Join Our WhatsApp Group

ILLAR AUREN DOLE Complete Hausa Novel Document by ILLAR AUREN DOLE


ILLAR AUREN DOLE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 31239



ILLAR AUREN DOLE

Reading Time: 2 Hours

Added On: 03, Jan 2024

Author: Aisha A Yabo Fulani ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM

Author Phone : 08032176520

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 177.33 kb

File Type: txt

Views: 533+

Download: 143+

Last download: 2 days ago

Description/Story: ο»Ώ[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani,*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

*MANUFARMU ANNABINMU*

*YA RASULILLAHI MANUFARMU KAI A FARKO MANUFARMU KAI A QARSHEN MUNA NEMAN TAIMAKON KA DAN MUTUN CIN NANA FAD'IMA*

*barka da JUMA'ATU BABBAR RANA*


_sadaukarwa ga duk macen da ta tsinci kanta arayuwa ta AUREN DOLE, Allah ya Baku hak'uri da jureyar wannan babbar jarabawar_

*Kira ga iyayanmu, dakuji tsoron Allah ku kuma tausaywa yaranku da Allah ya bamu amanarsu, ku daina tilasta yaranku auren wanda basa so, aure anayin sa ne dan durewar sa har abada, amma ba agina rayuwar aure kan soyayya ba, taya zai d'ure, bak'in cikine zallah aciki, wannan auren zai iya sauya ma tarbiyar yarinya, agyara dab Allah iyaye*πŸ™πŸ»πŸ˜­


*1*

Wata 'yar matashiyar budurwa ce ta k'arasu wajan wata yarinya da za suyi sa'annin juna, tace

"Bistey tun d'azun fa ina can ina yawun nemanki ashe kina nan"

ta fad'a dai dai sanda take zaunawa kan kujeran ruban da aka k'awata wajan cin abincin,

wace aka kira da bistey ta d'ago fuskarta daga duban littafin da ke gabanta, da alama nazari take yi,

cikin murmushi tace "ayya yi hak'uri bistey da zan zo nan malam Hashem ys aiki ki shiyasa nazo nan, amma ai nace Nabila tukur ta fad'a maki"

"ok bamu had'u ba, kinga nifa yunwa nake ji"

ta fad'a tana shafa cikinta cikin ya mutsa fuska,

"Kai bistey idan dai ciki ne sam ba kya wasa da shi, mi zamu ci"?

"ah kema dai kin san bana wuci donot da cok"

"ok ni kam limo kawai zan sha, nan suka kira d'ai daga cikin ma'aikatan wajan suka fad'a mata abunda za akawu.

suna gamawa suka koma aji ganin lokacin komawa yayi, biyu aka tashe su, 'yar b'urb'ura suka shiga kasan cewa ugnuwarsu d'aya.

suna zowa ko wace ta yi hanya layinsu akan sai kuma da yamma idan an had'u islamiya,

tana shiga gidan nasu kai tsaye d'akin mamansu ta shiga fad'awa kan kujera tayi tana fad'in "wash!"

Mama da idar da sallahn ta kenan tana karanta littafin addu'oi ta juyo tana kallonta cikin fad'a tace

"Oh ni Asma'u, wai Balkisu yaushe za kiyi hankali? sabida Allah ki shigo man d'aki ba sallama"

turo baki Balkisu tayi tana cewa "kai Mama na fayi sallama jini bakiyi ba"

"da yaki kurma ce ni ba" murmushi Balkisu tayi tana fad'in "yi hak'uri Mamana na daina insha Allah, wallahi gajiya ce na kwasu,

ga 'yar banzan rana yau da aka kwad'a agarinan"

"Hum kyaji da shi, yanzu kalli ko takalmi baki cire ba kin wani shigo dasu d'aki kamar k'aramar yarinya"

cikin sauri ta zami takalmin tana dariya,

tana ciri Hijab tace mama yunwa nake ji yau mi aka dafa mana"?

"idan kinje kitchen d'in ko mi aka dafa gani za kiyi ai"

tashi tayi ta fita zuwa kitchen d'in da murna ta dawo ta zauna kusa da Mama

"wayyo mamana dad'i na gode maki da kika mana d'an wake, Allah ya k'ara maki lafiya da tsawon rayuwa da ke da Abbana"

cikin murmushi Mama tace "amin d'iyar albarka".


da dare suna zaune tare da Abba da Mama suna fira Abba yace "mai gadon zinari yaushe ne zaku gama makaranta"?

"Abba saura wata uku insha Allah muyi Kandy"

"madallah Allah ya nuna mana, hadda fa? dan akwanakki kince man saura kad'an ki idar"

"uhm saura hizu goma Sha biyar insha Allah, litattafan ma har mun sauke wasu mun fara harda"

"yayi kyau Allah ya taimaka ina alfahari da ke Balkisu,

ki d'aya muka haifa amma kin zame mana 'ya tamkar dubu, Allah ya maki albarka"

dukan su suka amsa da amin, haka suka cigaba da firan su ciki farin ciki.


suna zaune cikin aji sai hayaniyar d'alibai suke, balkisu da aminiyarta Ummu suna gefe suna karatu,

kafin daga bisani Ummu ta rufi kittafinta tana kallon Balkisu tace "beste kin san mi"?

kad'a kai tayi tana fad'in "Aa sai kin fad'a"

cikin gyara zama tace "yawwa ina gayenan na kusa da gidanmu"?

cikin ya mutsa fuska tace "ni wani gaye na sani na kusa da gidan ku, kawai fad'aman miyi mutuwa yayu"?

duka Ummu ta kaimata abaya "kai wallahi wani lokacin iskancinki yawa ne dashi, daga tambaya sai kiran mutuwa,

kinga iskanci ne duk kinsan wa nake magana, Haris d'an gidan alhajin Allah,

Kin san tun sanda ya ganmu tare ya nace yana sonki,

kuma k'arya ne kice baki gane shi ba,"

"mts to miye idan na gane shi, goya shi zanyi, ni fa bana son kwashe kwashe , ba tara samari 'yan I love you ne agabana ba,

sarai kin sani karatu ne agabana burina na zamo likita, pls karki koma yi mun maganarsa"

Ummu ta kalleta tsantsar gaskiya ta hango acikin kwayar idanunta, cikin girgia kai tace "amma dai kin san na fad'a maki baya da matsala duk na fad'a masa,

ya kuma ce yaji ya gani yana sonki auren ku ba zai hana ki karatu ba,
wallahi yana da kirki sosai Bistey,

Karkiyi wasa da damarki, ki bashi dama dan Allah, kinga ni ya matsa man da zan cin ki"

"Ni fa Biste ba ruwana kawai karma ki k'ara zo man da zan cin sa Allah, taya zan had'a karatu da soyayya"

Ummu za tayi magana Balkisu tayi saurin d'aga mata hannu "dan Allah Biste ki bar maganar nan haka"?

shigowar malami ne ya sa dole ummu tabar zancin.


*Bayan kwana biyu*


Ranar juma'a da wuri aka tashe su makaranta, tana zuwa gida jakarta kawai ta ajiye ko kayan makaranta bata cire ba ta shiga kitchen tana taya Mama aikin abinci,

suna idarwa taje tayi wanka, dama tana fashin sallah wannan yasa kaya kawai tasa riga da sikit na kanti masu yalwa, ta kwanta tana duba wani asamint da aka basu makaranta daga haka barci yayi awun gaba da ita.

"Salamu alaiku" Mama da fitowarta kenan daga ban d'aki taji ana sallama tana ajiye buta ta amsa da


"Amin alaiki Salam, ah maraba ummu yau kece agidan namu"?

cikin murmushi tace "eh wallahi, Mama ina wuni"

"lafiya k'alau Ummu, ya iyayan naki"?
"lafiya k'alau suki sunce a gaishe ki"
"Madallah ina amsawa, shiga k'anwar taki tana ciki barci take"

"to mama" ta amsa tana mai kutsa kai cikin d'akin Balkisu,

tana zuwa ta d'ana mata duka a cinya, zumbur Balkisu ta mik'i tana shafa wajan a tsoraci,

dariyar da Ummu tasa ni ya sa ta saurin duba wajan da take zaune gefin katifa,

"amma wallahi ki d'in ko muguwa ce, Allah ba zan yarda ba sai narama"

ta fad'a tana shirin kaiwa ummu duka, da sauri ummu taja baya tana dariya tace "haba my beste yi hak'uri"

"ai wallahi baki isa ba, sai na rama" nan suka shiga 'yar tsere cikin d'akin, Mama da taji hayaniyar tayi yawa ta lik'o tana fad'in

"kai lafiya, Mike faruwa kuke hayaniya haka"?

cikin turo baki da shagwaba Balkisu tace "Mama tana zuwa fa kawai ta dakeni, shine ba zata bari na rama ba"

"Mts wallahi ku kam Allah ya canza maku hali, ba yanda zaku had'u baku sayar da hali ba"

"wayyo Mama tun fa amakaranta tasan munyi magana zamu je walimar Safiyya Adam 'yar islamiyar mu da zatayi aure,

shine tazo take barci ko shiryawa batayi ba, shiyasa na d'anyi mata duka, kuma fa Mama kad'an nai mata"

"hum ko dai kuka sani, Ke balkisu ki tashi ki shirya ku tafi, ku samu ku dawo da wuri"

"to Mama" ta fad'a tana mai bin hanyar fita,

har takai k'ofa tayi saurin shammatan Ummu ta kai mata duka, ta fita da gudu ta fad'a ban d'aki tana dariya,

"kam wallahi yarinya kin d'au bashi" Mama dariya tayi tare da shigewa d'akinta tana cewa "halinku kenan ba kwa had'uwa baku yarda hali ba.

suna fitowa wajan walima Balkisu tace "beste kinga kusa da gidan Yaya Ahmad ne mu biya mu duba shi, jiya ko da yazo gida naji yana fad'awa Mama baya jin dad'i"

"ok muje, Allah ya bashi lafiya"
"Amin".

da sallama suka shiga gidan, Affan kawai suka tarar a tsakar gida, da saurin sa yazo yana masu oyoyo oyoyo,

rungumeshi Balkisu tayi tana shafa kansa yace "my Affan nayi kewarka, ka daina zuwa mana"

cikin shagwaba yace "Aunty Dady ne yace sai munyi Hutu sannan zai kaimu gidan Mama"

"ayya bakomai, ai kun kusa ko"
cikin gyad'a kai yace "eh"

Ummu tace "ina adda Jidda"

"sun fita da Aunty Meena" (k'anwar mamansa)

"Momy fa"?

"tana kitchen" rik'i hannunsa tayi suka wuce kitchen,

"ah 'yan mata adon gari, yau ko ni agidan namu, lallai na taki babba sa'a"

"Kai aunty kin jiki da wata magana, Allah idan wani yaji sai ya zaci bama zuwa"

harararsu tayi kafin tace "yaushe rabun ku da gudanan harfa na manta"

dukansu sukayi dariya, kusan atare sukace "afuwan Aunty makaranta ce ta b'oye mu,

ya jikin Yaya"?
"alhamdulillah yaji sauki, yau dai kam ko masallaci baije ba, kuje yana d'akinsa,

kuma taimaka man mu kaiwa bakin sa dan Allah"

abinci da abunsha suka d'auka zuwa d'akin Yaya Ahmad.

tana ajiye abinci ta matsa kusa da shi ta zauna kamar zata shige jikinsa, "Yaya ina wuni ya jiki"

rik'i hannunta yayi yana cewa "lfy kalau auta, alhamdulillah jiki yayi sauk'i, yasu Mama"?

"lafiya k'alau suki, bamu ma fada zamu zo ba, munzo walima Nan unguwar nace muzo mu duba ka"

"kun kyauta nagodi" Ummu da take zaune gefin kujera ta gaishe shi da jiki, ya amsa cikin fara'a yana tambayar mutan gidansu,

suka gaida bak'in tare da mik'ewa tsaye Yaya zamu tafi Allah ya k'aru sauki"

"haba auta tun yanzu"

cikin shagwaba tace "Yaya bamu fad'awa Mama ba"

"naji duk da haka ku bari ayi magarib sai muje na kaiku, dama ina so na je"

"to Yaya" suka fad'a tare da barin d'akin

d'akin aunty suka shiga suna ta firan su.

d'aya daga cikin abokanan Yaya Ahmad da tun shigowar su Balkisu ya kafeta da idanu,

bayan fitarsu yace "injiniya wad'annan fa"?

"k'anne na ne"
"Allah sarki yara masu hankali"

cikin murmushi Yaya Ahmad yace na gode sosai, nan suka ci gaba da firan su, kafin daga bisani sukayi masa sallama, anayin sallah magarib ya kwashe su a motarsa, sai da suka ajiye Ummu sannan suka wuce gida.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo, ta Annabi S.A.W nake maku fatan Alkhairi*
[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*NA KASA MALLAKAR HAQURINA*

*MADINA TAYI SANSANI AQIRJINA*

*INAMA YAQININA YA GASGATA BURINA*

*KAMAR AJALINA YANA CIKIN RASHIN ZUWA NA MADINA*

*YA ALLAH KA GAFARCEMU KA WANKE DAUDARMU TA RUHI DATA ZUCIYA KA SADAMU DA SHUGABA KALAMUNCE MANA ZIYARAR MAI GIDA KAFIN ZUWAN AJALINMU*

*SOYAYYA NANA FAD'IMA BA AIBU BANE*
*DARAJACE GA MAI RABO*


*Ga ba d'aya nvl dinan sadaukarwa ne ga duk matan da suka tsinci kansu a AUREN DOLE, Allah Ubangiji ya baku hak'uri da juriyar cinye wannan babban jarabawan, Allah ya kawu sauyi da HASKE arayuwarku ta duniya da lahira*πŸ™πŸ»

*3*

Bayan sa jingini yake jikin bungon suron, duka hannayinsa cikin aljihunsa, ya zubawa k'ofar da zata fito ido ciki da zak'uwa,

sai dai sautin kukanta yasa komai nasa ya tsaya cak, ga ba d'aya sai yaji jikinsa yayi sanyi,

tsaye ta masa k'im tana jiran taji da me yazo kafin ta wanke shi,

zuba mata idanu yayi ciki da damuwar ganin hawayen da ke zuba afuskarta, cikin sanyin murya yace

"kiyi hak'uri ban zace zuwan nawa zai saki damuwa harda kuka ba, dan Allah kiyi hak'uri kinji"?

har cikin jinin jikinta taji muryar na ratsata, wani irin sanyi taji da natsuwa, sai ta tsinci kanta da had'iye kukan ba tare da ta shiryawa hakan ba,

"kinji kiyi hak'uri"
ta sake tsintar muryarsa mai dad'i da sanyi,

cikin inda inda tace "u..u..m.m.b.b.a.k.m"

ajiyar zuciya yayi kafin ya koma cewa "ba dai zuwana ya saki kuka ba ko"?

sunkuyar da kai tayi tana wasa da k'asan mayafinta, ba tare da ta iya cewa uffan ba,

murmushi yayi kafin yace "duk da baki ban amsa ba, alhamdulillah naji dad'i sosai da kika daina kukan, da fatan kina lafiya"?

"lafiya k'alau" ta bashi amsa cikin yin k'asa da murya hakanan ta tsinci kanta da jin kunyarsa,

"am sunana Mahamod abdulnasir, ina zaune ..... magana ta gaskiya ina ganinki ne aduk sanda zakije islamiya,

ganin farko da na maki naji kin mun ma'ana ina sonki, so ba na wasa ko yaudara ba, so ne na aure,

ya nayinki tarbiyarki sune suka yi jagura wa zuciyata ta fad'a sonki, har dai na bin cika gidanku cikin yardar Allah na samu"

yaja numfashi kafin ya cigaba da cewa "Balkisu gani agaban ki da k'ok'on barana, da fatan zan samu kyakyawan masauki a zuciyar ki,

ba koma zan b'oye maki ba, ni d'in talaka, d'an gilulu ne ni"

ya k'arasa maganar cikin wasa,

shiru tayi ta kasa cewa komai, sai dai har ranta tana jin saukar muryarsa mai dad'i tare da dad'ad'an kalamai,

jin shirun yayi yawa yace "oh Balkisu dan Allah kice wani abu dan Allah kinji"?

barin wajan tayi da gudu tana murmushi,

da murmushi afuskarsa ya bita da kallo aransa yana addu'a Allah yasa Balkisu rabunsa ce, dan yana jinta har cikin jinin jikinsa,

ba dan yaso ba ya tafi aransa yana jin lallai goben ma sai ya dawo dan yaji ina aka kwana.

abakin k'ofa ta tsaya, sai da ta dai daita na tsuwarta sannan ta shiga gida.


kallon mamaki ya bita da shi, ganin yanayin da ta fita ba da shi ta dawo ba,

sai sussuna kai takeyi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "to Mama auta ta dawo zan tafi"

cikin murmushi tace "Allah ya tsare agaida kishiyata da mai gidan kwali"

"zasu ji insha Allah"
"Yaya ina gaida yara da aunty"

cikin mamaki ya kalleta "iyye autar Mama yau ba ko rakiya ko"?

b'oye fuskarta tayi tana dariya tace "Aa Yaya, dama fa tasuwa zanyi"

ta fad'a tana mik'ewa tsaye, Mama tace maza koma ki zauna, kai kuma sauka lafiya"

cikin dariya yace "oh Mama duk tsarunne yasa aka hanata rakiya, to na tafi ina gaida baba idan ya dawo"

itama cikin dariya ts bashi amsa "zaiji"

har cikin ranta taji dad'in da Mama ta hanata binsa, dan bata san mi zata ce masa ba,

yana fita tayi saurin yiwa Mama sai da safe, dan bata so ta yi mata tambaya akan bak'onta,

"yau ba za ajira Baban ba"

"Mama barci nake ji"

"to Allah ya tashemu lafiya"

"Amin Mama" ta fad'a tana mai shigewa d'akinta.

ranar kam barci tayi mai ciki da mafarkin Mahamod, dan kuwa ba k'aramin shiga ranta yayi ba.

washe gari haka ta tashi cikin farin ciki da tunanin Mahamod, cikin sauri ta shirya, koda Ummu tazo har ta kimtsa,

rik'i baki tayi tana fad'in "ah Lallai yau anyi abun kirki, nazo ban tsaya jira ba, kin shirya"

fuskarta d'auki da murmushi tace "oho maki dai ni yau bana jin fad'a,

"aikam dai naga alama, har wani annuri naga fuskarki tana yi, miye sirrin"?

tana d'aukar jakkar makarnta tace "indai gulma ke cinki komai ba za kiji ba, sai dai tasan yanda tayi da ke"

dariya Ummu...


Read / Download ILLAR AUREN DOLE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album