Join Our WhatsApp Group

YAZAN YI DA AUREN ADNAN Complete Hausa Novel Document by YAZAN YI DA AUREN ADNAN


YAZAN YI DA AUREN ADNAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22095



YAZAN YI DA AUREN ADNAN

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Jul 2023

Author: Ummu Sabreena ,Anty Aisha ,Jameela ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 124.78 kb

File Type: txt

Views: 1336+

Download: 359+

Last download: 8 days ago

Description/Story: [1:41PM, 2/22/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN.?```



```© UMMU SABREENA
ND
ANTY AYSHA
ND
JAM33LA```



<<1~5>>





Gudu take acikin daji, cikin tsakiyar duhun dare, nan taci karo da wani babban dutse ta fadi a 'kasa tana nishin wahala,ta waiga hagu ,ta waiga dama, bata ganshi ya biyo ta ba, ta tsugunnan da kanta idanunta na zubar da hawaye mai cike da firgici , 'dagowan da zatayi kawai ta ga macijin a gabanta ya fasa kai zai sareta ,ta fasa wani wawan ihu wanda yayi sanadiyyar tashin ta daga baccin datakeyi ,ta ri'ke kai tana maimata sunan Allah a fili, "mafarkan data keyi kenan yawanci ,sai taga maciji ya biyota , yana zuwa zai sareta sai ta farka ,
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un",ta sauko a hankali daga kan gadonta ta nufi bayi tayo alwala duk da tsoron dake cikin ranta bai hanata gurfana agaban ubangijinta ba tana mai kai kuka gurin mai ji kuma mai ganin ta a kodayaushe ,bayan ta idar ta dauki alqur'ani ta karanta sannan ta mi'ke ta cire hijjabi ta ninke daddumar ta kwanta ,sai wajajen asuba sannan nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
wanshekare da safe misali karfe goma na safiyar asabar ,mama ce zaune ita da dad zaune suna breakfast ,dad ya kalli mama yace "wai haryanxu aisha bata tashi bane ?", mama ta aje cup din dake hannunta tace "kasan ai sabida yau ba makaranta shiyasa take ta hutawa ", yayi murmushi yace "mamana kenan akwai san hutu ga shagwaba", suka gama karyawa sannan mama ta rakashi ya wuce office.
Karfe daya na rana ya buga dai dai ,mama ta mi'ke ta nufi 'dakin Aisha ,ta tura 'kofa ta shiga ta hangota can tsakiyar gado tanata baccinta ,
mama ta matsa kusa da ita tana tashinta "Aisha! Aisha!! Aisha!!! Ki tashi mana ,karfe daya na rana fa ,ko karyawa bakiyi ba,lafiyarki kuwa?
" ta bude manya manyan idanuwan a hankali tace " mama wallahi duk gajiyar schl ne ," "to ai baccin ya isa haka ko" tace "to mama ganinan fitowa",
ta mi'ke tayo wanka da brush sannan ta yi alwala ta nufo falo gurin mama dake zaune tana karanta jarida ,ta matsa kusa da ita ta kanga jikinta jikin mama tana sha'kar kamshin turaren dake tashi a jikin mahaifiyar tata ,ta dan lumshe ido tana fadin "mama mun wuni lafiya "? "Lafiya lau auta ya gajiya ?
" Alhamdulillahi kije ki zubo abinci mana ya kitchen nasa miki a cooler",
Alhaji muhammad shine mahaifinsu, yanada mata daya mai suna hajiya hassana (mama) ,dan kasuwa ne sosai wanda suke zaune a kaduna u/sanusi ,
Allah ya albarkacesu da yara guda uku dukkansu mata ,
Hannatu itace babbar 'yarsu tanada yara guda hudu, maryam,afrin,al'amin sai karaminsu muhammad ,tana zaune a unguwar dosa anan kaduna .
Sai maryam wacce take da yara biyu ,Abduljabbar da Amatullah wacce taci sunan mama ,tana zaune a zariya wanda anan gidanta Aisha wacce ake kira da adla kuma itace autar mama ,sabida anan zariyan take karatu, yanxu ta dawo weekend ne wurin mama wannan kenan!





```YAZANYI DA AUREN ADNAN.?```



```©UMMU SABREENA,
AUNTY AYSHA
ND
JAM33LERH```



5~10




Da yamma adla na kwance a falo ,wayarta ce a hannunta tana latse latse ,bakar riga ce a jikinta 'kirar blackberry ta daure kanta da bakin dankwalin rigar ,duk da bawani kwalliya tayi ba amma kyanta ya fito sosai ,idanuwan nan nata manya, ga gashin kanta daya kusan rufe mata goshi nan ya kwanta luf a kanta '
Lebanta dan dai dai kaman ita tayi kanta, komai nata cis cis dan irin jikin mama gareta.
Nan taji dawowan dad ,
Da sauri ta tashi taje anso jakar dake hannunshi tana mishi sannu da zuwa ,ya amsa cikin jin dadi yace
"Adla , dazun nake tambayar mama baki tashi bane tace min kinata bacci ne , nace gaskiya adla tayi min wayau sai hutawanta take ,ya fadi haka yana mai zama a kusa da ita ,
Tayi murmushi wanda beauty point dinta suka lotsa " abbana bawani wayau ,wallahi na gaji dayawa ne, kuma gashi bana samun baccinne sosai sai nazo gidan mama",
Mama ta fito daga 'dakinta jin dawowar mai gidan nata, ta zauna tana mai mishi sannu da dawowa ,
tace "adla har kin gama girkinne ?", "eh mama ta gama har na jera a dinning ma ",
Dad yace " maman adla wai kinji autarki bata samun bacci a gidan maryam sai tazo nan, ya fadi haka da zolaya ,
"Eh mana abbana wallahi idan mai sunan mama ta fara kuka cikin dare a gidannan kowa sai ya farka dan har karnukan gidan tashin su take ",
Dad yayi dariya sosai , yayinda itakuwa mama ta harareta tace " banason sharri adla ,mai sunan nawa ai tafi abduljabbar hakuri ,ita da ba ruwanta ",
"Bawaninan mama wallahi ummi fitinanniya ce " ,
Dad yayi murmushi yace " kyalesu adla , da mamarku da mai sunanta duk zanyi maganinsu ",
Mama ta tashi ta nufi dakinta dan taji anata kiraye kirayen sallar magriba, itama adla ta mi'ke ta wuce nata dakin tana mai jin dadin yanayin garin domin hadari ne ya hadu ,iska ta ko'ina shigowa yake .
Bayan sunyi sallah ne suka sauko falo ,
Mama ta mi'ke ta kawo musu abincin nan tsakiyar falo ta zuzzuba musu sunaci suna hira cikin nishadi.
Dad ya dauki tissue ya goge bakinsa yana fadin " naga alama auta ta kusa tafi mamarta iya girki ",
Mama ta aje cokalin hannunta tace " da sauki ai tunda dai nina koya mata " ,
Adla tayi dariya " abbana dama nagaya maka nafi mama iya girki ,nata hannun ya tsufa ,nawa hannun kuwa sabo ne ",
"Kice min kawai mamarku ta tsufa ",
Mama ta 'danyi murmushi mai sauti " kowa yasan dai da tsohuwar zuma ake magani ",
Adla ta mi'ke tana dariya ta wuce dakinta ,
Wayar dad tayi 'kara ya dauka tare da sallama dan ganin nombar amininshi ne wato Alhaji Aliyu ajiya , bayan sungaisa ne yake shaidawa dad cewa yananan dawowa ranar monday daga italy , dad ya mishi fatan alkhairi sannan ya kashe wayar ,
Ya kalli mama yace " abotarmu nida aliyyu ta har abada ne dan kuwa jinsa nake har cikin raina ,tun muna 'kanana muke tare gashi har girma , ban 'dauke aliyyu a matsayin amini kawai ba ,na dauke shi ne a matsayin 'dan uwa",
Mama tayi murmushi " gaskiya alhaji aliyyu mutun ne ,matar shi ce kawai sai a hankali dan kuwa a tunanina gaskiya baiyi sa'ar mata ba ",
Dad ya 'dan kalleta da gefen ido yayi dan dariya "wannan matsalar kuce ta mata maman adla ,amma bata shafemu ba mu mazajenku ",
Tayi shiru bata ce masa komai ba sabida tasan cewan aliyyu mutmin kirki ne kuma shine babban aminin dadyn adla ,
Yanada mata daya mai suna Hajja balaraba , mazajensu aminai nai amma matansu halinsu yasha bambam ,
Ita hajja balaraba mace ce mai son duniya da 'kawarta gata da kyaman wanda baida shi ,abinda yasa ma batawa maman adla sabida tsakaninsu kar tasan kar ne , kuma dai mazajensu tare suke kasuwanci balle ta nuna mata kudi , sai dai tayiwa wasu amma batayi agaban mama ko tayi mata ,
Dan mama bata daukan rainin hankali irinna hajja , suna shiri da juna amma ba chan sosai ba kuma suna gaisawa amma kowacce tasan halin kowacce ,
Danta daya namiji mai suna "ADNAN" ,ba anan yake karatu ba yana 'kasar Germany ,
Domin tunda yagama primary abban shi ya kaishi can , ta 'dauki son duniya ta daura mishi domin shi kadai gareta
[8:28PM, 2/23/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN?.```




```© UMMU SABREENA,
ANTY AYSHA
AND
JAM33LERH```

```20-25```




Bayan alhj.aliyu ya tafi ne da yamma banyan Dad yqdawo Daga masallaci suna zaune da mama a bedroom dinsa ya kalleta " inaso ki saurareni da kyau ,wannan maganar da zanfada miki yanxu ba shawararki nake nemaba ,a ah! Kawai dai a matsayinki na mahaifiyar adla ne yasa zanfada miki ,sabida mun riga mun gama maganar ,abinda kawai nakeso naji Daga gareki shine fatan alkhairi, nasanki maman adla kinada fahimta da hakuri Dan haka na yanke shawarar koban gayamikiba zaki fahimta ,to inaso ki saurareni da kunnan basira .

Ta juyo tana kallonsa " ya zayyanemata duk yadda sukayi da abban adnan,ido kawai tazuba mishi ko kyaftawa babu, itadai bazatace ADNAN yaron banza bane tunda ance zato zinibi ne, amma wani hanzari ba gudu ba, tarbiyyarshi take kokwanto, ba'a Nigeria ya girma ba, tun tasowarshi a germany yake rayuwarshi, gakuma uwa uba hajja balaraba da gaskiya bata fatan hada zuriya da ita, kuma yadda takeson ADNAN bata tsammanin akwai abinda yaron zaiyi aga laifin shi, inta Abban adnan ne to bazata guji zuriyarshi ba "

Ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tace "Hmmm Allah ya sanya alkhairi, amma ai jibi ne jumma'ah ko? ",

Dad yace " eh ranar jumma'ah za'a daura insha'allah, amma banaso ki fadama ita adlan, nafiso insunyi hutu tadawo sai a gaya mata ",

Ta gyada mishi kai taja bargo ta kwanta zuciyarta cike da sak'e sak'e akan wannan aure

Saukowa take a hankali daga matakalan jirgi ,tana amsa waya, ta isa ga driver dayazo daukanta, ya fito ya dan du'ka yana gaisheta,

Ta amsa tana kokarin shiga cikin motar, suna isa gida 'yan aikin gidan suka fito sunata kwasar gaisuwa .

Ta dauko wayarta ta latsa nombar maigidan nata take sanar masa dacewa gata a Nigeria tadawo.

Kafin kace wani abu masu kula da girkin gidan sun cikata da abinci kala kala. Ta dan kalli inda abincin yake ta yatsina fuska tace "bari nayo wanka nayi.sallah sai nazo naci abincin ",

Da yamma Alhaji aliyu ya iso gidan, ta tarbeshi da sannu dazuwa, bayan sun zauna yake tambayanta ina Adnan?,

Tayi murmushi najin dadin an ambaci dan nata " adnan yana can karatu yakusa ya kare, baka ganshi ba yakoma bature sak ",

Alhj aliyu yayi dariya " lallai germany ta anshe shi 'dan nema",

Sukayi dariya dukka




```YAZANYI DA AUREN ADNAN?```



```UMMU SABREENA,
ANTY AYSHA,
ND
JAMEELERH

25-30```

Wanshekare dasafe, mama ta dauki waya takira hannatu da Maryam tace suzo tanason ganinsu, amma tacewa maryam karta fadawa Adla cewan nan zatazo sabida kar tace zata biyo ta.

Hannatu ce ta fara isowa sannan maryam, duk sun hadu a falo sun gaisa, nan ne mama take kora musu jawabin abinda mahaifinsu ya cemata gameda auren adla, ta kara da cewa " kune 'ya 'ya na kuma kune yayyinta, dan haka ya kuka gani?,

Hannatu ta nunfasa "lallai dole hankalinki yayashi mama, ba komai bane abinji sai hajja, ga shi kuma sudai yara ba son juna suke ba, ina tsammanin ma bai santa ba a fuska itama bata san shi ba, sukuma su dad sun yanke hukunci, amma wannan saidai muyita musu addu'a yadda dai dad yace tunda anyi angama ",

"Amma kina tsammanin adla bazata 'ki ba?,

Maryam tace "ai mama kinsan autar taki akwai hakuri nasan.zata yadda, dan haka karkisa damuwan hajja acikin zuciyarki tunda ba tare zasu zauna ba, inaa ganin bawani problem ",

Mama ta sauke ajiyar zuciya "shikenan Allah yamana zabi na alkhairi ".

Suka amsa da amin

Maryam tace " ranar juma'ah kikace ko mama? ",

"Eh ranar Friday ne ",

"Kenan gobe ne, to ko na kwana ne?,

"A ah mairo ki koma gida kar ita auta tayi zaton ba lafiya ne, ai daurawa kawai zasuyi, taron biki kuwa sai yadawo saura wata biyu",

"Ohk Allah ya kaimu.",

Shiko Alhj aliyu bai gayawa hajja ba sabida yasan halinta yadda taci buri kan adnan dayawa, ya barine sai an daura sai ya sanar mata, ba yadda zata iya .

Ranar juma'ah misalin karfe sha daya na safe aka shaida daurin auren ADNAN DA AISHA (ADLA) wanda dad ya zama waliyyin ango shikuma Alhaji aliyu Waliyyin amarya.

Daurin auren duk da a qurarran lokaci suka sanar amma bai hana mutane taruwa sosai ba. Kowa kagani cikin farin ciki

Da yamma Alhaji aliyu ya shigo gidansa, hajja yasamu kwance ta mik'e k'afa ana mata tausa ita kuma tana ansa waya, ladi mai aiki ta mi'ke ta na mai gaisheshi sannan ta fita da sauri ,ya gitgixa kai yasamu wuri ya zauna.

Ta kare wayar sannan ta juyo tana murmushi tace " Alhaji sannu dazuwa yau naga ka shigo da wuri ne ",

Ya cire malunmalun dayasa ya kalleta "eh sabida naje wani wuri ne ",

Taga alamun yau ba wasa a fuskar shi dan haka tasha jinin jikinta, dan kuwa tana shakkarsa komai abinta.

Ya katse mata tunani tahanyar fadin " inaso kibani hankalinki anan balaraba, magana ce zamuyi mai mahinmmanci, banason tashin hankali, abu dai anriga anyishi dan haka ki saurareni dakyau kiji hukuncin dana yanke, nida aminina mun yanke shawarar hada zuriyar mu aure, kamar yadda kika sani wannan bawani bane illa alhj Muh'd, yau an daura auren ADNAN da ADLA, dan haka banason jin komai daga gareki sai addu'a,

Ta hadiya wani kakkauran miyau, tadan goge zufar data keto mata tace "amma maiyasa baka fada min ba a matsayina na mahaifiyar shi? ",

"Sabida nasan halinku na mata abun zai iya baci, dan haka shima Adnan din dan inada iko dashi ne, kuma kar ki sanar mishi har sai yadawo zangaya mishi sannan sai kiyi taronki ",

Ta sauke ajiyar zuciya badan taso ba, sai dan ba yadda ta iya, kuma ita before akwai wata yarinyar kawarta da takema adnan sha'awar ya aura, ba'anan suke zaune ba suna italy, kuma masu azziki ne sosai, amma bakomai zata yi shiru akan wannan maganar sabida kar ace matsala daga wurin ta ta bullo, zata yi musu bakam amma zasu sha mamaki, "hmm tayi dariyar mugunta ", hajja kenan
[7:37PM, 2/24/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN?```




```© UMMU SABREENA,
AUNTY AYSHA,
ND
JAMEELERH```



```40-45```



Wanshekare a safiyar laraba, dady aliyu ne tare da iyalansa suna karin kumallo, hajja ce tayi tayi serving kowa, sunaci suna hira cikin jin dadi da annashuwa, dady aliyu ya aje fork din dake hannunsa ya kalli adnan yace " dama adnan akwai wata magana mai mahimmanci da zamuyi dakai ",
Hajja najin haka ta tsuke fuska ta hade rai,ita za'a takura mata 'da, kunji fa masu karatu kamar wani 'danta ita kadai!,
dady aliyu yacigaba " munyi shawara dakai da dadynka (dadyn adla ,dan haka yake cemasa) lokacin baka 'kasar, muka yanke hukuncin hada auren ka da Aisha 'yar wurinsa, dan haka nasan kai yaro ne mai hankali da bin iyaye, inafatan bazaka bani kunya ba ",
Adnan yayi shiru yana kallon dadynsa ,yayi murmushi a ransa yace " shi ko da yayi rayuwarsa a germany bai damu da mata ba, ko a chan yanda mata ke binsa har gida baya kulasu, balle kuma anan Niger, to zaidai yadda...


Read / Download YAZAN YI DA AUREN ADNAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album