Join Our WhatsApp Group

HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI Complete Hausa Novel Document by HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI


HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 26566



HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Bukar Mada ,Danladi Z Haruna ,Prof Ibrahim Malumfashi ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08032767547, 08071051138, 08032767547

Book License : Free

Category: Tales

File Size: 134.33 kb

File Type: txt

Views: 854+

Download: 334+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: 01 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
A wani dadadden zamani da ya wuce, a cikin birnin Misira, an yi wani attajiri da ake kira da suna Shamsuddin. Mutum ne mai gaskiya da rikon amana, ga shi da saukin kai, ga kuma hakuri sai ka ce kasa. Yana da rumfuna da yawa a cikin kasuwar Misira, dukkan rumfunan nan nasa cike suke da haja iri daban-daban. Yana da bayi da kuyangi, bakake da farare, masu yawan gaske. Saboda halayensa na kwarai da kuma yawan rumfunansa a cikin kasuwa, aka nada shi Sarkin Kasuwar Misira.
Shamsuddin yana da mata daya, wadda suke matukar son juna. Sai dai babbar damuwarsa shi ne, shekarunsu arba'in da aure amma ko batan wata matar tasa ba ta taba yi ba, don haka Allah bai nufe shi da samun da ko diya ba.
Wata rana, ranar Juma'a da hantsi, Shamsuddin na zaune a cikin rumfarsa ta kasuwa, sai ya lura da cewa, kusan kowane dan kasuwa yana zaune tare da dansa, wasu 'ya'ya biyu, wasu fiye, a cikin rumfa, suna koya musu sha'anin kasuwanci. Ya zauna yana ta tunani. Da lokacin sallar Juma'a ya kusa, sai ya nufi gidan wankan da ke cikin kasuwar, domin yin wankan Juma'a da kuma alwala. Bayan ya fito daga gidan wanka, a bakin kofar gidan wankan, sai ya amshi mudubin wani wanzami yana duba fuskarsa, yana cewa, "na shaida babu sarki sai Allah, na kuma shaida Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa."
Ya dubi gemunsa ya ga ya cika da furfura, sai ya raya a cikin ransa, furfura fa alama ce ta sakon mutuwa. Da ya tuna ba ya da magaji, sai hankalinsa ya dugunzuma. Bayan an gama sallar Juma'a, sai Shamsuddin ya nufi gidansa. To, da ma matarsa ta san a daidai wannan lokaci yakan dawo gida duk ranar Juma'a, don haka kafin ya shigo ta riga ta yi wanka ta caba kwalliya. Ta shirya masa abinci da abin sha bisa shimfidarsa.
Yayin da ya shigo gida sai ta tare shi da fara'a, ta ja hannunsa ta zaunar da shi bisa shimfida. Ta ce masa, "barka da wannan yammaci, mai albarka."
Shamsuddin ya harare ta, ransa a bace, "ni ban ga albarkar da ke cikin wannan yammaci ba!"
To, da ma ta san abin da ke damunsa a rai kullum, sai ta kyale shi. Ta jawo akussan abinci ta ajiye a gabansa, ta ce, "ci abinci, ya maigidana." Ya sa kafa ya shure akushin abinci, "ni ba zan ci abincinki ba."

Matar ta tambaye shi, "me ya same ka yau, maigida? Menene sababin damuwar ka?"
Shamsuddin ya amsa mata, "ke ce sababin damuwa ta” Matar ta ce, “me ya sa ka ce haka?” ya amsa mata ya ce, “na buɗe rumfata yau da safe na ga kowanne Bafatake yana da ɗa guda ɗaya ko fiye da haka a tare da shi suna zaune a rumfar tamkar mahaifinsu. Ni kuma na gan ni haka babu kowa, sai na ce a raina, “mutuwar nan da ta ɗauki mahaifinka ba za ta bar ka ba kai ma.” To ke kuma tun haɗuwa ta da ke da farko kin sa na rantse cewar ba zan yi mata ta biyu ba bayan ke, kuma ba zan yi kuyanga ba, ‘yar Habasha ko Barumiya ko ma wata k’abila daban. Kuma kika sa na rantse cewar ba zan kwana a ko’ina ba sai tare da ke. Ga shi ke kuma juya ce ba kya haihuwa, kuma zama da ke tamkar zama ne da kurman dutse.” Matar ta ce, “wallahi ba haka ba ne, Allah shi ne shaida ta cewar laifin daga wajen ka ne, domin maniyyinka rarrauna ne, ba zai iya samar da ciki ba ballantana ‘ya’ya.

Sai ya ce mata, “to menene zai kaurara shi? Faɗa min na tafi na sayo shi domin ya kaurara min nawa.” Matar ta ce, “ka tafi wajen masu magani.” Ya kwana da ita a wannan daren. Washegari ya tashi yana mai nadamar kaushin harshen da ya yi mata a jiya, ita ma ta yi da-na-sanin martanin da ta mayar masa. Ya tafi kasuwa yana neman masu magani har ya dace da wani mai maganin ya yi masa sallama ya amsa sannan ya tambaye shi, “yalla kana da maganin da ke kaurara maniyyi?” mai magani ya amsa, “na wajena ya k’are, sai dai ka tambayi mak’wabcina.” Ya tambayi na gaba shi ma ya ce babu. Haka ya yi ta zagaya masu maganin nan kaf yana tambaya babu wanda ya ce akwai sai dariya suke masa. Da ya gaji sai ya koma rumfarsa yana cike da damuwa. A gefen rumfarsa wani babban dillali yana faɗin amfanin ganyen shayi da zoɓorodo da kuma taba. Shi wannan mutumin ana kiransa Sheikh Muhammadu Samsami, matalauci ne, kullum yana yi wa Shamsuddin addu’ar fatar alheri. Bayan ya gama tallar ya zo bisa al’adarsa ya gaishe shi, ya lura cewa yau Shamsuddin na cikin damuwa sai ya ce masa, “ya shugabana, yau me ya ɓata maka rai?” Shamsuddin ya faɗa masa dukkan abin da yake damun sa da yadda suka yi da matarsa, ya k’ara da cewa, “yau shekara arba’in kenan da aure na amma ba ta taɓa haihuwar namiji walau mace ba. Kuma an ce wai dalilin rashin haihuwar ta saboda maniyyina ne bai yi kauri ba.
Na zagaya wajen masu magani kaf ban samu dacewa ba.” Sheikh Muhammadu ya ce, “ya shugabana, ina da maganin da ke kaurara ruwan halitta ɗa namiji, amma me za ka ce ga wanda ya yi sanadin matarka ta haihu bayan tsawon shekaru arba’in bata yi haka ba? Shamsuddin ya ce, “idan ka yi min haka zan maka tagomashi mai yawa.”
“To ba ni dinari.” In ji Sheikh Muhammadu. Shamsuddin ya ce, “ɗauki waɗannan dinarai biyun. Sannan ya nemi a ba shi tasa da kasko, duka Shamsuddin ya ba shi. Ya ɗauka ya tafi zuwa wajen mai sayar da hakukuwa ya awo bibiyu na albasa da tafarnuwa da zanjabilu da citta da kaninfari da masoro da farin barkono da sauran kayan yaji. Ya daka su gaba ɗaya sannan ya tafasa su cikin man zaitun sannan ya k’ara ganye uku na gamji da ararraɓi da ruman. Sannan ya cika kaskon da garin alkama. Sannan ya cuɗa da zuma, ya rufe cikin wannan tasa ya kai wa attajiri ya ce masa, “ga maganin da ke kaurara maniyi.” Ya faɗa masa yadda zai yi amfani da shi. “ka rik’i wannan a matsayin ruwan sha. Amma da farko ka samu naman rago ka ci, kuma a dafa maka ‘yan shila da yaji mai zafi ka ci. Sannan idan zafin yaji ya dame ka sai ka haɗa da nono da sukari domin su ne ke hana yaji zafi.” Attajiri ya haɗa dukkan abubuwan da ake buk’ata har da naman da tattabarun ya aika da shi ga matarsa ya ce a sarrafa su kafin ya dawo.
Da ya dawo da yamma ta kawo masa girkin ya buɗe ya cinye gaba ɗaya sannan ya sha haɗin maganin. Ya ji daɗin maganin sosai. Bayan ya kammala ya kwanta da matarsa. A wannan dare Allah ya k’addara ta ɗauki ciki, bayan wata uku sai ta ga al’adarta ba ta zo ba, a nan ta fahimci ta samu juna biyu. Yayin da ciki ya girma ya isa haihuwa, ciwon nak’uda ya kama ta, ta kasance tana k’ara saboda farin ciki da kuma wahalar haihuwa. Aka kirawo unguwarzoma ta taimaka mata tana ambata sunayen Allah da na Annabi Muhammadu da na sahabbai sannan tana kabbara har ta haifi ɗa namiji. Aka yi masa kiran sallah da kalmar shahada a kunnuwansa. Sannan unguwarzoma ta naɗe shi cikin zane ta mik’awa uwarsa, ta karɓe shi ta ba shi nono. Bayan ya k’oshi ya mik’a da barci abin sa. Unguwarzoma ta zauna tare da ita har kwana uku, aka shiryawa mai jego kayan k’anshi da nama mai kyau, kuma bayan kwana bakwai aka rabawa jama’a alawa da dabino. Sannan aka barbaɗa gishiri a k’asa wai maganin mugun ido. Attajiri Shamsuddin ya shiga wajen matarsa ya taya ta murnar haihuwa lafiya sannan ya ce mata, “ina ajiyar Allah ɗin yake?” Aka kawo masa jaririn kyakkyawa bisa cikakkiyar surar mahalicci wanda yake tabbatacce har abada ba zai gushe ba. Kodayake kwana bakwai kenan da zuwan jaririn duniya, amma ga wanda bai sani ba sai ya yi tsammanin ya shekara guda, saboda girman da Allah ya ba shi
Uban ya dubi fuskarsa na haske da k’yalk’yali kamar wata ɗan daren sha huɗu, ga kundukukinsa ja mai k’ayatarwa. Ya ce da matar, “wanne suna kika kira shi?” ta amsa da cewa, “da a ce mace ce sai na ba ta suna, amma tunda namiji ne babu mai ba shi suna sai kai mahaifinsa.” A wancan lokacin kuwa mutane sun kasance suna raɗawa ‘ya’yansu suna bisa faruwar wani al’amari a lokacin da aka haife su, attajiri da matarsa suka kasance suna tambayar sunan da ya kamata su raɗa wa ɗansu. Can sai wani daga mahalarta ya ce, “Allah ya raya Alaldini!” Sai kuwa attajiri ya ce, “to sunansa Alaldin Abul Shamatu.”
Sannan ya mik’a yaro ga masu shayarwa, ya sha nono na tsawon shekara biyu sannan aka yaye shi. Yaro ya rik’a girma har ya kai shekara bakwai, sannan uban ya ɗauke shi ya ɓoye a cikin gida domin tsoron idanun mahassada, ya ce, “ba zai fito waje ba har sai ya yi gemu.” Ya sa kuyanga da bawa su rik’a kula da shi; kuyangar na shirya masa abinci, bawan kuma yana ɗaukarsa a bayansa. Daga nan aka yi masa kaciya ya shirya k’asatacciyar walima. Bayan nan ya samo malamin da ya rik’a koya masa rubutu da karatu da alk’ur ani mai girma da sauran ilmi har dai ya samu ilmi mai yawa. Rannan bayan an kawo masa abinci sai bawan ya manta ya bar k’ofar gidan da yake a buɗe bai rufe ta ba. Saboda haka Aladdin ya fito ya tafi wurin mahaifiyarsa tana tare da wasu matan suna hira. Yayin da suka ga ya shigo sai suka yi tsammanin farin bawa ne wanda ya yi sha don tsananin kyawonsa. Yayin da suka gan shi gaba ɗaya sai suka rufe fuskokinsu da mayafi suka ce da uwarsa, “yaya za ki bari farin bawa ya shigo mana nan wurin? Ba ki san cewa kunya na daga sashen imani ba.” Ta ce musu, “ku ambaci sunan Allah da bismilla! Kada ku sa mini laifi Wannan ɗana ne furen zuciyata kuma magajin falke kuma attairi Shamsuddin mai dukiya a birnin nan, wanda uwar goyonsa ta yalwata da tufafi da abinci da abinsha.” Suka ce, “mu kam tsawon zamanmu da ke ba mu taɓa sanin kina da ɗa ba.” Sai ta ce, “haka ne, domin mahaifinsa ke tsoron sharrin idanun mahassada ya ɓoye shi a gidan k’ark’ashin k’asa, yanzu ma watak’ila bawa mai kula da shi ne ya manta k’ofar a buɗe shi ya sa ya fito. Ba ma nufin fito da shi yanzu sai ya soma gemu tukunna.

Matan suka nuna jin daɗin su game da shi, saurayin ya tafi k’ofar gida ya zauna, sai ga bayin babansa haye da alfadararsa. Ya tambaye su, “wannan kuma fa daga ina?” suka ce masa ta babanka ce, mu raka shi kasuwa ne muka dawo da ita.” Sai ya ce musu, “menene sana’ar babana?” Suka ce “mahaifinka falke ne na k’asar Misira, shine ɗan sarkin ‘ya’ya a zamaninsa.” Daga nan ya tashi ya tafi wajen mahaifiyarsa ya ce da ita, “mecece sana’ar mahaifina?” Ta ce masa “mahaifinka tajiri ne mai alheri, mafificin tajirai na k’asar Masar, shi sarki ne a kan ‘ya’yan Larabawa, ko bayinsa ba sa yi masa magana a harkar cinikin da ya gaza dinari dubu. Duk wanda yake da kaya na kamar dinari ɗari ko fiye, zai sayar ne kurum gwargwadon aniyar sa. Su tafi zuwa garuruwa masu su saro kaya su sayar ba tare da tuntuɓar sa ba saboda amincin sa da su. Yana da dukiya mai yawa a hannun mutane suna jujjuya su bai kula ba yana ta sha’anin sa. Wani abu na daga dukiya bai taɓa damun sa ba balle ya sa tsone masa ido, Allah ubangiji ya hore wa mahaifinka dukiya mai yawan gaske.”

ZANCI GABA GOBE INSHA ALLAH02 HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

Da ya ji haka daga bakin mahaifiyarsa sai ya cika da farin ciki, ya ce, “ya uwata, yabo ya tabbata ga Allah wanda ya k’addara mahaifina shi ne sarkin ‘ya’yan Larabawan Masar kuma falke mai dukiya. Amma me ya sa kuka sa ni k’ark’ashin k’asa kuka tsare ni sai ka ce ɗan kurkuku?” Ta ce, “haba ɗana, ba mu saka ka ko tsare a ciki ba face saboda tsoro idandunan mutane. Domin kambun ido gaskiya ne, mafi yawan waɗanda suke ga kaburbura daga ido suka tafi.” Ya ce mata, “to yaya za ku yi da hukuncin Allah? Tsoro ba ya hana k’addara aukuwa. Abin da aka rubuta gudu baya hana zuwansa, wanda ya ɗauki kakana ba zai bar mahaifina ba ballantana.

Wanda ya rayu yau ba lallai ya rayu gobe ba. Idan mahaifina ya mutu ya rage saura ni na mutu kenan, ni Aladdini ɗan Shamsuddini bafatake, idan na ce wa mutane ni ɗansa ne na san babu wanda zai gaskata ni saboda kun ɗauke ni ku ɓoye babu wanda ya san cewa Shamsuddini yana da ɗa. Bayan ransa ba za a bar min komai ba za a ɗauke dukkan dukiyarsa da mallake – mallakensa a zuba a baitalmali. Ni zan rik’i gaskiya na bar k’arya. Wanda ya ce saurayi na mutuwa saboda idanun mutane wannan bai gaskata hukuncin Allah ba. Yanzu abin da za a yi ke uwata ki faɗa wa mahaifina ya tafi da ni kasuwa ya buɗe min rumfa ya zuba min kaya, na zauna tare da fatake da dillalai ya rik’a koya min yadda ake saye da sayarwa da karɓa da bayarwa.” Uwar ta ce, “an jima kaɗan mahaifinka zai dawo zan faɗa masa wannan buk’ata.

Yayin da Shamsuddin ya dawo sai ya tarar da Aladdini a zaune yana hira da mahaifiyarsa, ya ce da ita, “don me kika bari ya fito waje?” ta ce da shi, “ya ɗan baffana, ba ni ce na fito da shi ba, bayin ne suka manta k’ofa a buɗe ya samu ya fito lokacin ina tare da mata sun hallara gare ni daga manyan wannan gari, ya shigo gare mu.” Ta habarta masa yadda suka yi da shi. Da ya ji haka sai ya ce, “ya ɗana gobe idan Allah ya yarda zan ɗauke ka zuwa kasuwa. Amma ka sani zaman rumfa yana buk’atar ka zam mai ladabi ga abokin ciniki da tausasa masa domin akwai jama’a mabambamta a kasuwa. Ana buk’atar natsuwa da kwantar da hankali a kowanne al’amari mutum ya gani a kasuwa.” Aladdini ya yi barci a wannan dare yana mai farin ciki bisa wannan alk’awari na mahaifinsa....


Read / Download HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

2 Comments On HIKAYAR ALADDINI MAI FITILAR SIHIRI
avatar
saidou

7 months ago

Reply

Tyhfhhhjg

avatar
ummitah

7 months ago

Reply

Wow

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album