Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MATAR GWAMNA Complete Hausa Novel Document by MATAR GWAMNA


MATAR GWAMNA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 66564



MATAR GWAMNA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 06, Feb 2025

Author: Rahma Ladingo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : KAINUWA WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 547.79 kb

File Type: txt

Views: 170+

Download: 233+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: 
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA






Bismillahir Rahmanir Rahim









Book one









*Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani iko da kuma damar fara rubuta wannan labari. Ina addu'ar Allah ya sa yadda na fara lafiya na ƙare shi lafiya. Amin*



*wannan labari zai zo daga kashi na ɗaya zuwa kashi na uku Insha Allah. Na ɗaya zai zo a kyauta yayinda kashi na biyu da na uku zai zo na kuɗi a farashin 400*



*wannan labari ƙirƙirarre ne, idan yayi kamaceceniya ta wani fanni da rayuwar wani, wata ko wassu to bisa kuskure ne, ba ayi dan cin zarafin kowa ba*







01







(CONGO STATE is a fictional state in Nigeria. Jahar Congo ƙirƙirrerren Jaha ce a Nigeria)



*MAFARI*






Da ƙyar kyakykyawar matashiyar budurwa da ke riƙe da hannun Mahaifiyarta ke jan numfashi da dogon hancinta da ya zauna ɗas a tsakiyar fiskarta wanda ya ƙara ƙawata ma ta fiskar sosai. Iskar asibitin wanda ke gauraye da warin magunguna, allurai, jini, fitsari da sauran su shi ya ke yiwa mutum iso a duk lokacin da ya kusancin farfajiyar asibitin. Ansan Asibitoci da wari amma wannan warin na sa ya fita daban. Ko dan Asibitin ta gwamnati ne, oho. Rabonta da zuwa General Hospital Congo tun wani ciwo da Abba yai kusan shekaru biyar da su ka wuce.



Ba su jima da zama a wajen reception ba wata mata mai ɗauke da jaririya ta fito daga office ɗin Likita ta ce " wai Zainabu Inusa ta shiga"



Budurwar nan ta kama hannun mahaifiyarta su ka shige ofishin Likitan.




Lokacin da su ka shigo Likitan yana ta cike-cike a file ɗin su. Ba tareda ya ɗago ba ya ce "Malama Zainabu mi ya ke damunki?"



"Ciwon ciki"



Da sauri Likitan ya ɗago fiskarsa saboda yadda muryar budurwar ya shige shi, bama wannan ba, a file ɗinsu an rubuta Zainabu Inusa matar aure ce mai shekaru talatin da takwas wannan budurwa kuwa da ƙyar idan ta haura shekaru ashirin da ɗaya.

Lokacin da ya haɗa ido da budurwar sai da numfashin sa ya tsaya na ɗan wasu sakanni. Muryar da fiskar ba baƙon sa ba ne amma wannan ne karo na farko da ya ke ganin ta gaba da gaba.



"Mu ne wanda Dr Ubaydullah Gidaɗo ya turo" ta faɗa da siririyan muryarta me ratsa zuciyar mazaje.




"Masha Allah! ke ce ƙanwar mu kenan. ya jikin Umma?"



Sai da ta yi murmushi kafin ta amsa mi shi da cewa jikin Umma da sauƙi.

Duban Umma Dr Hassan yai ya ce "Umma tun yaushe kika fara jin ciwon cikin?"

Ido kawai Umman ta bishi da shi har ya gama maganar sannan ta maida dubanta ga 'yarta wacce ta fara ma ta bayani da yaren kurame. Dr Hassan ya sake baki yana kallon ikon Allah, sai yanzu ya gane dalilinta na iya sign language na kurame dan watarana a wani rahoto da ta naɗa ta yi amfani da shi wajen yiwa wani kurma tambayoyi. Abin ya burge mutane da dama amma yanzu da ya ke ganinta tana yiwa mahaifiyarta tafintan (interpreting) duk abinda ya ke faɗa sai tausayinta ya kama shi. Bayan ya gama sauraron bayanen ta ya ma ta tambayoyi sai ya rubuta mu su takardar scanning ya ce su je su yi su kawo ma sa ya gani.




Ba su suka bar Asibitin ba tun takwas saura minti biyar da su ka shigo har sai ƙarfe shaɗaya da minti biyu.

Lokacin da su ka fito daga Asibitin Keke daban-daban su ka hau saboda sauri da budurwar ke yi dan ta je wajen aiki yayinda Ummanta ta wuce gida.






Da gudu-gudu sauri-sauri ta shigo cikin ma'aikatar ta su, kai tsaye studio na biyu ta wuce domin yau ne za ta fara gabatar da sabon shiri da za a fara a tashar su. Ƙarfe shaɗaya da rabi saura minti huɗu ta gani lokacin da ta duba agogon hannun ta. Ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe studio ta shiga.



Zaro ido waje ta yi ganin wanda ke zaune akan kujera tareda baƙon su na mako.



Gefen C Y ta tsaya wanda ke ta faman saita Camera dan fara ɗaukan shirin.




"C Y mi yake faruwa? ya na ga Iklimah a nan"



"Sorry Sweery, Oga ya chanja ki"




"Amma..."



"We are going live in one, two, three" C Y ya faɗa yana ɗagawa Iklimah hannu.



Iklimah ta yi wani fari da ido ta fara bayani kamar haka: ma su kallon mu kuna tareda gidan Talibijin na HILL TV, inda a dai-dai wannan lokaci mu ke gabatar mu ku da sabon shiri mai suna BAƘON MU wanda ni Iklimah Jibril zan gabatar. To a yau dai mun taho mu ku da babban baƙo. Jajirtaccen Ɗan kasuwa wanda duniya ta ke damawa da shi. Baƙon na mu dai shine Alhaji Isa Madara...




Juyawa ta yi cike da ɓacin rai ta bar cikin studio ɗin. Wannan wani irin walaƙanci ne Oga ya ma ta haka.

Kai tsaye ta wuce sama inda office ɗin Ogan su ya ke.



Gaisawa ta yi da Sakatariyar sa wata mata wacce za ta iya kaiwa shekaru Arba'in zuwa Arba'in da biyar.





"Madam Deborah Oga na nan?"



"Yana ciki" ta amsa tana cigaba da latsa na'urar computer da ke gaban ta.



Wucewa ta yi ciki zuciyar ta cike da jin haushin Ogan na su.

Office ne da ya fi kowanne girma a cikin kamfanin. Mamallakin office ɗin na zaune kan kujera yana duba wa su takardu.

A ɗan ƙaramin katako da aka ajiye a tsakiyar table da ke gaban sa an rubuta *MD Adamu Ribaɗo*



"Ina kwana Sir"



"Lafiya"



"Sir na ga Iklimah ta karɓi shirin BAƘON MU"



"Eh" ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba.



"Sir amma ni aka ba wa shirin nan, ranan Jummu'a kai da kan ka ka jaddada mini cewa ni zan fara shirin nan, ni na tsara tambayoyi, ni ne na kira Alhaji Isa Madara..."



"Kin zo da wuri?" Yai tambayar yana ɗago ma ta ƙananun idanun sa.





"Sir inada uzuri, na yiwa C Y text tun da sassafe, kuma na zo kafin lokaci ya cika"



"So?"



"Sir wannan ba adalci ba ne, kuma..."



"Fita" ya faɗa da ɗan ƙarfi.



Ranta a ɓace ta fice daga office ɗin da sauri. MD ya bi bayan ta da kallo yana ƙara yabawa da wannan halitta ta Asiya.



Kai tsaye office ɗin su ta wuce wanda su takwas ke amfani da shi. Mutum biyu ta tarar a wajen ta gaishe su kafin ta wuce kan madaidaicin desk ɗinta ta zauna, ta ajiye jaka da wayoyin ta sannan ta kifa kan ta a kan desk ɗin.



Idan mutum ya ce yana son ka ka ƙi shi shikenan sai ya zama abin damuwa. Tunda ta fara aiki a wannan waje MD ke takura ma ta.



"Da wani ƙaton tumbinsa a wajen" ta furta a fili tareda jan dogon tsaki...



Yinin ranan gaba ɗaya a hasale ta ke saboda abinda MD ya ma ta. Ita gani ta ke ma da gangan yai hakan, dama tun asali Iklimar ya ke so ta yi shirin ba ita ba. Dama ƙwalele ya ke son yi ma ta...



Kusan ƙarfe biyu na rana su ka fita ɗauko rahoto chan wani ƙauye. Faɗa ne ya ɓarke tsakanin manyan ƙabilu guda biyu da su ke wajen.

Sun samu sun tattara bayanai sannan sun yi hira da mutane da dama a ƙauyen kasancewa an ɗaura labarin ne life. Faɗa ne da ya faro daga ƙona gona guda ɗaya sai abin ya zamo rikicin ƙabilanci akayita ƙone-ƙone.



*"bayan Gwamnatin Jahar Congo ta turo jami'an tsaro zuwa wannan ƙauye, ƙura ta fara lafawa, yayinda iyayen da aka yi awun gaba da 'ya'yan su su ke cikin Alhini. Na tambayi wani jami'in tsaro wanda ya tabbatar mini da zaran sun gama bincike sun tabbatar babu hannun yaran nan guda biyar a sakawa gonar Malam Bala wuta za su sako su wa iyayen su. Muna fata dai wannan abin da ya faru zai tsaya a iya haka domin zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki. Ta ku ASIYA-SHAHIDA FARUQ BABA, tashar Hill TV"* ta ƙarasa maganar tana murmushinta mai shiga rai.



Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da C Y ya ce cut. Ba yau ta fara kawo rahoto ba amma yau tunda ta fara ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi. Ko dan ranta a ɓace ya ke oho. Ta ɗan ɗaura hannunta a ƙirji tana jin yadda ya ke bugawa da ƙarfi. Ikon Allah! Ko ranan da ta fara tsayuwa gaban camera ta kawo rahoto shekara ɗaya da ya wuce bata ji irin wannan tsoron ba. Lokacin da ta ke kallon camera ta sani tana fiskantar duniya ne, amma yau ji ta ke kamar mutum ɗaya ta ke fuskanta, kamar wannan mutumin da ke kallonta koma wanene idonsa yana ma ta nauyi, ya saka ma ta tsoro, ya kassara duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi.


Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MATAR GWAMNA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album