Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

BIBIYAT YAKE YI Complete Hausa Novel Document by BIBIYAT YAKE YI


BIBIYAT YAKE YI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22843



BIBIYAT YAKE YI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 14, Jun 2024

Author: Zainab Bawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08161146563

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 132.76 kb

File Type: txt

Views: 774+

Download: 567+

Last download: 4 days ago

Description/Story: *PAID BOOK 300*

*BIBIYATA YAKEYI*
_(WAYE SHI?)_


*بسم الله الرحمن الرحيم*


ZAYNAB BAWA

Marubuciyar
*BIBIYATA AKEYI*
*Y'AR FARI*
*YARIMA FAYAD* paid 200
*ƘADDARAR RAYUWA*

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

INA MASOYANA WANDA SUKA KARANTA LITTAFIN BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!

TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).

WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!

BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝




*Allah yabani ikon rubuta muku abu mai amfani kamar yanda nafarashi Lafiya Allah yasa nagamashi lafiya.*


Page 1

Jin alamun za'a shigo ɗakin ya sanya nayi saurin ɗauke idanuwana daga kan madaidaiciyar tv ɗin dake manne ajikin bango nayi saurin maida hankalina ga littafin dake gabana. Da sallama ta buɗe labulan ɗakin ta shigo ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da suke cikin falon. Matashiyar matace wacce bazata wuce shekara talatin da takwas ba. Kallona tai ta taɓe baki ta zare remote tana faɗin.

"Nida ɗakina amma ban isa abarmin tashar dana keson kalla ba kulllum sai dai wannan tashar kwallon ta jaraba, ke kina mace ni bansan mai ya hadaki da wannan kallan kwallon azabar ba."

Nidai bance komai ba harta canja tashar ta maida zuwa tashar shirye-shiryen Hausa sannan ta ajiye remote din. Mikewa nayi ina zumburo baki nafice daga ɗakin ina jiyota tana faɗin.

"Dama nasani wannan karatun na munafunci ne kallon ball kawai kike yi."

Nidai bance komai ba na wuce zuwa ɗakin matar mahaifina wacce muke kira da Aunty na zauna na cigaba da kallon ball ɗina acan. Sai da aka gama sannan raina yayi sanyi domin tawagar da nake so itace ta lashe wasan kwallon. Raina fess na fito na nufi ɗakin mahaifiyata. A uwar daki na sameta na shiga na zauna tana faɗin.

"Angama kallon ball din kenan?" Batareda ta jira amsata ba ta cigaba da fadin. "To sai amaida hankali maza ayi karatu tunda angama ibadar." Zumburo bakina nayi nace.

"Nifa dama Mama na rigada nagama karatu, kawai bita nake yi."

"Gara dai ki maida hankali kiyiwa kanki faɗa Mamee kitsaya kiyi wannan karatu dakyau ke kanki shaida ce kinga yanda aka samu kika fara wannan karatu, har indai kikaki nutsuwa kici wannan jarabawar kika fadi kinsan yanda mahaifinku zai ji. Idan kuma so kike ki karasashi toh, kina gani dai da ya ya aka yi aka hado har dubu casa'in aka biya miki rijista dan kawai kin nuna kina so, idan kika zuba masa kasa a ido baki yiwa kanki adalci ba. Ki daure kiyi karatu kici weeding ɗin nan in sha Allahu har indai kin wuce zamu san yanda zamuyi mu hada karfi da karfe wajan ganin mun taimaka kinci gaba. Idan kuma kika tsaya wasa kika fadi ko shakka babu nasan cewa aure babanku zai yi miki da karancin shekarunki dan ya samawa kansa saukin rayuwa. Amma idan kinci wannan jarabawar koda ace auren ya yi miki sai mijinki ya karasa daukan nauyin karatun naki ki karasa agidansa." Saurin girgiza kai nayi nace.

"Dan Allah Mama ki daina fadin haka, zanyi karatu kuma in sha Allahu zanci." Sai da ta kalleni na wani lokaci sannan tace.

"Shikenan Allah yasa." Nace,

"Amin." Saboda yanda nakeso naci jarabawar nan haka na hana idanuwana runtsawa sai da na raba dare sannan na kwanta.

Washe gari kuwa kafin kowa ya tashi na tashi kusan kaff gidan na rigasu tashi ina jiyo mahaifinmu zai fita sallar asubahi yana bubbuga kowa ne ɗaki domin atashi ayi sallah. Ina idar da sallah na shiga wanka na shirya ban tsaya karyawa ba dan karfe bakwai zan shiga jarabawa mama tabani kudin abun hawa nafito harabar gidan babu kowa haka naabude karamar kofar dake jikin gate dinmu na sanya kaina nafice yar, dakyar nasamu abun hawa nashiga yawuce dani makarata zuwa 12:00pm nagama duk wani abunda zanyi a makaaranta na nufo gida dan ban fita ta ishesshen kudin da zai isheni nayi karin kumallo ba kuma yunwa nakeji shiyasa ina gama abunda zanyi na nemo hanyar gida dukda kasancewar bawai dama ina tsayawar bane,

Da sallama na shiga gidan a tsakar gida na samu Mamana da Anty suna gyaran shinkafa sannu nayi musu sannan nawuce ciki na cire kayan jikina na sanya kayan gida sannan na nemi abunda zanci, sai da na tabbatar cikina ya ɗauka sannann na fito izuwa cikin gida na zauna na sanya hannuna a cikin gyaran shinkafar ina yi ina kallon agogon wayar Mama domin kar lokacin da za'a fara wasan kwallon ya yi bana kusa. Da sauri na mike ganin baifi saura minti 2 biyu afara wasan ba Mama tana magana ko jiyota banayi har nakai daki na canja tasha na zauna kallon kwallon.

Ko kawarda idanuwa na bana yi dan bana so wani abun ya wuce ni ba tare da na gani ba duk da kasancewar yau ba team din da nake supporting bane suke buga wasan, Daya daga cikin dan wasan kwallon ya zura kwallo araga wani irin ihu nasaki daya sanya mama ta mike ta shigo ɗakin ina kallonta na bata fuska dan nasan saita hanani kallon kwallon nan. Aikuwa hakan aka yi domin masifa ta fara yi min tana faɗin.

"Sai yaushe zakiyi hankali Mami? Kin gwammaci kibar iyayenki suna aiki kizo ki zauna kallon banza? Kina ihu kamar tababbiya? Toh wallahi gara ki mike tun kafin mahaifinki ya leko yaga muna zaune muna aiki ke kuma kinanan kina kallo kin san ranki da namu gabaki daya baci zai yi." Na karairaye murya nace.

"Wallahi Mama nagaji kinga yanzu na dawo daga makarantar nan kuma zuwa jimawa karatu zan shiga dan Allah kiyi hakuri na zauna na ɗan huta." Mama tace.

"Har mai kikayi da zaki gaji? Ki tashi tun kafin ran mu duka ya ɓaci."

Mikewa nayi raina bai so ba na koma cikin gida mukaci gaba da gyaran shinkafar, muna gamawa na karɓa na shige kitchen na zuba ta a cikin tukunyar dake kam murhu wacce tun ɗazu take tafasa. Haka a tsaitsaye na taya su muka karasa aikin hankalina yana wani waje daban. Muna zaune mu dukkan mu a cikin gidan mahaifina ya shigo cikin girmamawa dukansu matan suka yi masa sannu da zuwa, ni kuma na gaisheshi dake yau fitar sassafe nayi bamu gaisa ba. Ya amsa cike da kulawa yana faɗin.

"Ya ya jarabawar?" Nace.

"Alhamdulillah da zarar munyi gobe mun gama." Yace.

"Toh Allah ya bada sa'a, amma da zarar kin gama taya su aikin saiki tashi kije kici gaba da karatun koh kar ayi wasa."

"Insha Allahu bazan yi ba Baba."

"Toh shikenan Allah yayi miki albarka." Mu dukkan mu muka amsa, yana gama magana yayi sashinsa Aunty dake itace da girki ta tashi ta bishi,

Muna zaune ƙananun ƙannena suka dawo daga makaranta. Mama tace na tashi na taimaka musu su canja uniform izuwa kayan gida. Nan na samu hanyar barin wajan da sauri na mike na shige ɗakin Aunty na fara taimakawa yaranta suka shirya. Gabaki daya yaranta guda uku ne babbar ba tafi shekaru takwas ba Meema sai twins Hassan da Hussain. Ni kuma a wajan mahaifiyata ina da ƙannena guda biyu dukkan su maza ne, Sadeeq sai Amir. Sai da na fara shirya su Meema sannan na fito daga ɗakin Aunty na shirya su Amir. Ban yarda na koma cikin gidan ba dan na san wani aikin zan riske dan haka na zauna karatuna. Koda akayi la'asar ban damu da saina tashi ba tunda nasan cewa ba sallah zanyi ba.

Washe gari kamar jiya da sassafe na fice daga gida dan zuwa zana jarabawata ta karshe. Alhamdulillah babu laifi jarabawar tayi daɗi sosai ina gamata na sanya kai na dawo gida ba tare da na tsaya wani abun ba.

Yau kam na tsaya na taya su aiki sosai dake na san ba jarabawa gareni washe gari ba kuma aranar babu wata kwallon da za'a buga. Yau kam na huta da fadan Mama dan sam ba tayi min shi ba, koda yake dama takance duk ranar da babu wasan kwallon kafa nafi kowa hazaka wajan aiki a gabaki ɗaya kaff gidan mu.

Yau ta kasance ranar Asabar tun safe na shirya kannena na sakasu a gaba muka tafi islamiyya, da safe ake zuwa duk ranar sati ba zamu dawo ba sai yamma. A kafa muke tafiya dake bawani nisa ne tsakanin haddar tamu da gidan mu ba, sai da na tabbatar kowannen su ya shiga aji kamar yanda na saba sannan nima na wuce nawa ajin.

Karfe sha biyu Aunty da kanta ta kawo mana abinci kamar yanda ta saba, bayan an fito sallah na haɗe kannena dukkan
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download BIBIYAT YAKE YI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album