Join Our WhatsApp Group

SIHIRTACCIYA 1 AND 2 Complete Hausa Novel Document by SIHIRTACCIYA 1 AND 2


SIHIRTACCIYA 1 AND 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22462



SIHIRTACCIYA 1 AND 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Ismail Abdullahi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 122.32 kb

File Type: txt

Views: 1385+

Download: 371+

Last download: 8 days ago

Description/Story: 






SIHIRTACCIYA
.
Littafi Na Daya 1 part A
.
author:abdul,aziz sani m/gini
.
TYPING:goni a abubakar
.
POAT: REAL PRINCE RAYYANU
.
Kasar manohar ta kasance mai girma wanda
tana dauke da mutane sama da milyan dari
biyar ta kasance mai tarin arziki wanda
awannan zamanin samun kasa kamarta sai
antona wata hamshakiyar sarauniyace ke mulki
akasar anace mata sarauniya YAXRINA a kalla
zatakai shekara sittin amma bata taba yin aure
ba shahararrun matsafa na duniya sun tabbtar
da cewa duk ranar da sarauniya Yaxrina ta
kwanta da wani da namiji to tarihin kasan zai
karya zakuma su shiga cikin masifu da bala o i
daban daban wanda a karshe sai sun fi kowa
talauci a duniya wannan daliline yasa
sarauniya Yazrina tacire aure a ranta gaba
daya tana gudanar da mulkinta cikin adalci da
tausayi shi yasa talakawan kasan na mutukar
son ta har suna jin za su iya bada ransu sabo
da ita mutanan kasar Manohar sun kasance
suna bautama wata kyakykyawar gunkiyace
wanda suke kiranta da suna makarbiya wannan
gunkiya tana da mutukar girma da daraja
agaresu hakika sunyi imani itace take basu
komai sabo da koyaro karami bai kaunan
wanda baison gunkiya manuniya
.
Sarauniya Yaxrina tana da wani kani mai suna
SAMAR wanda kuma shine sarkin yakinta
cikakkaken jaumine nagaban kwatance domin
duk girman kasar manohar babu mai iya kaishi
kas sunyi mutakar shakuwa da juna wanda
takai in ba barci ba ba abin dake rabasu kai ko
barcin ma wataran a dakin sarauniya yake
kwana domin sau da yawa inya shiga dakin
sarauniya suna hira idan barci ya kwashe shi
maimakon ta tashe shi sai kawai ta dora shi a
gado sai da safe.
.
Watarana fada ta cika tayi makil ana fadanci
sai gawani jarumi yashigo fada ya nufi gurin
sarauniya dakaru su tare shi yace nidan sakone
ya mika musu takarda suka karba suka
mikama saraniya Yazrina tamikama maga
takarda shi kuma yafara karanta takarda
kamar haka.
Daga sarki JUNDARU na birnin Bangus hakika
na sami labarin sarauniyarku bata da aure to
tasami miji lallai in kunaso kutsira daga
mutuwa to lallai kugama shiryamin amaryata
nan da wata uku zanzo indauketa idan kukaki
to lallai zan rushe birninku inkashe maxajenku
kuma in kame matayen ku amatsayin bayi
kuhuta lafiya daga sarki Jundaru mai duniya
na birnin bangus.
Koda mutane sukaji abinda ke cikin wasika sai
fada tarude take wasu suka fashe da kuka kai
hatta sarauniya Yazrina sai da takama zubar
da hawaye bawani abu bane yasa mutanen
kasar Manuhar rudewa face sanin wanene sarki
jundaru mai duniya na brinin bangus wani
hatsabibin mutumne wanda gaba daya ya
gallabi duniya gagararrene tun yana dan
shekara goma yazama rikakken dan fashi
wanda in yaje fashi saidai yashigo gari da
rundunan sa yafarma mutane da sara tun yana
yaro ba ataba galaba akansa ba lokacin daya
girma yakai kimanin shekara ashirin sai ya
tunkari kasar Bangus da yaki wanda alokacin
duk duniya itace na daya ayawan jarumai da
kuma iya yaki a tarihi babu wata kasa data
taba nasara akansu saboda haka kusan sune
suke juya manyan sarakuna duniya amma
Jundaru yatunkari kasar da mayaka dubu
goma akayi wata guda ana zuba yaki gaba
daya sai da dakarunsa suka kare amma shi sai
da akwana uku ana dauki badadi dashi wanda
arana na hudune Jundaru yai nasaran sare kan
sarkin kasar Bangus kuma ya kashe sarkin
yakin garin ya zamar musu kamar aljan kashe
mutane yake kamar kiyashi bisa tilas suka
mika wuya ya zama sarkin Bangus tun daga
haka sarakunan duniya suka masa mubaya
indai yaga mace yanaso tokuwa zai aikone
kushiryata zai zo yadauketa rana kaza inko
kukaki to kasar garimma bazatai kyan gani ba.
Ranar da majalisar kasar Manuhar taxauna
akan yadda za afitoma lamari majalisa tarikice
wasu nacewa amika saraniya ga sarki Jundaru
wasu nacewa bazai yuwuba domin ko an
mikata ba atsiraba tunda mutukar sarki
jundaru yakwanta da ita to sai nasifata rufto
makasar manuhar nan gardama tasarke ana
neman aba hammata iska Samar wato sarkin
yaki kuma kanin sarauniya Yaxirina ya
takarkare yakwarara wani wawan ihu gaba
daya majalisa tai tsit sannan ya fara magana
yace tabbas mun shi ga tsaka mai wuya in mun
bada sarauniya bala i yabiyo baya in muka
hana masifa tazo ta samemu yace to akwai
mafita guda daya tak sukace wace mafitace
Samar yace sai dai mutashi SIHIRTACCIYA
WATOGUNKI MANUNIYA gaba daya majalisan
babu wanda bai mikeba gami da kokarin
ficewa daga majalisan
Wannan .SIHIRTACCIYA Part 2
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini
Lokacin da Samar ya ga yan majalisa na kokarin watsewa
sai ya takarkare ya kwarara ihu wanda tasa dole yan
majalisa suka tsaya cak kamar an hura musu usur sai
suka juyo sukai ido biyu da samar ya dube su ya daga
murya yace wato mutuncin kasar namu kuke so mu
mikata a banza to ku sani idan duk duniya zata taru babu
wanda ya isa ya dauki yar uwata ya mika wani wawan
sarki ya mai da ita baiwa to sai dai inna mutu.
.
Gaba daya yan majalisa suka dawo suka zauna daya
bayan daya Samar ya kare musu kallo sannan yayi
murmushi yace shuwagaban nina ina mai tabbatar muku
indai har zaku mika gimbiya Yazrina to ku shirya shirin
yaki da ni ya juya zai fita shugaban yan majalisa ya kira
shi cak ya tsaya sannan ya juyo ba tare da yayi magana
ba cikin takama da nuna izza ya tako yazo ya tsaya a
gaban yan majalisa shugaban majalisa ya dube shi yace a
matsayinka na dan gidan sarautar kasar nan zaka iya gaya
mana wacece sihirtacciya
.
Samar yayi gyaran murya yace shekaru dari uku da
hamsin da biyu a wannan kasa na Manuhar anyi wani
gawurtaccen sarki mai suna Maridu shi wannan sarki ya
sha hare hare a duniya domin a zamaninsa babu wata
kasa da takai kasar Manuhar tarin arziki da yawan jama a
da kwanciyar hankali sarki maridu yana da wasu kannai
tagwaye Sarbilu da Sarbila waɗan nan kannan sarki
maridu sun kasance yan gata kuma yan lele a kasar
Manuhar Sarbilu kwata kwata bai da jarumta kuma sam
baya sha'awar koyan fada duk da yana da zubin jarumai
sabanin yar uwan sa Sarbila wanda ta kasance zakakuran
jarumai indai har za a lissafa jarumai to dole za asa da ita.
A can kuma kasar Dulima wani
hamshakin bokane wanda yasha alwashin sai ya mayar
da duniya an koma bauta masa yayi rantsuwa da kakansa
bazai bar wata kasa tazauna lafiya ba matukar ba su karbi
bautan gunkinsa ba boka Kalibu bn kalab ya shafe sama
da kasa arba'in gaba daya ya ruguza abubuwan bautansu
ya gina katon gunkinsa a kasashe da yawa idan boka
kalibu yazo zai yaki gari to mika wuya kawai sukeyi domin
sun yi imani ko sun futo agabza yaki to dai dole zasuyi
biyayya bayan an kashe musu mutane wannan ne yasa
ake kiransa da boka karibu da gagara badau.
.
Kwatsam boka Karibu da tawagarsa na aljanu da mutane
ta sauka a bayan garin Manohar boka karibu ya rubuta
takarda zuwa ga sarki maridu ni boka karibu gagara
badau na sauka a bayan garinka ina mai umartanka da ka
dauko abin bautanku kai da jama arka ku futo bayan gari
ku rusashi a gabana sannan ku konashi in baku gunkina
kuci gaba da bautamin in kukayi haka kun kubuta daga a
zabata lallai kuyi nazari kuna da yaya kuna da mata kuna
da tarin dukiya to kusani bjiremin yana nufin kun sallama
yayanku da matanku da dukiyarku da rayukanku gaba
daya koda sarki maridu ya samu sakon Boka karibu sai ya
rude ya tara mashawartansa gaba daya sun rude kai tsaye
suka amince da a dauki gunkinsu abin bautansu mai
tarihi a kai gaban boka karibu a kona amika wuya koda
jin wannan batu sai jaruma sarbila ta takarkare ta
takwarara ihu wanda
daukacin kasar Manohar sai da suka ji tai zarya ta zare
takobi tace narantse da kasata babu wanda ya isa ya
dauki abin bautana ya rusashi in har ina
nunfashi tabbas zaku iya mikashi amma sai bayan mun
gabza yakin cikin gida in kun kasheni to sai ku mika in
kun kasa to ya zama dole kubini ta daga murya tace
tabbas nasan karo da boka karibu masifane amma zan
tunkareshi koda zai hallakani to sai na bar masa abin
fada.
Sarki maridu zaiyi magana ta daga mai hannu tace in har
mutum ba zai goyamin baya ba to kada ya kuskura ya
samin baki gaba daya a kawatse ana mata kallon ta
haukace ita kadai ta rage a wajen sai dan uwanta sarbilu
ya ruga da gudu yaje gaban ta yace
yake yar uwata hakika ni ban kasance jarumi ba amma
ina da karfin zuciyar da zan biki wannan yaki koda zan
halaka Sarbila ta dubi dan uwanta
tayi murmushi sannan tajawoshi ta rungume tana cewa
tabbas za muyi nasara gobe ni dakai sai mun barma
duniya babban labari lallai zamu kafa
tarihin da sai jaruman duniya sun sara mana
Zan cigaba insha Allah
Admin Goni S Abubakar
SIHIRTACCIYA Part 3
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini
Gari na wayewa Sarbila ta kama shiri ta sanya wata farar
riga da wando wanda aka sana annta ta da gashin farar
damisa ta daura fatan zaki a kanta ta dibo wasu kananan
wukake zasu kai hamsin ta shiga ɗanasu a damararta kaf
sai da kowacce wuka ta samu wurin zama ta dibo wasu
kana nan adduna guda biyu ta soke a kugunta hagu da
dama ta rataya takobi a kafadanta sannan ta makale wasu
kana nan gatura guda biyu a gadan bayan ta takalli
sarbilu yayi mata jinjina kawai sai tayi waje sarbilu ya
take mata baya duk inda ta ratsa acikin gari sai mazaje su
sunkuyar da kai kasa.
Ta isa kofar futa dakaru suka bude mata tayi waje ita da
sarbilu aka kulle
kofa. Abin mamaki boka karibu ya dube ta ya daka mata
tsawa yace ke yarinya ina sauran jama ar gari da sarkinku
da kuma abin bautanku Sarbila ta daka mai tsawa tace kai
bakin azzalumi lallai kasani ni ba yarinya bace kuma zan
tabbatar maka da hakan sarkina da abin bautana sun fi
karfin su zo su amsa gaiyatarka kayi kadan nine dai dai da
kai yaro wayyo boka karibu yaji kaman sarbila ta
watsamai wuta ya takarkare ya kwarara ihu sannan yace
bana son takara dake daya a duniya.
Tuni wani yanki daga cikin dakarun boka karibu sunyo
kanta sarbila taja da baya tayi taku uku kawai sai ta zaro
kananan wukaken nan guda hudu
ta watsa su wukaken suka farma dakarun nan sai da suka
caki sama da mutum talatin sannan wukaken
suka koma hannun Sarbila ta cukesu adamararta tayi
kururuwa tazare adduna guda biyu ta falfala da gudu ta
daka tsalle ta fada tsakiyan mazaje.
Nan fa yaki ya kullu masifa ta tashi karan takubba ya
gauraye wajen ta shiga farke cikin maza tana datse
kawunan su nan fa jini ya fara malala dakaru sai
tuttudowa sukeyi ita kuma tana ajalinsu ta zamar musu
alakakai ta addabesu ba mutun ba aljani.
.
Shi kan shi boka Karibu sai da zuciyarsa ta buga ganin
yanda Sarbila ke sama da mutane da
Sai da suka dauki sa'a shida ana fafata yaki tsakanin
jaruma Sarbila da dakarun boka Karibu gawarwakine
kwance kamar an hake gyada mai yaya, kura tayi sama ta
mamaye sararin samaniya ba a ganin kowa sai kura sai
sautin haduwan karafa can komai yayi shiru bakajin koda
motsi
sannu ahankali kura ta lafa duhu ya yaye.
Kawai sai ga sarbila a tsaye tana layi jiri na dibanta
saboda gajiya amma kuma ilahirin jaruman nan ta aikasu
kiyama ko ina ajikinta jini ne ke zuba kamar hawaye
ganin haka boka karibu ya kwarara ihu ya zaro takobi
yayi kan sarbila a guje da mugun nufi.
Ganin haka sarbilu ya daka masa tsawa cak boka karibu
ya tsaya sannan ya dubi sarbilu yace to kai
da ba jarumi ba meye namin tsawa kabari in kashe
jaruman daga nan sai in dawo kanka sarbilu ya fashe da
dariya ya dubi Boka karibu yace aikai ma ragon ne domin
ka kasa nuna jarumtanka ga yar uwata sai da tayi yaki
sama da mutum du arba in ta gaji shine dan lalaci zaka
afka mata da yaki.
Take boka karibu ya watsar da makamansa ya nuna
sarbila da yatsa yace lallai dan uwanki ya ceci rayuwarki
da kalamansa kije kiyi jinya na wata biyu a sannan ne zan
fuskan ceki gaba da gaba dan in nuna ma dan uwanki
nacika sadauki uban mazaje kawai sai boka karibu bn
kalab ya bace sarbilu ya ruga da gudu ya rungume sarbila
suka fashe da kuka.
Labarin jarumtar sarbila ya cika
duniya ana ta fadin wata jaruma ta kada boka karibu
wannan labari ya ba tama boka karibu rai inda yayi na
dama rashin kashe ta sarbila gashi
yanzu shi da yake so sunansa ya gauraye duniya sai ya
sami tozarci da nakasa ita kuma Sarbila sunanta ya bazu a
duniya yan mata da kananan
yara har waka suke mata.
Wannan abu sai da Boka karibu yaji kamar ya kashe
kansa dan haushi amma sai yasha alwashi indai suka sake
haduwa to sai ya mata kisan wulakanci irin kisan da a
duniya baza ta taba manta shiba
Zan Cigaba Insha Allah
Admin Goni $ AbubakarSIHIRTACCIYA Part 4
Littafi Na Daya 1
Marubucin Littafin
Abdul aziz sani m/gini.
Al amarin jaruma sarbila da dan uwanta Sarbilu sai
yarugume ta suka koma gida koda suKa shiga gari sai
jama a suka fara taransu da murna take sarbilu ya daka
musu tsawa ya ɗaga murya yace narantse da yar uwata
sarbila duk wanda yayi gangancin matsowa kusa da mu
to
lallai sai na kashe shi kun kasa futa yaki saboda tsoran
mutuwa yanzu kun ga mun dawo shine zaku dau murna
ko to ku sani lallai babu wani maha lukin da zai zo kusa
da yar uwata ni kadai zanyi jinyarta sai da yayi sati yana
mata magani sannan ta watsake kuma har ta warke bai
taba magana da Dan uwansa ba wato sarki maridu
haka ita sarbilatu data warke sai taci gaba da ba kanta
horan yaki takara kwarewa da zama hatsabibiya.
Akwana a tashi har wata biyu da boka karibu bn kalab ya
diba ma Sarbila suka cika tun da dare take shiryawa tayi
shiga irin ta manyan sadaukai tayi juguf acikin kayan yaki
tun asubahi aka din ga jin wasu mahaukatan saututtuka
da zantuttuka irin na surkulle sannan ana kyakyata dariya
wata kakkausan murya tana cewa hakika yau mutanen
kasar manohar bala i da musifa ta afka musu kuma ba
kowa ya jawo muku ba sai yar ku jaruma sarbila ina
umurtanku gaba dayanku mazanku da matanku yara da
kankananku da ku fita bayan gari an shirya filin gasa inda
ni Boka karibu bn kalab zan fafata yaki da jarumarku
jaruma sarbila lallai rayuwarku na hannunta in tayi
nasara to kun tsira idan ko nayi nasara wayyo lallai kusani
zan dandana muku azaba kala kala ta yadda kowane
dayan ku sai ya mutu sau goma maza kufuto
dan kallan yadda zanfara wulakanta jarumarku.
.
Kai tsaye ja ama ar kasar manohar suka fara futa bayan
gari sun sha mamaki ta yadda suka ga an shata fili
ankawata shi dakujeru wanda yan kallo zasu zauna abin
mamki shine duk wani sarki da ka sani ya tun batsa a
duniya to yana gurin shi da jama arsa suka zauna a inda
aka tanada dominsu ga kuma mutane bila adadin ba iya
ka sai ihu sukeyi wasu kuwa tuni sunbude filin kasuwanci
jama a inda kasan antara mutanen duniya mutanan kasar
Manohar antaja musu gurin zama na musamman suka
samu wuri suka zauna hankalinsu a tashe
domin sun san an shirya musu wulakanci maigirma a
wannan rana saboda haka kowa ka gani afilin
yana murna amma banda mutanen kasar manohar.
.
Shi ko sarki maridu yayan sarbilu da
sarbila tunda ya zauna ba abinda yakeyi sai kuka domin
ya tabbata yaune ranar karshe na rayuwan yan uwansa
agefe guda kuma yana tunanin irin wulakanci da kaskanci
da zai fuskanta a wajen boka karibu ibn kalab.
Kwatsam sai akaji wani ihu da kururuwa daga sama nan
take kallo ya koma sama aiko sai aka hango boka karibu
bn kalab yana sauko wa daga sararin samaniya ran shi
abace take
guri yagauraye da ihu da kuma sowa harda tafi inda wasu
suka tashi ganguna aka kama rawa sannu ahankali boka
karibu ya sauko ya dira afilin da aka tanada dan fafatawa
jama a suka kaure da ihu harda tafi suna tsalle inda
mutanen kasar manohar suka fashe da kuka domin sun
tabbatar mutuwarsu tazo.
Boka Karibu ya kwarara ihu gaba daya...


Read / Download SIHIRTACCIYA 1 AND 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album