Join Our WhatsApp Group

NANA JAWAHEER Complete Hausa Novel Document by NANA JAWAHEER


NANA JAWAHEER

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51423



NANA JAWAHEER

Reading Time: 4 Hours

Added On: 11, Sep 2023

Author: Jameela Jameey ƴar mutan Kankia ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : +234 816 050 8316

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 293.47 kb

File Type: txt

Views: 624+

Download: 331+

Last download: 9 hours ago

Description/Story: *🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*Story and writing by*

*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*



*DEDICATED TO MY* *FAMILY* 👨‍👩‍👧‍👦

*"Tofa jama'a gawani sabo nan mai cike da soyayy💋❤ dakuma tausayi😢😭 sannan da darasi da dama acikin wannan labarin mai taken (NANA JAWAHEER🧕🏽 ) wanda marubuciyar ta zauna tabaje basira domin farantama masoya😍😘""ammn dan Allah inkinga gyara ki gayaman nikuma zan gyara" saboda gaba sannan dan Allah inkingani kuyii share sbd yan uwa su amfana da abunda ke cikin wannan labari mai ban alajabi da kuma tausayi,,, inga comment sannan xani cigaba dayi maku typing din wannan litafi mai albarka 🤗🤓 !!!!!*



```Nikuma xanyi kokari zakuga posting akowace rana,, nagode kudae kubi wannan labarin mai ban alajabi..```



~Sannan wannan labarin kirkirarshi nayi in labari yashafi rayuwar wani ko wata dan Allah ayafeman domin dae dan Adam ajazine nagode....~



Page 0⃣1⃣




"Tafe take tana kuka wiwi!!! ga bukitin markade a hannunta, tana kuka.Nabani ni nana yau inna nasan kasheni ne kawae baxatayi bah sbd makarden kokon nan nata da ya zube, yau ni nana ya zanayi da wannan bakar kaddarar da ta hau ni yau, haka ta kama maganganu kala kala masu sosa zuciya!!! har ta iso soron gidansu ta kasa shiga ta leka ta koma tana tsoron ukubar da zata tadda a wajen Inna, wai wanene a soron nan? Oh ashe kece yar nema, to shigo laben me kikeyi, shigo ki kawomin markadena, marece keyi kar a kira sallah bamu gamaba, wai bazaki shigoba, ko sai nazo na shigo dake dakaina ne banza me hali irin na uwarta "Inna dan Allah kiyi hakur!! Inyi hakuri dame ja'ira? "Inna wlh makarden ne ya zube shiyasa;kam ubannan! dan ubanki, ubanki ya bani jarin da zakimin asara toh wlh yau saina ci ubanki muddin baki biyani kudinaba, mai mugun hali.....
"A hakadai Inna taita balbalin bala'i, ahaka nanan ta shigo gidan, Inna ta hauta da duka tako ina tana cewa antafi anbarmin annoba cikin gida.....
"Lafiya ! Lafiya! Talatu nakejin hayaniya me taimaiki k? aidole kace haka, daga ba yarinyar nan markade taje ta zubarmin da markadena dan haka wlh sai anbiyani kudin gerona dan bazanyi asaraba ehe!! Kika cewa sai anbiya? yanzun dik wahalan da yarinyar nan kemaki a cikin gidannan bakyagani, ita ke maki aiki ba dare ba rana, komai sanyi komai ruwa Amman kuma daga yau ta zubarmaki da markade shine zaki kama bugunta toh wlh bani biya, kuma baki sake bugaman yarinya tunda na lura kedae bakisan asamaki ido bah... ke wake matsa maki duk kuwa abunda kike yimin cikin gidannan amman nasama ki ido saboda da darajar yaranki.... ae kema kina da yara mai xai hana ki ringa aikinsu sae ita toh talatu ki fita idona na kulle, ya dubi inda nana take kwance a galabaice akan dukanda tasha yace ke mamana tashi kije ankusa kiran sallah ga kuma wannan azumin ana fama dashi, tashi ga wata sauran naira dari biyu nan tafi keda sabi'u kuje kasuwa kusamomana abunda da zamusa abakin salati. Inna ta dubishe tace wato malam ai haka kace ko? to shikenan zamu hadu watarana!!!.
"Ke Nana wannan wani kallar bacci ne kike yi har yanzun baki tashi bah? har bakwai tayi wakika ajiye yayimaki aikin gidan ko dan kinga ubanki jiya ya dauremaki shiyasa yau kika samu daman yin bacci, koh mutunniyar banza, mai hali irin na uwarta! yoh ni talatu in ba kaddara ba antafi anbarni da annoba da bala'i acikin gida,"inna dan Allah kiyi hakuri, wallahi ko jinayi yau bani jindadi shiyasa na dan kwanta amman yanzun xantashi.
"Bakijin dadi fa kikace nana to bari naci uwarki sannan ki dawo dai dai "Inna dan Allah kiyi hakuri tashi kije kiyi wanke wanke da shararki ga kuma wanki na da dana su sabi'u kije ki wankesu tas, sannan ga gero nan ki gyara shi sannan kikaishi markade dan Allah ba zuda markade ba inkin tashi kifasa har bokitin kiga yanda yau zanyi maki acikin agidan nan,, "to inna amman yau akwae boko yau littinin inna, "oho Wato ina magana kina yi ko ga sa'ar uwarki koh, toh bara kiji yau baki zuwa Wani boko har sae kingama man aikin gidana baki daya sannan ke ga yar zamani koh? Shin zaki tashi ko sai na buge wannan bakin eyye shashasha kawae dake... A haka nana tagama yima inna talatu aikin gidan kamar jaka amman ita yaranta suntafi boko sunbar nana gida tana aikin walaha idan tayi wannan ta yi wanca, "Inna nagama!! "kingama komae harda wanki? "eh duk nagama" to wakika ajiye ya kaima maki markaden?."Inna dan Allah kiyi hakuri wallahi na makara a makaranta sosae shiya amman idan nadawo xani kai shi.
"Nana yaushe nafara fada kema kina fada, eyyeh ko dan kinga kwana biyu bani cika taba lafiyar jikinki bah?.."A'ah bahaka bane bah inna yi hakuri, da hakurin ya mutu sadakar nawa kika badah eyye!? zaki tashi kibani waje ko sai na yimaki mugun bugu mai baqin gado kawae, wannan mugun halin can gun dangin uwa aka gado shi....tana fada kamar duketa...duk akan masifar da take mata idanunta har sun fara kwallah.. au wato kuka ma zakiyi man koh mutunniyar banza kawae..tashi kije ko na makeki..nan nana ta tashi ba kwari ta tafi !!
" Sallama tayi ta shigo gida, tazo wajen inna ta kawo mata markedem, Inna ga markaden nan ni natafi...tana sauri..zo nan wakika ajiye yayi maki tatan kokon nana?. "yi hakuri inna yanzun zani yi to tashi kiban waje; ahaka nana tagama yima inna tatan koko tace ma inna nagama na tafi makaranta...a sauri sauri ta shirya ta tafi...
"Nana sai yanzun kike xowa makaranta yanzun ankusa tashi fa nana kinsan ko karfe nawa yanxun sha biyu takusa fah. "Zee kema kisan inna bata barina nazo makaranta har sae nagama yi mata aikin gida sannan; "wae nana sai yaushe Inna talatu zata rage yimaki wannan bakar azabar acikin gida?, yakamata ace yanzun ta ajiye wannan bakin kishin nata datakeyima umman ki haba mana..!!!

" Toh zee ya zanyi inba hakuri bah, haka xanta hakuri da inna har mai rabawa ta raba. "nana har yaushe mai rabawa zata rabaki da inna ko kin manta duka duka yanzun muka shiga SS one.. nana Allah yasaka maki...
"Nidae yanzun zee mubar wannan maganar dame-dame akayi yau ?! "toh kinsan dae yau munada chemistry da biology da Islamic yanzun kuma mai hausa zai shigo xee dan Allah idan ansha ruwa zani shigo gida ki koyaman kinsan banison inayin missing din lesson din chemistry saboda yana bani wuya gashi kuma naji ance a jami'a, ya zama dole kayishi inkana level one/two shiya nike son nakoyeshi.. "Nana kedae kinason kiyi boko mai zurfi, aikom dae zee inada burin wannan saidae kinsan baba baida hali ammn inata adu'a allah yacika mana burin mu na alkhary amin.
"Kawata kinga ga malam nan ya taho yakamata muyi shiru kafin ya shigo ko kawata hakane gaskiya.
"Ahaka dae malamin hausa ya shigo class ya koyamasu darasin karin magana ya kuma yi masu tambayoyi, ahaka aka tashi daga makaranta kowa ya koma gidansu yayin da nana taji daman karda atashi a makaranta saboda taa son karatu a rayuwarta....

" Ahaka nana dai takama shan wahalar rayuwa a wajen matar ubanta, watarana babanta ya shigarmata, watarana kuma sae dae ya bata hakuri yacema ta watarana sae dae labari yakan cemata *" mai hakuri shi keda riba"* kuma tasa karatun secondary dinta agaba saboda Allah yaba nana baiwar kwakwalwa sosae don itace ke zomasu na uku a class.


*Asalin labarin....!!!*

Toh Alhmdulh indan labarin nana yayimaku dadi to naga comment dinku sannan xani cigaba dayi maku labari wannan labarin maicike da Soyayya, tausayi sannan kuma da darasin da za'a dauka duk cikin wannan novel mai sunan da kuka gani daga sama wato (NANA JAWAHEER).....

"Allah ya karemu daga sharin wannan annoba ta covid_19 yan uwana musulmai dan Allah mu yawaita addu'a domin addu'a itace takobin mumuni, Allah yasa muyi kyakkyawan karshe ya kuma haskaka mana kabarin mu ameen ya hayyu ya qayyum....

"Please sisters share to your friends domin su amfana da abunda ke cikin wannan littafi ngd...




Share and comment 😍



🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕
*NANA JAWAHEER*
🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```




*Story and writing by*


*Jameelah A Belloh*
*(Jameey)*

*DEDICATED T O YAR UWA RA'BIN JIKI AUNTY FATEE 💖💘*

*Bissimillah Rahamanir Raheem*



Page 0⃣2⃣



*A gaskiya bani da bakin da zaniyi maku godiya sae dae nace Allah yasaka maku da alkhari"" domin maganar gaskiya na ga ruwan comment ngd sosae harda wanda dasuka bini ta PC domin sukara bani kwarin giwa,, dakuma nunaman dadin litafin hakan yayiman dadi sosae ngd ana mugun tare🤗😁*


*ASALIN LABARI*


Malan Sabi'u shine asalin sunan kakan Nana jawaheer wanda ya haifi babanta, haifaffen dan jahar katsina ne a unguwar kofar kwaya. ya hadu da matarshi mai suna nana jawaheer akasuwar charanci takai tallar nono, shikuma yana sae da kaba da guga, anan ne suke haduwa duk sati har shakuwa tashiga tsakinsu, suka kulla soyayya, tana wani kauye maisuna kafin dangi wani kauyen fulani ne dake karamar hukumar kankia, a haka har yaje gidansu ya gaishe da iyayenta manya suka shiga cikin maganar akayi bikinsu.


Nana jawaheer ta tare agidanta take cikin birnin katsina, Allah ya azurta malan Sabi'u da yara uku, adamu shine babba sannan Suleiman sae autarsu Khadija suntaso cikin aminci da kaunar juna sannan sun masu tarbiyya mai kyau sunyi karatun addini, yayinda Adamu ya kama sana'ar baban shi, shi kuma Sulaiman ya kama karatun boko domin yanason boko sosae, itama kuma Khadija tana girma akayi mata aure, tana auren wani abokin yayanta, mai suna Musa.


A kwana a tashi ba wuya gurin Allah. Malan Adamu yahadu da Aminatu inda suke kaunar junansu.. itama Aminatu yar garin kar'karku ce, wata rugar fulanice dake cikin karamar hukumar sandamu, dake daura a jahar katsina sun hadune a kasuwar mai'aduwa taje kaima babanta nono da yake babanta shike sayarda nonon baya barinsu suyi talla, sae dae kiyo anan ta hadu da malan Adamu ya kai kaba da guga shima a kasuwar, da yake babban Aminatu yasan malan Adamu sosai saboda duk sati yakan kai guga a kasuwar, shiyasa kawae sukayi bincike yaturo manyanshi akasa bikinsu wata hudu......


Anyi bikin malan Adamu da amaryarsa Aminatu akan sadaki naira dubu ishirin, sannan kuma dayake su dama fulani al'adarsu ce sai ankawo marakin sa balle daman Aminatu kyakkyawace "(kunsan dae yanda auren fulani yake basae nagayama ku bah balle kuma fulanin ruga😁)".

Suna zaman su cikin amana da kaunar juna, a inda malam adamu yake bama Aminatu kulawa ta musamman...

Anyi aure su malan Adamu da shekara daya, Allah ya azurtata da d'a namiji mai kama da maman shi yaro yaci suna *Abubakar* amman ana kiranshi da suna *(Sadiq)* " saboda sunan kakan shine wanda ya haifi babanshi....

Ranar wata juma'a, zuri'ar malan Sabi'u suka tashi da wani tashin hankali wanda ya girgiza duka wannan ahali nasu, an wayi gari Allah yayima malan Musa mahaifin Sadiq rasuwa, lokacin Sadiq yanada shekara hudu da haihuwa wannan rasuwa ta girgiza Khadija sosae, da kuma yayanta Sulaiman wanda a lokacin yana da degree dinshi na biyu wato masters, yayi kukan mutuwar abokinshi sosae sai dai muce Allah yajikan malan Musa... bayan Khadija ta fita daga takaba takoma gida wajen babarsu itada yaronta, lokacin malan Adamu ya matsawa Sulaiman yayi aure shima, tunda ya gama karatunshi, ya karanta business administration kuma yana aikinshi a Access bank dake cikin unguwar kofar kaura dake cikin birnin katsina. Har lokacin Allah baiba malan Adamu haihuwa bah sun fauwalawa Allah lamarinsu. suna cigaba da yin addu'a, Sadiq yana da shekara bakwai. Sulaiman yayi aure yasamu matarshi a cikin katsina a unguwar rafin dadi, anyi aurensu suna zaune acikin unguwar layout anan yayi gidanshi nagani na fada...

Anyi auren Sulaiman da shekara daya Allah yaba Aminatu ciki, murna wajen malan Adamu in nace xani tsaya in gayamaku bata lokacine, a haka malan Adamu suka reni cikinsu har ya kai haihuwa" Allah yasauki Aminatu lafiya inda tasamu santaleliyar diyarta maikama da babanta murna wajen su Sadiq abun ba'a magana, dan gidan kawun nashi yadawo da zama, yana ganin kanwar tashi, anyi suna inda yarinya taci sunan maihaifiyarsu watoh Nana jawaheer ammn suna kiranta da suna *NANA* , lokacin sadiq yanada shekara tara aduniya, sulaiman yaje makka inda yakai mamanshi da babanshi suma saudia, bayan dawowarsu daga saudia Allah yayima Alhaji Sabi'u rasuwa, matuwar da ta girgiza wannan ahali sunyi kuka har Allah yasamasu dan ganar rasuwar mahaifin su......

Bayan rasuwar baban su Sulaiman yamaido mamanshi da Khadija da Sadiq da zama awani bangare na gidanshi inda alokaci Sadiq yana primary two, a haka yamaidashi private school dake kt mai suna kiddies pride school dake cikin layout ya dauki nauyin karatunshi.

A bangaren su malan Adamu kuwa jawaheer tanada shekara uku malan Adamu ya hadu da Talatu ne tana tallar kayan miya acikin unguwa, ita yar unguwar tudun dan lihidda ce a katsina, Talatu takamu da son malan Adamu ne lokacin da takawo tallar kayan miya acikin gidanshi, tunda taganshi taji tanasonshi sae ta kula mutunci da matarshi Aminatu, lokacin Nana tanada shekara shidda, tagayama malan Adamu tanasonshi amman sae yaki yarda saboda baida tsarin yin mata biyu, A...


Read / Download NANA JAWAHEER

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album