Join Our WhatsApp Group

KWARATA Complete Hausa Novel Document by KWARATA


KWARATA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 141189



KWARATA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 21, Apr 2023

Author: Jameela Musa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : BRILLIANT WRITERS ASSO

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 777.84 kb

File Type: txt

Views: 2063+

Download: 1745+

Last download: 2 days ago

DOWNLOAD
Description/Story: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIR*


*GABATARWA:•* _Yabo da godiya da'iman wa abbadan na Allah ne. Salati da sallama su ne na fiyayyen halitta, shugaban annabawa kuma jagoran manzanni Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya._



*Shafin farko sadaukarwa ne ga kungiya mai albarka da marubutan cikinta, BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION Allah ya kara hadin kai.*


*Bazan manta da ku ba aminan albarka ina alfahari daku saina tunaku ko ina a bakin kura* 🐆

*HALIMATU SADIYYA* _{{ My Leema }}_

*HABIBA IDRIS* _{{ Hubbie }}_

*HAUWA'U USMAN* _{{ Smasher }}_

*MAIMUNA O . G*

_Gaba daya littafin nan sadaukar ne gareku,_


*ASMA'U ZAYYAN* _{{Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 1



^^Shekaruna goma sha bakwai cas a duniya. Babana yana da mata hudu da "ya "ya hamsin da bakwai.^^


Mahaifina ya kasance dan auri saki ne, bakin abinda kunne na yaji mahaifina ya auri mata ashirin da takwas.

Babana ya kasance talaka ne baya da wata sana'a wadda ta wuce "yan bige bige, ya gwanance wurin iya karya sannan kuma babu abinda kware dashi sai cin bashi.........

Talaka ne amma baya saka sutura irin tasu, idan kika gansa zaki rantse da Allah yana iya kyautar naira miliyan biyar, yasan dadin kudi sosai amma a sutura baya tausawa naira.

^^°Baya da gidan zama haka kuma baya da fili ko taki daya, munyi zama a anguwanni da dama sosai wanda duk anguwar da muka sauka suna mana lakabi da gidan inna ratata, ko kuma suce gidan yawa...

Baya da aiki sai shaye shaye sannan kuma duk gidajen cacar dake garin katsina babu inda ba'asan shi ba, ya saka kansa caca wanda ake kira da nigerful, caca ce wacce take cinye tattalin arziki kuma ba kananan talakawa keyinta ba sai masu kudin gaske saboda idan har za'a buga wasan cacar mahaukatan kudine ake zubawa.

Baya bayar da abinci haka kuma babu abinda ya damesa da rashin lafiyar "ya "yansa ko matansa, idan dai caca tayi masa dadi zai siyo kwanon shinkafa daya da kuma rabin doya,

Da safe idan zai fita zai bayar da kudin kalaci ko wane daki naira talatin babu wani abinda ya damesa da yawanku.

{}{{{}}} Wata rana can wurin wasan caccarsa aka cisa, amma baya da kudin da zai biya daga cikin abinda aka saka masa, dan haka suka cire masa sutura, tun daga inda ya buga wasan har zuwa gidanmu daga shi sai gajeran wando haka ya ratso mutane saboda tsabar shi tantirine har ya iso gida.

Babu ruwansa da tarbiyar dan sa ko yar sa, shi yasa muka mayar da gidanmu kamar gidan karuwai, domin dai kowa abinda takeso shi takeyi dan babanmu yace sana'a itace tafi cancanta ga duk diyar daya haifa, ya daina biyan kudin haya yace mu zamu rika biya tunda kowa ya kawo karfi, dan haka duk yayuna suka tashi dan neman na kansu kowa ya kama sana'a amma banda ni,

Abinda yasa kuwa shine, lura da irin kyawun da Allah yayi min, karkuyi tunanin kyawu na wasa ko ku lakaba abin da shirme ni nake gaya muku haka, bawai a gidanmu ba gaba daya zuri'armu babu yarinya mai kyau da daukar hankali kamar nawa....

Ina da kyau fiye da tunanin mai tunani, ina da diri daidai irin wanda maza ke so, ina da babban kugu sannan kuma Allah ya bani baiwar iya murzasa.

Haka kuma ina da cikar kirji ina da manya idanuwa sannan ina da fari irin na fulanin asali, gaba daya zuri'armu babu mai haske na, idan na shigo taro mata sun gama wali haka kuma babu macen da zata kara tasiri harsai na bar wurin.

Ni "yar gayu ce, na iya wanka kuma na iya shafa turare gaba daya bani da tsara idan na ziyarci wuri kamshina zaiyi ta kasancewa a wurin, haka kuma idan na barsa turarena zai dade bai daina tasiri ba, sannan duk gidanmu babu mai ilimin addini na wanda na samesa ta dalilin mahaifiyata saboda nayi sauka kuma bakin gwargwado nasan hadissai amma gaba daya zuri'armu babu mai barna irin tawa, ga sani ga barna dan duk yanda nake dakai a danginmu idan har na kwallafawa raina saina bata ka tou fa lallai saina bata maka rayuwa.

Ku kasance dani a cikin littafin *KWARATA* domin jin wannan wane irin ubane ita kuma wace irin diya ce ? Kuma a cikin ita da uban waye yafi tantiranci ? Domin dai ni sana'ar da na zabawa kaina itace *KARUWANCI* danni a gani na itace sana'ar da tafi saurin kawo kudi.

Babana mahaifi shine mutum na farko daya fara budemin lasisin karuwanci, domin dai a wurin wasan cacarsa yayi kyauta da budurcina, wannan dalili yasa na zabi sana'ar karuwanci, shine ya fara ni kuma naci gaba da kasancewa da wasan domin dai masu iya magana sunce so da yawa kana koyawa mutum abu amma saiya fika kwarewa.

Ni babban kamfani ce kamar yanda ake sakawa a jikin kayan masarufi ace ingrediants to nima ina da nawa ingrediants in, kamar yanda company yake sarrafa abubuwa to nima company ce mai zaman kaina.

Wannan labari a kiyayi juyashi ta ko wace siga domin yin hakan babban kuskure ne , ba kagoshi nayi ba a haka ta fadamin shi domin ina so ya zama izina ga matan aure,

{{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}}


Baba da Allah ka bamu naira goma zamu cika mu siyo magi,

Ba tare daya kalleta ba yace me zakuyi da magi ? Cikin in ina tace dama kanzo ne zamu kwada,

Naira biyar ya fiddo daga cikin aljihunsa, ya mika mata tare da cewa anshi idan kin samu kudin magin ki cika ki siyomin sigari......

Mahaifiyar ta dake tsaye tana daka kulin da za dasuci kwadon tace haba mai gida idan tana da kudin zata tambaye ka ? Itama bai kalleta ba yace wannan matsalarku ce keda ita, keni yi sauri ki kawomin sigarita jiranki nake ya fada tare da shashantar da maganar matar sa.

Fa'iza mahaifiyarta ta kirata tare da cewa ina zaki samo kudin ? Bai bari Fa'izar ta bada amsa ba yace samarinta zasu bata ? Ke kike ganin bata da kudi duk yaran nan da kike kallo sun fiki kudi , ke ki hadomin da lemu mai sanyi kafin mai samomin abincin da zanci ta shigo.

Fa'iza na kokarin fita daga gidan sukaci karo da Farida a bakin kofa, da yake gidan baya da zaure wanda ke wucewa ta waje ma zai iya hango na cikin gida, gidan kuma babu kaure sai labulen buhu da aka saka a jikin kofar,

Babu sahihiyar katanga sai fasashshin buloluwa da aka jera, wanda ko yaro karami ya wuce zai hango na zaune.

Fa'iza ganin Farida yasa ta tsaya tare da cewa, Farida da Allah ko kina da kudi ki rantamin na siyowa Baba sigari da lemu, anjima idan nayi awara zan baki, babu sauran kudi a hannuna duk na kasosu kasuwa canjin daya rage kuma nakai zubin adashe kinga lokacin biyan kudin haya ya kusa.

Dan murmusawa Farida tayi tare da cewa ai tunda kika ganshi can ya mimmike kamar gawar sababi yau bashi da ko sisi, dan haka ma wallahi bazan shiga gidan ba komawa zanyi.

Tun kafin Farida ta rufe bakinta ya fara kwarara mata kira amma tayi kunnen uwar shaggu dashi ta fice abunta.

Rungume na fito da magena sanye cikin kayan islamiyata, nasha nikaf dina kayana sun dauki guga sai zabgaga kamshina nake da turarena dana siya na naira hamsin wurin masu siyar da turaren dure.

Da sauri Baba ya tashi zaune tare da cewa Mamana barka da fitowa ? Murmushi nayi tare da cewa yawwa Babana barka da hutawa,

Yawwa Mamana za'a tafi neman ilimin ? Eh Baba na fada a takaice, mikewa yayi tare da cewa muje in rakaki, wannan shine dabi'ar mahaifina duk inda zan tafi indai yana gida tou fa lallai shine zaiyi rakiya,

A kofar gida muka hadu da Fa'iza sigarin ya ansa tare da cewa ki ajiye min lemun in dawo, shigewa tayi gida tare da cewa tom.

A tafiye muke yana zukar sigarinsa hankali kwance, Baba wai har yanzu baka samu kudin da zaka siyamin keken ba ? Na tambayeshi, magen hannuna ya ansa tare da cewa machine zan siya miki uwa ta gari.

Murmushin farin ciki nayi sannan nace Allah ya bada sa'a Babana , da amin ya ansa tare damin fatan alkairi dan mun iso bakin islamiya, magena na ansa na shige shi kuma yayi gaba.

Yau inacikin farin ciki, domin dai idan har Babana yacemin zaimin abu tou fa ko zai mutu sai yayimin, yana min san da duk duniya bayayi wa kowa irinshi, yana kaunata fiye da yanda yake san kanshi, yana so ya ganni a cikin farin ciki saboda ina da sunan mahaifiyarsa.

Yau ban wani yi karatu ba, hankalina ya tafi makarantar boko, na kagara gari ya waye dan injewa kawaye na da labari mai dadi zanyi sabon machine, nidai makarantar bokon haka nan nake zuwa dan ba abinda nake ganewa kaina fanko ne , a islamiya kadai Allah ya dafamin nake ganewa, amma a boko bana gane komai. Haka nan nake zuwa na dawo,

Koda na dawo gida na kasa boye farin cikina, amma babu damar na fada, uban da ya kasa biyan kudin haya taya zan fada zai siyamin machine ? Dan haka naja bakina nayi shiru, saboda nasan idan suka ganni da machine in zasuyi tunanin kanin Mamana ne ya siya domin shine yake dauke da hidimata.

Ina cire kayan islamiya ta na matsawa Inna sai ta bani kudi na siyowa magena kifi, bazan bayar ba shine amsar data bani , tare da hadamin da cewa itama kanta gari taci , saboda haka bataci kifi ba babu wanda zata siyama kifi.

Gaskiya Inna bazan iya ba "yar madara gari taci ba, nice sheda saboda kin hana kanki kin cida magen banza, inna ta bani amsa,

Tana fadar haka ta shige daki, na dade zaune a wurin ban samu mafita ba dan duk wanda ke gidanmu haushina yakeji kamar ya sakani wuta wannan dalilin yasa bana shiga sabgar kowa,

Saida na gaji da zama na tashi a wurin ganin ban samu mafita ba, daki naje na kwantar da "yar jinjirar mage na nabar gidan dan samo mata abinda zataci, gidane babu kayan dadi daga gari sai kanzo inama amfanin talauci, shi kuma Baba ko tsoron Allah bayayi yazo gaban kowa yaci kaza dan zalinci,

Amma duk wannan masifar Maman Fa'iza hada wani ciki ina tausayin dan nan da za'a haifa domin dai zai shigo rayuwar bala'e dama ya sani yayi zamansa baizo ba.

Haka nayi ta galbaro a cikin anguwa babu tsiyar dana samo, dole na hakura na dawo gida dan lokacin sallar magrib yayi,

Har bayan sallar isha'e Baba bai dawo gida ba, tunda naga ya wuce lokacin dawowarsa na sanyawa zuciyata salama tare da ba "yar madara hakuri, tunda ko mun tsaya jiransa bige zai dawo nasan yana can ya shawu iya shawuwa, mata hudu a gida amma yana neman matan waje. Tirrr da wannan hali.

Tunani barkatai a zuciyata, ciki kuwa harda tunanin yanda zamu wayi gari ba tare da bango ya fado mana ba, dan gaba daya gidan nan ya rube ga wani irin hadari sai bakin rai yake, lallai wannan ruwan yau idan ya kwace gaskiya akwai matsala.

Allah ka tsaremu da rayuwar talauci, rufe idona nayi domin inyi bacci addu'a nayi a fili cewa ya Allah ka tsare bayinka daga mutuwar katanga, kasa in kasance rayayya, in wayi gari cikin farin ciki, Allah ka shirya Babana ya daina abunda yakeyi,

Inna ta ansamin da amin, tare da cewa Allah ya tsare gaba daya gidan, ban mata magana ba dan haushinta nakeji ta hanani kudin da zan siyowa mage na kifi, wani busashshen garinta can ta ajiyemin kuma banci ba, nasan idan naje makaranta gobe Amisty zata kawo mana shayi da biredi daga gidansu, shi yasa kafin kekena ya lalace nake saka "yar madara cikin kwandon gaban keken mu tafi tare itama ta maida miyanta.

Da tunanin shayin gidansu Amisty nayi bacci, kuma dashi na tashi, tunda na farka naji yanayin garin da sanyi nasan jiya an kwana kwarara ruwa, dan haka tun kafin na sauko daga saman katifa nace Inna halan kin tara ruwan sama ?

Na tara, ai jiya banyi bacci ba saida na tabbatar na cika komai nawa da ruwa, cikin damuwa na kara jan yagaggen zanin da nake rufa dashi tare da cewa wallahi bana san wanka da ruwan sama sai jikinka yayi ta wani sulbi kamar ka kama maciji,

Banza tayi dani bata...


Read / Download KWARATA

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

6 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album