Join Our WhatsApp Group

KARAGAR MULKI 1 to 4 Complete Hausa Novel Document by KARAGAR MULKI 1 to 4


KARAGAR MULKI 1 to 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 32743



KARAGAR MULKI 1 to 4

Reading Time: 2 Hours

Added On: 19, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 178.26 kb

File Type: txt

Views: 1931+

Download: 900+

Last download: 3 days ago

Description/Story: ¶KARAGAR MULKI¶
Littafi Na Daya (1) Part A.

Abdul'aziz Sani Madakin Gini.

A•Haleefah-Physicist.

¶A wani zamani can baya mai tsawo daya shude a kasar Hindu.Anyi wani gawurtaccen Sarki wanda ya shahara akan KARFIN MULKI da kuma karfin SIHIRIN TSAFI wanda masana da masu bincike suka tabbatar da cewar a wannan zamani babu wani matsafi daya kaishi karfin sihirin tsafi a duk fadin duniya. Komai ba jin dadin duniya Allah ya baiwa wannan Sarki wanda ake kira da suna Kanzal face rashin haihuwa.
A wajen mahaifinsu su tara ne kuma gaba dayansu maza ne babu mace ko daya. Sarki Kanzal shine DAN AUTA a GIDAN SARAUTAR. Lokacin da mahaifinsu ya kwanta ciwo sai gaba dayansu su Taran kowa ya kwallafa ransa akan Sarautar har ya zamana cewa suna ta kaiwa junansu hari domin su hallaka junansu.
Bisa dole kowannen su ya nemo hayar DAKARU na waje domin tsare lafiyarsa da rayuwarsa. Amma duk da haka saida kowannen su yasha BAKAR WAHALA ya kusan rasa rayuwarsa saboda MUGUN TANADIn da sukewa juna. Wadannan yan uwa guda tara suna yin tsananin gaba, babu wanda yake son yaga wani a raye.
Babu wanda yafi shan wahala a cikinsu sama da Sarki Kanzal domin a wannan lokacik shine mafi kankanta a cikinsu. Sau uku ana sassarashi ayi masa DUKAN KAWO WUKA ana zaton ya mutu, kai akwai lokacin ma da aka daddaure shi tamau da Igiya aka the sashi a cikin buhu aka kulle buhunwkuna aka jefashi cikin teku. Anna bayan sati biyu sai gashi ya dawo fada a raye. Duk jikinsa yasha dinki na saran takobi.
Koda ragowar yan uwansa su takwas suka ga Kanzal a raye sai suka firgice kuma suka kamu da tsananin mamaki saboda a gaban idanunsu aka sassarashi aka sashi a ckkin buhu aka jefa shi a teku.
A wannan rana ne da Kanzal yazo fada ya iske mahaifinsu ya mutu kuma ya iske za'a fara gabatar da GASAR HAWA KARAGAR MULKI a tsakanin Yayyansa su takwas, dama a wannan lokaci hankalin fadawansa Sarki wato yan majalisa masu zaben sabon Sarki a tashe yake saboda tsawon sati uku ana neman Yarima Kanzal ba'a ganshi ba kuma ko duriyarsa ba'a ji ba. Tuni a wannan lokaci ya zamana cewa Mahaifiyar Yarima Kanzal ta saduda cewa an kashe danta duk da cewa ba'a ga gawarsa ba. Sai tayi ta kuka DARE DA RANA har ma tasa aka shirya bikin mutuwarsa.
Da gawa daga cikin yan majalisar kasar Hindu sunfi son ace Yarima Kanzal ne ya zamo Sarki saboda shi kadai ne yayi gadon mahaifin nasu a halaiya ta kirki. Kanzal yana da tausayi, jin kai da taimakon talakawa sabanin ragowar yan uwan nasa wadanda babu abinda ya shige musu gaba face MULKI, DUKIYA da kuma ZALUNCI. Shi kansa mahaifinsu Yarima Kanzal tun yana da rai ya nuna tsananin Soyayyarsa akan Yarima Kanzal saboda kyawawan halayensa kuma yafi son ace shine ya gaje shi amma saboda dokar MASARAUTAr itace Sarki bashi da ikon bayar da karagar ga wani 'da nasa face anyi gasa. Dole ya hakura da batun bawa Yarima Kanzal karagar.
A ranar da Sarki zai mutu ma yini yayi yana kuka gami da ambaton sunan Yarima Kanzal saboda bakin cikin rashin ganinsa. Al'amarin da yasa ciwon nasa ya kara tsamari kenan har zuciyarsa ta buga sanandin ajalinsa.
Lokacin da Yarima Kanzal ya shigo cikin fadar birnin Hindu a lokacin da fada ta cika ta batse babu masakar tsinke saboda yawan bil'adama sakamakon anzo kallon 'DAN SARKIn da zai lashe gasar hawa karagar mulki.Sai fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta.Ba komai yasa fadar tayi tsit ba face ganin shigowar Yarima Kanzal cikin fadar tare da wata Mace JARUMA a cikin shigar YAKI wacce ke sanye da fararen tufafi Tana take masa baya. Ta rufe fuskar ta da farin rawani idanunta kadai ake gani kuma ta rataya wata zabgegiyar takobi a bayanta, babu wanda ya taba ganin wannan Jaruma a NAHIYAR gaba daya don haka mamaki biyu jama'a sukeyi. Musamman ma yan uwan Yarima Kanzal.
Mamaki na farko shine ganin Yarima Kanzal a raye. Tunda kowa ya dauka cewa ya mutu. Mamaki na biyu kuma shine na ganinsa da wannan bakuwar Jaruma kuma a Ina Yarima Kanzal ya samota.
Wannan sune tambayoyin da gaba dayan mutanen dake cikin fadar suke yiwa kansu a cikin zukatansu Amma kuma babu wanda ya iya baiwa kansa amsa. Bayan kowa ya mike tsaye a cikin fadar sakamakon ganin Yarima Kanzal an kama kallon kallo a tsakanin Yarima Kanzal da yan uwansa guda takwas sai Kanzal ya durfafi inda alkalan gasar suke fuskarsa cike da murmushi. Koda yazo daf dasu saiya risina ya gaishe su cikin girmamawa yace Ubangijinmu Zakur ya dawo dani gida lafiya bayan batana na tsawon sati uku, gashi na dawo daidai ranar da za'a fara wannan gasa don haka maimakon ayi gasar ta tsawon kwana takwas sai a kara kwana guda ya zamo kwana tara. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube gaba dayan jama'ar dake filin fadar, kalilan daga cikin yan majalisar tare da 'ya'yan Sarki su takwas ne suka kamu da tsananin bakin ciki gami da takaici saboda tsananin mamaki da firgici na ganin Yarima Kanzal, basu san sa'adda gumi ya fara karyo musu ba. Take shugaban alkalan gasar ya mike tsaye wanda shine Wazirin Marigayi Sarki ya dubi jama'a fuskarsa cike da annuri yace yaku mutanen kasar Hindu kuyi sani cewa Ubangiji Zakur ya dawo mana da Yarima Kanzal lafiya bisa batan da yayi na tsawon sati uku don haka lallai shima yanzu ya shigo wannan gasa. Koda jin haka sai fadar ta rude da shewa gami da tafi aka shiga yiwa Yarima Kanzal kirari ana kodashi anace masa MURUCIN KAN DUTSE baka fito ba saida ka shirya. Wasu kuma suma rinka cewa dashi lale Marhaban da gagarau, kangarau, kai haka akayi ta yiwa Yarima Kanzal kirari iri iri ya zamana cewa fadar ta rude da hayaniya har saida Waziri ya daga hannu ya daka tsawa sannan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta. Waziri yayi gyaran murya yace kamar yadda kuka sani yanayin wannan gasar shine ana yiwa kowane dan Sarki tambayoyi ne guda goma akan ILMIN MULKI da sha'anin harkokin kasa dake tafe. Idan har ya amsa tambayoyin dai dai ya haye zagayen farko na gasar kuma zagaye uku kadai akeyi.A zagayo na karshe ne za'a fitar da zakaru biyu su amsa tambayoyi na karshe wanda duk ya amsa tambayoyin dai dai bai fadi ko guda daya ba shine zai zamo Sarki gaba daya. Tambayoyin za'a yi ne guda dari ba daya kuma kowanne Yarima da kansa zai zabi lambar tambayar da za'a yi masa. A cikin tambayoyi goma da za'a yiwa Yarima a zagaye na farko idan ya fadi a tambaya daya koda kuwa ta farko ce to ba zai shiga zagaye na biyu ba, don haka kowane Yarima saiya kula da kyau kuma ya nutsu sosai don kada ya amsa tambaya ba daidai ba. A kullum mutum biyu za'a yiwa tambayoyi don haka yanzu za'a ajiye lambobi a cikin akushi, lambobin guda tara ne maimakon takwas amma wadanda zasu sami damar amsa tambayoyin yau zasu dauko lamba ta farko ne ma'ana mutum biyu da suka dauko lambar daya sune zasuyi gasa a yau. Koda waziri yazo nan a zancensa saiya daga hannunsa ya yiwa wani hadimi inkiya take wannan hadimi ya shigo tsakiyar filin fadar dauke da akushi rufe ya ajiye gaban alkalan gasa. A cikin akushi an sanya wadansu dunkulallun takardu guda tara. Nan take aka umarci yayan SARKIn su tara dasu zo daya bayan daya su zabi lamba. Nanfa idanun yayan sarkin ya zazzaro kowannensu hankalinsa ya tashi zuciyoyinsu suka fara bugawa da karfi saboda kowannen su a cikin fargaba yake, idan har zai dauko lamba daya, babban abin fargabar shine zai iya amsa tambayoyi guda goman da za'ayi masa a yau? Idan ya fadi tambaya daya jal daga cikin goman ya fita kenan daga cikin gasar bashi ba hawa KARAGAR MULKI saidai waninsa. Gaba daya ya'yan sarki su tara suka nufi inda wannan akushi yake sai suka far noke noke suna jajja da baya mutum biyu ne kadai daga cikinsu suka durfafi inda akushin yake ba tare da shakkar komai ba. Ba wasu bane face dan autan cikinsu Yarima Kanzal. Shidai Yarima Kanzal mutum ne mai tarin ilmi akan karatun sarauta ta kasar har dama ta sauran kasashen dake makota don tun yana da shekara biyar a duniya ya haddace Littattafai na tarihin sarautar kasar kuma daya shekara goma sha daya sai ya bazama izuwa sauran kasashen dake nahiyar yana neman ilmi akan MASARAUTAr saboda yin tanadin wannan rana. Tunda Yarima Kanzal yabar gida bai dawo birnin Hindu ba sai bayan shekara tara a sannan ya cika shekara ashirin daidai a duniya. A wannan lokaci an zata ya hallaka a wani wuri cikin YAWON DUNIYAr tasa amma sai gashi ya dawo gida a cikin gagarumin shiri na neman Sarauta saida ya zama gawurtaccen matsafin da babu kamarsa a nahiyar. Yana sauka a gida ya far nunawa mutane abubuwan AL'AJABI na sihiri kuma ya rinka bayar da labarai na sihiri iri iri wanda tsofaffi da masana tarihi ma na kasar basu San dashi ba. Wannan al'amari ne ya tayar da hankalin sauran yan uwan Yarima Kanzal su takwas. Ba shiri suma suka bazama cikin duniya don neman ilmin da Yarima Kanzal yaje ya samo. Yarima Kanzal ne kadai bai tafi neman wannan ilmi ba. Sai ya zauna a gida ya cigaba da yiwa mahaifin sa hidima a lokacin baifi shekara tara ba. DARE DA RANA Yarima Kanzal na tare da mahaifinsa kai hatta Kwanciyar baccin ma bata raba su, saboda tsananin shakuwa saida takai cewa hatta abincin da abin sha wanda Sarki zaiyi amfani dasu Yarima Kanzal ne ne dafawa da shirya su saboda yadda idan kuwa wani ya kawo Sarki bazai ko kalle su ba.
Matan Sarki su goma sha daya ne saida suka zamo basu da kishiyar da tafi mahaifiyar Yarima Kanzal. Babu wacce take kaunar Yarima Kanzal a ciknsu face mahaifiyarsa Lamisa. A cikin matan Sarki akwai wacce bata taba haihuwa ba ana kiranta da JALILA. Jalila ta kasance amaryar Sarki don haka itace matar da Sarki ya aura a karshe kuma itace mafi kankanta a duk cikin matan na sarki domin shekarunta sun haura sha takwas. Jalila ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance kuma a wannan lokaci da shekara uku kacal Yarima Kanzal ya girme ta. Asalin mahaifiyar Jalila Sarki Kairus ya baiwa mahaifin su Yarima Kanzal auren Jalila ne ba don komai ba sai saboda tsohon wani buri dake karkashin zuciyarsa wanda ya gagari iyayensa da kakanninsa cikawa. Burin kuwa shine a cikin yankin kasar Hindu akwai wani SIHIRTACCEN KOGI wanda ba'a shiga Cikinsa domin Su ko debo ma'adanan kasa dake karkashin sa sana da shekaru dari uku baya ko tsuntsu ne ya shiga cikin kogin take zai mutu. Babu daga inda ba'a gaiyato bokaye ba domin su karya asirin da yake kashe mutane da dabbobi da tsuntsaye a cikin wannan kogin amma abu ya gagara. Gaba daya sarakunan da suke mulki a kasar Hindu sun kasa gano asalin wanda ya sihirice wannan kogi bare su sami hanyar da zasu Karya asirin don haka bisa dole aka kewaye kogin kuma aka rufe shi aka hana kowa da komai rabarsa domin sama da dakaru Dubu uku ne suke gadin wannan kogi.kafin a asirce kogin masana albarkatun kasa sun gano cewa inda za'a shekara dubu ana hako dukiyar dake cikin sannan kogi ta nau'in Zinare da lu'ulu'u ba zata kare ba duk sarkin daya hau KARAGAR MULKI a birnin Hindu da wannan bakin ciki yake mutuwa na rashin samun damar debo wannan dukiya dake cikin kogin wanda aka yiwa lakabi da BAHAR LAHIRAM. As he ba wani bane ya asirce wannan kogi ba ba bahar Lamiram face Kakan Gimbiya Jalila na hudu. A dalilin kogin yayi yaki da kasar Hindu sau tara domin ya sami damar shiga kogin ya debo dukiyar dake ciki amma bai sani nasara ba saboda duk sa'adda akayi yakin KARE JINI BIRI JINI akeyi saidai ya hakura bisa dole ya hada ragowar MAYAKANsa ya koma gida. Bayan anyi yaki na taran ne wanda shine na karshe sai CIWON ZUCIYA ya kama Sarkin Kasar Ramhaz ya kwanta CUTAR AJALI. Kafin ya mutune ne ya baiwa Hadimansa dukiya mai yawan gaske suka bazama a duniya neman bokan da yafi dukkan bokayen duniya KARFIN SIHIRIn Tsafi. Saida suka shekara shida suna yawo a duniya sannan suka riski wani boka wanda ake kira da suna Daibul Usara. Wani akasi da sukayi shine Hadiman sun riski Boka Daibul Usara shima a kwance yana kan cutar AJALI, bayan sun gabatar da bukatar sarkin nasu ga boka Daibul Usara kuma suka ajiye masa jakunkunan Dinare manya guda tara a gabansa sai boka Daibul Usara ya yunkura da kyar ya mike zaune ya leka cikin jakunkunan kudin. Koda yayi arba da makudan Dinaren da aka kawo nasa saiya bushe da dariyar farinciki daga can kuma saiya fashe da KUKAN BAKIN CIKI.Al'amarin dayai matukar baiwa Hadiman sarkin mamaki kenan har daya daga cikinsu ya dube shi yace Ya kai Mafificin Bokayen Duniya Ina dalilin wannan KUKA DA DARIYA taka duk a lokaci guda haka? Sa'adda Boka Daibul Usara yaji wannan tambaya sai ya kawo gwauron Numfashi ya ajiye sannan ya dubi hadimin da yayi nasa wannan tambaya yace...............

Abubakar Haleefah physicist.

Via:-Triple Abubakar Hausa Books
KARAGAR MULKI
LIttafi Na Daya(1) Part B.

™Abdul'aziz Sani Madakin Gini.™

A•Haleefah--Physicist

*Sa'adda Boka Daibul Usara yaji wannan tambaya sai ya kawo gwauron Numfashi ya ajiye sannan ya dubi hadimin da yayi masa wannan tambaya yace, ba wani abu bane ya sani wannan dariya ba face ganin na mallaki adadin dukiyar dana dade ina mafarkin mallakarta amma ban samu ba sai yau. Duk da cewa nafi kowa karfin sihirin tsafi a wannan nahiyar. Dan gane da dariyar da kaga inayi kuwa Ina farin ciki ne akan zan mutu na bar wani abu guda daya wanda zai gagari gaba dayan sarakunan da za'a yi a kasar Hindu, har kasa ta nade babu wani Sarki daya isa ya amfani dukiyar dake cikin karkashin kogin Bahar Lihiram duk duk bakin cikin hakan zai rinka zama sanadin Ajalin Sarakunan. Ku sani cewa a cikin binciken da nayi a duk fadin duniya babu inda yafi kasar Hindu yawan dukiya ya Zinare, Lu'ulu'u da Jauhari kuma kaso ba saba'in na wannan dukiya tana cikin karkashin kogin Bahar Lihiram. Ni ma babu yadda banyi ba akan na debo wannan dukiya amma abu ya gagara har dakarun aljanu na tura izuwa Kogin amma sun kasa dauko Koda Dinare daya saboda karfin sihirin aljanun dake rayuwa a cikin kogin na Bahar Lihiram. Tunda dai...


Read / Download KARAGAR MULKI 1 to 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album