Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na biyu 2 Complete Hausa Novel Document by RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na biyu 2


RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na biyu 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 144341



RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na biyu 2

Reading Time: 12 Hours

Added On: 28, Jun 2024

Author: Umar Muhammad Sangaru ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 800.62 kb

File Type: txt

Views: 489+

Download: 1460+

Last download: 11 hours ago

Description/Story: RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 51: *Taswirar Barban*
*
Wannan littafin sadaukarwa ne ga ZAHRA A. ADAMU.
*
UMAR SANGARU
*
Aljani Sheezuwa ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Lallai kai Kuffuru ka fi kowa sauri, kawai daga ganin Hodon sai kace aje a kamo shi? Inda ace Hodon zai kamu cikin sauƙi haka, da zai kai wannan lokaci yana sata?
"Na farko Barban yana tare da aljanin da yafi kowanne aljani ƙarfin sihiri a duniya. Na biyu ba ku gina kurkukun da za'a kulle shi a cikin ta ba. Waɗannan abubuwa guda biyu su ne zasu hana mu zuwa kamo Hodon a yanzu.
"Kuffuru, idan baka manta ba, nace bazan amsa maka waɗannan tambayoyi guda biyu da kayi ba, face kun gama haɗuwa SADAUKAI UKU. Tambayoyin naka su ne mene ne dalilin da yasa Barban ya bari aka samar da taswirarsa? Wanne tubali za'a gina wannan kurkuku da shi? Ku nutsu da kyau ku ji wannan bayani nawa.
"Duk duniya babu wanda ya isa amsa wannan tambaya akan dalilin da yasa Barban ya bari aka samar da taswirarsa face shi kansa. Wataƙila yana so yayi amfani da wannan dama ne wajen nuna ƙarfinsa a duniya, wataƙila kuma yana so yayi amfani da wannan dama ne domin ya bayyana kansa ga idon duniya. Amma ko kaɗan bana tunanin yayi haka ne domin ya miƙa wuya.
"Tubalin da za'a gina wannan kurkuku da shi kuma, duk duniya babu inda ake samunsa face kwarin Jekish. Wannan tubali ragowar wani ƙaton dutse ne, da ya yi bindiga ya narke. Ruwan dutsen ne ya haɗu a waje guda ya samar da wannan tubali. In dai kuka sami wannan tubali aka gina wannan kurkuku dashi, kuma aka kulle Barban a ciki. Duk duniya babu wanda ya isa ya fiddo shi daga ciki.
"Shin kun san a ina wannan kwarin Jekish yake?" Aljani Sheezuwa na zuwa nan a zancensa ya ɗan yi shuru ya baiwa su sarki Kuffuru dama ko zasuyi tambaya. Tsahon ɗan lokaci shuru babu wanda yayi tambaya.
"Kwarin Jekish, na can yankin birnin Auzur wanda yayi iyaka da yankin Dilikem. Daga wannan wuri zuwa kwarin Jekish tafiya ce ta kusan watanni goma. Koda akan aljani mutum zaiyi wannan tafiya saiya shafe waɗannan watanni goma, amma daɗinta shi ne, har mutum ya isa wannan wuri ba zai haɗu da komai na sharri ba.
"Babbar matsalar ita ce babu wanda ya san mene ne a cikin kwarin Jekish. Saboda haka dole ne muyi taka-tsantsan idan muka je wannan wuri."
Sarki Kuffuru, sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu suka fara kallon juna cikin tsananin mamaki, ko sunan wannan kwari basu taɓa ji ba, ballantana su san haɗarurrukan dake cikinsa.
"Ina da tambaya," inji sarki Darwazu. "Idan muka je wannan kwari, tayaya zamu iya ɗebo wannan tubali mai yawa wanda zai isa a gina wannan kurkuku?"
Aljani Sheezuwa yayi murmushi ya ce, "Tare zamuyi tafiyar, sannan ni ne zan ɗebo wannan tubali. Akwai wata tambayar?"
Tsahon ɗan lokaci suka yi shuru. Aljani Sheezuwa yayi gyaran murya ya ci gaba da bayani.
"Aljanin dake tare da Hodon yafi ƙarfin ifritu. Kuyi sani cewa ifritu ba su da yawa a duniya, kowanne ifritu yana da makami na musamman wanda zai hallaka shi a duniya. Amma, ga aljanin da yafi ƙarfin ifritu babu makamin da zai iya kashe shi, face ƙarfin ruhi wanda babu kamarsa a duniya.
"A taƙaice dai, ina so na sanar da ku cewa ba zamu iya kashe wannan aljani dake tare da Barban ba, face Kuffuru ya mallaki RUHIN SAMUDUL ANSARI. Da wannan ƙarfin ruhi ne kaɗai zai iya amfani wajen tarwatsa ruhin wannan aljani."
Sarki Kuffuru na jin wannan batu yaji wani abu a cikin ransa, ya tabbatar da cewa kamo Barban ba ƙaramin aiki bane. "Meye amfanin gina wannan kurkuku, idan har bamu kamo Barban ba. Nake ga ai kamar wahalar banza ce. Me zai hana mu fara tunkarar mallakar wannan ruhi daga yanzu, idan yaso bayan mun mallaki ruhin sai muyi tunanin gina wannan kurkuku?" inji sarki Kuffuru.
Aljani Sheezuwa yayi murmushi ya ce, "Ba zaka gane bane. Shi wannan aiki da kake kallo, dole ne a bi komai daki-daki. Gina wannan kurkuku shi ne aiki na farko, daga nan sai tarwatsa ruhin wannan aljani. Kana tunanin mallakar ruhin sarki Samudul Ansari zaiyi sauƙi ne?"
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska ya ce, "Shi kenan. Na amince."
Lokacin da wannan madubin tsafi yazo wannan wuri, sai boka Biu Lin yasa hannunsa yaja abinda ke faruwa gaba, inda aka nuno sarki Kuffuru, sarki Darwazu, boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya zaune bisa aljani Sheezuwa suna ta tsala azababben gudu a cikin gajimare.
Sarki Ayubul Zairiy ya dubi wannan boka cikin tsananin mamaki ya ce, "Me sarki Kuffuru yake shiryawa?"
Boka Biu Lin ya dube shi ya ce, "Sarki Kuffuru da waɗannan mutane sun haɗa kai domin kamo Barban. Sun samar da taswira mai ƙarfin gaske wacce zata bi diddigin Barban. Na san zai yi wuya ace kun san wannar sarauniya, ba wata bace illa sarauniya Rauziyya. Duk wanda ya samu labarin gumurzun da ya faru a kurkukun-mutuwa zaiyi mamaki idan aka ce masa sarauniya Rauziyya da sarki Kuffuru sun haɗa kai.
"Kuyi sani cewa sarki Kuffuru ya kashe sarki Ratanam, sannan ya ɗauki yarima Marganu ɗan sarki Ratanam ya kaiwa shi wannan sarauniya. Wannan shi ne dalilin da yasa ta amince suka haɗa kai da sarki Kuffuru a yadda suka nunawa duniya, amma dole nasan akwai ɓoyayyen sirri.
"Wannan kuma, ɗan ƙabilar Adbenchan ne. Sarki Darwazu sunan sa, ƙasar Askandariyya yake mulki..." Kafun wannan boka ya ƙarasa jawabinsa sarki Ayubu ya dakatar dashi da hannu.
"Mene ne ma'anar nuna wannan abu da yake faruwa a cikin wannan madubin tsafi?" sarki Ayubu ya tambaye shi.
Boka Biu Lin ya ɗan haɗe gira, kafun daga bisani ya amsa masa. "Dole ne ku tafi farautar wannan taswira, kuyi ta bin su sarki Kuffuru a baya har zuwa inda ya dace, ku farmake su ku kwaci wannan taswira. Saboda a halin yanzu babu taswirar da za'a samar ta nuna ainihin inda Barban yake face wancar ɗin."
Sarki Ayubul Zairiy ya zaro idanu cikin mamaki ya ce, "Ah haba! Wannan abu zai yiwu kuwa? Sarki Kuffuru mai aljanin duwatsu. Sarauniya Rauziyya mai aljani Barzasa. Ga wannan baƙon sarkin. Ga boka Hubbazu mai ƙarfin sihiri. Ga wannan aljani dake tare dasu. Anƴa zamu iya kwato wannan taswira daga hannunsu kuwa?"
Boka Biu Lin ya yi dariya ya ce, "A ɓangaren ku, ga ka nan kana da aljani Jizid. Ga boka Ruguzan jikan Shashamu. Sannan ga sarkina Kim Sam, babu abinda kuka sani akansa. Uwa-uba gani nima zanyi muku rakiya gani nake daidai muke da su."
Koda sarki Ayubu yaji wannan batu sai hankalinsa ya ɗan kwanta amma da yake yasan waye Kuffuru har a wannan lokaci, bai gama samun nutsuwa ba. Amma, ga dukkan alamu wannan boka ma zai kasance mai tsananin ƙarfin sihiri duba da yadda yake sarrafa tsafi kamar kayan gidansu.
Sarki Kim Sam ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Mu a wannan nahiya tamu, ba kamar wajajen ku bane. Mu ba ma sarrafa aljanu, mun fi yin imani akan sihirtattun makamai masu firgitarwa. Zan iya ce muku tunda nake a rayuwata bai fi sau uku na taɓa yin ido-da-ido da aljani ba. Tun da yanzu mun haɗa kai zan zayyane muku dukkanin ƙarfin sihirina da ƙarfin shiri na.
"Kamar yadda na faɗa muku da farko, a wannan nahiya bama sarrafa aljanu. Ni wani sihirtaccen mashi na sihiri nake sarrafawa. Komai yawan runduna ta mayaƙa idan na shiga cikin su da wannan mashi sai na ragargaza su. Komai duhun waje idan na shiga da wannan mashi sai yayi haske. Sannan bugu-da-ƙari wannan mashi nawa yana iya rikiɗa ya zamo jibgegen shaho na hau kansa ya kaini duk inda nake so a faɗin duniya."
Sarki Kim Sam na zuwa nan a zancensa ya fiddo wani mashi dake ɗaure a gadon bayansa ya nunawa shi su sarki Ayubu. Mashi ne dogo mai haske da walwali kamar fitila.
Boka Biu Lin yayi murmushi ya ce, "Haka ne. Ni kuma abubuwa guda biyu nake sarrafawa. Na farko wata dardumar tsafi ce, na biyu kuma wata isga ce ta tsafi. Wannan darduma tawa tana iya ɗaukar mutane komai yawansu ta kai su waje. Wannan isga tawa kuma, komai ƙarfin sihirin mutum kafun ya iso inda nake da tafiyar mako guda zata nuna min. Kuyi sani cewa tun kafun kuzo wannan birni namu, na riga na kalle ku sannan na kalli abinda ke tafe...


Read / Download RUHIN JARUMTAKA Mujalladi na biyu 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album