Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

A TAUSAYAWA JUNA Complete Hausa Novel Document by A TAUSAYAWA JUNA


A TAUSAYAWA JUNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 6447



A TAUSAYAWA JUNA

Reading Time: 0 Hours

Added On: 18, Oct 2024

Author: Aisha Ali Garkuwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 35.33 kb

File Type: txt

Views: 894+

Download: 329+

Last download: 4 days ago

Description/Story: Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239

: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
بسم الله الر حمن الرحيم

8:59 pm 01/06/2017

*A TAUSAYAWA JUNA* pg 1⃣to5⃣Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Ramadan Kareeeeeeeem*

*Barkanmu da shan ruwa ga dukkan 'yan uwa musulmai*

``` Barka da shan ruwa Namecy tawa Aysha Aliyu tsamiya Allah ya karbi iba dunmu Allahu rabbi yasa muna cikin bayinsa entattu zuwa cikin rahamarsa```

Zaune suke a parlon nasu mai dan girma da d'an kayan k'awa dai-dai gorgodo Bashir dake zaune kan 2 str ruggume da yarsu k'aramar Salima mai kyau cikin kula ya kuma kalli Rukayyat wace ke konce kan 3 str sai cika da batsewa take ta had'e fuskar nan kamar zatayi ruwan jini,
Babban d'ansu Salim ne ya d'an matsota cikin muryar bacci yace.
"Ummee bacci nakeji zan konta".
Kai ta d'ago cikin salon bak'ar mgn wa Uban yayan nata tace.
" wlh Salim tausayi kuke bani kai da salima sabida kun rasa ganta da duk sauran yaran jama'a ke samu a wannan wata sabida ko wanne uba mai k'aunar y'ayansa da son faran ta musu da fiddasu kunya tuni ya gama samawa iyalen sa kayan sallah Amman ku naku uban bai damu da kuba bare akai ga kaina".

Shi kam Bashir murmushin yayi cikin mmkin hali irin na rukayyat ace tsakanin ma'aurata a rasa tausawaya juna ba uzuri ita komai sai dai ayishi cikin gaggawa,
Kai ya kuma jinjinawa tare da mik'ewa ruggume da Salima ya kamo hannun Salim sannan ya kalleta cikin kula dan shi har kullum uzuri yake mata tunda ita macece mai rauni sai anbita ahankali,
Murmushi yayi tare da cewa
"Konta ki huta Baby bari nai musu wonka na kontar dasu kafin nan kin huta dan nasan kin gaji da aikin Abin bud'a baki".

Bata kula shi ba sai yatsuna fuska tai tare d'an yin kasa-k'asa da murya tace .
" jishi sai kace wani kayan azo a gani yake kawo mana na bud'a bakin"
Carab sai cikin kunneshi Amman duk da haka sai ya wuce ya shirya yaran sannan ya kontar dasu tare da musu Addu'a ya rufe musu jiki,
Sannan ya dawo parlon
Cikin k'arfin hali yace.
Baby tashi muje mu konta kar mu makara muresa tashi mu raya darenga da Ambaton Allah".
Shiru taimai sai tura baki da tayi shiko cikin danne abin yaci gaba da cewa.
"Muje mu konta dan gudun kar bacci yafi karfinmu ya sa muresa koda dare dayane a cikin wannan wata gwara mu zage damtse tunda bamu da tabbacin wanne darene na lailatul k'adir toh mafitarmu kawai mu dage mu raya dukkanin dararen da amba ton Allah ta nanne in munyi sa'a muyi muwafak'a da wannan daren na lailatul k'adir".

Cikin d'an Jan tsaki tace
" ban jin bacci".

Kauda kai yayi tare da cewa "toh muje dai"
Mik'ewa tayi ta zauna cikin kufula tace.
"Ai dama tanan kafi kauri muje dai ko? Wato kai baka da wata matsala ma ko kai dai aje bedroom ko?
Shin anya kuwa
Abban Salim kana tuna baka sayawa yaranka kayan sallah ba shin kana sane kwana kin watan nan nata tafiya yau axumi nawa muka kai amman ko k'elle banga ka shigo da shiba ko kai so kake yaran nan suyi sallah da tsoffin suturun su wlh ni har tsoro kake bani
ai kana sane da ko wanne uba ya gamawa yaran shi komai".

Gefe ya koma ya zauna cikin sanyi ya zura mata ido tare da son gano gskyar zuciyar ta a d'aya gefen kuma mmkin ta yake da kuma son ganar da ita,
cikin sanyi yace.
" Rukayyat kiyi hakuri ki nitsu ki gane halin da nake ciki ke kanki kinfi kowa sanin nauyin dake kaina tunda kina sane nike kula da gidan mu tunda mahaifina bay da karfi sannan inkula dake da yaran mu kuma kina ganin irin halin tsadar rayuwar da muke fama dashi kuma kinsan samuna bai kai yawan nauyin dake kaina ba Allah ne ke rufamana asiri Baby duk da kasawana da kike gani baki rasa ciba baki rasa shaba yaran mu ban barsu ba ilimiba na sasu a makaran mai kyau ban barsu da rashin sutura ba kuma tunda muke kema baki rasa sutura ba bare yaran mu ko ba sallah ba ina musu sutura bare sallah asheko yaci kimin uzuri ki jira har sai kinga anyi sallah ban muku abinda kuke buk'ata ba".

Tunda ya fara mgn ta kafeshi da ido har saida taji yayi shiru sannan tace.
"Kawai in bazakayi ba mu sani ai kana sane tsakanin da Allah yanzu duk cikin abokanka akwai Wanda bai gamawa iyalansa komai ba?
ai kana gani d'azu Maryam matar ya Umar na tazo nan kuma kaga dai abin da tashigo dashi kasuwa taje tawa yaran ta seyeyya komai tsap sannan ta biya gun telanta ta karb'o dinkunan ta kuma ka fini sanin Ya Umar dinne ya bata kud'in tunda ai abokin kane komai kasani,
Haka kuma Aysha ma matar Yusuf abokin naka dai har wayau itama an mata komai har tayi d'inkunan ta da salima d'azu ta turo mata,
abin kunya babanta bai mata ba,
Su suna neman yaran Allah bai basuba kai ka samu ka kasa rik'ewa".

Sosai yaji zafin kala manta toh Amman ya zaiyi da hali irin na Rukayyat sai Addu'a cikin jin zafin ya mik'e ya nufi bedroom ensu al'wala yayi sannan ya d'au k'ur ani ya rink'a karatu cikin kushi'i da k'ank'an da kai.
Ita ma d'akin ta shigo tai wonka sannan ta koma kan gado tai baccin ta tana mai ganin kasawar mijin nata,

Shiko a hankali ya fara jin sanyi bakin cikin ya rink'a gushewa a ransa a haka a wurin bacci ya d'an saceshi.

1:30 am dai-dai ya farka cikin sanyi yaje gaban ta a hankali ya tasheta tare da cewa "Baby jekiyi al'wala kizo muyi nafila"

Cikin baccin ta mik'e taje tai alwalan dan inda sabo ta saba dolene muddin Bashir ya tashi to zai tasheta.
A haka kuma sukai ta nafilfilin su sannan daga bisani sukayi ta karatun k'ur ani mai girma har zuwa lkcin Sahur sannan sukayi sahur bayan sun gama shiko yayi al'wala ya tafi masallaci dan samun jam'i asubahi,.
Itako tai tata sallan a gida.
Rayuwar gidan Bashir kenan....

*Gidan Yusuf da Aysha*

K'arfe 5 dai-dai Aysha ta kammala Ayyu kanta tsab ta share ko ina ta goge komai ta shirya musu abin bud'a bakin su tayi wonka ta shirya cikin doguqar riga mai d'an girma ta d'an yafa gyale.
tana zaune a parlon ta,
Cikin sanyi da gajiya Yusuf yayi slm hannushi rik'e da wota bak'ar leda,
Cikin hamzari da kulawa Aysha ta taryeshi hannu tasa ta karbi kayan hannushi sannan ta wuce gaba tare da cemai.
"Barka da yammah Hamma".
Ajiyar zuciya ya sauk'e tare da zama can gefen ta kan 1 str ido ya lumshe tare da cewa.
" Alhamdulillah Aysha sai dai gsky yau kam akwai rana ga k'ishi gashi na biya cikin kasuwa na d'an saya miki takalmi da mayafi".

Sai kuma ya mik'a mata hannu alamar ta mik'o mai ledar,
Cikin girmama wa ta mek'a mai tare da rabawa gefen shi ta zauna tana kallon 'yan kayyayakin da ya sayo mata ta kalmin ya dauko ya zauna a kasa kan carpet ya zura mata takalmin cikin kula yace.
"Wlh yayi miki kyau kinga yadda k'afarki ta gyara takalmin insha Allah inna samu kudi zan saya miki jakarsa "

Itama zamewan tayi ta zaune d'an nesa dashi cikin sanyi da tausayawa tace.
"Hamma meyasa kake son kashe kud'i a banza da wofi ni ba yarin yaba ka rink'a kashe min kudi yanzu ba da safe kake cewa ba kudi a hannun kaba kuma shine daga samo su ka saya min wannan tarka cen meyasa bazamuyi tattali ba?".

Kai ya jinjina cikin jin dad'i yace.
" Aysha Allah ya miki albarka Ngd da tausaya sarki gareni amman kibar korafi kar ina kashe miki kud'i dan kuwa Aysha duk wani namijin kirki toh burinsa ya faran tawa matar sa da yaran sa muddin kikaga ba'ayiba toh ba'asamu damar yi bane inko haka ta faru sai *A tausayawa juna*
d'an ba Wanda zaiso yaga iyalanshi a k'askance sai dai in abin yafi karfi kinga ko tunda na samu dole namiki tunda dama nauyi nane ai ko matata?".

Murmushi tayi cikin farin ciki tace.
"Allah ya saka da alkhari ubangiji yaa jibanci lamuran ka Allahu rabbi ya karama arzik'i da wadata Allah ya had'aka da halal d'inka ubangiji ya rabaka da haram Ngd Ngd Ngd Hamma na"

Gdy take mai cikin farin ciki da ganin girman kyautar da ya mata,
Cikin jin dad'in halin matar tasa yace.
"Nifa kin San ban son wannan godiyar kinsan irin godiyar da nake so yanzu kuma muna cikin watan Ramadan ne kuma da ranane
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download A TAUSAYAWA JUNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album