Join Our WhatsApp Group

RABO AJALI Complete Hausa Novel Document by RABO AJALI


RABO AJALI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 73980



RABO AJALI

Reading Time: 6 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: Aysha Ya'u Kurah ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 399.47 kb

File Type: txt

Views: 1485+

Download: 821+

Last download: 20 hours ago

Description/Story: [◆ RABO AJALI ◆◆ 1⃣
By Aysha Ya'u Kurah

بسم الله الرحمن الرحيم الحمد لله رب العالمين والصلاة والسلام على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه وسلم. .....

Affan... Affan... Affan..
sau uku saurayin dake tsaye a kanshi ya kira sunanshi amma ko waiwayowa baiyi ba bare ya amsa,, hankalinshi na kan ruwan dake malale cikin wani katon ramin kiwon kifin dake cikin gidansu yana kallon yadda suke wuntsil wuntsil ciki yana girgiza kanshi da jikinshi hakoranshi waje yana dariya da karfi,
duk wanda ya ganshi yasan hankali sam bai isheshi ba, dafashi saurayin yayi hade da zama gefenshi ya watsa ma kifin abincinsu nan take suka kara hautsinewa suna yawo cikin ruwan gwanin ban sha'awa, ihuu Affan yasa yana kaďa kanshi yana kokarin kai hannunshi cikin ramin kuma yana nokesu alamar tsoro, saurayin yayi murmushi ya kara watsa abincin,,, affan ya cikwikwiyeshi cikin murna yana fadin yeeehhh Jabeer kara zuba musu yunwa suke ji dama,
jabeer ya shafa fuskarshi cikin tausayin halin da amininshi yake ciki yace affan lokacin sallah yayi muje muyi sallah mu dawo sai in cigaba da basu abincin,
affan ya no'ke wuyanshi kamar karamin yaro yace um um ba yanzu zanyi sallah ba mummy tace ko da yaushe nayi sallah dai2 ne saboda ni ba a rubuta min zunubi, Jabeer da idonshi ya fara canza kala dan ya riga ya saba da jin hakan a bakin affan kullum in yayi mishi maganar sallah,
cikin dabara yace waya fada maka ba a rubuta maka zunubi Affan,
to bari kaji kasan wutar nan da ake kunnawa mai zafin nan?
Affan cikin firgici yace eh na santa wanda ake dafa min indomie mai zafi ko,
jabeer yace of course ita ay kasan tafi indomie zafi ma ko, affan ya gyada kanshi, jabeer yace to wutar da Allah ke kona waďanda basa sallah tafi wannan zafi sau "dubu malala gashin tinkiya"
affan ya mike a firgice idonshi zuru2 yace tafi wutar dake dafa ruwan toilet heater ma wanda yake kona ni in zanyi wanka,
jabeer yace sosai ma ay wannan ruwan kamar ruwan sanyi ne akan wutar Allah,
affan ya fara ja baya yace karya kakeyi sai naje na tambayi mummy,
jabeer ya mike da sauri dan yasan yana zuwa ya tambayi mummy to fa bazata taba bari yayi sallah ba,
da sauri ya rike hannunshi yace affan ni ke karya,
ya fizge hannunshi yace eh mana kaine kake karya ya juya ya ruga cikin gida da gudu jabeer na kiranshi yayi banza dashi,
dafe kai jabeer yayi cikin damuwa sai da yafi minti 5 tsaye sannan ya wuce ya tafi masallaci,,,,

Jabeer ďinne ya fada maka haka,
affan ya gyada kanshi yana daďa kwanciya jikinta alamun tsoro yakeji kar wuta ta kona shi,
mummy tace rabu dashi makaryaci ne na fada maka ka daina kulashi kullum burinshi ya tirsasa maka yin abinda da bakayi niyya ba kuma ko a musulunce babu takura a addini,
rabu dashi kaji affan din daddy tashi kaje kaci abinci kayi wasanka kaji,
ya daga kanshi ya mike yana tsalle har ya karasa gurin cin abinci yana kiran sunan Hansa'u mai aikinsu tazo ta zuba mishi abinci,

murmushi mummy tayi hade da ajiyar zuciya,
Salma babar diyarta ta ajiye laptop dinta tace mummy wannan tsinannan jabir din so kawai yake ya ruguza miki plan dinki, kullum shi kenan maganar sallah sai kace wani sallau,
mummy tayi dariyar mugunta ta kalli gurin da affan ke cin abinci duk yayi kaca2 da gurin amma ko digo bai diga a rigarshi ba saboda tsananin tsaftarshi,
tace barni dashi ummu, jabeer yana wuce gona da iri tabbas zan san duk yadda zanyi in rabasu da affan in ba haka ba wata rana zai sa kwaba ta tayi ruwa,
Fareedah tace wallhy I so much hate him sai ya dinga wani ďadďaga kai kamar kadangare shi a dole ga kyakykyawa mtsww taja tsaki,
mummy tace ku barni dashi dani yake magana in yasan wata ay bai san wata ba.....

Mrs tijjani shattima......
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Da gudu ta shigo gida ta tarar da jarababbiyar kishiyar uwarta a tsakar gida tana fiffita,
sannu da gida kawai tace bata jira amsa ba ta wuce ďakin kakarta Hajja Giďe,
fadawa dakin tayi babu ko sallama ta cire skul Bag ďinta tayi wurgi da ita a kan gado sam bata kula da mutum a kan gadon ba ta fita da sauri ta shiga toilet,
Hajja ta idar da sallah tayi tsaki tace wannan yarinya saidai Allah ya shirya yi hakuri jabeer, ya mike zaune yana murmushi yace zata sani ay bari ta dawo, hajja tace ay kai baka iya yi mata faďa sai dai kullum kace zata sani kullum kai ke kara sangarta ta,
kafin yayi magana ta shigo ta ďane kan cinyar hajja tace hajjanah" sannu da gida,
hajja ta tureta tace dalla ni sauka karki karya ni,
sai a sannan idonta yakai kan jabeer dake kallonta baya ko kiftawa, da sauri ta mike tana murmushin jindadi ta zauna kusa dashi kamar zata shige jikinshi tace dama kana cikin dakin nan,
ta shagwabe fuska tace shine kana kallon hajja tana tureni ko kayi mata magana kalli fa hannu na saura kaďan taji min ciwo,
Hajja tace Allah ya kiyaye dai banji miki ciwon ba ko, ta turo baki tace kinso kiji min mana inaga ma dan kinsan yaya jabeer na nan ne shiyasa baki ji min ciwon ba,
hajja ta kwashe da dariya tace to yau dai sharrin kaďan ne ko Allah nagode maka ma yana cikin dakin da yana zuwa nasan ce mishi zakiyi yau da kyar na barki da rai,
jabeer ya kwashe da dariya,
ta kwabe baki ta fashe da kukan shagwabe harda buga kai a gado,
jabeer yace subhallahi me kuma akayi miki, hajja ta mike tace tabarar fa,
ni bari kaga in fita dan in ina dakin nan zane yarinya zanyi, cikin kuka tace kaji ko wallhy bulala takemin kullum yauma dan ta ganka ne,
jabeer ya haďe rai yace gaskiya hajja zamu kai kararki can kotun karshe a yanke miki hukunci,
hajja tayi dariya tace mu fara shariar daga yau ma in dai akan AFEEYAH ne,
afiyah ta dago kai ta harareta,
jabeer yayi murmushi ya ciro hndky dinshi yana share mata hawaye, yace so sorry babynah, ya dago fuskarta ya kalli cikin idonta yace baki san kin girma da kuka ba, ta kara marairaicewa kamar karamar yarinya tace to baka ganin abinda takemin, yace to nace kiyi hakuri kinji, ki daina yarda suna saki kuka kinaso a dinga ce miki ruwa2,
ta noke wuyanta tace ah'ah, yace to sai kin zama mai hakuri kin daina yawan kuka kinji,
tace tam zan daina, yace yauwa wifey nah,, ya dakko ledar gefenshi ya fito dasu biscuits da chocolates, rungumeshi tayi cikin murna ta mishi peck a kumatu tace I love u so much hubbynah, wani abu yaji yana mishi yawo cikin kwanyarshi,
a hankali cikin rashin kuzari yace more than u do babynah,, ta sakeshi tana dariya, nan suka cigaba da hirah cikin jindadi tana shan chocolates,
sai da aka kira la'asar sannan ya fito zai tafi, rakoshi ta fito yi bayan yayi sallama da hajja, a dai2 kofar dakin inna suwaiba kausar ke zaune tana ganinsu ta shiga wakar habaici tana fadin Allah wadai da halin yan iska sai a shige daki afi karfin awa wai da sunan ana hira,
ran Afiya ya baci matuka jabeer ya lura da hakan ya rike hannunta gam ta fisge, tace da uban wa kike , kausar ta mike tace da ubanki nake kinji na kira sunanki, in ba tsarguwa kikayi ba meye na jin haushi shegiya marar kunyar banza,
Afeeya ta kuma hassala tayi kanta da sauri jabeer ya riketa da iya karfinshi ya jata da kyar suka fita,
kukan bakin ciki ta fashe mishi dashi tana ta tirje hannunta, murmushi yayi dan yasan in bata tsaya ta mayar da martani ba bazata taba hucewa ba,
hakuri ya shiga bata amma ko kalma daya bata iya rikewa ba saboda zuciyarta cike take da bakin ciki gani take idan basuyi fada da kausar ba yau sai tayi ciwo mai tsanani,
matsowa sosai yayi kusa da ita yace haba afee nah, ba nace kiyi hakuri ba, kinaso inyi fushi ne, ta turo baki tana kuka tace ko zaka fashe yau bazanyi hakuri ba,
ya hade rai yace to ni kuma in bakiyi hakuri ba mun bata garin ma zan bari gaba daya, cikin dakewar zuciya tace ka tafi gaba da birnin sin ma dan wallhy bazan hakura ba,
sakin hannunta yayi yace ni ko? Ta juya mishi baya tace eh ďin,
yace to shikenan bye yasa kai ya fita,
ko ajikinta a lokacin saboda zuciyarta na azalzalarta taje gurin kausar.......

Mrs tijjani shattima.....
[15/12 09:32] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣
By Aysha Ya'u Kurah

Tana shiga ta tarar da kausar na buga k'ullun alale, sam kausar bata kula da shigowarta ba sai saukar wata sanda taji akanta da karfi, zafin ya gigita ta sosai tasa ihun da ya fito da inna suwaiba da hajja daga ďaki,
cikin rudewa inna suwaiba ta kama kausar tace kausar meya faru, kausar ta kasa magana sai kuka takeyi hannunta rike da gurin jini na fita,
hajja ta kwace sandar hannun Afiya tace yanzu ke saboda tsabar mugunta wannan murďaďďiyar sandar kika buga mata,
Afiya ta turo baki tace hajja fa baki san abinda tayi min bane shiyasa,
inna suwaiba cikin fushi ta saki kausar tace uban me ta miki, Afiya ta murguďa baki tace gata nan ki tambayeta,
inna suwaiba tace lallai yau za'a haifi ďa mara ido a gidannan wallhy,
Afiya tace a haďa harda mara hanci ma a haifa,
hajja ta bige bakinta tace ke wai wace irin yarinya ce da baki jin maganar kowa,
Afiya tace to wai hajja ita baki tambayeta me tace mana ba, ce mana fa tayi yan iska, inna suwaiba tace ay kunfi karfin ya'yan iska saidai na guguwa, wallhy yau saina miki shegen duka a gidan nan sai na tabbatar wannan tsinannan bakin naki yayi laushi,
Afiya tace Allahn da halicci baki na shi kadai zai iya sashi yayi laushi ba wata ca--- hajja ta toshe mata baki tace na shiga uku ni Giďe, yanzu ke Afiya bazan miki magana kiji ba, inna suwaiba tace hajja ki wuce daki ki barni da yarinyar nan wallhy yau sai na mata lahani a gidannan, Hajja tace kiyi hakuri suwai--- karki bani hakuri ki cuceni hajja kullum mu kenan a cuce mu a taushe mu, to wallahi bazan dauka ba,
ji yadda jini ke zuba a kan kausar ay dan tasan kuna daure mata gindi ne ke da malam shiyasa take abinda takeso, in ba ta raina mutane ba ay kausar ba sa'arta bace,
hajja tace kiyi hakuri dai nace suwaiba, Afiya ta harari hajja tace wai hajja hakuri kike basu ni baki bani hakuri ba sai su da babu abin ma da nayi musu,
inna suwaiba ta hassala sosai tayi kan Afiya ta cakumota, hajja ta riketa tace wallhy suwaiba karki taba min marainiyar Allahn nan,
wallhy kika kuskura kika sata kuka sai ranki yayi matukar baci,
inna suwaiba tace ay ko sai dai ya baci ta kaima Afiya duka ta goce tana kicikicin kwacewa,
kausar dake jin kanta kamar dutse ta mike tazo ta bayan Afiya ta kai mata duka, Afiya tayi kukan kura ta kwace jikinta a gurin inna suwaiba ta haye kan kausar inna suwaiba na jibgarta ita kuma tana jibgar kausar, hajja na gefe tana kuka ita sam bata ma ga dukan da afiya kema kausar ba ita dai tafi jin dukan da akema Afiya,
dakyar da taimakon shigowar malam faďan ya rabu kowa na maida numfashi, kausar bayan inna taje ta boye tana kuka sosai saboda taji jiki, Malam Atiku cikin bacin rai yake ma inna faďa itama cikin fushi take mayar mishi,
yace yanzu in banda ke babbar kwabo ce meye na shiga faďan yara, wai ke in an barki ga mai ýa ko, kin gama zubar da mutuncinki a idon karamar yarinya, inna cikin fushi tace faďa min mai mutunci a idon wannan shegiyar yarinyar,
hajja ta fashe da kuka tace wallhy ba shegiya bace, Danbaba ni na gaji da zaman gidan nan kullum sai sun tsokani yarinyar nan ita kuma Allah bai ďiga mata hakuri a ranta ba gara muyi nesa dasu su zauna su kadai a gidan,
malam Atiku yace babu inda zaku hajja, baku da inda yafi nan, zan dauki tsatstsauran mataki akan wannan alamarin,
inna suwaiba tayi tsaki ta hararesu tace ka daďe baka ďau mataki ba, wannan yarinyar wata rana saita dauko muku na barin gari, ta kama hannun kausar suka wuce ciki tana masifa zuciyarta na ķuna saboda Afiya, ta rasa dalilin da yasa ta kasa samun nasara akan Afiya,
zama tayi bakin gado idonta yayi jajur dan ba karamin caza mata kwakwalwa Afiya keyi ba,

Can kuma dakin hajja fada sosai suke ma Afiya akan rashin hakuri, malam atiku yace ni wallhy na rasa inda yarinyar nan tayi gadon wannan halin hajja ko kadan bata da hakuri komai aka mata tace saita rama kuma rayuwa bazata taba tafiya haka ba,
Allah na tuba kayi hakurin ma ya ka kare a wannan zamanin bare kuma bakayi ba, hajja tace ay ni yanzu inaga nawa ido tsakanina da Afiya dan gani sukeyi kamar goyon bayanta nakeyi ni take ďaura ma bakin jini dan kawai taga banason abinda zai bata mata rai shiyasa takeson a dinga ci min mutunci,
Afiya ta fashe da kuka tace dan Allah hajja kuyi hakuri in shaa Allahu ko duka na zasuyi bazan kara tanka musu ba,
hajja tayi tsaki tace ke ďin ce zaki faďi magana in yarda, malam atiku yace hajja muyi mata addua babu mamaki bazata kara ba,
Afiya tace Allah abba bazan kara ba,
hajja tace to Allah yasa da gaske kikeyi, duk suka ce ameen, nan suka cigaba da yi mata nasiha akan rayuwar duniya cikin dabara suke mata nuni da illar rashin hakuri,
Afiya jinsu kawai takeyi dan ita bataga rashin hakurin da aketa ikirarin tana dashi ba ita dai tasan ko manzon Allah s.a.w yace in aka bata maka ka rama dai2 yadda akayi maka, to ita kuwa akan me zata yarda tanaji tana gani a taka ta, bazai yiwu ba,, har suka gama nasiharsu Afiya tana gyada kai kamar taji abinda suka ce sai gab da magriba malam atiku ya fita suma suka tashi suka je yin alwala...

Tun daren ranar take zuba idon ganin jabeer shiru har kofar gida ta fito ta tsaya tana kallon kofar gidansu ko zata ga fitowarshi amma ko giftawarshi bata gani,
kullum ta dawo...


Read / Download RABO AJALI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album