Join Our WhatsApp Group

DUGUNZUMA 1 to 4 Complete Hausa Novel Document by DUGUNZUMA 1 to 4


DUGUNZUMA 1 to 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41923



DUGUNZUMA 1 to 4

Reading Time: 3 Hours

Added On: 21, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 233.45 kb

File Type: txt

Views: 1566+

Download: 711+

Last download: 4 days ago

Description/Story: DUGUNZUMA!!!
LITTAFI NA DAYA
PART 1
LITTAFIN YAKI

typing NASEER SHEhu

post real prince rayyan

*******
Kai da ganinsu kaga sadaukai, musamman idan
kayi la'akari da yanayin siffofin jikinsu,
Tafe suke a cikin faffadan dajin a cikin shiga irin ta
kwararrun mafarauta wacce ke nuna cewa sun san
sirrin daji matuka,kuma babu alamar tsoro ko
shakkar komai a tare dasu.
Komai dakewar mutum idan ya tsinci kansa a cikin
irin wannan mugun daji da zaratan samarin su
bakwai ke kutsawa dole ne ya razana saboda
kwarjininsu da irin yanayin bishiyoyi,duwatsu da
koramu dake cikinsa, da kuma tsananin
shirunsa,domin kunne baya jin sautin komai face na
kukan tsuntsaye, sai kuma mugun gurnani na
manyan dabbobin daji.
Wadanan ZARATAN SADAUKAI sun fito ne daga
wani karamin kauye da ake kira GARUL ASWAR
wanda ke karkashin birnin LURHAJ inda sarki
ARYAN ke mulki, ZARATAN SADAUKAN bakwai sun
hada da Humairu, ILsam, Zuraif, Hashim, Sahal,
Kaimur,da Hashlar.
Dukkaninsu sun shaku da juna saboda tun suna
yara basu taba rabuwa ba, bisa wannan dalili ne
suka dauki alkawari komai na rayuwa tare zasu yi,
hatta Aure kuwa, ko farauta suka fita idan ma
mutum daya ne ya sami nasarar kamo dabba to fa
sai dai a raba dabba gida bakwai dai-dai, idan
kuma kowa ya kamo tasa bazai tafi da ita gida ba
sai dai a tara duk dabbobin a waje daya a rabasu
dai-dai kowa ya debi rabonsa
Sai da su Humairu suka shafe sa'a daya da rabi
suna gudu a cikin daji suna bin wata Barewa,amma
sun kasa cimmata, ya zamana cewa su basu gaji
da gudu ba, ita kuma barewar ta kasa samun wajen
tsira.
Shi dai Humairu yafi kowa gudu a cikinsu, don
haka shine akan gaba, ILsam yafi kowa iya harbi da
baka,kuma shine na biyu a iya gudu,don haka duk
inda Humairu ya dauke kafarsa anan yake saka
tasa.
Zuraif shine yafi kowa iya tsalle da hawa kan
bishiyoyi tamkar Danbiri.
Hashim shine mafi sanin sawun kowacce irin
dabba, shi kuma Sahal Allah ya hore masa jin sauti
a kunnensa, domin yana iya jiyo sautin sawun zaki
ko giwa daga nisan tafiyar zango, kuma a duk inda
dabba tayi kuka zai iya fadin nisan tazarar dake
tsakaninnsu da ita.
Kaimur Allah ya bashi tsananin karfin kirji, domin
ko da zaki ya hada kirji sai dai zakin ya fadi, shi
kuwa a tsaye daram zaka ganshi, kai hatta manyan
bishiyoyi idan Kaimur ya fusata yana iya bangajesu
da kirjinsa kaga suna tuttukowa daga cikin kasa har
jijiyoyinsu suna zubewa kasa.
Shi kuwa Hashlar Allah ya hore masa iya sarrafa
takobi, komai yawan dakaru ko dabbobi in dai
yana rike da takobi babu abinda zai sameshi sai ya
tarwatsasu ya kashe na kashewa - Masu Gudu Sun
Gudu.
Bayan su Humairu sun kasa kama wannan barewa
sai ILsam ya fusata ya ruga Izuwa kan wani dutse
mai tsawo ya tsaya cak! Sannnan ya dana kwari
akan bakansa ya saita wannan barewa duk da cewa
tana gudu kuma ta bashi tazara mai yawa saura
kiris ma ta kule sai ya tabe bakansa iya karfinsa ya
saki harbi, take kibiyar taje ta soki barewar a
kuibinta cikinta na hagu ta bullo ta kuibin dama.
Saboda karfin harbin sai da barewar tayi sama ta
cake a jikin bishiya ko surawa bata yi ba , ta zama
gawa.
Koda su Humairu suka ga wannan gagarumar
bajinta da ILsam yayi sai suka hau shewa suna yi
masa tafi da jinjina, nan take suka sami inuwa suka
zauna sannnan suka fede barewar suka tsireta a
jikin ice mai gwafa suka hada wuta suka fara
gasata domin suci.
Idan suka gama sai su kara gaba su koma gida,
dama haka ka'idar farautarsu take, wato kullum idan
suka fito sau daya suke aiki, ma'ana duk abinda
suka fara arangama dashi to fa in dai sun kamashi
bazasu sake neman wani dabam ba.
Bayan barewar ta gasu sunci sun koshi sai kuma
kishirwa ta addabesu, gashi baduda sauran ruwa a
cikin buttocinsu duk sun shanye, haka kuma tun
safe da suka shigo dajin rana ta fito da wuri ta
kwalle kuma sun dade da yawa suna falfala
azababben gudun da suka sha Lokacin da suke
kokarin kama wannan barewa.
Nan take suka yanke shawarar tafiya neman
ruwa,da yake sun san dajin sossai sai suka durfafi
wata hanya wacce zata kaisu Izuwa ga wani rafi
wanda ake kira HUZURA sai da suka shafe kusan
rabin sa'a suna tafiya sannnan suka fara hango rafin
huxura.
Tun daga nesa suka hango wani abu kamar mutum
kwance a gabar rafin tamkar gawa, domin ko motsi
bayayi
Cikin hanzari su duka suka ruga Izuwa bakin rafin,
da zuwansu sai suka iske ashe kuwa mutum ne a
kwance cikin jini kaca-kaca ba kyan gani mutumin
bai mutu ba amma idanunsa sun fara rufewa suna
lumshewa da budewa alamar cewa ransa na daf da
fita, kuma sai bude baki yake yanason ya fadi wani
abu amma ya kasa.
Cikin sauri ya durkusa bisa guiwoyinsa ya dora kan
mutumin akan cinyarsa sannnan ya dubi ILsam yace
" maza ka debo masa ruwa a cikin rafin nan ya sha"
ILsam ya cika umurni da gaggawa,koda Humairu ya
baiwa mutumin ruwa yasha sai yai dogon ajiyar
numfashi sannnan ya dubesu daya bayan daya su
bakwan nan, kawai sai ya gyada kai yace,
"YA ku wadanan mafarauta ina mai shawartarku
daku ruga da gudu ku koma Izuwa cikin kauyenku
ku hada jama'arku gaba daya ku gudu daga wannan
nahiya gaba daya, domin masifar da ta bullo a
wannan nahiya tafi karfin kowa da komai.
Wannan hali da ku ka na shiga sanadiyar masifar
ne, kuyi sauri kuje ku ceci mutanenku in ba haka
ba kuwa duk mazan dake kauyenku duk sai sun
zama gawa.
Koda jin wannnan batu sai mamaki ya kamasu su
duka, har ma wasu daga cikinsu suka fara dariya
domin ganin suke kamar dacin mutuwa ne yasa
wannan mutumin yake sambatu.
Shi kuwa Humairu bai dauki abin da wasa ba.
Don haka sai ya gyara kwanciyar kan mutumin akan
cinyarsa ya dubeshi yace, ya kai wannan mutum,
wai shin wacce irin masifa ce haka tazo wannan
nahiya tamu?"
Mutumin ya kara bude baki da kyar yace "wadansu
irin mutane ne sukazo mana wadanda adadinnsu
ba zai kirgu ba, kuma kirarsu irin ta mutanen farko
ce, saboda girmansu idan suka hau kan doki take
kashin bayan dokin yake karyewa, don haka ne
yasa basa hawa dawakai sai dai giwaye, suna
dauke da mahaukatan makamai irin wadanda idanu
ma bai taba ganinsu ba.
Ina dada gaya muku ku gaggauta barin dajin nan ku
koma kauyenku ku ceci jama'arku "
Gama fadin Hakan keda wuya sai idanun mutumin
suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare, ya zamana
cewa babu wani abu dake motsi a cikin jikinsa.
Humairu ya shimfide gawar mutumin a gefe daya,
sannnan ya dubi sauran jaruman shida yace, to fa
kun ji sakon da wannnan mutumin ya isar mana
dashi.
Ina ganin zai fi kyau kuzo mu koma gida da sauri
domin ni dai jikina ya bani cewa maganar da
mutumin nan ya fada gaskiya ce."caraf sai ILsam
yace, haba ya kai Humairu ya ma za ai ka yarda da
maganar mutumin dake kan gabar mutuwa? "
Ai ni ina ganin cewa kawai radadin fatar rai ne yasa
shi sambatu ".
Cikin fushi Humairu yace "to idan kace haka,
menene kuma abinda yayi masa wannnan mugun
raunika ajikinsa?"
Idan ma sara ne na takobi tunda muke yawo a
dazuzzukan nan bamu taba ganin dabar da ta yawa
mutum irin wannnan rauni ba.
Idan dukkaninku babu wanda zaiyi amfani da
wannnan shawara ni kam sai nayi amfani da ita.
Koda gama fadin Hakan sai Humairu yaje bakin
rafin ya cika battarsa da ruwa ya tsuke bakinta,
kuma ya ratayata a kafadarsa.
Kawai sai ya falfala da matsanancin gudun tsiya ya
nufi hanyar da zata mayar dashi kauyensu na Garul
Aswar"
Koda faruwar hakan sai su ILsam suka hau kallon
juna, tsawon yan dakiku dayansu baice uffan
ba,kawai sai ILsam yabi bayan Humairu da gudu,
nan take sauran samarin ma suka yi koyi dashi,
wato gaba dayansu suka ruga Izuwa hanyar gida.
Bayan sun shafe sama da sa'a daya da rabi ne
suna gudun suka tsaya cak. Gaba dayansu cikin
tsananin tashin hankali suna haki, sakamakon
abinda suka hango a gabansu.
Ba wani abu suka hango ba face turnukewar hayaki
mai yawan gaske acan kauyensu.
Saboda yawan hayakin har basa iya hango komai
na kauyen, hatta gidajensu na bunu kuwa.
A firgice suka zare makamansu lokaci guda suka
sake rugawa da gudu domin su isa cikin birnin.
Kaico! Suna shiga cikin garin sai sukayi BAKIN
GANI, domin sun fara tuntube ne da gawarwakin
mazajen garin duk inda suka duba basa ganin
gawar mata ko ta yara sai ta maza samari da
tsofaffi.
Koda ganin wannan Al'amari sai su Humairu suka
fara kuka domin sun fahimci cewa an kashe gaba
dayan mazajen kauyen nasu, ko mutum daya ba'a
bari ba.
Gawarwakin mazajen dake zube a wajen sun haura
dari uku kuma babu babban abin takaici face ganin
irin mugun kisan da akayiwa mutanen, babu gawar
da zaka ga sara daya a jikinta sai dai biyar ko
sama da haka,
Nan fa kowanensu ya fara lalubar gawar mahaifinsa,
Humairu ne ya fara ganin gawar mahaifinsa yaga an
sharbe masa makogwaro kuma an fede kasan
cikinsa har tumbinsa ya fito waje.
Koda da ganin wannan gawa sai Humairu ya kurma
uban ihu mai tsananin firgitarwa wanda ya cika
kauyen gaba daya har ya amsa kuwwa Izuwa cikin
daji.
Kash! Rashin sani yafi dare duhu, inda Humairu
yasan abinda zai biyo baya sakamakon wannan ihu
da yayi da bai yi shi ba.
Ashe rundunar wadanan mugayen mutane da
sukazo suka yi wannan muguwar barna basu dade
da barin kauyen su Humairu ba.
Tazarar dake tsakaninnsu da kauyen bata wuce ta
tafiyar rabin zango ba.
Ai kuwa sai suka jiyo wannan ihu da Humairu yayi,
nan take shugaban dakarun wani jibjejen kato
wanda kamar zanashi akayi saboda girma da
munin gaske. Ya dubi wadansu zakwakuran
dakarunsa guda uku kacal! Wadanda su kansu yin
arba dasu ba karamar masifa bace saboda
kwarjininsu,
Ya daka musu tsawa yace, ku koma da baya Izuwa
wannan kauye da muka baro, lallai akwai sauran
namiji acikinsa.
Ku tabbatar da cewa baya numfashi, kuma ku ciro
kansa kuzo mini dashi domin na tabbatar da cewa
yaje kasa.
Idan banga sabon jini a jikin kan ba nasan kun
kasa cika aikinku, don haka kuma zaku sheka
barzahu.
Koda jin wannnan umurni sai zaratan dakarun uku
sukayi sujjada ga shugaban nasu sannnan suka
kada giwayensu da baya cikin sauri suka nufi
hanyar da zata mai dasu kauyen Garul Aswar.
Koda ganin wannan abin da ya faru sai wadansu
mata guda goma sha hudu daga cikin wadanda aka
kamo a kauyen Garul Aswar suka fashe da kukan
bakin ciki. Wadanan mata ba wadansu bane face
iyayen su Humairu da yan matansu wadanda zasu
Aura.
Da farko da wadanan mata suka ga cewa sa'adda
wadannan samudawan mutane suka barko musu
mazajen nasu basa nan ba'a kashesu ba,sai suka
cika da murna duk da cewar sun san abune
mawuyaci su sake saduwa dasu,amma yanxu da
suka ga an tura a kashesu sai murna ta koma ciki,
suka cika da tsananin bakin ciki.
* * *
A can kauyen Garul Aswar kuwa, kamar yadda
Humairu ya ga gawar mahaifinsa ya rungumeta
yana kuka haka suma sauran abokan nasa shida
duk suka ga gawar iyayensu maza, suma suka
kama kuka cikin matsanancin bakin ciki.
Bayan sun dan jima ne a wannnan hali sai suka
mike tsaye gaba dayansu suka shiga neman matan
kauyen da sauran kananan yara, amma sai da suka
kewaye kauyen gaba daya ko mace daya basu gani
ba,kuma basu ga yaro ko daya ba.
Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsu kenan
suka tabbatar da cewa lallai kwashe su akayi gaba
daya aka tafi dasu.
Nan take duka suka fusata ainun, jikinsu ya kama
tsuma tsuma, saboda tsananin bakin ciki suka fara
tunanin daukar fansa.
Duk wanda ka kalli fuskarsa a cikinsu sai kaga har
tana yatsini saboda fushi,
Humairu ne kadai mai dan sauran nutsuwa a
cikinsu domin su ILsam ma kamar wadanda suka
zautu domin sun kasa zama sun kasa tsaye.
Koda ganin haka sai Humairu ya kira sunayensu
daya bayan daya duk suka zo gabansa suka
tsaitsaya.
Cikin nutsuwa ya dubesu yace, "Abinda nake so ku
fahimta shine, mu bakwai kacal bamu isa mu bi
wadanan mugayen mutane ba, mu yakesu har mu
karbo iyayenmu da masoyanmu, domin Sarkin yawa
ma yafi Sarkin karfi bare ma ga yadda wannan
mutum ya siffanta mana yanayin wadanan mutane,
karfi ma sun fimu, saboda haka ina mai
shawartarmu damu bi wadanan mutane Izuwa inda
suke domin muyi nazarin yawansu, karfinsu da
karfin sihirinsu ba tare da sun ganmu ba, sannnan
muyi tunanin hanyar da zamu bi mu karbo
mutanenmu a hannunsu ta hanyar hikima da dabara
koda kuwa ba zamu iya yakarsu ba.
Sa'adda Humairu yazo nan a zancensa sai Sahal,
Kaimur, Hashlar suka fusata ainun suka nuna cewa
yaushe za a tsaya wani bata lokaci ace sai an
tsaya nazarin wadanan mutane, ai kawai abi
sawunsu ba wani tsoro ko labiya a afka musu ko
su ko mu tunda sun gama cutar damu tunda sun
baje mana garinmu kuma sun kashe mana gaba
dayan mazajenmu, yanzu mune kadai mazajen da
basu mutu ba a wannnan kauye ".
Kaimur ne yayi wannan jawabi.
Koda ILsam yaji abinda Kaimur ya fadi sai Ya
fusata ya daka masa tsawa yace, "shin baka da
hankali ne ko kuwa ka sami tabin kwakwalwa ne?"
Ashe ka manta cewa tsawon shekara da
shekaru a iya tasowarmu Humairu ne yake bamu
shawara bisa duk abinda ya kamata muyi a duk
sa'adda wata matsala ta bijiro mana kuma muna
amfani da shawarar tasa a dace ba a taba
fuskantar rashin nasara ba.
Saboda me yanzu kakeson ka kawo mana rudani a
cikin al'amarinmu? "
Da jin haka sai Kaimur ya mike tsaye zumbur! Ya
zare takobinsa yayi kan ILsam a fusace shima
ILsam sai ya zare tasa takobin ya yiyo kansa yana
huci tamkar bakin kumurci.
Saura kiris su hadu su kacame da yaki sai Humairu
yai sauri ya shiga tsakaninnsu yace, "yanzu kuna
ganin fada da junanmu shine abinda zai warware
mana matsalar dake gabanmu?"
Koda jin haka sai jikin kowa yai sanyi, kunya ta
kama Kaimur da ILsam suka sunkui da kawunansu
kasa, har Humairu ya bude baki zai ce wani abu sai
suka ji kasa ta kama girgiza, ai kuwa suna dago
kawunansu sama sai suka hango wadansu giwaye
manya-manya guda uku sun durfafo inda suke a
guje.
Ashe karfin takun sawayen giwayen ne
Ya haddasa wannan girgizar kasa.
Ba giwayen bane suka firgita su Humairu ba,
mutanen dake kan giwayen sune wadanda suka fi
razanasu.
Wadansu irin girda-girdan mutane ne wadanda ko a
misalin mutanen farko masu ma su daban suke.
Saboda tsawon mutanen sai kaga kamar idan suka
mike tsaye kansu zai iya tabo sararin samaniya.
Kaurin kwanjinsu guda daya kamar an cure
mulmulan kasar gini guda arba'in a waje daya.
Gaba daya jikinsu a murde yake kuma cike da
damatsa da jijiyoyin kai da gani kasan cewa taurin
jikin nasu zai zo kunnen doki da taurin dutse.
Kai da gani ba tambaya kasan cewa baza a rasa
nono a riga ba.
Wato dole ne su kasance masu karfin Allah ya isa.
Dukkanin samudawan uku na rataye da wata irin
zabgegiyar takobi mai tsawo,fadi da tsinin gaske,
Wacce nauyinta yafi gaban daukar karti goma
majiya karfin gaske, amma samudawan ji suke
kamar kara suka goya a bayansu.
Tun sa'adda su Humairu suka hango wadanan
samudawan a guje bisa wadannan giwaye sai
dukkaninsu hankalinsu ya dugunzuma domin sun
tabbatar da cewa kawarda samudawan ba karamin
aiki bane.
Tun daga nesa samudawan uku suka zare
takubbansu suka wangame bakunansu suna masu
kwarara uban ihu,duk da cewa su Humairu sun
firgita da ganin wadanan samudawan sai suka dake
suka ki guduwa.
Lokaci guda suka kalli junansu su bakwan kawai
sai kowa ya gyara zaman makaminsa a hannunsa,
sannnan suka kwarara uban ihu a lokaci guda,
amma karfin sautin ihun nasu su bakwai bai kai na
basamude daya ba daga cikin wadanan samudawa
uku da suka durfafosu a guje.
Kawai sai suma suka rugo da gudun tsiya a jere
suka durfafi samudawan, inda mutum na nan a
tsaye a Lokacin da wannan abu ke faruwa da cewa
zaiyi su Humairu sun haukace domin yasan cewa
ajalinsu suka tara.
Yayin da ya rage baifi saura taku biyar ba giwayen
samudawan su takesu Humairu sai kawai
samudawan suka ga su Humairu sun daka tsalle
sama sun kawo musu wawan hari a sama, ai kuwa
suma sai suka maida martani.
Koda su Humairu suka fado kasa a bayan giwayen
sai dukkaninsu suka kasa mikewa tsaye.
Daga can sai Humairu ya mike tsaye shi kadai,
koda ya dubi sauran 'yan uwansa su shida sai
hankalinsa yayi...


Read / Download DUGUNZUMA 1 to 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album