
takalli aminiyar tata tace, Ladingo wani alherine nagani
nace to lallai kece kika cancanta dashi. Wato can gidan
hajiyar danake zuwa birni kai mata yan aiki. Da sauri
ladingo ta kada kai tace inajinki jummai. Wato wani
alhajine mai shegen kudi a acan habuja, `dansa dayafiso
fiyeda komai aduniyarnan yasamu matsala ta tabin
kwakwalwa ta sanadin shan ko menene ma sunan?ni
namanta sunan abun. Mahaifiyar yaron ta rasu tun yana
yaro ta a kasar turawa yatashi acan yakoyi shan abun
har yasamu matsala. Matar alhajin ita tace bazata iyaba
shinefa akayi takai masu aiki duk wadda aka kai giduwa
suke basu iyawa sbd. Mahaifin yaron kuma bai cika
zamaba. Anyi na asibin tarsun gaji shine aka kira malami
yace sammu ne akayiwa yaron. Atakaice dai baasamu
me iya zama dashiba shine malamin yace ayi masa aure
sbd matarsa bazata gujesaba. Anyi neman matar dazaa
aura masa babu sbd kowa tsoro yake. To matar alhajin
saita bugowa hajiyar danake zuwa gurinta tace asamo
masa koda yar kauyece idan yaso inya warke sai ya
saketa.kuma ta bada kyautar miliyan daya ga duk wanda
yabada 'yarsa aka daurawa yaron. Shine naga wannan
mai kamada masillar kitson batada wani amfani agareki
ba gwara ki badata ki hutada dangin mayuba. Wani irin
fitsarine yakusa kufcewa ladingo ta waro ido jikinta na
rawa tace, Jummai miliyan daya? Yazamuyi dasu?
Kwantar da hankalinki Miliyan daya dinnan rabawa
zamuyi muda 'yayanmu tunda duk babu mai abinyi
acikinsu sai sace sace kinga kuwa mun huta. Wata irin
guda ladingo tasaki tana shewa tace, Wllh jummai idan
kinje yau kice nabasu ita ko gobe sukeso suxo adaura
nabasu........ ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†dedicated
toโ˜† Husna bbchoudiallo 6โ†’10 Cikeda farin ciki tareda
kwarin gwiwa ta isa kano gidan haj salamatu ta zayyane
mata ansamu yarinyar daza'a daura auren da ita. Cikin
farin ciki itama haj salamatu takira matar alhajin haj
zeenat tafada mata ansamu. Murna tayi sosai tareda
cewa, To shikenan yanxu zan aiko da kudi dubu dari
biyar asiyawa yarinyar kaya, Kuma akoya mata
abubuwan daya kamata dan nan dataxo babu me
lokacin koya mata yanda zatayi aiki da abu kuma inson
tadanyi clean kafin nanda sati sbd daddynsa dayazo
za'azo adaura auren aranar juma'a. So banason yazo
yaganta kaca kaca yace anfasa dan gskia baxan iya
cigaba da wahalar nema masa masu kula dashi. Kuma
inason tazo nan kano gidanki ace kece uwarta dan
banasan yasan 'yar kauyece. Kin gane zance kuwa. Cikin
rawar jiki tace, Ai duk abunda kika fada kamar
angamane haj. Yauwa to sai anjimanku. Tana datse kiran
haj salamatu takalli jummai tace, To jummai kindai ji
abunda tace dan haka ya kike ganin xaayi da iyayen
yarinyar? Cikin washe baki jummai tace, Ai haj ita
yarinyar batada kowa sai matar mahaifinta data bada ita
wato aminiyata sbd uwar yarinyar tarasu kuma batada
dangi sbd buxuwace daga nijar ta tsallako wai iyayenta
gobara ta cinyesu shinefa mijin aminiya ta ladingo ya
aureta suka haifi yarinyar. Bayan haihuwar yarinyar
awuein haihuwa ta biyu ta rasu batareda ta haihun ba.
Bayan rasuwarta da shekara bakwai shima malam din
yarasu sai yarinyar ta taso hannun aminiyata ladingo.
Kuma haj yarinyar shegen kyau ne da ita kamar jikar
aljanu ga gashi kamar ka ara kayi kitso dashi,sannan duk
kauyen nan ita kadai tayi karatu dan malam kafin yarasu
dakansa yake kaita yadaukota. Wata irin dariyar farin ciki
haj salamt tayi tace, Gaskia shiyasa nake yaba miki
jummai dan kin iya xaben kwarai Ta shekarar yarinyar
nawa?kuma yaya sunanta? Shekararta goma sha shida
kuma sunanta NAZLI. ******** Karfe uku a kauyen
takai tayi musu cikin gidan babah ladingo. Kudi masu
yawa kimanin dubu hamsin haj salamatu ta zubewa
ladingo agabanta tace, Wannan somin tabine na abani
yarinyar naje da ita nafara shiryata kafin sati saiku
samemu acan kano sai a daura auren acan suwuce da
ita. Idi ne yayi saurin waftar kudin yace, Ai dama ko
bakizo yau daukartaba mun shirya kaita gobe dan kawai
ayi auren mu musamu kudin shanawa. Buba yace, Nidai
kubani kasona na wannan daaka kawo natafi dan inada
gurin xuwa kafin akawo masu yawar. Ladingo kuwa
kwalawa nazli dake tsakar gidan tana jibgar wankin
ladingo hardana buba da idi kira tayi tana xuwa ta
durkusa kofar dakin cikin nutsuwa da sanyin murya
tace, Gani. Maza je kihada tsummanki birni xamu yanxu.
Rass gabanta ya buga dan tasan abunda suke niyar yi
mata na aura mata mai tabin hankali dantayi jinyarsa
akan kudi sbd taji firarsu lkcin datake fadawa su buba
jia. Kwana tayi tana kuka dan ta kara tabbatarda rashin
gatanta amma bazata bijire mataba dan kota bijire din
to ta tabbatarda korarta zasuyi a gidan data rasa gurin
zuwa gwara tabi umarninsu ko kashe tane marar lfyar
yayi ta huta da bakin ciki da azabar datake ciki. Amotar
haj salamatu sukazo har ladingo din dan tace itace uwar
amarya sai andaura aure zata koma. โšœโšœโšœโšœโšœโšœ Satinsu daya
a kano kuma ayaune ake daura auren bayan anyi komai
na neman aure a gun mijin haj salamatu dan shima
lashe money ne bare dayaji 'dan hamshakin mai kudin
nanne ALH ZAID OMAR. Duk wani abunda akeso takoya
haj salamatu ta tsaya takoya mata irinsu, Amfani da
abubuwan dake cikin toilet din gidan masu kudi, Da
hada shayi, Da gyaran guri da sauransu. Sannan sun siya
mata kaya dai dai misali shidinma dan dai kada haj
zeenah taganta da tsumman kayanta. NAZLI kyakkyawar
yarinyace fara tas me dogon gashi da dogon hanci
gatada manyan idanu da dan lips dinta jajaye. Duk da
tana cikin tsananin wahala hakan bai hana tsananin
kyawunta da nutsuwarta fitowaba. TAFARU TAKARE Karfe
goma sha daya alh zaid umar ya iso kano da tawagarsa
kai tsaye suka wuce babban masallacin jumaa dake kano
dan acan xaa daura auren na dansa tilo dayake
masifarso duk da dai angon bazai yiyu afito mutane
dashiba yana can abj yabarosa. Mijin haj salamatu alh
yaro shi ne uban amarya wakilinta. Guri yacika ya batse
da manyan mutanen nigeria harma da jajayen fata
jiniyoyine kawai ke tashi. Karfe 'daya daidai dubban
jamaa suka shaida daurin auren na TAMEER ZAID OMAR
DA NAZLI ADO TAKAI. Tanajin alh yaro yashigo gidan
yace andaura aure kuma ga jeep jeep nan guda goma
alh ya aiko akai masu kai amarya airport suwuce abj. Ido
ladingo ta zaro tace ita wllh ba inda zata asallameta
kudinta takomawarta gida taredasu buba dasuka dauri
auren. Dubu dari hj slmt tabata suka wuce bayan nazli ta
riketa tana sakin wani irin kuka maiban tausayi wanda
har akaro nafarko da ladingo taji tausayinta amma tana
duba gudin hannunta saita fincike tafice tana fadin,
ALLAH YASA YA 'DIRKO MIKI CIKI ACIKIN HAUKARSA.
Kuka take sosai mara sauti har suka isa aiport din itada
hj slmt da jummai da wasu aminan hj salamatun. Sam
tashin hankalun datake ciki baibarta taji tsoron jirginba
har suka isa abj wasu jibga jibgan motocin suka kuma
daukarsu. Wani hamshakin katon gida suka suka shiga
mai hawa uku. Haduwar gidan hartayi yawan fada ga
masu tsaro zagaye da gidan. A boys quaters aka saukesu
yan aikin gidan suka dingi kawo musu abinci danasha.
Ruwa kawai tasha ta tsaya kallonsu iya jummai sunata
kwasar gara. Suna gamawa aka aiko haj nason ganinsu
suka mike dukkaninsu suka bi bayan yar aikin. Ya salam.
Falon dasuka shiga haduwarsa sam ta baci abd uwar
dukiyar da aka narka acikinsa. Zaune take akan daya
daga cijin sofa din falon ta xuba ado tana baza kamshi.
Kallonsu tayi tace, Tunda kun gama abunda yakawoku ga
motanan yau komai dare xata kaiku kano. Mint dun
dubu daya ta mika musu tareda cewa su wuce idanda
wani abu xata kira hj slmt a waya. Mikewa sukayi jiki
asanyaye suna mamakin wulakanci irin na hj zeenat din
Sun kawo mata 'ya amma ba godi bare nagode saima
maidasu gida dazatayi adaren ko hutawa bazata bari
suyiba. Hj slmt ta kalli nazli tace, Kiyi hkr nazli allah
yabaki dauriya da hkr. Suna ficewa ta fashe dasabon
kuka dan ita gidan tsoro yake bata. Kallonta dakyau hj
zeenat tayi taga tayi yarinta amma aitunda andaura aure
ai xata iyane tayi gyaran murya tareda cewa, Kidaina
wannan kukan dan bautar aure xakiyi idan kuma ya
warke yasan yanda zaiyi da auren.amma dai yanxu
kitashi akaiki part dinsa.ma'ana hawan karshe can ne
part dinsa Hawa na biyu kuma namu nida dad dinsa
saina kasa gaba daya shine na baki da masu aiki. Tameer
baya iya mgn, Baisan kowaba sbd kwakwalwarsa ta juye
dan hk yanxu aikinki kulada cins,shansa,tsaftarsa da
komaima nasa. Nafeesa dauki akwatinta kikaita sama
part din tameer kafin gobe taxo tagaida dad dinsa dan a
goben xaikoma paris. Stairs suka haye har hawa na
karshe ta bude kofar falon dayafi na kasan tsaruwa da
haduwa tashiga har kofar dakin dayake cike takalli nazli
tace, Ni daganan xankoma kixo ki rufe muku falon dan
yana fitowa idan akabar kofar abude. Jikinta babu inda
baya rawa amma haka ta rufe kofar falon hwy nabin
fuskarta na tsoro da fargaba. Hakanan taji tanason ta
leka dakin taganshi taga ya yake. Ahankali gabanta na
faduwa ta tura kofar dakin ta leka. Wani dan saurayin
farin balarabe ta hango kwance a makeken gadon dakin
yana bacci hnkl kwance kamar me cikakkiyar lafiya... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰
mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• NA MAMUH GEEE โ˜†dedicated
toโ˜† Husna bbchoudiallo 10โ†’15 Saurin komawa tayi da
baya tayi tareda jan kofar jikinta na makyarkyata fitsari
na neman kufce mata tsabar tsoro Sannan hawaye suka
balle mata tayi saurin kuwa bakin kofar fita ta durkusa
tana kuka tareda toshe baki dan kada kukan yafito.
'Kiyayyar dasu babah ladingo kemun harta kai su aurawa
ajani ni dan wllh wannan ba mutum bane dan bantaba
ganin mutum mekyau irin hakaba sannan gashi fari sosai
yamafi 'dan megari dake birni karatu fari. Kuka takara
fashewa dashi rawar jikinta na tsananta. Jin karar bude
kofar datake tsugune ne yasa ta mike da sauri kamar
fitsari zai zubo mata fuska cike tab da hawaye. Wadda
takowota dakince tadawo daukeda tray din abinci da
magunguna takalleta taga yanda tayi shabe shabe da
kuka da zufa duk da splite air con dake palon kusan guda
uku batasan sanda tabushe da daria ba. Ganin dariyar
datakene yasa hankalin nazli yakara tashi takara barkewa
da kuka. Ganin dai da gaske take kukan ne yasa ta daina
dariyar ta aje tray din akan center table din palon takalli
nazli duk saitaji tabata tausayi sbd kasancewarta yarinya
amma sbd kwadayi iyayenta sun aurawa mai tabin
hankali ita. Yi shiru kidaina kuka ki fadi maiyasa kike
kuka. Jan numfashi tayi cikeda tsoro tace, Tsoronsa
nakeyi wlh bantaba ganin mutum mai kamarsaba. Wata
muguwar dariyace tazowa nafeesa amma saita gimtse
sbd kada ta kara tsoratata akan wanda take ciki. Kinga xo
xauna nafada miki komai akansa. Kasa xama tayi akan
royal kushins dake palon sata sulale ta zauna akasa tana
cigaba da shararar hawaye. Itama nafisar akasa tazauna
dan dama basa hawa kujerun gidan sbd zamansu yan
aiki kuma hakan umarnin hajiyar gidanne wato haj
zeenat. Yaya sunanki? Cikin muryar tausayi tace nazli. To
nazli zan fada miki komai gameda tameer dan yanda
zakiji saukin fara dawainiyarsa. Na farko abunda zan
fada miki shine Baya tashi bacci kullum sai karfe goma
sbd allurar da dr yake zuwa kullum dare yana masa sbd
yasamu yayi bacci dan idan bada alluraba baya bacci.
Abu nabiyu kuwa shine daya tashi zaki kama hannunsa
kikai toilet kiyi masa brush kafin nan nikuma nakowo
masa abincinsa saiki bashi kibashi magani daga nan sai
masu yi masa wanka zasuzo suyi masa sai sauran aikin sa
masa kaya nakine. Atakaice dai sallarsa da cinsa da duk
wani abun bukatarsa yana kanki. Sannan babban abun
shine ba'a barinsa shikadai adaki ko afalo ko a inama sbd
tabin hankalin nasa mugun tsoro yasakar masa.
Kidainajin tsoronsa dan mutumne kamarki. Abunda yasa
kika ganshi haka mahaifiyarsace yar kasar larabawa Dan
haka ki kiyaye duk abinda kikaga baki saniba idan nashigi
kawo abincinku kya sanar dani dan haj bataso yan aiki
na hawowa sama saini kadai nima idan ba abinci xan
kawoba bana hawowa. Mikewa tayi da sauri ta fice sbd
kada haj tafara kiranta bata kusa. Wani irin wawan
tagumi ta rabka tana juya bayanin nafisa a xuciyarta
kafin tamike ta nufi dakin dan kara lekawa taga
balaraben. โšœโšœโšœโšœโšœโšœ Ahankali yabude dara daran
idanuwansa jin babu motsin akwai mutum adakin yasa
yayi saurin xabura ya mike tsaye a tsakiyar gadon yana
raba idanu. Motsin shigowa dakin yaji aiko tsoronsa ya
tsananta ya diro daga gadon da sauri yayi bayan kofar ya
labe tareda saurin ciro durowar madubi ya lafe bayan
kofar. Ahankali kamar barauniya ta turo kofar tareda
turo kanta aiko batayi auneba taji saukar abu kamar an
kwada mata guduma ta dago idanuwanta dasuka fara
ruwa ta dorasu akansa kafin ta sulale ta zube asume... ๐ŸŒ•๐ŸŒ•๐Ÿ‘‰
mamuh geee ๐ŸŒ•โšœDAIMAN daga www.hausaebooks.com.ngโšœ๐ŸŒ• Na MAMUH GEEE โ˜†in
dedication toโ˜† Husna bbchoudiallo 16โ†’20 Ahankali
suke saukowa daga stairs din hannuwansa makale da
nata. Gabantane ya fadi da karfi nan jikinta yafara rawa
badan komaiba sai dan haj xeenat data gani hakimce a
falon tana aiko musu da kallon, Tsana,haushi dakuma
mamaki dan idanda abundata tsana arayuwarta to
tameer ne sbd son da mahaifinsa ke masa yasa takasa
samun yanda takeso da tarin dukiyar ta alhajin. Shima
tameer na ganinta yayi saurin lafewa abayan nazli yana
kara kankameta. Cikeda izza tana yamutsa fuska tace,
Kifadamun ubanda yasaki sauko da wannan dan iskan
mahaukacin nan inda nake baki. Aminanta dasuke tare
azaune palon ne suka bushe da daria 'dayar nacewa, Wlh
komai yafaru laifin kine zeenat dan babu yanda bamuyi
dakeba akan kisan yanda kikayi aka turashi gidan
mahaukata ki huta gaba daya amma kinki. Cikin haushi
tace, Aike badan matsiyatan kudin danake tatsa a gurin
ubansaba idan yana nan din da tuni na gargadasa gaba
sa gidan mahaukata. Maida kallonta tayi kan nazli datayi
wuki wuki tana sauraran makircinsu. Tace, Wuce
munafuka matsiyaciya kuma wllh kinkusa barin
gidannan dan naga alamar mahaukacinnan yafara
sakewa dake nikuma ko acijin...


Read / Download DA IMAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album