Join Our WhatsApp Group

DIYA MACE Complete Hausa Novel Document by DIYA MACE


DIYA MACE

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 37113



DIYA MACE

Reading Time: 3 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Khadija Sidi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 168.84 kb

File Type: txt

Views: 687+

Download: 351+

Last download: 24 hours ago

Description/Story: DIYA MACE
Khadija sidi
Creat by Shuraih Usman
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) khadija SIDi
Khadija
Sidi: DIYA MACE
Jabir na dariya ya ce da Hajjo kamar fa kin ruda kanin
nawa,cikin girmamawa da kuma jin nauyin maganar
Jabir ta gaida Khalid,ya amsa idanun sa kanta. Jabir ne ya
janye shi ya na fadin wallahi child abuse din nan ta ka ce
ka ma bar kokanto yaro! Ta na jin shi ya na wlh Jabir kada
fa ka matsa min! Sai na fadawa Nabeela abunda ka fada
min rannan! Shegen maza! Ta ciyo Jabir na zagen
Khalid,ga dariyar su na tashi kamar su kadai ne a gidan.
Hajjo ta saki ajiyar zuciya,damuwar da ke kwance cikin
ranta ce ta taso,gaba daya ji ta ke ranta a dagule,ya za ta
haifi diya ta na gudun ta? Su ma su rikon ta ba su sheda
ma ta wacce mahaifiyar ta ba? Me ma su ke nufi ne? Kai
lokaci ya yi da za a dawo ma ta da diyar ta gaskiya! Da
wannan tunanin ta cigaba da wanke wanken ta,tsabar
bacin rai ma ta kasa katsewa ta je su gaisa da Hauwa. Sai
da ta gama tsaf.
Can falo kuwa Hajiya zaune tare da su Khalid ana hirar ya
bayan rabuwa,Jabir ya tafi gidan sa. Tin fitowar su
hankalin sa ke kan hanyar fitowa daga kitchen,Allah Allah
ya ke ya kara sa Hajjo a idon sa,ya ga baiwar Allah,kamar
da diyar ta kamar an tsaga kara,kawai dai dan ita yar fara
ce,ita kuma uwar wankan tarwada,da kuma ita Innar
yarinya ce da sai ma ace yan biyu ne.bini bini Hajiya sai ta
kalli Inna ta ce yarinya fa ta zama budurwa,yanzu wa zai
kalle ta ya ce mahaifiyar ta ce ta haife ta,ai sai dai ayi
zatan yaya da kanwa ne. Khalid ya ce wlh kuwa,ni kai na
na yi mamaki kwarai da na ga uwar! Ita dai Hauwa da
anyi maganar Hajjo gaban ta faduwa ya ke,duk da dai ta
san Neenan ta ta ba diyar ta ba ce,amma ba ta ji za ta iya
rabuwa da ita,shi ya sa ma ko zancen Hajjon ba ta ma
ta,kunga karfin hali barawo da sallama. Hajjo ta fito
fuskar ta dauke da murmushi,da Khalid ta fara hada ido
saboda dama dai shi ne ya kasa ya tsare ya ke jiran
tsammanin sake ganin ta. Ta yi saurin janye idanun ta da
ga na shi gaban ta na faduwa,wajan Hauwa ta karasa ta
na maraba sannun ku da zuwa,ita ko Inna da ta ga haka
sai ta koma gefan Khalid. Hajiya ta ce aw ku ga yar butan
uwa! Uwar ta ki ki ke gudu? Hauwa ta ce ina ruwan
Neenan Mama,kin san ba ta san ta ba. Maganar ta yiwa
Hajjo daci,amma sai kawai ta boye,ta ma dauke kai daga
kan Innar. Bayan sun gaisa ta tashi ta ba su wuri,wanda
hakan be yiwa Khalid dadi ba,ita kuwa Hauwa hakan
daidai ya ma ta.
Bayan tashin Hajjo, Hajiya ta bijiro mu su da maganar
Inna,hankalin Hauwa ya tashi gudun kar Inna ta gane
zancen da ake ta ce da ita ta Neena tashi ki je daki ki
kwanta abun ki. Tana tafiya Hajiya ta ce kun dai san ya
kamata ba sai an fada mu ku ba,amma na ga alamar ba
ku ma shirin yin abunda ya kamata,kamata yayi ayau
dinnan ku taho da komai na yarinyar nan ku damkata
hannun mahaifiyar ta,ta mu ku kara ai. Idanun Hauwa
yayi rau rau zai kawo ruwa,Khalid ya gyara zama,ya ce
dama Hajiya za a yi hakan,dama so mu ke mu gama
settle....ah ah! Hajiya ta katse shi,yarinyar nan fa alkunya
ta ke mu ku,it is high time auta,ku dawo ma ta da diyar
ta. Khalid ya sosa kyeya,idanun sa kan Hauwar shi,ganin
yanda gaba daya ta sauya yanzu yanzu sai ta ba shi
tausayi,dole ya nemo mu su mafita. Ya ce toh Hajiya
ta,yanda ki ka ce haka za a yi,ta ma yi kokari ai,amma dan
Allah ki ba mu zuwa sati na gaba sai mu dawo da ita din.
Hajiya ta ce ko ku fa,Allah ya nuna mana,ya ce amen.
Farin cikin Hauwa ya gushe,daurewa ta yi kawai har su ka
gama wuni a gidan,amma kowa ya san ta na cikin
damuwa. Suna komawa gidan su kuwa,ta samu ta kebe
da Khalid sai kuka. Kuka sosai ya ma kasa rarrashin ta dan
tuni ta riki ta shi,sai da kukan na ta ya tsagaita,kwance
cikin sa ya ke ba ta baki,haba baby-luv,toh menene na
kukan? Ta na ajiyar zuciya ta ce ya bazan yi kuka ba?
Kasan matsala ta Khalid,kasan ba na haihuwa ba zan taba
haihuwa ba ma wasu likotocin da ba su iya magana ba su
ka ce....shhhhh ya toshe ma ta baki da dan yatsa,ya ce
kema kin ce wanda ba su iya magana ba,ki sa Allah a
ranki baby-luv,shi kadai ne mai iya bawa bawan sa kyauta
sanda be yi zato ba,shi zai ba mu haihuwa...Hauwa ta ce
haka ne,ban fidda tsammani ba duk da kowani indication
ya nuna kishiyan haka,amma Beb idan aka dauke min
Neena ban san inda zan sa rai na ba,ya zan yi da rayuwa
ta,na riga na saba yarinyar ta shige jiki na.. shiru ya yi
daga bisani ya ce ba yanda za mu yi,dole mu mayar ma ta
da diyar ta,kar ki damu,Allah na sane da mu. Nan fa sai
Hauwa ta kara fashewa da kuka,tin ya na rarrashi,har ya
kyale ta,kusan kwana ta yi ta na kuka,wai za a raba ta da
diyar da ke kiranta Momma.
Washagari abun duniya ya ishi Khalid,shi ma din tafiyar
Neena na damun shi,babu yanda zai yi ne kawai,da ga shi
har matar ta shi babu mai walwala,zuciyar sa na sake
sake kala kala,hez 37 yanzu,Hauwa 31,amma ko kwai be
taba ajewa ba,shekaru na ja,tsufa da mutuwa na
gabatowa,shin rayuwa za ta yiyu a haka kuwa? Da sam
haihuwar ba ya gaban shi,sai yanzu da ya manyanta ya
fara damun shi,duk da kuwa be taba nunawa baby-luv
din ta shi ba. Da yamma ta yi sai ya wuce gidan
Hajiya,ganin ta tare da Hajjo zaune cikin dakin Hajiyar sai
abun ya bashi sha'awa,ita Hajiyar ma kenan da Allah ya
ba ta haihuwa,dan dai kawai ba ta da diya mace ji
soyayyar da ta kewa Hajjo da ta yi kusan rabin rayuwar ta
a hannun ta,bare shi da be san dadin haihuwa ba,sai akan
Neena,wacce tin ta na shekara biyu ta ke tare da shi.
Hajjo sanye da doguwar riga baka,ta rufe kanta da
mayafin rigar,daga gani fita za ta yi ko kuma daga fitar ta
dawo,ganin sa ta yi saurin tashi za ta fita,Hajiya ta ce ina
dawo ki zauna,kin ga shigowar Khalid za ki sami damar
fita,zauna shima ya taya ni ai,Hajjo ta koma ta zauna a
takure. Idanun Khalid kan ta,shi dai mamakin girma,kyau
da wayewar ta ya ke,gaba daya ta canza kamar wacce
makirin mata ya kyera. Ya dan kalli Hajiya ya gaishe
ta,sannan Hajjon ma ta gaisheshi,yanda ta saba cikin
girmamawa. Khalid ya ce Hajiya kamar ki na zan taya
ki,me zan ta ya ki? Hajiya ta ce jin ta baki Hajjo,sam na ga
alama ba zancen aure a gaban ta,ya kamata ta yarda
tsayayye ya fito. Dim! Ya ji wani irin mummunar faduwar
gaba,sai da ya koma ya dan jingina da bango....
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[7:06pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYAMACE
Ya gyara murya ya ce Hajiya ai gwara dai kar a ma ta
shisshigi,tin da ba yarinya ba ce,auren nan ta yi na fari
dama,kar a azalzale ta a jira na gari ya zo sai ta tsayar din.
Hajiya ta ce ahaf,kar ka mai da mu baya kai kuma,wani
na gari ya zo? Ai tuni Hajjo na da nagarin ta a hannu...da
sauri ya daga ido ya kalli Hajjo,wani abu ne ya tsaya
kamar kashi cikin ransa,well obviously mace kamar Hajjo
ya kamata ace ta na da manema,plus shi ina ma ruwan sa
ne? Tambayar da yayiwa zuciyar shi kenan! Ina ruwan ta
da kaduwa akan maganar child abuse? A zahiri tambayar
Hajiya ya yi waye shi na garin? Hajjo ta saci kallan sa ta
wutsiyar ido,see dis man! Ina ruwan shi da ni da har zai
na tambaya kan rayuwa ta! Ni fa shisshigi ne ban so,dan
ya na ruke da Inna ta be zama uba na ba! Tafasar da
zuciyar Hajjo ke yi kenan. Hajiya ba tare da ta kawo
komai ba cikin ran ta,ta ce wani likita ne,Surajo,Jabir ma
ya san shi,yaran arziki wlh. Ran sa idan yayi dubu ya
baci,ya kasa gane mai ke ma sa dadi,wai ma ina ruwan sa
ne! Toh Allah ya sa a yi da mu. Hajiya ta ce amen amen.
Hajiya bari na tafi,dama gaishe ki na zo yi na yi da Jabir
zan dauko sa daga asibiti,akwalar motar ta sa da ya kasa
rage ciki ya sake ta kara samin matsala. Hajiya ta dara ta
ce kamar a kunnan sa. Shi ma darawan yayi duk da de ba
dadi ya ke ji ba,ya ce kin san dai gaskiya na fada. Zuciyar
Hajiya daya ta ce in dai haka ne ka ragewa Hajjo
hanya.....Hajjo kamar ta kurma ihu,sam ba ta san abunda
zai hada ta da Khalid,da sauri ta ce ah ah Hajiya ba ma sai
ya rage min ba sai na hau a daidaita sahu. Hajiya ta ce
AKTH zai je,kin ga ina kundila ina AKTH,ai ya fi sauki ya
sauke ki..dan kar na bata ma sa lokaci Jabir na jira
Hajiya,Hajjo ta kara kan bayanin ta. Da ya fuskanci bin shi
ne ba ta so,sai ya ce no ba bata lokaci,mu je na sauke ki
kidin. Kamar ta yi kuka ta yiwa Hajiya sai ta dawo,Khalid
ya ma ta sallama,su ka fito ya na gaba ta na biye da shi,sai
watsawa bayan sa harara ta ke. Ko da su ka kai mota,ya
bude ya shiga sai ta bude baya ta shiga ta rufe. Sai a
sannan kamshin ta ya mamaye hancin sa,ya bi numfashin
sa,kamshi ne mai dadin gaske ga sanyi,da ke ta na amfani
da turaren the body shop(indian nyt jesmine) wanda
Suraj ke yawan aiko ma ta da su,sai kuma wani hadadde
kuma dadadden Humrah da Aunty Hussaina ta ba ta,so
wani kamshi ta ke mai rikitarwa,kaji kamar ka janyo ta
jikin ka ko ka samu kai ma ka shafa. Ya lumshe ido ya
bude,gaskiya babu abunda ya kai kamshi dadi a duniya
dadi,zaman Hajjon a baya ya sa ya ki tada motar,sun kai
kusan minti goma a haka,shi dai be damu ba,as long as ya
na jin kamshin nan,zaman is worth. Hajjon ce ta gaji,ta
ce ko motar na da matsala ne?ya ce me ki gani? Ta ce na
ga ba mu motsa ba. Ya gyada kai, Yes ta na da matsala,as
long as u sitting der,ba za ta tashi ba. Cikin mamaki ta ce
ikon Allah,me ya hada zama na a nan da kuma tashin
mota? A hankali ya juyo suna fuskar tan juna,tini Hajjo ta
daina numfashi na dan sakanni,ganin yanda mischievous
idanun shi ke kallan ta,ta yi saurin nisar da na ta idon. Ya
lura da yanayin da ta ke shiga duk sanda ya kalle ta,she
catches her breath duk sanda ya kalle ta su ka hada
ido,kamar yanda shi ma his hrt beat faster dan normal
duk san da ya sa ta a ido. Ya na murmushi ya ce am nt a
driver Hajiya.....ido a kasa ta ce nan ne wajan zama na a
motar ka 11 years ago,u knw dat as well Alhaji... darawa
yayi,indeed ba wai kamannin Hajjo ne kadai ya canza
ba,hatta maganar ta ta sake,ta za ma brazen! Juyawa yayi
ya na murmushi mischievously,ya ce yes u made ur
point,noted,so dawo gaba in ki na so mu tafi,idan kuma
kina san ki ta zama ne,i wil nt mind,cos i love ur scent,ya
sunan turaren ne? Ta ma sa banza,ya dara tare da fadin
shi ya kamata a kira a ba rai dadi,i soo much luv it.
Ji ta yi kamar ta fasa fitar,sai dai sakon na Hajiya ne,kuma
ba ta so Hijiyar ta ga ta ki bin maganar ta da ta fita ta hau
dan sahu. Da wannan tunanin ta fito ta shiga
gaban,kamshin na ta ya kara shigar Khalid har cikin ran
sa,cikin zuciyar sa ya ce Astagafirullah! Allah ka yafe mana
ni da wannan baiwa ta ka,dan gaskiya kamshin na ta ya
ma sa,kamar ba shi ne mai sauke glass ko dauke
numfashi da ta gifta shi. Hmmm duniya juyi juyi kwado
ya fada ruwan zafi.
Ganin ta dawo din,kuma be motsa ba,ta ce na dawo.
Murmushi ya sakar ma ta,wacce ita kanta ba ta san na
menene ba,yayinda ya kunna mota su ka fito su ka dauki
hanya.
Babu wanda ya sake magana har ya sauke ta,ta bishi da
Allah ya tsare. Ya amsa amen. Sai da ta shiga gidan da ya
kai ta sannan ya kunna mota ya tafi,ran sa cike da sake
sake iri-iri ya karasa AKTH. Maimakon Jabir ya taho shi
kadai sai ya taho da abokin aikin sa,Doc Ahmad,wai za su
aje shi na'ibawa. Khalid na driving amma gaba daya
hankalin sa ba ya wajen,kamar daga sama yaji Jabir ya ce
wata kanwar ta wa ka ke so? Hajara?....kiiiiiiiiiiiii Khalid ya
yi saurin ta ka birki,dan ya kusa bugawa wani jin inda
maganar ta su ta dosa. Jabir dake zaune tare da shi a gaba
ya daki kafadar sa ya na dan uban ka ka goga yar motar
ta ka da ka ke ji da shi kamar kwai! Khalid yayi karfin hali
ya murmusa gami da dagawa wanda ya kusa bugawa
hannu,cikin ba da hakuri,ya ce ahaf tawa za ta siyi
akwalar motar ka goma,ka ga ko dole na ji da ita! Jabir ya
ce karya ne wlh,yaro karya ka ke! Gaba daya dariya su
ke,Jabir na shirin cigabawa da maganar Doc Ahmad ya ce
pls mu yi maganar Hajara,na kusa sauka,ya za a yi ne?
Wlh shez exactly the womon of my dream,ga kyau,ga
kwalliya irin na matan da su ka san ciwan kan su,ga sanin
darajar mutane,ga tsafta.... o yes! Jabir ya katse shi,she is
neat,exceptionally neat wlh,ga ga ga ga din Hajjo da yawa
su ke Alhaji. Khalid dai ya baza kunne,ya na jira ya ga iya
gudun ruwan su. Jin Doc Ahmad ya ce ka tabbata ba
maganar kowa as in ba ta sasansan ta da kowa ba? Jabir
ya ce etoh gaskiya.. kafin ya karasa Khalid ya saurin
dakatar da shi ta hanyar tare maganar...gaskiya nauyin
bayani ya ke ma,wato kai ma Jabir ka iya bugan cikin
mutum,ka ma sa shiru ya na ta sakin layi,baki bude Jabir
ya ke kallan Khalid,Khalid ba kunya bare shakka ya ce Doc
Ahmad,na gode kwarai da yabon my wife to be da ka
yi,amma an ba da ita. Jikin Doc Ahmad yayi sanyi,Jabir ya
ce kut! A gidan ubanwa...... Jabir ka yi shiru kawai,ya dan
kifta ma sa ido,ai Ahmad wil undstnd,kawai so...


Read / Download DIYA MACE

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album