Join Our WhatsApp Group

INAYAH Complete Hausa Novel Document by INAYAH


INAYAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 59408INAYAH

Reading Time: 4 Hours

Added On: 09, Apr 2023

Author: Mamuh Gee ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa Biyar

Author Phone : 07040727902, 09134848107

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 351.11 kb

File Type: txt

Views: 5662+

Download: 2185+

Last download: 3 days ago

Description/Story: *_INAYAH_*

_(Riba Biyu)__Mamuhgee_1

_*please masu daukamun Sunayen books da Labarai suna sauyawa suyi nasu lamarin ina ganinku dan Allah ku daina ba kyau, kuma masu copying nagani allah ya kyauta ngd duk cikin Qaunace allah yaqaro kauna🥰*_

_BismillahirRahmanirRaheem_

Tasowa tayi ahankali tana takowa zuwa tsakar gidansu datake jiyo maganar mahaifiyarta da yayyunta maza tareda kishiyar mahaifiyartata suna magana duk a jujjuye sbd hankalinsa daya tashi lokaci daya cikin mummanan yanayi da tashin hankalin mugun labarin dayazo musu yanzu yanzun.Ita kanta hankalinta baa kwance yakeba dama can sbd halinda take ciki na jinyar mijinta dake kwance asibiti Yana jinyar accident dasukai kwana biyu dasuka wuce a hanyarsa ta dawowa daga gurin daurin auren qaninsa dasuke uwa daya uba daya,Kaman a fizge kunnuwanta suka jiyo mata abinda babban yayanta Umar ke fada saidai Sam takasa fahimtar abinda yafada din zahirance Dan haka tana buqatan jinsa da kyau,Ta qaraso jikin kofar ta yaye labule ta fito tana kallonsu daya bayan daya fararen idanuwanta dasuka jima da shigewa ciki ciki sbd damuwar datake ciki kwanakin,Suma ita suke kallo Kaman yanda take binsu da kallo kowannensu fuskarsa cike dauke da alhini dakuma tausayinta Dan kuwa Rashin miji a irin shekarunta abin tausayi

Ga Kuma 'da da ciki dake jikinta.Kallon mahaifiyarta tayi taga yanda tayi qasa da Kai cikin yanayi na hawayen dasuke Neman saukar mata takasa kallon Yar TataDan haka ta kalli kishiyar mahaifiyarta kai tsaye tace"Inna Menene duk kukai wani iri haka?

Lafiya kuwa?

Wani abin yakuma faruwa ne?Maida kallonta tayi kan yayyunta dake tsaye suna kallonta tace"Yaya Umar,Yaya kabiru?

Lafiya duk kukai shiru haka?

Jikin Abban Abdul ya tashi ne?Ajiyar zuciya Yaya kabirun ya sauke tareda gyara tsayuwarsa ya kalleta da Dan alhininsa irin na maza masu taurin zuciya Kai tsaye yace"Khadija bayan barowarki asibiti yanzu Allah yayiwa Salisu cikawa........Bai qarasa ba ta waiwayo gefensa tana kallonsa cikeda zallan mamaki da faduwar gaba muryarta na gwamutsuwa tace"Yanzu fa na Barosa Yana barci,

Wanka fa kawai zanyi nakoma asibitin shine zaace ya rasu????

Yanzu yanzu fa?Da sauri innar ta riqota cikin tausayawa tace"Hadiza karkiyiwa ubangijin haka,

Tawakkali zakiyi tunda kinsan dai baa wasan mutuwa...Idonta na sauya zuwa ja da hawayen dake kokarin cikowa saidai taurin zuciyarta ya hanasu fitowa

ta katse innar da cewa"Inna bacci nabarosa yanayi fa,

Yaji sauki sosai yau,

Rasuwa fa akace,

Mutuwa fa kenan, ya tafi ba dawowa har abada,

Ta Yaya zanyi.......Cikin Dan daga murya Yaya kabirun yace"Ke Khadija Menene hakan?

Rasuwa fa akace Miki salisun yayi,

Ki nutsu ki fahimci ita rasuwa babu ruwanta da yanzu yanzun dakike fada,

Kiyi gaggawar bude hankalinki ki fahimci abinda yafaru dake,

Salisu ya rasu bazai taba tashiba......Bakinsa take kalla kanta na juyawa

Zuciyarta na harbawa da mugun qarfi Kaman zata faso kirjinta,Mamarta ta kalla idanuwanta na qafewa taga alamar gskiyar zancensa akan fuskan mamar,Ta waiwaya ta kalli Yaya kabiru Shima hakan tagani.Wani busasshen yawu ta hadiye wanda har yankan maqoshinta yake

Ta juya kai tsaye Takoma dakin mama ta dauki doguwar hijabinta data cire bayan shigowarta gidan ta zira ko waya da kudin adaidaita Bata daukaba ta fito ta zira slippers din mamarta daya Da nata takalmun daya batareda ta luraba ta nufi kofa tana jefa ka kawai dan bata cikin hayyacin kallon gaban nata

asibitin take buqatan isa kawai.Inna ce tayi saurin janyo nata hijabin tabi bayanta tana Kiran sunanta,Mamarta kuwa kallon Yaya Umar tayi tana cewa"Bisu kabasu kudin adaidata ban Saka ran kowannensu ya daukaba.Juyawa yayi ya bisu

A titi yayi saurin taddasu ya ciro 1000 ya miqawa Inna Yana cewa"Ga kudin adaidata Inna

Ki lura da ita Inna kartaje asibiti tayita wainnan maganganun

Tawakkali akeyi kifada mata Inna.Da sauri innar ta qarasa gurin hadizar daketa zuba sauri tana tafiya ta riqota ta riqe hannunta gam tana kokarin Kiran sunanta saiga adaidata gabansu ba Bata lokaci suka fada ciki

innarce tafada masa asibitin da zasu

Khadijan kuwa Banda rawa babu abinda qafafunta da hannuwanta keyi.Isarsu asibitin ko Gama tsayuwa baiyiba Khadija ta sauka tareda wucewa da sauri ta nufi hanyar Emergency ward da har lokacin Salisu anan yake.,Tun daga nesa Yan uwan Salisu din maza da mata suka hangota tana tahowa a gigice ko ganin gabanta batayi

Hankalinsu yakuma tashi da tsananin tausayinta dan haka da yawansu suka qara fashewa da sabon kukan Rashin Dan uwansu.Tana qarasowa da kallo tabisu daya baya daya taga yanda mahaifiyar salisun ke rusa kuka take taji Rabin jikinta na neman mutuwa ta qarasa dakin tashige da gudu ta nufi gadonsa da gawarsa kawai ta tadda a rufe da zanin gadon data zo masa dashi yau da safen.Tsawonsa ta kalla tareda hannuwansa da aka miqar,Kasa gasgatawa tayi Saida takai hannu ta yaye zanin tayi arba da kyakkawar fuskarsa ta asalin fulanin Yola....Mummanan bugawa zuciyarta tayi ba tsammani idonta yarufe tana kokarin zubewa Inna tayi saurin tarota tana Kiran sunanta Amma Sam batajinta sai neman somewa takeyi.Da sauri hajiyarsu salisun ta qaraso tana cewa"Ku koma gida da ita karta shiga wani Mummanan halin ga juna biyu a jikinta.Qwacewa takeson yi Dan Bata tunanin zata bar gawar salisun ta tafi koina Amma batada qarfin motsawa bare magana Dan bakinta take ya manne Kaman an Saka mata glue.Tana kallon gawar mijinta Salisu aka jata aka fice da ita har waje aka kuma sakata napep tareda Inna da qanwar salisun suka nufi can gidan iyayen salisun.Suna isa ko tsakar gidan Bata qarasa shigaba ta yanke jiki ta fadi jini nabin qafafunta.Hankali tashe sukai kanta tareda ciccibarta zuwa dakin hajiyarsu salisun Inna na Kiran sunanta hankali tashe.Jini sosai take zubarwa Wanda ya tabbar musu da cikin zubewa ne yayi babu tantama Dan haka basuyi wani yunqurin maidata asibiti ba haka Inna da dattijuwar gidan qanwar mahaifinsu suka taimaka mata gurin ganin jinin yagama zuba ta Dan gyara.Kururuwar koke koken da gidan ya dauka ne ya tabbatar musu da isowar gawar Salisu gida

Tana jin hakan ta rintse idonta cikin tsananin azaba sauran abin dake cikin nata ya qarasa zubowa sai alokacin wani irin gunjin kuka Mai tafe da radadin zuciya ya kufce mata.Inna dake kanta ta qara matsowa tana dafata cikin tausayawa jin irin girman kukan datake,Kuka takeyi sosai zuciyarta na radadin Rashin mijinta uban 'danta dakuma wannan cikin daya qwallafa ransa akansa,

Ashe tareda cikin zasu bar duniya Rana daya shiyasa Allah ya saka masa tsananin kaunar cikin abokin tafiyarsa ne kenan.Bata damu da yanayin datake ciki ba

Haka ta dafa ta miqe tsaye tareda qarasawa tsakiyar bayin dakin hajiyar ta wanke jikinta daqyar sbd tsananin rawar da hannuwanta da qafafunta keyi.Fitowa tayi Kai tsaye ta karba zanin da inna ke miqo mata ta daura wani irin tsananin jiri da ciwon mara Mai tsananin gaske Yana nukurkusarta Amma taqi yarda tazauna Kai tsaye ta fito tsakar gidan sanyeda hijabinta tanajin yanda tako ina gidan ke amsa amon kukan Yan uwan Salisu.Gawarsa dake shimfide a dakin da zaai masa wanka ta nufa ta zube gabansa tafara rero wani irin gunjin kuka tana Kiran sunansa.Duk yanda akaso janyeta kasawa akai sbd kuka takeyi sosai zuciyarta na tsananin qunar Rashin mijinta datake tsananin so da kauna yau gashi ya tafi yabarta cikin duniyar da kowa babu abinda yasani sai kansa,Ina zata da 'danta Abdul Wanda tasan babu Wanda zai daki kirji a cikin danginta Kona salisun ya tallafi rayuwarsu.Lokacinda za ai masa wanka da sirita aka samu aka janyeta daga dakin musamman da itama wani irin gagarumin zazzabi ya rufeta lokaci daya dakuma sabon jinin daya Kuma balle mata sai alokacinma kowa ya San da Bari tayi.Baa kaita asibiti ba a dakinta dake gidan aka kwantar da ita kasancewar a gidan suke zaune tareda iyayen salisun tunda dagasu har iyayen ba masu hali ban Dan hakan nema sukeda daki daya tal da Dan qaramin palo da bandaki acikin palon,

Tana daki ana fama da ita har aka tafi da gawar makwancinsa,Iya fatu aka kirawo makociyarsu Mai karban haihuwa ita tazo ta duba hadizan ta tabbar musu da cikin yagama zubewa

Nan aka shiga wani jimamin aka fara kulawa da hadizan.Sbd yanayin jikinta dakuma zaman gaisuwar da ake gidan yasa dole Inna ta zauna tareda ita tadawo da kwana gidan tunda maman hadizan bazatazo ta zauna ba.Sosai take fama da jinyar kanta bayan kwana biyu da rasuwar sbd takasa daina kukan mutuwar Salisu,Salisu mijine ma gari Kuma uba nagari hakama 'da na gari gun iyayensa.Cikin kwana biyu duk tabi ta yamutse da tsananin damuwa dakuma ciwo dake damunta na tsananin ciwon mara na barin datai.Angama zaman gaisuwar har anyi sati biyu babu wani Abu daya sauya daga gareta saima sabon ciwon damuwa daya kamata Sam takasa fita daga halin damuwar Rashin mijinta,Inna na tareda ita har lokacin Kuma dai ita zata zauna da itan har tsawon watannin dazata Gama takabarta kafin sukoma gida tare.Abdul Yana gurin mama dama tun tana zaman jinyar abbansa asibitin kafin rasuwar tasa Dan haka kullum a daki suke wuni daga ita sai Inna,Abincinta Wanda yake kicin dinsu tun Wanda salisun ya siya shi Inna ke dafa musu yana qarewa babu Wanda yakawo musu wani saidai aka ringa Basu daga cikin gidan Idan an dafa,Wanda ake basun baya wani isarsu itada innar dan haka so da yawa innar Idan taci na safe yafe mata na ranar take ita taci,Itakuma Idan anbasu na daren saitace ta koshi saita barwa innar taci.Tun daga Nan yanayin yafara kulle musu

Da innar dai taga daga ita har hadizan sunfara dogayen wuyan yunwa Kamar Yan gudun hijira dole taje gida ta sanarwa mamar hadizan sukai shawara akaiwa Umar da kabiru magana akan su taimakawa hadizan da abinci

shine suka Dan fara taimakawar duk bayan kwana biyu suna Bata dubu daddaya ko dari Biyar Biyar.Tun suna Bata tana samun na siyan abinci da Kamar su sabulun wanki hardai Suma ana Jan lokaci suka daina sbd Suma da nauyin nasu iyalan akansu dan haka suka koma Yar gidan jiya.Watan salisun uku da satittika da rasuwa gabaki daya rayuwarta ta juya mata upside down sbd hajiyarsa itama ta kanta takeyi Dan dama shine kawai Mai tausayi da tallafa mata acikin yayanta shiyasa itama bazata iya daukan nauyin hadizarba Dan haka kowa tasa ta fisshesa akeyi a gidan.Hadizar ta rame ta hargitse ta sauya kamanni sosai bayan dogon wuya da dogon hanci sai ido dasuka fito kaman me Neman allura a duhu haka Takoma dama ita Inna sun saba da talaucinsu Dan haka masifar quncin Rashin ba wani damunta tayiba Kaman dai yanda tausayin rayuwar hadizan tafi damunta sbd tasan wani sabon gararin ne zata tadda gida koda tagama zaman takabar sunkoma.Ta bangare daya tunda tayi barin cikinta lokacin rasuwar Salisu har yanzu takasa ganewa lafiyaarta sbd ciwon mararta yi yakeyi Yana tasan mata,

Wani lokacin idan yatasar mata Kaman zata rasa ranta haka take fama dashi Amma Bata taba zuwa asibiti ba Dan babu hali,Ko innar dasuke tare Bata sanarwaba Dan karta daga mata hankali bayan daga ita har mamarta tada hankali kawai zasuyi basuda wata mafitar.Cikin wani irin tsanani da matsuwar Rashi da tarin damuwa tagama zaman takabarta suka fara Shirin tattarawarta komawarta gidansu.Hajiyar Salisu tayi sabon kukan mutuwarsa lokacinda hadizan zata tafi,

Tanajin inama tanada halin cigaba da kulawa da matar salisunta da 'dansa data riqesu

Amma batada Wannan halin,

Ko Abdul dinma tana tsananin kaunarsa saidai bazata iya riqonsaba shiyasa batamayi maganar karbarsaba,

Da mahaifinsu salisun Shima Yana raye tasan bazai taba barin hadiza da Abdul din su tafi ba.Ita kanta hadizan ta San cewa Rashin halin ne yasa hajiyar batai yunkurin cewa a bar mata abdul ba Dan tunda salisun ya rasu itama yanzu abincinta neman gagarta yake

Gwara tabarwa hadizar 'danta tasan duk tsanani zata nema ta kula dashi.

##MAMUH#

#ZAFAFABIYAR#

_ZAFAFA BIYAR_*_INAYAH_*

_MamuhGee_*_GURBIN IDO_*

_Safiya Huguma_*_SANADIN LABARINA_*

_Hafsat Rano_*_FARHATAL QALB_*

_(Miss Xoxo)_*_BABU SO_*

_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_

*_Littafi biyu 400_*

*_Littafi uku 500_*

*_Littafi hudu 700_*

*_Littafi biyar 1k_*

_BREAKDOWN OF ZAFAFA BIYAR VVIP SINGLE PAID BOOK__4 BOOKS 4500_

_3 BOOKS : 3500_

_2 BOOKS : 2500_

_1 BOOK: 1500_

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾ZENITH BANK

HAFSAT UMAR KABIR

2270637070SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:

07040727902[10/15, 3:51 PM] Mariyamah: *_INAYAH_*
_Mamuhgee_
*_Arewabooks@Mamuhgee_*


2
Dawowarta gidansu dole dakin Inna ta tare tareda innar tunda babu wani extra daki dazata zauna a gidan bayan  nan,

Duka duka dakuna biyu ne gidan sai bandaki dake tsakar gida,
Daki daya na mama daya na innar,

Ko acan dah da mahaifinsu na raye zagayen dakuna yake,
Ita Kuma Idan Yana kwana dakin mama saita kwana a dakin Inna,

Idan a dakin Inna zai kwana saita kwana a dakin mama
Ahaka ta girma harya rasu itama akai mata aure.

Dawowarta gida wata sabuwar rayuwar zullumin kullum tashiga acikinta,

Daga Inna har mama babu Mai wata qwaqwarar sana'a,
Mamace ke Saida lallen hausa
Inna Kuma tana saida su kanwa da borkono
To tundama ta tafi taya hadizan zaman takaba sana'ar ta tafi sbd jarin ba wani Mai yawa bane dakuma hardashi suka hada duk suka cinye a can gurin zaman tunda sun shiga tsanani,
Dan haka sana'ar innace kawai yanzu take Dan taimakawa ta wani bangaren Amma kam suna cikin gararin yanayi sbd Suma dama can salisun ne yake dauke da nauyin nasu tunda nasu yayan basa taimakonsu kansu da matayensu da yayansu kawai suka sani.

Ita Inna Bata taba haihuwaba shiyasa tun take riqon hadiza tun tana yarinya gashi Kuma hadizar ce kawai mace acikin yayan mama dukansu mazane su uku,
Malam Nafi'u Wanda Allah yayi rasuwa watannin baya,
Sai Kabiru da Umar dasu kuma ayanzu kownanensu yakeda mata daddaya da yara kusan Biyar biyar,

Sai ita autarsu Khadija wadda Rashin tsayayyan manemi yasa batai auren wuriba sai data dan girma a gida sosai takai kusan shekara ashirin da takwas  kafin tasamu salisunta dasuke tsananin so da kaunar juna sukai aure ya dauke nauyin tallafawa su Inna daidai gwargwadonsa.

Daga Yaya Umar har Yaya kabiru babu Wanda  ya dauke lalaurar kula dasu mama,
Saidai idan an kwana biyu su samu Kamar dubu daddaya su Basu ko 500 Wanda sukam suke ganin kokarinsu a hakan suyita saka musu albarka duk da innar tasan basa kyautawa suna kallo Salisu ke ciyar dasu bayan Shima ba wani karfin yake dashiba kawai zuciyar alkhairi yafisu.

Yya Kabiru koyarwa yakeyi a secondary school din gwamnati dake kusa da anguwar dayake da iyalinsa
Kusan shekara goma kenan Yana aikin koyarwar Amma babu wani cigaba kullum Yana Nan a yanda yake.

Yaya Umar kuwa sanaa kowacce yi yakeyi baida tsayayya guda daya Amma dai yafi yin ta dillancin harkar Saida filaye da gidaje Dan Yana samu sosai acikinta shiyasa yafi yya Kabiru rufin asiri,
Qarshema dai fadawa yayi siyasa sbd uban gidansa dayasashi fitowa Dan samun kudin jam'iyyar da zasu fito ta karkashinta tunda sunsan dai ba ci zasuyiba Amma sunsan jam'iyyar zata Basu kudi sosai Dan haka gadan gadan yafada siyasa baji ba gani,

Yaya kabiru daya fahimci akwai samu sosai a harkar take ya marawa Umar din Baya Dan Shima ya samma masa Idan ta 'bulle.

Itakam hadiza ganin zaman baida wata mafita
Ga Abdul ya isa sakawa makaranta tuni
Sbd abbansa koda ya rasu yanada burin sakasa makaranta alokacin,

Yanzu komai ya juye musu Kuma tanada burin bawa Abdul din ilimi Dan ya anfana rayuwarsa,

Gasu Inna da mama kullum cikin dubaru ake
Yau aci kwadon kwaki,
Gobe aci kwadon qanzo,

sai ankwana hudu ko Biyar Daqyar ake hada cinikin da...


Read / Download INAYAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

3 Comments On INAYAH
avatar
amira-3-1

9 months ago

Reply

Mashallah

avatar
rilwan

8 months ago

Reply

Masha Allah

avatar
zainab-aliyu-rabiu-dal

3 months ago

Reply

mashaAllah

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album