Join Our WhatsApp Group

MUTUM DA ALJAN 1 to 6 Complete Hausa Novel Document by MUTUM DA ALJAN 1 to 6


MUTUM DA ALJAN 1 to 6

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 37820



MUTUM DA ALJAN 1 to 6

Reading Time: 3 Hours

Added On: 17, Sep 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 206.68 kb

File Type: txt

Views: 1235+

Download: 621+

Last download: 5 minutes ago

Description/Story:
MUTUM DA ALJAN!!!
Littafi Na Daya (1)
Complete book 1
Typing Suleiman Zidane Kd.
Whatsapp 09064179602
A WANI ZAMANI CAN BAYA MAI TSAWO daya
shude,anyi wani gawurtaccen sarkin Aljanu mai
suna MASARUL ANJANA.Sarki Masarul Anjana
yana mulkin wata babbar kasa ne mai suna DILHAR
wacce ke can karshen birnin SIN.Duk wata
daukaka ta duniya babu wacce sarki Sarki Masarul
Anjana bai samu ba walau ta DUKIYA,KARFIN
MULKI,JARUMTAKA,GIRMAN KASA DA TARIN
'YA'YA,yana da MATAN AURE guda DARI UKU DA
SITTIN,'ya'ya kuwa sai da aka haifa masa guda
DUBU DAYA DA DARI HUDU amma cikin iko na
ALLAH sai ya zamana cewa duk shekara sai
'ya'yan nasa kimanin dari da wani abun sun mutu
kuma basa yin wata doguwar jinya ta rashin lafiya
sai rai yayi halinsa.Abu dai kamar wasa sai 'ya'yan
nasa suka cigaba da mutuwa da daidai har saida
ya zamana cewa saura guda daya jal wacce ta
kasance itace 'YAR AUTANSU ana kiranta da suna
ZULFULAIFA.Zulfulaifa ta kasance kyakkyawar
budurwa ta gaban kwatance domin tun tana jaririya
da aka haifeta sai labarin ya bazu a ko ina a cikin
duniya a kasashen bil'adama saboda tsananin
kyawunta yafi gaban kwatance,tun a sannan ne
sarki Masarul Anjana ya dauki son duniya ya
dorawa Zulfulaifa ya zamana cewa dare da rana
yana tare da ita baya yarda ta gusa daga kusa
dashi kuma ko kuda baya son yaga ya sauka a
jikinta,kai ko ciwon kai sarki Masarul Anjana yaga
Zulfulaifa nayi tofa sai an tara gaba dayan likitocin
garin a kanta,wanda duk ya bata maganin data
samu sauki nan taje tofa shi kakarsa ta gama
yanke saka,domin za'a bashi dukiyar da tattaba
kunnensa ma basu isa su iya karar da ita ba.Idan
kuwa likita yayi kuskure ya bata maganin daya
wahalar da ita HUKUNCIN KISA ya tabbata a kansa
har dama dukkan iyalansa.Bisa wannan dalili ne
kowane likita yake yin taka tsantsan gami da yin
baya baya a duk sa'adda Zulfulaifa ta kamu da
rashin lafiya.Lokacin da Zulfulaifa ta cika shekara
goma sha takwas da haihuwa sai sarki Masarul
Anjana ya tara gaba dayan gwamnonin jihohin
dake kasarsa a babbar fadarsa wadda girmanta ya
ninka gaba dayan birnin sin sau uku ya dubesu
yace,yaku shugabannin jihohin kasata,ku sani cewa
saura wata uku 'yata Zulfulaifa ta cika shekara
goma sha takwas da haihuwa,ni kuma zan cika
shekara dubu uku da saba'in da uku a duniya
saboda haka ina farin ciki mara misaltuwa.Bisa
wannan dalili ne nake son na shirya gagarumar
walima irin wacce ba'a taba yin kamarta ba a
duniya,kuma za'ayi shagalin biki na tsawon
kwanaki arba'in.Inason a tara mini gaba dayan
mawaka da makada na duniya daga jinsin Mutane
da Aljanu kuma inason a tara mini dukkan jaruman
duniya na mutane da aljanu sannan a tara mini
duk wanda zai iyasa 'yata Zulfulaifa tayi dariya.Tun
Zulfulaifa tana jaririya kawo iyanzu data shekara
goma sha takwas a duniya bata taba yin
murmushi ba bare tayi dariya.Baby mahalukin
daya taba ganin hakoranta saboda tsananin rashin
dariyarta da maganarta,tana da tsananin fushi,dan
kankanin abu na iya sata kuka.A kullum takan yi
kuka kamar sau dari(Uhmm Sarauniyar
Shagwaba),duk mahalukin daya sata dariya ko ya
sauya mata yanayin rayuwarta daga yawan kuka ya
koma murmushi da farin ciki zan mallaka masa
duk abinda yake so a cikin wannan duniya indai
akwai shi.Akwai sharadi guda daya,sharadin kuwa
shine idan mutum ko aljan yasa Zulfulaifa tayi kuka
a maimakon murmushi ko dariya a lokacin da yake
kokarin sata walwala tofa zan kaishi kurkukuna ne
na daureshi ba zai taba fitowa ba har sai ranar da
Zulfulaifa tayi dariya.Idan kuwa kuwa zata shekara
dubu arba'in nan gaba a duniya batayi dariya ba to
saidai shima yayi ta zama a kurkukun tsawon
wannan lokaci koda kiwa ya mutu ya rubde
kashinsa ma ya zama kasa.Inason yanzu nan a
rubuta wasikun gayyata aje a rarrabasu izuwa ga
dukkan kasashen duniya da aljanu a cikin abinda
bai wuce sa'a uku ba kuma a sanar da kowane
sarki cewar idan bai tara jama'arsa ba ya amsa
wannan gayyata zan turo dakaruna na yaki su baje
kasarsa,gidajensu su zama turbaya.Koda jin
wannan batu sai gwamnonin gaba dayansu suka
amsa da angama ya shugaban.Nan take sarki
Masarul Anjana ya sallami gwamnonin nasa
kowannensu sai ya tashi sama tare da
mukarrabansa suka luluka a cikin gajimare,kafin
kiftawr idanu sun bace bat a cikin gajimare.A
wannan lokaci a duk fadin duniya ana tsaron sarki
Masarul Anjana saboda babu wata kasa mai karfin
mayaka don haka duk inda yaje da bukatar ana
rawar jiki za'ayi masa.A fagen arziki kuwa yayi
fintinkau bashi dasa a sannan Allah yayi shi
sadauki na gaban kwatance domin idan ya fusata
shi kadai ma yana iya zuwa ya yaki kasa guda ya
murkushe ta a cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba
komai yawan al'ummar dake cikinta walau ta
kasance kasar mutane ko ta aljanu.Wani abin
mamaki a tare da sarki Masarul Anjana shine yana
da matukar saukin kai,in dai za'a bashi girma
kuma za'a bi umarninsa to za'a zauna lafiya ba zai
taba zaluntar mutum ba ko aljan.Babban abinda ya
tsana shine girman kai ko gardama,komai
matsayin mutum ko aljan komai daukakarsa da
mulkinsa indai ya yiwa sarki Masarul Anjana girma
kai ko rashin kunya tofa tasa ta kare saidai a tuno
dashi a tarihi.Abinda yake daurewa dukkan jama'ar
aljanu da mutane kai dangane da halayen sarki
Masarul Anjana shine ko kadan addini bai dameshi
ba,a cikin kasarsa aljanu suna yin addinai kala kala
sama da guda dubu kuma kowa yana da yancin
yayi nasa a ko'ina babu mai hanashi ko
tsangwamarsa.Shidai sarki Masarul Anjana yana
bautar wani gunki ne mai siffar mari babban kifi
wanda aka sassakashi da zinare aka sanya shi a
cikin wata katuwar kwalba wacce ke cike da
ruwa.Ita dai wannan kwalaba ba'a
★Abubakar Haleefah Physicist★
budeta kuma bata da murfi ko kofa.Duk wanda ya
ganta sai yayi mamakin ta yadda aka zuba ruwan a
cikinta.An anjiye wannan kwalaba ne a cikin wani
daki na musamman dake cikin gidan sarautar
kuma tafi shekara dubu goma a wajen domin tun
iyaye da kakannin sarki Masarul Anjana akayi ta
kuma kowane sarki a zamaninsa dole ne kullum ya
ziyarci wannan gunki sau uku,safe da rana da
daddare ya kwashi gaisuwa yayi sujjada sau uku a
gaban gunkon sannan ya mike ya fita amma shi
sarki Masarul Anjana a zamaninsa sai ya sauya
yanayin bautar ta koma sau daya kawai a
rana.Itama sujjadar saiya mayar da ita sau
daya,lokacin da fadawansa sukayi masa magana
akan sabon tsarin da yazo da shi sai ya dubesu
yace ai sarki goma zamani goma,iyayena da
kakannina a lokacinsu basu da aikin yi don haka
suna bata lokacinsu ne a banza amma ni yanzu ko
sauraron harkokin fada ya isheni don haka bani da
lokacin da zan rinka batawa haka mai yawa a
dakin bauta.Daga wannan rana kowa ya kunshe
bakinsa ba'a sake yi masa wannan magana
ba.Lokacin da gwamnonin jihohin dake cikin kasar
Dilhal suka baro babban birni inda fadar sarki
Masarul Anjana take basu zame ko ina ba sai
kasar daya daga cikinsu wani gwamna wanda ake
kira da suna Asmaru bin Aiyan suna sauka a
fadarsa suka wuce izuwa dakin taro inda suka
zauna suka fara tattaunawa akan wannan babban
aiki wanda sarki Masarul Anjana ya basu.Bayan
sun zauna kuyangi sun kawo musu dan abin sha
kowa ya dan zuka sai shugaba Asmaru ya dubesu
yace yaku yan'uwana gwamnoni ku sani cewa
wannan aiki da sarki ya bamu bazai kammalu ba a
cikin sa'a uku ba saboda duniya ta wuce wasa.Duk
da kasancewarmu Aljanu kuma babu wani jinsi na
aljanu daya fimu karfin gudu a cikin sararin
samaniya ba zamu iya karade dukkan kasashen
mutane da aljanu ba a cikin sa'a uku mu isar da
wannan sako ga kowane sarki.A kowane nahiya sai
mu kaiwa manyan sarakunansu in yaso su kuma
sai mu dora musu alhakin kaiwa kananan
sarakunansu.Tunda dai saura kwanaki ca'sain
ranar walimar tazo,to kafin sannan zasu isar da
sakon ga kowane sarki.Koda sauran gwamnonin
sukaji wannan batu sai suka kamu da tsananin
farin ciki saboda sun san cewa wannan itace kadai
mafita a garesu.Ba tare da bata wani lokaci ba
kuwa aka tara manzanni sama da guda miliyan
dubu aka danka musu wasikun,rabin wadannan
manzanni zasu kai wasikun ne izuwa ga kasashen
aljanu,rabi kuma izuwa kasashen bil'adama.Duk
manzon da aka turashi izuwa kasar bil'adama sai
aka umarceshi daya kai sakon izuwa ga babban
boka na birnin da yaje,shi kuwa bokan shine zai
kai wasikar ga sarkinsu.Nan da nan kuwa cikin
abinda bai kai sa'a uku ba kowane manzo ya cika
aikinsa.A wannan lokaci a kasashen bil'adama
babu wata kasa wacce tayi shaharar birnin Misra
saboda daukakar ta,arzikinta da kuma girman
masarautarta da karfin mulkinta,sarkin dake mulkin
birnin Misra a sannan shine sarki Alkasim Bin
Mas'ud.Kamar yadda Allah ya baiwa sarki Masarul
Anjana komai da jin dadin duniya haka ya baiwa
sarki Alkasin,bambancinsu kawai shine sarki
Alkasim mutum ne shi kuma sarki Masarul Anjana
Aljani ne.Baya ga haka kuma shi sarki Alkasim sau
daya ya taba haihuwa kuma 'da Namiji,Allah ya
bashi wani kyakkyawan saurayi mai suna
KAMSUS.Yarima Kamsus ya zama daya tamkar
dubu a cikin dukkanin samarin dake nahiyarsu
domin shi tun yana da shekaru goma a duniya ya
shahara ya zamo abin kwatance kuma abin
misali,abin al'ajabi harma wasu nayi masa kirari
da KYAUTAR ALLAH.Abu na farko daya ajiye na
tarihi shine ba'a taba ganin ranar da yarima
Kamsus yayi fushi ba saboda tsananin hakurinsa
da kawaicinsa,kai ko zaginsa akayi ko a dokeshi
fuskarsa ba zata sauya yanayi ba saidai kawai yayi
murmushi kuma ya baiwa mutum hakuri koda
kuwa zaluntarsa akayi.Yarima Kamsus ya kasance
gawurtaccen sadauki mai jarumtaka ta ban al'ajabi
domin komai yawan runduna ta abokan gaba baya
tsoron ya shigesu ko shi daya ne,kuma duk irin
bala'in da za'a yi saiya tsira,ko rauni ba'a taba yi
masa ba a filin yaki.Duk wani mugun abu daya
gagara a nahiyar yarima Kamsus ne ke zuwa ya
kau dashi walau wani mugun dodo ko mugun
aljani ko kuma wata muguwar dabba.Kamsus yana
da matukar tausayi,taimako gami da jin kai,kuma
tun yana jariri kawo izuwa girmansa mahaifiyarsa
ta tabbatar da cewa banda kuka da yayi a ranar da
aka haifeshi irin na jarirai bata sake jin kukansa
ba,kuma bata taba ganin hawaye ya zuba daga
cikin idanunsa ba.Wuya,farin ciki ko bakin ciki
basa sashi kuka saidai murmushi da fara'a.Yana
da tsananin sa'a bisa duk abinda yasa a gabansa
bai taba samun akasi ba.Wannan baiwa da Allah
ya baiwa Yarima Kamsus ce ta janyo masa FARIN
JINI a wajen mutane maza da mata,musamman
'YAN MATA wadanda suka haukace kuma suka
dimauce a cikin KOGIN SOYAYYArsa.Amma sai
yayi biris dasu yaki karbar soyayyar kowa saboda
yana da wani buri a cikin zuciyarsa wanda yayi
alkawarin cewa saiya cikashi sannan zaiyi
aure.Wannan buri na Yarima Kamsu babu wanda
ya sanshi hatta sarki Alkasim kuwa.
FADA RA CIKA MAKIL DA JAMA'A,duk inda mutum
ya duba babu abinda zai gani face kawunan
bil'adama fululu babu masakar tsinke.Sarki
Alkasim tare da Yarima Kamsu na zaune bisa
KARAGAR MULKI suna daf da juna ana tafiyar da
harkokin mulki kamar yadda aka saba,ga fadawa
sun kewayesu,A wannan lokaci ana cikin
nishadi,wasu kyawawan yanmata sanye da korayen
tufafi su hudu suna ta faman tika rawa a tsakiyar
fadar a lokacin da wani kida mai taushi ke tashi
irin nasu na larabawa.Kowa ka kalla a cikin fadar
sai kaga yana dariya ko yana murmushi,wasu
kuma suna fadin albarkacin bakinsu saboda suna
jin dadin kallon wadannan yan
★Abubakar Haleefah Physicist★
yanmata dake debe musu kewa sakamakon cewa
rawar tasu akwai burgewa da ban
sha'awa.Kwatsam!Ana cikin wannan hali saiga
boka Rausum ya shigo cikin fadar da sauri a
hannunsa akwao wata fata mai daraja.Koda ganin
boka Rausum a cikin wannan hali sai aka daina
kida da rawa,fadar tayi tsit tamkar babu kowa a
cikinta.Nan take aka budawa boka Rausum hanya
ya wuce ta tsakiyar fadar ya nufi inda sarki Alkasin
ke zauna.Koda daya rage saura baifi taku biyar ba
tsakaninsa da karagar mulkin saiya risina ya
kwashi gaisuwa sannan ya dago kai ya dubi sarki
Alkasim a lokacin da kowa ya kasa kunnuwansa
domin yaji abinda zai fada saboda wasikae da aka
gani a hannunsa ba'a taba ganin irinta ba.Boka
Rausum yayi gyaran murya sannan yace ya
shugabana yanzun nan manzo yazo daga birnin
Dilhar ya kawo mini wasika daga hannun sarki
Masarul Anjana.Koda jin wannan batu sai idanun
gaba dayan jama'ar dake fadar ya zazzaro,aka
firgice wasu ma nan take cikinsu ya duri
ruwa,hantar cikinsu ta kama kadawa,amma banda
sarki Alkasim da yarima Kamsus,maimakon ma
yaji tsoro sai farin ciki ya turnuke shi ya kama
murmushi da fara'a yana ta yake baki tamkar
wanda akayi masa bushara ta samun duniyar
duka.Shi kuwa sarki Alkasim sai ya turbune fuska
tamkar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa ya
dubi boka Rausum cikin matukar fishi yace maza
ka baiwa magatakarda wannan wasika ya karantata
a fili muji abinda ke cikinta.Dajin haka sai Boka
Rausum ya mikawa magatakarda wasikar da sauri
ya karba hannunsa na karkarwa saboda tsoro ya
budeta a hankali saboda gani yake kamar bakin
kura zai bude.Ba wai hannayensa ba hatta
kafafuwansa ma karkarwa sukeyi.Koda ganin haka
sai sarki Alkasim ya dakawa magatakarda tsawa ya
ka nutsu ka daina barin jiki,domin kana gaban
SHUGABAN SARAKUNA wanda fushinsa ya ninka
na mai wannan wasika sau dubu.Idan baka nutsu
ba yanzun nan zan sare maka kai.Koda jin haka
sai magatakarda ya nutsu a lokacin da gumi ya
karyo masa amma gaba dayan jikinsa ya daina
karkarwar.Lallai masifa ta zahiri tafi wacce ba zata
zo ba.Nan yake magatakarda ya fara karantawa
wasikar a fili kamar haka...
-Takarda daga hannun SARKIN
SARAKUNA,shugaban Attajiran duniya kuma
SADAUKIN SADAUKI Sarki Masarul Anjana,zuwa ga
Alkasim na birnin Misra,yakai wannan shugaba
kayi sani cewa ni Sarki Masarul Anjana tare da
yata Gimbiya Zulfulaifa zamuyi gagarumar walima
ta murnar cikar shekarunmu sha takwas da dubu
uku da saba'in da uku,saboda haka ina umartarka
daka tara gaba dayan mawakan kasarka da
makadanku da kuma jarumanku da duk wani
ma'abocin barkwanci ko wata baiwa azo dashi
birnina a wannan rana domin a debe mana
kewa.Ka sani cewa yata bata taba yin dariya ba a
rayuwarta kuma bata tabayin murmushi ba.Wanda
duk yasata tayi dariya ko murmushi zan bashi duk
abinda yake bukata idai akwai shi anan
duniya.Wanda duk ya sata tayi kuka zai shiga
kurkuku bazai fito ba sai ranar da wani yasata tayi
dariya.Duk sarkin da baibi umarninmu ba zamu
turo mayakanmu su baje birninsu su kashe duk
wani abu mai numfashi a kasarsa.Koda
magatakarda yazo nan a karatun wasikar sai sarki
Alkasin ya mike tsaye zumbur cikin tsananin fushi
har fuskarsa nayin gatsine ya bude baki cikin daga
murya yace ba za'abi umarnin nasa ba.Waye shi
dazai shiga cikin harkokin mulkinmu na bil'adama?
Lallai ya tsaya iya matsayinsa da kuma
jinsinsa.MUTUM DA ALJAN ba daya bane,suyi
al'adarsu,Addininsu da mulkinsu a iya kasashensu
da jama'arsu muma mu tsaya a iya
matsayinmu,maza a rubuta masa wasikar raddi a
baiwa Boka Rausum.Kafin sarki Alkasim ya gama
wannan jawabi tuni fadawa da sauran jama'ar gari
sun tsure kuma sun firgice saboda sanin masifar
Sarki Masarul Anjana.Shi kuwa Yarima Kamsus
saiya mike da sauri ya kama hannayen sarki yace
yakai abbana ka sanyawa zuciyarka ruwan sanyi ka
kwantar da hankalinka,ka sani cewa durkusawa
wani ba gajiyawa bane,ina mai tabbatar mala da
cewa wannan ce babbar damar dana samu wacce
zan cika babban burina na duniya,burin daka
matsanta mini akan na sanar dakai amma naki.To
ka sani cewa kana daf da sanin ko menene
wannan buri nawa amma sai idan ka amince mini
na tafi birnin Dilhar a matsayin daya daga cikin
wadanda zasu sa gimbiya Zulaifa dariya.Koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke kowa
musamman sarki Alkasim ya dubi yarima Kamsus
cikin tsananin damuwa yace ta yaya kana matsayin
dan sarki guda zakaje wajen wata yar sarki a
matsayin mai barkwanci,ka kaskantar da kanka?Ka
sani cewa babu wani abu wanda Zulfulaifa tafika
dashi face kawai ita Aljana ce kai kuwa mutum
ne.Yarima Kamsus yayi murmushi yace nasan da
haka yakai Abbana amma ka sani cewa daukaka
bata zuwarwa mutum kawai dole ne ya sha wahala
ko kuma ya kaskantar da kansa kafin ya sami
matsayin da yake nema.Sa'adda Yarima Kamsu
yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki Alkasim yayi
sanyi kuma hankalinsa ya DUGUNZUMA yayi shiru
yana tunani gami da nazari a cikin kwakwalwarsa
har izuwa tsawon yan dakiku a lokacin da fadar
tayi tsit kuma kowa ya zuba masa idanu ana
sauraron a ji amsar da zai baiwa Yarima
Kamsus.Kawai sai akaji ya kawo gwauron numfashi
ya ajiye sannan saiya dubi Yarima yace yakai dana
na yarda da bukatarka.Zan barka ka tafi izuwa
birnin sarki Masarul Anjana amma face idan ka
amince zamu tafi tare.Nima zan batar da
kamannina naje a matsayin mai baiwa gimbiya
Zulfulaifa dariya kamar yadda kaima zaka bata
dariya.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa
dake fadar ya...


Read / Download MUTUM DA ALJAN 1 to 6

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album