Join Our WhatsApp Group

RANA DA WATA Book 1 Complete Hausa Novel Document by RANA DA WATA Book 1


RANA DA WATA Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 9829



RANA DA WATA Book 1

Reading Time: 0 Hours

Added On: 21, Nov 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 55.3 kb

File Type: txt

Views: 819+

Download: 260+

Last download: 3 days ago

Description/Story: RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- A

Masu karatu ayimin afuwa don kuwa farkon fallen littafin ya yage amma ga abunda ya kunsa
.
Acan cikin wani kauyene wata mata mai suna shafhila sai faman naku da ta ke tayi yayin da sararin samaniya kuwa sai amsawa yake, ba'a bata lokaci ba matar ta haifo yaranta guda biyu
.
Babu abun da zai baka mamaki da wayannan yara face sam basa kaunar junansu, don kuwa koda yaran suka fara girma sai ya kasance suna matukar GABA da juna tamkar RANA DA WATA ,
A kowani lokaci kuwa babu abunda suke yi face fada da junansu wanda wannan abu yana matukar damun mahaifiyarsu shafhila
Shekaru suna ta ja har takai sun girma sun mallaki hankulansu amma basu daina wannan gaba da fada ce fadace ba
Macen mai suna zuhaisa zuciyarta bakine sam babu ko digon tausayi ko imani a tattare da ita
Shi kuwa namjin mai suna huzainu babu abun da ya tsana face zalunci , kuma shi kadai ne acikin wannan gari wanda yake hana Zuhaisa ai kata zaluncinta don kuwa aduk lokacin da zata aikata zalunci sai ya bayyana, sannan su cigaba da bakin yaki tamkar ba ciki daya suka fito ba
.
Hakan shi yasa mahaifiyarsu ta nufi wajen boka wani shahararren boka mai suna sharanu koda isarta wajensa har ta budi baki zatace wani abu sai boka shuranu ya dakatar da ita sannan yace" yake wannan tsohuwa kiyi sani cewa nasan abun da ke tafe dake ,"koda jin haka sai shafhila tace
Shin boka yaya za'ai su hada kansu su daina wannan gaba da fadace fadace

Koda jin bukatar shafhila sai boka sharanu ya tuntsire da dariya
Al'amarin da yai matukar firgita shafhila kenan
Lokaci guda boka sharanu ya murtuke fuska ya dubeta yace "yake wannan uwar jarumai ki sani cewa har abada yayanki ba zasu taba kaunar juna ba , kuma ba zasu taba zama ba a waje daya domin tamkar RANA DA WATA suke .
.
Sai aranar da dayansu ya kashe daya sannan nadama da takaici zasu zo masa.
Ki sani cewa kin haifi yayanki ne a ranar da aka samu kisfewar rana.
Ita macen kin haifeta ne a dai dai lokacin da rana zata kisfe , don haka ta zamo mai bakar zuciya da bakin rai . Saboda rana aba ce mai zafi,
.
Shi kuwa namijin kin haifeshi ne a dai dai lokacin da wata ya kisfe, shi yasa ya zamo mai tausayi da sanyin rai (kaman ni kenan, kar dai ku shagala Alkalamin shuraih 99% ne]
.
Wadannan yaya naki zasu daukaka a duniya irin wacce babu kamarta a wannan zamani.
.
Macen zata zamo gagarumar matsafiyar sarauniya .shi kuwa namijin zai zamo gawurtaccen sarki ma'abocin wani bakon Addini,
.
Zasu yi ta yakar junan har izuwa lokaci mai tsawo, yayansu ma sai sun gaji wannan gaba kuma a karshe sai dayansu ya kashe daya"
.
Koda jin wannan labari sai tsohuwa shafhila ta dafe kai tana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki tamkar ba zata daina ba .
.
Da kyar boka sharanu ya lallasheta tayi shiru snnan ta dube shi tace da shi.
"Yakai wannan boka mai daraja , yanzu wace hanya zan bi na sauya wannan al'amari ya zamana cewa wadannan yaya nawa sun hada kansu sun daina gaba?"
.koda jin wannan tambaya sai boka shuranu ya sake tuntsirewa da dariya a karo nabiyu , daga san ya takarkare ya kwarara uban ihu mai firgitarwa , har yana birgima a kas,
.
Al'amarin daya firgita tsohuwa shafhila kenan har ta ja da baya .
Ta takure jikinta ajikin bangon dakin kamar zata saki fitsari saboda tsananin tsoro daga can kuma sai taga boka shuranu yayi doguwar ajiyar zuciya a lokacin daya jike sharkaf da gumi sannan ya dubeta yace "yake wannan tsohuwa, kiyi sani cewa babu wani abu da zai iya canza wannan al'amari face ki sallama rayuwarki don inganta tasu.
Kuma yin hakan ma ba abu bane mai sauki ba domin dole kije har can kogon darul yazmin dake can karshen birnin sin ki yanka jijiyar hannunki na hagu a cikin kokon dodonniya HUJUMU-MAJNUN har sai kokon ya cika ta zo ta shanye jinin duka , nan take rana zata kisfe .
.
Idan da rana ne abin ya faru. Haka kuwa wata zai kisfe, idan a lokacin da abin ya faru dare ne ki sani cewa a tarihin kogon darul yazmin tun daga wanzuwarsa kawo izuwa yanzu, babu wani bil'adama ko aljani daya taba shiga cikinsa ya fito a raye sai dai a mace aciki har ya rube, ya zama kwarangwal.
.
Duk abin da mutum yake nema na duniya in dai ya shiga cikin darul yazmin sai ya sameshi walau dukiya ko maganin wata cuta data gagara . Matsalar dai itace koda mutum ya sami biyan bukatarsa bai isa ya iya fitowa ba araye daga cikin kogon saboda hujranul-majnun ce take gadin duk abin daya ke cikinsa
(Lallai dole nayi shiri na ttunkari kogonnan saboda wata bukata tawa ehm shuraih 99%)
.
Dodonniya hujranul majnun ta kasance gabjejiyar dodonniya mai tsawon gaske gami da kauri da fadi. Idan ta tsaya a gaban mutane komai yawansu sai su ga kamar a gaban tsauni suke.
Ta kasance basadaukiya mai tsananin karfin damtse domin komai girman dutse da kwarinsa
.
Idan ta dokeshi da hannunta sai yayi bindiga ya tarwatse, kuma tana iya kwakule duwatsu da kaifin faratan hannayenta ko ta yanka karafa da su ta sarrafa karafunan wajen kera abubuwa da yawa kamar kofunan zinare,gadaje,kujeru,da saurran kawa irinsu lu'u lu'u jauhar da sauransu wanda Aljanu suke zuwa su siya a wajenta
.
Masana da masu bincike sun tabbatar da cewar a duk fadin duniya babu wani makeri wanda yafi dodonniya hujranul-majnun iya kira da sanin karfe kuma babu wani boka wanda yafita karfin sihiri, babu wani sadauki wanda ya fita karfin damtse gami da zafin nama.
.
Kaifi da tsini basa tasiri a jikinta
.
Dukiyar data tara kuwa a kaf duniya babu wani Attajiri daya tara kamarta komai karfin arzikinsa da karfin mulkinsa.
Dodonniya hujranul-majnun tana iya tarwatsa runudunar mayaka ita kadai komai yawansu, sai dai su tsere su gudu su barta
.
A halin yanzu dodonniya hujranul-majnun tana da shekaru dari da talatin da uku a duniya.
.
Yake wannan tsohuwa isan har zaki iya siyar da rayuwarki kije har can dajin inda kogon darul-yamzin yake a karshen birnin sin to sai kiyi shiri ki zo nan akwai fataken da zan hada ki dasu su kai ki har birnin sin daga can kuma akwai aljanu wadanda za'a hada dasu su kai ki har bakin kogon darul-yamzin
.
Ammafa ki sani cewar wannan tafiya zata daukeki a kallah shekara shida, kafin ki isa birnin sin kuma zaku ketare ta cikin mugayen dazuzzuka masu dauke da mugayen aljannu, dodonni da mugayen dabbobin daji wadanda zasu iya zama sanadin ajalinku , sai mai cikakken rabo da matukar sa'ane zai iya kaiwa har can a raye kuma cikin koashin lafiya
.
Toh ana zan dakata sai kuma gobe in Allah ya kaimu da rai da lafiya
Daga shuraih Usman
Inkiya 99%
Sai kunjini da part BRANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
Part B

Shuraih 99% nake cewa daku Lokcin da boka sharanu yazo nan a zancensa sai tsohuwa shafhila tayi doguwar ajiyar zuciya , sannan ta dubeshi a cikin nutsuwa tace " yakai wannan boka mai yawan daraja ka dubeni ka gani , nifa na tsufa banida wani buri da yai mini saura a wannan duniya face ganin cewar bayana tayi kyau. Ina mai tabbatar maka cewa raina da duk abinda na mallaka ba'a bakin komai suke ba, muddin wadannan yayan nawa zau hada kansu su zauna lafiya a matsayin yan uwan juna na jini ba abokan gaba ba .
.
Yanzu zan koma gida naje na sayar da duk abunda na mallaka domin nayi guzurin wannan tafiya .
.
Abinda na ke so naji daga gareka kawai shine yaushene abokan tafiyar tawa zasu hallara anan mu gamu mu dunguma gaba daya mu tafi birnin sin(abokan tafiyarmu zakice don kuwa har dani acikin wanga tafiya ehm shuraih 99%)
.
Yayinda tsohuwa shafhila ta zo nan a zancenta sao boka sharanu ya kura mata idanu cikin natsuwa da mamaki, sannan yace " na rantse da darajar iyayena da kakannina da kuma darajar tsafina ke ce mutum ta farko data taba cin alwashin zuwa kogon darul yamzin ba tare data girgiza ba, hakika yake wannan tsohuwa shafhila , ina ji ajikina cewa zaki samu nasarar zuwa wannan kogon koda kuwa wannan bukata taki zata zamo ajali a gareki.
.
Saboda haka maza ki gaggauta kammala shirin tafiya nan da kwanaki uku"
.
Lokacin da boka shuranu ya zo nan azancensa , sai ya taba hannayensa a take ya bace a gurin , Tsohuwa shafhila ta daina ganinsa.
.
Kar dai ku shagala kuna tare da Shuraih 99% ne
.
Yayin da tsohuwa shafhila ta samu kwanaki uku. Daidai lokacin data karasa duk wani shiri nata tsaf .
.
Sai shafhila ta gabata a gaban boka sharanu zuciyarta ta kekashe a yanzu bata da wani buri a rayuwarta face taga yayanta huazainu da zuhaisa sun hada kansu wuri daya sun daina tsananin gaba da kiyayya da junansu .
.
Lokacin da boka sharanu ya dube ta sai ya tuntsire da dariya kamar bazai daina ba. Al'amarin daya dada karfafawa shafhila guiwar zage damtse kenan akan wannan tafiya kuma a
.
Lokacin ne fataken da zau tafi tare suka karaso. Daga cikinsu akwai manyan attajirai da jarumai masu tsananin kafiya da dakakkiyar zuciya. Yawan fataken duk su dari uku ne.
.
Boka sharanu ya dubi tsohuwa shafhila sannan ya mika mata fatar barewa yace da ita "ki rike wannan a duk lokacin da kike bukatar sanin wani abu a yayin wannan tafiya taku ki shimfida wannan fatar barewan sannan ki kirayi sunana sau uku fuskata zata bayyana a kai ki fada mini matsalarki"
.
Sa'adda boka sharanu yazo nan a zancesa sai tsohuwa shafhila tayi godiya a gareshi , sannan ta shige cikin a yarin fataken nan ba tare da bata lokaci ba suka kama tafiya cikin azama a wannan gagarumar tafiya tasu mai cike da hadarurruka.
.
Kwanci tashi har suka shafe kwanaki goma suna tafiya ba tare da sun sami wata matsala ba.
.
Dukkana fataken nan sun cika da tsananin mamaki akan tsohuwa shafhila domin tafi kowa doki da tsananin kuzari a wannan tafiya, sai ya zamana a yanzu tsohuwa shafhila ce ke jagorancin tafiyar duk da cewa akwai manyan sadaukai da jarumai a ciki.
.
Lokacin da suka sake shafe kwanaki uku a wannan lokacin sun zo wani daji mai tsananin duhuwa da dogayen itatuwa masu tsayin gaske . Daga cikin ayarin fataken akwai wani sadaiki mai suna sabitul-agadawur ibni ihwas.
.
Ya dubi tsohuwa shafhiila yace da ita .
"Hakika yake wannan tsohuwa ki sani cewa a yanzu munzo dajin mutane ma'abota cin naman mutane.
.
Ki sani a wannan daji duk girmansa babu ko dabba daya dake rayuwa a cikinsa.
Saboda tsananin shawagi irin na wadannan mutane shi yasa ko tsuntsaye basu kusanto wannan daji .
.
A tarihi ba'a taba samun wani ayarin fataken da suka taba ratsa wannan daji suka fita lafiya ba , face wasu da yawa daga cikinsu sun halaka
.
Sannan suna da yawa ,kuma suna da tsananin kafiya da naci, ance saboda maitarsu idan suka asa mutanen da zasu halaka su cinye, sai babbansu yasa ayi kuri'a duk wanda tsautsayi ya afkama to a wannnan ana sune kalacinsu.
.
koda sadauki sabitul-agadawur ya zo nan azancensa , sai ya dubi sauran abokan tafiyarsa ya kara da cewa "saboda haka ya zama wajibi mu yi taka tsantsan wasun mu su rika lua da bayanmu wasu kuma su rinka lura da gefen dama da gefen hauninmu"
.
Daga nan babu wanda ya kaa cewa komai suka ci gaba da ratsa dogayen itatuwan dake a wannan daji
.
Anan zan dakata , Kar dai ku manta kuna tare da
Shuraih Usman
Inkiya 99%RANA DA WATA
Littafi na daya 1
Na abdulaziz sani madakin gini
Typing:- Shuraih 99%
Post:- Shuraih 99%
PART:- C

*********
Al'amarin huzainu da zuhaisa kuwa arana da suka fahimci mahaifiyarsu bata na duk kuwa da cewa basu san inda ta tafi ba ha tsawon wata guda cur , sai zuhaisa ta hada kayanta tsaf tayi shigar kayan yaki, tayi tsalle ta dare akan ingarman dokinta a dai-dai wannan lokacin huzainu ya karaso a gurin
.
Zuhaisa ta dubeshi da tsana cikin tsananin kiyayya, sannan ta zare takobi tareda nuna shi da tsinin takobin tace "na fahimci mahaifiyamu tayi wata tafiya daba dta son mu san inda ta tafi, kama yadda kasani a duk fadin duniya babu wani mahaluki dana tsana da tsananin kiyayya sama da kai.
.
Kamar yadda na daukarwa kaina alkawarin da karfin damtsena sai na sanya takobi na datse jijiyar wuyanka, da iyakance numfashinka [ its shuraih 99%] a doron kasa .
.
Hakika bani da wani buri daya wuce na ga na shafe babin rayuwarka. Don haka na yanke shawarar barin mahaifata a yanzu , zanje na dada yin shiri da mummunan tanadi a akanka
.
Inasi ka sani daga ranar da muka sake haduwa da kai ,to ka sani a wannan ranar ne mala'ikan mutuwa zai gabata zuwa gareka, na rantse da iyayena ba zaka kubucewa kaifin takobina ba face na halaka ka"
.
Koda huzainu yaji wannan batu sai ya tuntsire da dariya, ya dade yana yi tamkar bazai daina ba, al'amarin daya harzuka zuhaisa kenan ranta ya baci jijiyoyin jikinta suka motsa sai kawai ta diro daga kan dokinta ta nufi huzainu da bakar zuciya tana gurnani kai kace zaki ne yayin da zaluncinsa ya motsa masa a lokacin daya ga wata karamar dabba
.[shuraih Usman nake inkiya 99]
Zuhaisa tana kusanto huzainu sai ta kawo masa wani gawurtaccen sara a saitin dokin wuyansa da niyyar ta sare masa kai cikin tsananin zafin nama, kwarewa da jarumta huzainu ya goce takobin ta wuce ta saman kansa ta kara kawo masa wani mummunan sara a anan ma ya kauce
.
Da huzainu yaga da gaske fa zuhaima take sai shima ya zare nashi takobin nan ne fa suka fara wani azababben yaki, suka kasance cikin kai ma juna sara da suka suna masu zafin nama, juria da jarumta
.
Sai da suka shafe sa'a uku babu wanda ya samu nasarar yiwa daya koda sara daya ne har sai da takubbansu suka dakushe saboda tsananin kai sara ga junansu
.
Sannan suka zubar da makaman nasu suka kacame da kokawa da naushe-naushe.
.
Babu jimawa kowannensu ya hada gumi woho ho mai karfi sai Allah ya isa nan fa tsagwaron karfin damtse ya soma amfani sai gashi su duka biyun kwanjin jikinsu ya dada kumbura , jijiyoyin suka tashi sukayi burdinburdum.
.
Can gabannin faduwar rana kowannensu kamar an yi masa umarni sai suka turje suna masu kallon juna kamar zakaru [shuraih Usman nake inkiya 99]
.
Zuhaisa ta nuna huzainu da dan yatsa ta ce da shi " kamar yadda na fada da farko ka saurari haduwarmu anan gaba kadan. Ka sanni bana afuwa , kuma bana mance gaba komai kankantarta"
.
Lokacin data zo nan a zancenta sai tayi tsalle ta dare akan dokinta taci gana da tafiya . Huzainu yai tsaye yana kallonta kawai ba tare da yace da ita ci kanki ba.
.
A haka har...


Read / Download RANA DA WATA Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album