Join Our WhatsApp Group

A MAKABARTA AKA HAIFE NI Complete Hausa Novel Document by A MAKABARTA AKA HAIFE NI


A MAKABARTA AKA HAIFE NI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 54911



A MAKABARTA AKA HAIFE NI

Reading Time: 4 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Nabila Rabi'u Zango ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 342.29 kb

File Type: txt

Views: 816+

Download: 301+

Last download: 21 hours ago

Description/Story: A MAKABARTA AKA HAIFE NI

Na Nabila Rabi'u Zango

Ebook creat by Shuraih Usman

Ebook publish by www.hausaebooks.cf

Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai

Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com



[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Bismillahir Rahmanirrahim, inafarawa da sunan Allah megirma da daukaka. Yanda zanfara rubutun nan lafiya

Allah yabani ikon kammalashi lfy.

GARGADI..... Banyarda wani ko wata su juyamun littafi naba, ko kuma su canzamun labarina. Allah yabada ikon

kiyayewa.

GODIYA.....Ina mika godiya ta ga dukkanin masoyana wadanda nasani dama wadan da bansani ba, nagode da

irin kaunar da kuke mani, duk da bazan samu damar

binku inyi maku godiya ba, amma nayi amfani da

wannan dama ga duk wanda yakaranta yazama

amatsayin sakon gaisuwa zuwa gareshi. Allah yakara

dankon zumunci.

Season 1⚜5

Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo

wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin

keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da

mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake

masa duk bayan kwana 3.

Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance

kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya

yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana,

Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine

hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.

Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin.

Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace

zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka

wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a

akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma

kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya

Uba daya suke.

Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi

yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi

afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa

farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.

Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan

mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh

Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska

acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da

Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika

sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya.

Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu

dasena zama babba ba, inde zanzama 'yar kore kuma

inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene.

Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki

Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu

muna cikin masarautar.

Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta

maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa

tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda

babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki

acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu

wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa

dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na

mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba

Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya

tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha

labari.

Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka

ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar

MAKABARTA. Wani tsohon kwanone ahannunta,abinci

ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba.

Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18

aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan

tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun

bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta

kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.

Dariya Uwar tayi cikin halin hauka tace a,a Babyta yau bazanci abinci ba, kece zaki faraci, dariya yarinyar tayi mata, dan taji abinda tafada, sede kawai maidawa ne

bata iyayi (KOMEYE DALILI

O

🤔 OHO HO 路♀ MUJE ZUWA).

Matsawa Wadda naji ankira da Baby tayi kusa da

Mamanta tasa hannu tafara bata abincin, itama hannu

tasa tana bata abinci. Kwalla ne, suka zubo ma baby tayi saurin gogewa.

Wani Kyakkyawan Matashi ne, me kama da Larabawan

Shuwa, baze wuce shekaru 25 aduniya ba, da Sallama

yashiga dakin kyakkyawar matar, wacce take kishingide

abisa kafet din dakin. Murmushi tayi tace, Yarima Arif

sannu dazuwa. Kwanciya yayi kusa da ita yace yauwa

Momy na, sannu da hutawa. Kallon bayin cikin dakin

tayi, lokaci guda suka fita, Madarar shanu tamiko mashi, ya amsa yana murmushi, yace Momy naje gurin Abba

ance yana dakin ganawa da baki, kuma inason magana

dashi. Kanshi tashafa tace to ai sekayi hkr kajira yagama ko, wace irin magana kakeson yidashi? Momy dama

akan rashin lafiyar Baffa ne,tunda nadawo naga

yakamata ace anfitar dashi waje ko za,a dace. Murmushi

tayi tace Arif bakasan komai akan ciwon Yaya ba,

Abbanka yana kokari sosai amma koma menene idan

yafito zamu gana dashi. Kwallan idonta tagoge.

Kubiyoni domin jin labarin masarautar.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

08028525263

[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ...🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

AMAKABARTA AKA HAIFENI

🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤

(The story of hard kingdom)

Nah

Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO

(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association

(H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

Season 5⚜10

Zaune suke adakin memartaba sarki Qaseem, Areef

yadora kanshi asaman kafar Abbanshi, Gimbiya Shuwa

Momyn Areef tana kusa da Sarki tana gyara mashi Inibi

tana mika mashi. Sarki yashafi kan Areef yace Yarima

inajinka wace magana kakeson kafadamun?

Tashi zaune Areef yayi yadauki inibi yasa abakinshi yace Abba dama akan maganar Baffa ne, naga yanda nabarshi

haka nadawo nasameshi, shine nace meze hana afitar

dashi waje koza,a dace. Murmushi Sarki yayi yace wlh

Yarima nafika son inga Yaya yawarke, kozamu samu

damar yin bincike akan babbar matsalar datayi

sanadiyar shigarshi wannan halin. To amma Abba baka

ganin fitar dashi ze iya temakawa gurin samuwar lfyrshi tunda acan sunfimu kayan aiki?

Hakane Yarima, amma babu yanda banyi da Yaya akan

yabari afitar dashi ba, yakiya gashi ba magana yakeyi ba, sede yana jin duk abinda muke fada, yana ganin kamar

gara abarshi yayi tazama haka, wanda kuma hakan

bashine mafita ba, dole se mutum yana da lfy yake iya

komai arayuwarshi, ni babban damuwata wadancan

munafukan matan nashi, danni wlh haryanzu banyarda

dasu ba. Gimbiya tace hakane Me martaba, sede kasan

bamuda wata hujjar dazata nuna mana sune sanadiyar

faruwar komai agidan nan, kamarde yanda kace acigaba

da addu,a hakan zamuyi, fatanmu de Allah yasa Fulani

da abinda ke cikinta koma menene, yasa suna raye,

kuma cikin koshin lafiya.

Sarki yace amin. Kallon Areef yayi yace Yarima yanzu

angama karatu gashi zaka fara aiki kaga dole ace kaima

kashigo sahun manya ko? Kwantar da kanshi yayi saman

cinyar Gimbiya ya lumshe idonshi, shiru yayi bece komai ba. Gimbiya tace Yarima yanaji kayi shiru kode boye

mana surikar tamu kakeyi? Murmushi yayi sosai wanda

har seda dimple dinshi ya lotsa duka 2, yace Momy

kubar maganar nan, niharyanzu banga macen danakeso

ba. Sarki yace aiko Yarima yakamata ace kafara

nemanta, dan kasan bazamu barka kazauna haka ba,

atsarin masarautar nan kasan baza,a barka kazauna haka

ba, damma de Yaya beda lafiya, ai da tunkafin kadawo

anduba maka acikin 'ya'yan sauran masarautun ansama

maka mata.

Dariya Areef yayi yace haba Abba niko aure zanyi ai

banason yar gidan sarauta, nafison insamu mace wadda

bata tashi acikin sarauta ba, kuma nibanason mace

wadda zatazo tarika rainamun iyaye, kawaide akaramun

lokaci ahankali zansamo wata wadda ra,ayina yayi dede

da ita.

Harararshi Gimbiya da Sarki sukayi atare, Sarki yace

uhm Yarima idanma mafarki kakeyi to kadena, acikin

masarautar nan babu yanda za,ayi kashigo mana da

bare, dole se yar sarauta, kana ganin yanda Momynka

dani kaina muka fito daga gidan sarauta, jininmu gaba

da baya cike yake da sarauta, kai kuma yanzu sekafara

zuwa mana da wani batu. Ka godema Allah Yaya beda lfy,

da kila seyafini daukar zafi akan wannan magana taka.

Duk da shima matar daya aura ta 2 data 3 basu fito daga cikin gidan sarauta ba, amma kowa yayi mashi uzuri,

matarshi ta 2, agidan nan kowa yasan yanda akayi ya

aureta, haka ma ta 3 dole ce tasashi ya aureta, sekuma

babban rabon daya shiga tsakaninsu, bayan wannan

babu abinda zesa Yaya ya auri wata mata wadda ba,a

gidan sarauta ta taso ba.

Gimbiya tace Allah yahuci ranka Me martaba, banason

ranka yana baci akan wannan maganar, abinda bamu

taba yima Yarima agidannan ba, Fada shine yau da

bakinka kake mashi, kaima kasan Yarima mebin duk

wani umarninmu ne, ai base anbata mashi rai ba,

sekasashi shiga damuwa, wanda kuma betaso acikinta

ba, karka manta mungina rayuwarmu abisa soyayya dan

Allah kada kabari zafin zuciya yacanza maka zuciyarka.

Sarki yakamo Areef wanda idonshi har yayi ja dan bacin

rai.

Kwantar dashi yayi saman kafarshi yana shafa kanshi

yace ba ina nufin bata maka rai bane, kaji, kawai ina

maka tuni da ra,ayin masarautarmu ne, banaso kasa

wannan aranka haryadameka. Hawayene suka zubo daga

idon Areef, cike da damuwa Gimbiya tamatso kusa dashi

tace kagani ko, kalli abinda kajawo mashi, yaushe rabon da Yarima yayi kuka agidan nan? Inajin tun yana yaro,

jawoshi tayi tamaidashi saman kafarta tace Ya isa haka

Yarima na, kasan Abbanka yana sonka baya son bacin

ranka yishiru hakanan.Sarki yace ya isa haka maganar

tawuce kaji, amma kaima kaje kayi tunani.

Lumshe ido Areef yayi, aranshi yana fadin akwai babban

aiki agabana, kuma gaskiya yanda ra,ayina yake bazan

taba canzashi ba, bana bukatar yar sarauta, duk da

haryanzu bansamu wadda nakeso ba, amma zantajira

seranan dana samu sannan, nasan suna sona, dole zasu

barni na auri ra,ayina. Amma dole nacirema su Momy

wannan ra,ayin nasu.

Anesa da masarautar Sarki Qaseem, wani dankaramin

gidane, me kyau, duk da karami ne, amma anyi mashi

gini mekyan fasali. wani tsoho ne, fari, yafito daga cikin gidan, daka ganshi zaka gane ba asalin bahaushe bane,

yafi kama da irin larabawan dasuka baro garinsu sukazo

nigeria har zama yakamasu anan, zama yayi bisa wata

kujera dake kofar gidanshi ya kunna redio yana kokarin

kamo tasha.

Tundaga nesa yahango fadawan sarki suna zuwa,

murmushi yayi, cikin hausarshi wadda bata gogeba, yace

aikin kenan, kullum azo adameni da kira, kuma haryanzu

ankasa samo mani Diyata, da abinda ke cikinta. Kwallar

data zubo mashi ce yasa hannu yagoge. Da sallama suka

karaso gurinshi, ahankali ya amsa masu. Daya daga cikin fadawan yace Barka da hutawa Baba, yace yauwa

sannunku, yauma wani kiran neko?

Murmushi Bafaden yayi yace a,a Baba, dama Sarki ne,

yace muzo mukawo maka kayan abinci. Murmushi yayi

yace to madalla, nagode, yajikin me martaba? Bafaden

yace to Baba dasauki zamuce, kasan sauki sede agurin

Allah, fatanmu de Allah yanuna mana inda Gimbiya take

ko zamu samu Hankalin kowa ya kwanta. Baba yace

addu,a kam kullum munayinta, sede haryanzu acikin

raina nakasa yarda cewa Rayhana itace tabar gidan Sarki da kanta, kuma nakasa yarda cewa bata raye, inaji

ajikina wata rana zamu gana da ita, fatana de Allah yasa kome tahaifa ace yana raye. Sukace amin Baba, bara

mushigar maka da abincin ciki, yace tonagode, dama

gashi bayin dasuke dafamun abincin sungama aikinsu

suntafi, kushigarmun dashi ciki.

Jakadiya ce take tafaman Sallama abangaren Gimbiyar

Babban Gida, daga ciki akace shigo mana Jakadiya, tace

Gafaranku de, ai nadauka ko bacci kikeyi, Allah

yatemakeki Babbar Gimbiyar Sarki, Allah yakaramaki

lafiya da tsawon kwana, Allah yabaki muma musamu

awajenki, ke kadaice Babbar mata agurin Sarki, duk

wanda yazo sede yabiyo bayanki. Daga gefe Gimbiya me

Daki tarika wurga mata harara jin irin kirarin datakeyi ma Kishiyarta.

Murmushi Gimbiyar Babban Gida tayi tamata nuni data

zauna, guri tasamu tazauna sannan takalli Gimbiya

medaki tace Ina gaisuwa ranki yadade. Murmushi tayi

tace sannu Jakadiya, daga ganin bakinki akwai magana,

meke tafe dake?

Babban labari ne yake tafe dani kuwa Gimbiya. Dazu

nazo wucewa tagefen Dakin memartaba Sarki Qaseem,

senaji yana magana kamar yana fada, dajin haka nayi

saurin daukar tsintsiya nayi kamar ina shara, sede na

boye fuskata, gudun kada aganni tunda ansan ba,a

bangarensu nake aiki ba, asalima nice mebada umarnin

ayi aikin........ nan takwashe duk abinda taji sunfada ta fada masu.

Tashi zaune Gimbiyar Babban Gida tayi, tace gaskiya naji dadin wannan labari naki Jakadiya, dan haka kina da

kyauta me tsoka. Washe baki Jakadiya tayi tace godiya nake Gimbiya, Allah yakara girma. Amma Me daki wace

irin shawara kike ganin yakamata mubi don mu samu

muyi amfani da wannan dama?.

Gyara zama tayi tace, inaganin tunda har Sarki ya furta Bayason Yarima ya kawo mashi bare, meze hana kisamo

daya daga cikin matan gidan sarautarku kimaidota gidan

nan. Murmushi Gimbiya tayi tace Medaki kenan, kina

tunanin Gimbiya Shuwa zata bari Yarima yaso wata data

fito daga bangare na? Kinfi kowa sanin bama ga maciji

da ita, dan haka wannan shawara taki bata karbu ba.

Jakadiya kawo mana mafita.

Kara hade rai Medaki tayi jin ba,a karbi shawararta ba, sede yata iya, tunda bata da karfi agidan, dole tabi

asannu kodan tasamu fada. Jakadiya tace Gimbiya

inaganin tabayan gida yakamata mubiyo masu, tunda

bazasu taba karbar abinda yafito daga gurinki ba,kamar

yanda mukayi da farko yanzuma hakan yakamata ayi.

Kayataccen murmushi Gimbiya tayi tace haka nake sonki

Jakadiya. Allah yakaimu.Yarima Areef ne kwance adakinshi, shida abokinshi Haisam, suna fira, Haisam yace Yarima yanaga kamar

wani abu yana damunka? Yamutsa fuska Areef yayi yace

kawai kabari Man, wlh jiya Abba da Momy suka kusa

samun hawan jini. Dariya Haisam yayi yace uhmm nasan

wasa kakeyi, yanda Abba Da Momy suke sonka, harzasu

iya bata maka rai, kaifa agurinsu haryanzu yaro ne, dan haryanzu baka girma da hawa cinya ba. Areef yace

banason sharri, idan wasu sukaji kace hawan cinya ai

sesu dauka rungumeni akeyi.

Dariya suka saka, Areef yace wlh Man ba maganar wasa

ba, aide kasan irin burina akan matar danakeso na aura

ko? Yace E, yauwa to jiya daga nafada masu kalar matar

danakeso shikenan, suka rufeni da fada, kasan ai ra,ayin momy da Abba duk daya ne, kuma nasan wannan

magana dasuka fada harcikin ransu. Haisam yace kada

kadamu, kaida ko matar ma baka samuba, meye naka na

damuwa?.

Areef yace kaide ai dole nadamu, kasan me kwarmin ido

dawuri yake fara kuka. Haisam yace abinda nakeso

dakai, addu,a zaka cigaba dayi domin itace mafita,

nikaina bana maka sha,awar auren macen gidan sarauta,

kasan mata da sarauta, basu iyata ba, nafison kaje waje ka auri wata daban, hakan zebaka kwanciyar hankali

sosai. Areef yace nima ai jinsu nakeyi, dan bansamu

wadda nakeso bane, shiyasa nayi shiru, amma duk

lokacin dana samu, agskiya sede kowa yayi hkr, dan

bazan iya biyayya anan gurinba. Haisam yace muje

mugaida Baban Umma fulani kwana 2 bamuje ba, tashi

Areef yayi yana fadin wlh nima yana raina, dan

bakaramin tausayi yake bani ba, ace mutum yazo gari da

iyalinshi amma yanzu beda kowa, matar ta mutu diyar

kuma babu wanda yasan halin datake. Muje mudawo,

dan dazu waziri yake fadamun gobe zamuje darazo wai Abba ze aikemu. Haisam yace kai gsky zanje, nima

inason zuwa Darazo, fita sukayi suna dariya.

Washe gari tunda safe suka dauki hanyar bauchi, daga

can suka wuce darazo, tare suke da Jakadiyar Gimbiya

Shuwa, dan itama garinsune shiyasa tabiyosu tanason

tayi kwana 2. gidan wani babban malami sukaje, kuma

dama shine malamin dayake masu addu,a akan batan

matar Sarki Fulani. Bayan sungama gaisawa, suka fadi

sakon Sarki, malam yace haryanzu muna nan muna

addu,a sede kuma babu abinda ya nuna mana bata raye,

akullum muna ganin tana raye, kuma akusa damu, danni

abinda nake gani tafi kusa dani akan inda kuke, to Allah shine masanin gaibu, shikadai yafimu sanin gsky. Zamu

cigaba da addu,a har Allah yasa mudace.

Ruwan addu,a yabada akaima Tsohon Sarki, godiya

sukayi mashi, Waziri yasa fadawa suka shigo da kayan

dasukazo dasu. Waziri yace to muzamu koma. Malam

yace tonagode, kallon Jakadiya yayi yace ammade

Jakadiya ke anan za,a barki kidan mana kwana 2 ko?

Tace E Malam, dama cewa nayi inzo inganku. Yace to ai

yayi dede kishiga daga ciki. Tashi tayi tace to Yarima

Allah ya kiyaye. Yace amin sekin dawo.

Bayan suntafi wani tsoho yazo...


Read / Download A MAKABARTA AKA HAIFE NI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On A MAKABARTA AKA HAIFE NI
avatar
najjwa

2 months ago

Reply

gaskiya littafin yanada dadi

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album