Join Our WhatsApp Group

CIZON YATSA Complete Hausa Novel Document by CIZON YATSA


CIZON YATSA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19054



CIZON YATSA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 16, Jul 2023

Author: Nasma ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 95.21 kb

File Type: txt

Views: 2250+

Download: 384+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: [2/23, 7:34 PM] Nasma: Bammm taji an turo ƙofar ɗakin da sauri daidai da suɓucewar wayar daga hannunta. Jikinta babu inda ba ya rawa da ta haɗa ido da Shaheed wanda ya dawo saboda mantuwa yana mata mugun kallo. A matuƙar fusace ya nufota ya kaiwa wuyanta shaƙa ta kufce tare da yin baya da sauri tana roƙonsa da yarbanci.
"Kada kayi min muguwar fassara da Haj. Manga nake magana."
Dakatawa ya yi na ɗan lokaci sunan da ta faɗa ya sauka a kunnuwansa kafin ya sake nufarta gadan-gadan ko cikin jikinta ba ya tunawa.
"Ni za ki cuta Sariat? Me ya haɗaki da Haj. Manga? Me yasa ki ke faɗa mata cewa Aidan yana gidan nan? A ina ki ka santa?"
"Tambayoyin naka da yawa, ka zauna nayi maka bayani yadda za ka fahimta. Hajiya ta daɗe tana taimakonka batare da ka sani ba."
Ta ce tana ƙara ja da baya. Wata irin tsawa ya daka mata yana jin kamar ya rufeta da duka. A zatonsa ya yi nisa da duk wani abu da ya shafi gidan Alh. Audi ashe ya yi kuskure. Wace alaƙa ce ta haɗa Haj. Manga da Sariat da har take cewa ta daɗe tana taimakonsa.
"You are leaving my house now (yanzu za ki bar min gidana)" ya ce yana wuceta zuwa jikin durowar kayansu. Watso su ya shiga yi a ƙasa da sauri yana wurga mata su. Duka zantukansu a kunnuwan Haj. Manga. Babu bata lokaci tayi saurin fitowa daga gidan nata ta faɗa mota. Sai da ta zauna ta sanar da direbanta inda zai kaita cikin ƙanƙanin lokaci kafin Shaheed ya yi aika-aika. Sun isa gidan akan gaɓa domin daga bakin benensu take iya jin muryar Shaheed yana ta masifa ya soma tara musu maƙota. Da bibbiyu ta dinga hawa benen cikin sauri ta buga ƙofar. Iyabo da take ta aikin bashi hakuri ta kama kofar za ta bude ya bita da mugun kallo.
"Na faɗa miki kada ki buɗewa kowa idan ba kwasar kayanta ta yi za ta fita ba."
Haj. Manga da taji shiru gashi ba gane me yake faɗa tayi ba sai ta matsa jikin ƙofar sosai ta kira sunansa.
"Shaheed ka bude min kofar nan."
Hannu ya ɗaga kamar zai mari Sariat da take ta kuka ya sauke. Da kansa ya buɗe ƙofar ya haɗe rai.
"Dukana za kayi ne?" Inji Haj. Manga tana ture shi domin matsuwa da son ganin halin da Sariat take ciki.
A durƙushe ta sameta akan gwuiwa inda take bashi haƙuri. Daga cikin wani ɗaki kuma ta ji muryar Aidan shi ma hayaniyar ta saka shi kuka. Bata tambayi kowa ba ta tafi inda take hasashen daga nan muryar ke fita ta buɗe ƙofar. Ƙamshin kaɗai ya tabbatar mata da na Tauhidanta ne. A kwance ta ganshi ya cukwikuye kansa da bedsheet wurin son ya sauko. Ƙarasawa ta yi bakin gadon ta kira sunansa da taushin murya. Yana ganinta kuwa ya saki dariyar ganin idon sani. Ɗan da bata taɓa riƙe ko da yatsansa ba saboda ƙiyayyarta ga mahaifiyarsa da kakansa ta rungume a ƙirjinta tana rarrashi. Tsayuwar mutum taji a kanta ta kuma san ba kowa bane illa Shaheed ta waigo a nutse.
"Kirawo matarka."
Jim ya yi yana son yi mata rashin kunya amma kwarjininta ya hana. Dole ya fita ba daɗewa suka dawo tare da Sariat. Tashi ta yi ta jujjuyata a gabanta ta kalli cikinta na huɗu wanda ya fara tasowa. Tunda ba hausa Sariat take ji ba sai Haj. Manga tayi masa magana da turanci.
"Haka aka koya maka hukunci ba bincike? Yanzu da banji me ku ke cewa ba sai ka koreta da cikin nan?"
Turo baki ya yi ya gama tattaro maganganu masu zafi zai faɗa amma sun makale. Samun kansa ya yi da tambayarta me ya haɗata da iyalinsa.
"To zauna mana ka tsaya min a ka." Ta ce tana ɗaure fuska. Ba yadda ya iya ya janyo stool a gaban madubi ya zauna. Ita kuma ta ja hannun Sariat ta zaunar a kusa da ita akan gadon. Iya abinda ta sani zahiri da wanda kunnuwanta suka jiye mata tun daga waye Alh. Audi a garesu har zuwa rasuwar Papa Abayomi da nema masa aiki da ta yi cikin sirri ta warware masa. Shaheed dama akwai raguwar zuciya. Zancen mahaifinsa kawai da aka yi ya sanya shi zubar da ƙwalla.
"Meye haka kuka a gaban matarka ko kunya babu? Me yasa Tauhida ta fika dauriya ne?"
Haj. Manga ta ce da hausa tana dariya. Murmushi ya yi kai a ƙasa ya kasa kallon Sariat da ya gama yiwa rashin mutumci yanzu-yanzu. Wayar Haj. Manga ce ta soma ƙara ta ɗauka ganin sunan Dr. Madaki. Tana karawa a kunne ya ce,
"Kada ki ce komai kawai ki saurara, yarinyarki ɗinnan na gani a asibitinmu tare da Alh. Audi." Tana jin haka ta kunna speaker.
"Wace yarinyar?"
"Wadda ya aurawa ɗansa shekarun baya."
Daga inda Shaheed yake ya taso da sauri ya dawo kusa da ita ya zauna. Zai yi magana ta girgiza kai tare da dora yatsanta akan leɓe. Su uku suka kasa kunne suna sauraron maganganun da suke tashi a ofishin Dr. Madaki. Alh. Audi ne ya share munafukan hawayen da suka taru da ƙyar idanunsa akan Tauhidat da jikinta ya yi sanyi kalau bayan ganin halin da Shamsu yake ciki.
"Nayi nadamar kin dawo dake gidan Shamsu da na gano sharrin yarinyar nan Suwaida. A tawa wautar zaki fi samun nutsuwa idan na nesantaki dasu duka. Shamsu bai san darajarki ba sai da ya sakeki. Ya so ƙwarai na jagoranci mayar muku da auren ni kuma na dage sai kin gama karatu kin wuce ajin da miji ko kishiya zasu taka ki son rai. Ashe tsautsayi na gaba..." Magana yake yana ta kwana-kwana. Su Haj. Manga hankulansu a tashe tunda ya fara zancen yana dana sanin rashin mayar da aurenta da Shamsu. Tauhidat sai ta kalle shi ta kalli Dr. Madaki da Alh. Ari sannan ta ce,
"Alhaji me ya kawo wannan maganar? Kada kaga kamar saboda haka naƙi karɓar case ɗinsu Susu. Nanna ta ce ta ɗaukarwa Jamal lawyer ita kuma Susu ..."
Bai jira ta ƙarasa ba ya sake karyar da wuya gwanin ban tausayi.
"Suwaida ta san bata kyauta miki ba shiyasa take jin kunyarki tana ganin kamar ba zaki wakilceta tsakani da Allah ba. Ni kuma wannan abu don yafi ƙarfina ne da zan zo muci mu cinye a cikin gida. Dr. Madaki yi mata bayanin abinda ka ce Shamsu zai buƙata a tafiyarsa zuwa UK."
Dr. Madaki ya fara da bayanin girman abinda ya sami Shamsu sannan ya kare da cewa, "yana buƙatar wanda zai dinga bashi kulawa sosai ba nurses ɗin asibiti ba kawai. Misali ɗan uwa ko mata wanda ba zai gaza da taimaka masa ba."
Faɗuwar gaban Tauhidat ta faru tare da ta Shaheed da Haj. Manga. Sun riga sun dago inda ya dosa. Amma duk da haka Tauhidat bata ce komai ba ta barshi ya gama bayanin rainin hankalinsa tukunna. Alh. Ari ne ya ƙarasa faɗa mata cewa suna neman alfarmar ta amince a sake ɗaura mata aure da Shamsu.
"Idan kina so zan biyaki ko nawa ne don ki kula min da rayuwarsa. Waɗanda ya kamata su tsaya masu sune suka sanya shi a cikin wannan yanayin. Ni kuma dole ana buƙata ta kamfani saboda satar kuɗaɗen ta taɓamu sosai. Kiyi min wannan alfarmar idan kun dawo kina son a raba auren ni da kaina zan sa shi ya baki takardarki."
[2/23, 7:34 PM] Nasma: Oga ya faɗa masa cewa za ta amince shiyasa hankalinsa kwance yake ta magana. Ya so ya sami hanyoyin halakasu ita da Susu da Jamal da sunan maƙiya ne suka yi ana tsakar case ɗin to gashi sunƙi amincewa da ita. Haɗa auren ya turasu can a hanya ya mata sharrin da ƙasar zasu bindigeta yake nema. Burinsa su duka waɗanda aka ce zasu zame masa alaƙaƙai su bar duniya ko ya sami nutsuwa. Haukan Susu akan Mubeen ya janyo masa sabon aiki duk da dai ba wai yana jin tsoro bane don bai ɗaukesu a bakin komai ba.
"Alhaji kayi haƙuri ba taimakon nasa bane bana son yi amma an riga an ɗaura aurena biki ne ya rage."
"Da wa?" Ya ce da sauri.
Haɓar hijabinta ta janyo ta rufe fuska wai ita kunya ta tashi ta bar office ɗin da sauri. Tana fita ya buga teburin Dr. Madaki fuskarsa kamar an aiko masa da mummunan saƙo ya dubi Alh. Ari,
"Ka binciko min gaskiyar maganar nan. Na daɗe ina zargin yarinyar nan akwai abinda ta sani game dani. Kai kuma..." ya nuna Dr. Madaki da ya yi tsuru kamar da gaske tsoronsa yake ji, "ka cigaba da yi masa shiri tafiyar ba fashi. Ka kuma iya bakinka, rufin asirin Shamsu nake so ko ta wane hali kada duniya ta zagar min ɗa."
Fita suka yi su biyun ya ɗauki wayarsa da ya kifa a jikin wani ƙaton littafi ya katse kiran. Abinda yake so Haj. Manga ta ji ya san ta ji. Original report ɗin Mubeen ya ɗauko ya sake karantawa sannan ya mayar inda ya adana takardar. Idan da hannun Alh. Audi a mutuwar abokinsa Alkali Umaru wato Baffan Haj. Manga to ya yi alƙawarin da wannan report ɗin zai yi amfani. Da fitar Tauhidat da gudu har tana tuntuɓe ta isa motarta ta shige. Hannunta na rawa ta lalubo wayarta ta kira Shaheed. Yana nan zaune kusa da Haj. Manga kamar mutum mutumi tunda yaji abinda ya ce. Da sauri shi ma ya amsa kiran nata. Kuka yaji tana yi wanda ya taɓa masa zuciya.
"Broda ka sama min miji daga yau zuwa gobe don Allah ka aurar dani. No, wait, zan faɗawa Deji idan da gaske yake ya kawo sadaki gobe a ɗaura aure. Kai amma Broda ba na son shi wallahi."
"Ki nutsu Tauhidat" ya ce da rarrashi.
"Ta ina zan nutsu? Ka san me Alh. Audi ya ce min kuwa yanzu?"
Haj. Manga ce ta karɓe wayar don shi ma speaker ya saka.
"Tauhida kin san school ɗina?"
"Nanna?" Ta ce cike da mamaki.
"Kin san makarantar?"
"Eh"
"To ki same mu a gidan da yake jikinta daga hannun dama. Zan sanar da maigadin idan kin rigamu zuwa ya buɗe miki."
Kashe wayar ta yi ta dubi Shaheed da Sariat"
"Ku haɗa abinda zaku iya na kayanku ka ɗauko yaran daga makaranta yanzu mu tafi. Alh. Audi ba zai haƙura ba tunda ya kawo zancen auren nan sai ya binciko gaskiyar lamari game da aurenta. A wannan binciken kuma za a iya ganin Aidan."
Sariat ta kalli yadda ya jiƙe da gumi da hawaye, "Tunda aka fara wayar ɗazu da yaji muryar Alhajin yake kuka."
"Na riga na san cewa case ɗinnan yafi yadda muke tunaninsa. Yanzu dai Shaheed ina da alfarmar da zan roƙa nima a gareka."
Juyowa ya yi don jin me za ta ce sai ta nuna masa hoton wani kyakkyawan matashi wanda kana ganin kayan jikinsa za ka gane cewa likita ne.
"Ɗana na fari kenan Arƙam wanda na baka labarin dalilin ɓatansa. Abinda ban faɗa maka ba shi ne sun so juna shi da Tauhidat sosai amma aurenta na bazata da Shamsu ya shiga tsakaninsu."
"Amma bata taɓa yi min zancensa ba."
"Abubuwa da yawa sun faru da baka sani ba Shaheed. Kaine uba ga Tauhidat a yanzu saboda haka zaɓi yana gareka. Wa za ka bawa aurenta tsakanin Arƙam Ibrahim Karam da Shamsuddeen Audi Karam?"
Buɗar bakinsa zai bata amsa sai sai jin wayarsa ya yi ta ɗauki ƙara ba zato ba tsammani. A take ƴar guntuwar nutsuwar da da ta rage masa ta kama gabanta. Yana karata a kunnensa kuwa ta yi masa wani nauyi na musamman a hannu saboda amon muryar Alh. Audi da ya ji. A take jikinsa ya ɗauki rawa, har sai da wayar ta faɗi a ƙasa ta tarwatse. Cikin tsoro yake faɗawa Haj. Manga waye ya kira a lokacin da yake haɗa wayar cikin sauri tana ƙara watsewa. Karɓa ta yi ta haɗa masa ta kunna. Ya miƙo hannu zai karɓa ta tsare shi da idanuwanta masu tarin kwarjini da haiba.
"Ka nutsu kai ba yaro bane. Idan kayi abinda zai sa ya zargi wani abu mu duka ne zamu ji a jikinmu. Na tabbata da Tauhidat ce ba zata yi haka ba saboda rainona ce."
"Gori ki ke yi min?" Ya tambayeta a ƙoƙarinsa na sako wasa domin ya saita kansa. Wayar ce ta sake shigowa, ya sake ɗauka yana bashi haƙuri da cewa faɗuwa ta yi. Ƙorafi Alh. Audi ya fara yi masa na rashin zuwansa jajanta masa halin da gidansa yake ciki. Cike da dakiya don ya burge Haj. Manga, Shaheed ya ce, "jiya na dawo garin nayi tafiya ne tare da maiɗakina. Mahaifiyarta ce ba lafiya tun a can naji labari. Gani nayi abin yafi karfin waya shi yasa ban kira ba nace sai dai na zo. Yanzu ma dawowata kenan daga office ko zama banyi ba na zo ɗaukar matata zamu taho."
Kai Haj. Manga ta girgiza kawai. Irin wannan dogon sharhi babu ko jan numfashi da yake yi ba shi ne nutsuwar da take so daga gareshi ba.
"Bana gida amma zaku sami Fanna. Yanzu muka rabu da Tauhida tazo duba Shamsu tana ta kuka."
Kalmar zagin da ta kusa suɓuce masa da yarbanci ya yi saurin daƙilewa, sannan ya nuna nasa alhinin na abinda ya sami Shamsun. Alh. Audi ya nuna jindaɗinsa sannan ya koma mitar ya akayi ya aurar da Tauhidat bai aiko masa da kati ba. Tun rasuwar mahaifinsa ya janye jiki daga gare shi amma ko sun ki ko sun so shi uba ne garesu.
"Ya sunansa kuma aikin me yake yi?" Ya tambaya a zuwan shi fa uba ne dole a bishi.
"Likita ne ɗan Kano." Ya amsa da sauri.
"Bahaushe ne kenan? Nan da kwana biyu bayan Shamsu ya tashi zuwa asibiti kana ganin zai iya zuwa gaisheni? Ko yaya zan so nayi wani abu a matsayin uba ga ƴar marainiyar nan. Ka bar zuwa ta'aziyyar ku zo tare."
Shaheed amsawa ya yi tare da ban haƙuri ya kuma tabbatar masa da cewa zasu zo in sha Allahu. Fayyacewa Haj. Manga yadda suka yi ya yi ta ce kada ya damu, amsarsa kawai take jira game da wanda ya zaɓawa ƙanwarsa. Ya san wanda ya kamata ya zaɓa, amma duk da haka ya ce ta yi masa haƙuri suje gidan ya gana da ita. Bata ƙi ta tasa ba ta ce su shirya nan da dare su taho. Sai ya nuna mata baya son ya bar gidansa zasu zame mata ƙarin nauyi. Da yaga ta matsa sai ya amince amma na ranar kawai. Washegari zasu dawo gidansu shi da yaran sai Tauhidat ta zauna a can tare da Aidan.
Bayan fitarta haƙuri ya bawa Sariat akan abinda ya yi mata sannan suka fara haɗa kayansu. Ita kuma Haj. Manga wurin...


Read / Download CIZON YATSA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album