Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR SADIK book 2 Complete Hausa Novel Document by MATAR SADIK book 2


MATAR SADIK  book 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 8996



MATAR SADIK book 2

Reading Time: 0 Hours

Added On: 22, Sep 2024

Author: Zainab Dodo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : TASKIRA WRITER'S FORUM

Author Phone : 09046495943

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 50.15 kb

File Type: txt

Views: 378+

Download: 187+

Last download: 4 days ago

Description/Story: 🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣8️⃣➡️1️⃣9️⃣

Washe gari
Sadik da yaje masallaci bai dawo ba sai da gari ya d'an fara haske sannan ya shigo gidan, d'akin khadija ya shiga, bata falo dan haka ya wuce ciki, kwance ya ganta saman gado tana sanye da wata rigar bacci red colour, rabin cinyoyin ta duk a fili, rigar kuma mai santsi ce duk ta kwanta a jikin ta, bai san lokacin da ya isa gadon ba har ya haye, hannun sa ya d'aura saman mazaunanta tare da shafawa a hankali


Cikin bacci taji ana shafata, ahankali ta bud'e idanuwanta dake cike da bacci, dan jiya bata samu wani baccin kirki ba, juyowa tayi tare da sakar masa murmushi Shima ya mayar mata, kallan idanuwan ta yake ganin sun d'an kumbura kana yace" Meya hanaki bacci? "Bakomai " gayamin dai" ya fad'a yana shafa jikin ta "Dagaske baccin ne yak'i zuwa min "Uhmmmm kodai kodai kinyi missing d'in, ya fad'a tare da ida maganar a kunnen ta, dariya tasa tare da fad'in"Bawani "


hannun sa yake k'ok'arin turawa cikin rigar tayi saurin rik'ewa tare da fad'in " Gafa matar ka can a d'aki" Ke kuma fa? " To ai kaga ba girki na bane please ka daina bana son mu shiga hak'k'inta " To wani abun nace zanyi? " Uhmmm bacci zanyi" Sauka yayi saman gadon ya nufi hanyar fita, dan maganar da ta masa ma ta 'bata masa rai,

da kallo tabi bayansa har ya fita, ta k'ara gyara kwanciyarta taci gaba da bacci



Yana fita daga d'akin yayi d'akin balkisu, itama tana nan kwance tana sharar bacci, duk da ita ce da girki amman aikin uwar komai batayi ba tayi kwanciyarta, falo ya dawo ya kwanta saman kujera, har ya kwanta ya tashi ya fito ya d'ibi ruwa yaje yayi wanka ya shirya ya je ya gaida Mahaifiyar sa ya fita




Balkisu koda ta tashi bata gansaba kuma bataji motsin sa gidan ba, ta fito ta had'a musu breakfast, ta kaima kowa nasa, khadija yau wankan k'ananun kaya akayi, balkisu da taga hakan itama taje tayi, dan ta lura idan khadija tayi irin wannan shigar sadik zai ta lik'e mata shiyasa itama taje tayi,


Da ta fito sai da dariya taso ku'bucema khadija, wallahi ko kad'an kayan basuyi mata kyau ba ga k'asusuwan wuya da take saki, tana tafiya tana wani juya jiki kuma jikin nan yak'i juyuwa

Khadija kasa jurewa tayi da taga tana wata tafiya sai da ta dara tare da fad'in " Ayi dai mu gani in tusa na hura wuta " Balkisu taji ta sarai ta kyale





Sadik koda ya dawo daya kalleta sai da ya fashe da dariya yayi mai isar sa,Sannan yasa ta cire su






Yau ma kamar jiya maganin ba aikin da yayi, bak'in ciki duk ya dameta musamman idan ta tuna bashin da ta kar'bo gashi tun jiya tayi alk'awarin zata kai kud'in amman har yanzu, gashi bata da ko sisi, tayi zaune bakin k'ofar d'akin ta tayi tagumi, muryar da taji tayi sallama ne yasa sai da cikin ta ya murd'a


Tashi tayi da sauri zata shige d'aki matar tayi saurin fad'in " Dakata dakata" ta k'ara so wajen " Ya mukayi dake eh har gida kuka sameni kuka lullu'be ni da bak'in bargo kukamin dad'in baki na d'auki kud'i na baku kuma sai da na fad'a muku uzurin da gareni kuka ce zaku bayar tun jiya nake dubin ku amman shuru ashe bakusan halarciba to idan baku zo ba ni gani nazo shiga d'auko min kud'i na" matar ta fad'a tare da Mik'a hannun ta


Susar kai balkisu ta fara tare da fad'in "Yi hak'uri shigo daga ciki muyi magana" Ke! Ke!, matar ta fad'a cikin d'aga murya " Dubi idona ki gani banda mutumci game da kud'i kafin kuje baku tambayi ko ni wace ba to wallahi ba inda zanje kud'i na kawai na sani "Dan girman allah kiyi hak'uri ki rufamin asiri mu shiga daga ciki bana son kishiyar nan tawa tasan abinda ake ciki" Au ai baki gudun abun kunya tunda har kika iya cin bashi ni duk ba wannan ba shin akwai kud'in ko babu? " Girgiza mata kai tayi tare da fad'in"Babusu " To ai ta kwana gidan sauk'i d'akin ki zan shiga na za'bi abun kud'ina" Dan Allah kiy"bata ko ida maganar ba matar ta tureta ta shige d'akin





Khadija na d'aki tana karatun al'Qura'an taji hayaniya sai da takai aya sannan ta fito, tayi tsaye bak'in k'ofar ta




Dube_dube take taga bata ga abun d'auka ba, taja tsaki ta fito, fita tayi daga gidan, balkisu har tana jin dad'i, jim kad'an sai gata ta dawo tare da wasu maza su biyu a bayan ta, d'akin ta nuna musu tare da fad'in "Babbar nan zaku d'auko"



Mama ce ta fito daga 'bangaren ta, ta nufosu tana fad'in "Lafiya kuwa" Mama lafiya k'alau, matar ta fad'a taci gaba da fad'in " Bashina aka ciyo nazo kar'ba babu kud'i shiyasa zan d'auki abun kud'i naje na siyar na rik'e kud'i na" Subhanallah y'ar nan da kinyi hak'uri in Sha Allah za'a biyaki kud'in ki"



" Hmmmm mama ina ganin girman ki dan allah ki cire bakin ki a wannan maganar "To allah ya kyauta"Amin


Fitowa sukayi da babbar kujerar d'akin ta, sukayi waje da ita itama matar tabi bayansu





"Haba balkisu! Haba balkisu!, khadija ta fad'a" Ai wannan abun kunya ne wallahi azo har gida a cimaka mutumci akan bashi gidan nan baki rasa ci ba baki rasa sha ba amman wai bashi kikaje kika ciyo" To ina ruwan ki bak'ar munafuka algunguma ta k'asa da wutar jahannama "

" Wa'iyazubillah, mama ta fad'a " balkisu wannan wane irin jahilci ne yake kan ki kike fad'a mata wad'an nan kalaman akan ta gayamiki gaskiya "


"Dallah tsohuwa dakata min, balkisu ta fad'a cikin tsiwa tana nuna mama " Nifa bana son katsalan da cikin al'amari na waya gayyato ki cikin maganar bana son shishshigi ehheeeeeee"

"Balkisu badai rashin kunya zaki mata ba" khadija ta fad'a

" Ban mata rashin kunya wacece ita ko dan ina auren d'an ta shikenan sai aka ce nima uwata ce mtsssww...................................


"Ni wallahi uwar miji ba uwata bace Allah ma ya tsare wannan ta zamo uwata" ta fad'a tare da nuna mama


Saukar mari taji a kumatun ta, tayi saurin dafe wajen ta d'ago kanta, khadija ce ta mare ta " Ya isheki haka balkisu idan kin min na kyale ki bazan juri ganin kinama mama na kyale ba sannan idan ke baki d'auke ta uwa ba dubun ki sun d'auke ta wad'an da suka fiki komai kuma ina alfahari da ita na k'asan cewar ta uwar miji na kamar yarda bazan iya d'agama Mahaifiya ta murya ba ita ma bazan iya d'aga mata murya ba na d'auke ta tamkar uwar da ta haife ni ina san ta Kamar yarda nake san mahaifiyata saboda haka zuciya ta bazata juri ganin ana muzguna mata na kyale ba"



Mama hawaye taji sun zubo mata, da sauri ta juya ta goge, allah sarki ita tasa ayo mata kishiyar nan amman gashi nan wacce tasa a auro tana ci mata mutumci ita kuma ta shige mata





Balkisu hannun ta tacire daga kan kumcen ta zata kaima khadija mari, sadik yayi saurin rik'e hannun,


kusan tunda suka fara wannan rikicin ya shigo yayi tsaye daga nesa yana sauraran su, k'ara bama khadija matsayi yayi a cikin zuciyar sa, tare da ganin girman ta



Yarfi yayi da hannun nata tare da nunata kana yace "Kin bani mamaki da ace fad'amin akayi bada kunnena naji ba da bazan yarda ba, Mahaifiyar tawa kike gayama bak'aken maganganu koda yake kince baki d'auke ta matsayin uwa ba to ni d'an ta wanda ta haifa ina san na shaida miki na janye igiyoyin aure na dake kan ki kije na sake ki saki d'aya "




" Me kunnuwa na ke jiyemin ne? Safiya ta fad'a wacce shigowar ta gidan kenan,

Balkisu hannu ta d'aura akai tare da fashewa da kuka tana fad'in "Wayyoooo na mutu na lalace wayyoooo uwata wayyoooo uba na" da sauri safiya ta k'araso wajen ta tare da fad'in "Ke lafiyar ki kuwa? " Safiya ya sake ni ya sake ni "


" Ahh saki amman dai wallahi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR SADIK book 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album