Join Our WhatsApp Group

BINTU Complete Hausa Novel Document by BINTU


BINTU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 47007



BINTU

Reading Time: 3 Hours

Added On: 02, Sep 2023

Author: Rufaida Omar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 263.96 kb

File Type: txt

Views: 1182+

Download: 492+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: BINTU
Na Rufaida Omar
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
BARKA DA SALLAH....!!!!

¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

(Ayimin afuwan rashin zuwan Yar Fillo, Allah bai nufa ba adalilin binciken da ba'a kammala yi ba akan abinda ya shafi sak'on da akeson isarwa. A cigaba da tayamu addu'a...Allah Yayi mu fidda litattafanmu.. Ameen..)



'Yar budurwa ce mai shekaru goma sha bakwai a duniya, kana ganinta ka san rainon k'auye ce. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa holan. D'inki na zamani ya zauna d'abas a jikinta, maimakon ta d'ora d'ankwalin sosai, sai ta rufe gashinta gami da sak'alo jelolin d'ankwalin ta wuyanta ta k'ullesu. Fuskarta fayau babu ko d'igon kwalli, wannan ya janyo bayyanar 6acin rai k'arara a saman fuskarta. Ita kam an takura rayuwarta a birni, Mami ta hanata shafa ko hoda, a ganinta ta kai minzalin da ya dace ace tana kwalliya, tana tsayawa da samari kamar sauran k'awayenta da ta barosu a k'auye, duk domin a matsawa rayuwarta da karatun bokon da ta tsana, na islamiyyar ma da ya Innarta ta ke turata ballantana wani bokon nasara.
Ta ja tsaki a daidai lokacin da ta k'araso babban falon Mami na saukar bak'i don kiran Anti Asma'u, kamar yanda Mamin ta umarceta. Saidai me? Ta yi turus ganin Anti Asma'u zaune tare da Yaya Ma'aruf a gefenta suna hira cikin murya k'asa k'asa.
Ta gwalalo ido ganin Yaya Ma'aruf ya saki fuskarsa sosai sai faman doka murmushi yakeyi har hak'oransa sun gaza 6uya. Ta dubi tazarar dake tsakanin masoyan biyu, ba wata tazarar azo a gani ba, kai zaman ma da sukayi ya 6aci.
"Tab! Ana iskanci a birni." Ta fad'a cikin k'ank'an da murya. Ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa ganin Yaya Ma'aruf ya rik'o hannun Anti Asma'u, da saurinta ta sanya hannu ta rufe bakinta gami da k'ara la6ewa jikin kakkauran labulen dake a falon wanda ya hanesu ganinta, hakanan ko kad'an basu ji motsinta ba.
Abin mamaki, Anti Asma'u ko a jikinta, sai ma dariya da takeyi har tana k'ok'arin fad'awa jikinsa.
Aikuwa tayi wuf ta fito daga ma6oyarta.
"Innalillahi!" Ta fad'a da k'arfi tana mai d'ora hannuwanta a ka, a firgice suka dubeta, sam basuji motsinta. Ma'aruf ya ja mugun tsaki. Sam! Ya k'i jinin yarinyar, bata da kan gado. Ita kuwa tuni ta soma ja baya zata fice, ai kuwa kamar yasan niyyarta ya yi azamar mik'ewa ya cafkota.
Ta runtse ido. "Wayyo na shiga uku! Don Allah Yaya Ma'aruf kayi ha.."
"Shii!!" Ya dakatar da ita ta hanyar sanya yatsu biyu a saman la66ensa. Ya zaro idanuwa yana dubanta fuskarsa a murtuk'e, ita kuwa Anti Asma'u tuni ta mik'e tsaye ta zari mayafinta gami da gyara zamansa sosai a jikinta. Babu inda baya rawa a jikinta, tana bala'in tsoron Yaya Ma'aruf, domin ko kusa baya shiga sha'aninta. Tafison Yaya Rufa'i sau dubu akansa. Haka kuma sunfi shak'uwa.
Durk'usawar da yayi a gabanta ne ya sanyata k'ara rud'ewa, kallo d'aya tayiwa fuskarsa tayi saurin mayar da dubanta ga Anti Asma'u wacce ke k'ok'arin ficewa, daga falon da saurinta, da alamun kunyar ganin da Bintu tayi musu a tattare da ita.
Jin ya kama kunnenta da k'arfi ne yasa ta sakin k'aramin k'ara, k'afafunta suka d'auki rawa tana mai runtse ido don azaba.
"Wayyo, don Allah kayi hakuri Yaya, wallahi bazan k'ara ba."
"Tun yaushe kike mana la6e?"
Tuni ta soma hawaye, sai k'aramin tsalle takeyi amma bai saketa ba. Dakyar ta girgiza kai cikin muryar kuka ta amsa. "Ni ba la6e nakeyi muku ba, Mami ce ta turoni kiran Anti Asma'u, kwarankwa..."
Ai bata k'arasa ba ya make bakin, bayan ya saki kunnen.
"Ban hanaki wannan rantsuwar ba? Idan na k'ara jin kin min rantsuwa da kwarankwatsa sai na 6allaki. Sannan ki bud'e kunne ki saurari kashedin da zanyi miki."
Ta bud'e idanu tana dubansa, sai kuma tayi saurin sadda kanta tana mai cigaba da kuka ciki-ciki.
"To." Ta fad'a, ya jinjina kai.
"Good." Ya mik'e ya koma saman kujera ya zauna kafin ya dubeta.
"K'araso nan ki durk'usa."
Ba musu ta k'arasa ta durk'usa fuskarnan kamar kace "Arr!" ta arce.

¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<02>>

Ya kwashi mintuna k'alilan yana mai danna wayarsa, ita kam ta k'agara ya barta ta tafi. Can kuma ta tsinci muryarsa.
"Ko da wasa, ko da wasa naji kina bawa wani labarin abinda idanunki suka gane miki yanzu, sai na yanke kunnuwanki. Kinji abinda nace ko?"
Da sauri ta gyad'a kanta, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi.
"Tashi ki wuce."
Abinda takeson ji kenan, da gudu ta mik'e zata fita.
"Ke!!!" Ta juyo a firgice. Ya rik'e kunnensa kad'an.
"Ko Mami kada na sake naji kin sanarmata."
Ta gyad'a kanta ta fice.
A falo ta sami Mami zaune tare da Anti Asma'u sai Yaya Rufa'i da 'yar uwarta Aisha da suke sa'annin juna.
Ta k'arasa shigowa tana kumbure-kumbure, ga hawaye sha6e-sha6e a saman fuskarta, wannan ne ya katse hirar da sukeyi. Ita kuwa Anti Asma'u gaba d'aya ta rud'e, tsoronta bai wuce abinda zai fito daga bakin Bintu ba. Yarinya akwai fitina, kada ta tonamata asiri.
"To sarkin kuka, ke da wa kuma?" Cewar Mami tana kallonta.
Bintu ta k'arasa gefen Yayanta Rufa'i ta zauna. Bata kai ga magana ba sai ga Ma'aruf ya shigo fuskarnan a murtuke. Ya nemi waje ya zauna a d'aya gefen hannun Rufa'i.
Mami ta dubeshi kafin ta k'ara duban Bintu. "Bintu keda wa? Me ka yi mata yau kuma?" Ta maida zancen kan Ma'aruf, sun san kukan Bintu, bai wuce adalilinsa. Shine kawai tasu bata zo d'aya ba a gidan, baya ragamata ko kad'an.
Ya d'aga kafad'a "Rashin kunya tayimin, na kama kunnenta nayi mata kyakkyawan gargad'i."
Bintu ta dubeshi ya harareta da sauri ta k'ara 6uya ajikin Rufa'i.
"Haba Yaya, me Bintu zatayi maka mai zafi kayimata hukunci haka? Mami kinga yanda kunnenta ya fashe, da farce ya kama mata." Fad'in Rufa'i kenan bayan ya duba kunnen. Ransa duk babu dad'i da abinda yayansa ke yiwa Bintu, kamar ba jininsu ba.
"Zo mugani." Ta k'arasa ga Mami. Bayan Mami ta ga wajen, ta dubeshi cikin 6acin rai, "Kai dai baka kyautawa abinda kakeyi, to wallahi ka kiyayeni. Koda wasa kada ka k'ara yi mata hukunci irin wannan. Ni ban yarda ma da abinda ka fad'a ba, nasan halin yarinyar nan, bata da tsiwa..."
Sai kuma tayi shiru, ta girgiza kai ta kalleshi "Koda tana da tsiwar ai ba yi maka takeyi ba inace dai?"
Yayi shiru baice uffan ba, ganin da gaske Mami ba shirun zatayi ba yasa ya mik'e ya dubeta.
"Kiyi hakuri Mami." Ta kauda kanta kawai ta maida ga Asma'u.
"Tafi da ita d'akina, akwai mentholata ki shafa mata."
A kunyace Asma'u ta mik'e, Bintu na kallonta. A ranta tana fad'in.
"Oh, dan Allah ji yanda take sunne kai yanzu, hum."
Bayan shigarsu d'akin, ta janye hannunta daga na Asma'u. Anti Asma'u ta dubeta da murmushi sannan ta nufi gaban madubin Mami.
Bintu ta hakimce saman stool tana kallonta. Asma'u ta dubeta ta madubi tayi d'an murmushi sannan ta juyo ta dawo gabanta ta durkusa. Ganin haka Bintu ta turo baki gami da dauke kanta, ita haushi take bata ma.
"Bintu, bakisan Yaya Ma'aruf mijina bane?"
Jin furucinta ya sanya Bintu dubanta baki sagale. Amma a 'yan iskan ma Anti Ma'u ta daban ce. Daman haka miji da mata sukeyi? To duk ba haka ba, ita bata da labarin anyi bikinsu ma, ballantana ta ga Innarta ta halarta. Wannan kawai k'arya ce, abinda Mami ta gayamata ko hannu namiji ya rik'e maka zakayi ciki ka haihu? Lallai ma.
"Latsi." Cewar Bintu a fili tana mai jinjina kai gami da jan majina don har lokacin ta kasa sakin ranta. Abin ya kusan bawa Anti Asma'u dariya, ta gimtse. Shakka babu, an d'aura mata aure da Ma'aruf wajen watanni uku ma, akwai dalilan da yasa ba'ayi tariya dai. Ta mik'e sanin da tayi ba ganewa zatayi ba. Ta lakuto man ta nufi kunnen tana fad'in "Yayanki mijina ne, ya ci ace a shekarunki na sha bakwai kinsan menene..." Sai kuma tayi shiru, Bintu babu kan gado, ba k'aramin aikinta bane ta nufi Mami da tambayoyi. Ita kam, ta fasa yini yanzu zata zo ta wuce tun kafin tayi mata wata ta6argazar.
Kamar kuwa ta sani, Bintu gaba d'aya ta jefa kanta kogin tunani. Ta hau cin farcenta, wai aure, ta k'ara tunano abinda ta gani, ta girgiza kai kamar wacce ta watstsake daga bacci ta dubi Anti Asma'u. Ai da sauri itama ta dakatar da ita.
"A'a, karki k'ara wata magana zan had'aki da Mami. Idan kiga bari ta ji wannan maganar dukanki zatayi, Mami ta tsani la6e."
Ta numfasa kawai ta kyaleta.
* * *
Zirga-zirga kawai Bintu keyi a d'aki, a fili take magana.
"Na tambayi Yaya Rufa'i?" Ta girgiza kai. "Kai a'a, kada shima ya zaneni." Ta zauna gefen gado tana cin farce, cikin ikon Allah sai ga Aisha ta shigo tana kiranta. Ganinta yasa tace "Au, kizo wai zamuje siyo takalmin sallah inji Yaya Rufa'i." Ai da sauri ta mik'e, ta janyo hannunta.
"A'i, au yi hakuri namanta, Aisha, gayamin wani abu."
Aisha ta nutsu ganin yanda fuskar Bintu ta nuna dagaske tambayar zatayi babu alamun shashancin nan tattare da ita.
"Mene?"

[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<03>>

"Anti Ma'u da Yaya Ma'aruf wai an d'aura musu aure?"
"Lallai, baki da labari? Ai tun kafin ya tafi bautar k'asa akayi aurensu. Nan gaba zaayi biki. Ai Inna ta sani."
Bintu dai bata gamsu da wannan kad'ai ba, saidai ta chanja akalar tambayar daga wacce tayi niyyar yi a farko.
"To gayamin, ai Mami dagaske takeyi idan namiji ya kama hannuna zanyi ciki ko?"
Aisha ta tuntsire da dariya, bata mantawa, itama Mami ta gayamata haka a baya, don kuwa ta zama budurwa tun tana da shekaru sha uku a duniya, watakila kuma hakan yana da nasaba da cimarsu da yanayin hutun da jikinsu ke samu, idan an ajiye wannan ma, Aisha Allah Yayi mata baiwar hankali, hakanan tana da ilimin addini daidai gwargwado, ana koyardasu duk wadannan hukunce-hukunce da sauran abinda ya dace su sani a addinance.
"Ke Bintu, ana fad'a ne fa kawai don a tsoratar. Ni ki kyaleni da wadannan tambayoyin, Yaya na jiranmu kada yayi fad'a." Ta wuce da sauri don d'aukar mayafi.
"Toh amma.." Ta katse maganar da tayi niyya sakamakon tunawa da gargad'in Yaya Ma'aruf gareta.
"Ki dauko mayafi, zamu biya mu sauke Anti Ma'u a gida sai mu wuce."
Dole ta nufi kayanta itama, bayan sun shirya suka fito, a tsaye suka sami Yaya Rufa'i da Mami, tana ba shi sak'o.
Aisha ta ja hannunta, "Zo muje wajen Anti Ma'u mu jira tana waje."
Suka fito, saidai a 'yar baranda suka iskesu da Yaya Ma'aruf, da sauri Bintu ta tsayar da Aisha suka la6e kad'an. A ranta tana fad'in asirinsu dai zai tonu yau idan itama Aisha ta ga sunyi wani abin.
Yaya Ma'aruf sukaji yana fad'in.
"Banyarda da wannan satar kallon ba na gulma, ke har yau kin kasa sakin jiki ki dunga kallon kwayar idanuna sosai..."

Basu kai ga jin k'arashen ba, Aisha ta figi hannun Bintu suka koma baya.
"Wallahi babu kyau la6e ba ruwana, kenan d'azu ma la6e kikayi ya kamaki ko?"
Ta harareta "Banza, so nakeyi kiga wani abu amma basuyi ba kika wani janyoni, zo mu koma kigani." Ta rik'o hannun Aisha, Aisha ta fisge ta k'ara janta baya.
"Wallahi baruwana, bazamu koma ba."
"Ke bakiji wani iskanci ba ma, wai ta kalli kwayar idanunsa. Nasan harararnan zaiyi mata."
Aisha tayi dariya.
"Ashe na fiki sanin abubuwa Bintu, lallai ke da sauranki. Ai kallon soyayya yake nufi. A shirin RAI DANGIN GORO naji Ahmad Isa yana fad'a, wai da saurayin ya kalleta saida ta ji yarr, wai ta sauke idanunta saboda ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba."
Bintu ta tuntsire da dariya. Yi takeyi tana k'arawa.
"Rainin hankali. Kalleni to mugani."
Ta gwalo mata idanuwanta, Aisha ta ja tsaki tana dariya.
"Ke dallah, sai da namiji wanda kakeso."
Bintu banda dariya ba abinda takeyi don abin dariya yake bata, suna tsaye sai ga Yaya Rufa'i.
"Au, maimakon ku shiga mota kuka tsaya anan?"
"Yauwa Yaya Rufa'i. Muga ida..."
Da sauri Aisha ta toshe mata bakin tana dariya.
"Ke wallahi ba'a sirri dake. Sirrine fa."
Yaya Rufa'i yayi dariya.
"Menene abin? Yau kuma ni kuke yiwa 6oye-6oye?"
"Yaya ba haka bane, sirri na bata ai babu kyau fad'awa wani kuma."
"Shikenan ai, ku muje, inaso naje amso d'inkuna na ne."
Suka kama hanya, har lokacin Yaya Ma'aruf na tsaye da Anti Asma'u. Yaya Rufa'i ya tambayeshi "To, ko mu tafi zaka kaita?"
Yaya Ma'aruf ya gyad'a kai, "Yeah kuje kawai."
Bintu ta kalleshi, ya bita da harara ta dauke ido. Wai wannan idan Anti Ma'u ta k'ura mishi ido, ai sai ya sanya ta firgice.
Koda sukaje nan ma Bintu saida ta tsaya ruwan ido, a k'arshe ta za6o mai shegen tsini, duk yanda Yaya Rufa'i da Aisha suka so hanata d'aukarsa ita kuwa ta dage lallai shi takeso. Dole suka kyaleta, ganin haka ya k'aro mata da wani flat mai kyau da rangwamen kud'i.
Murna ya cika Bintu har gwalo take yiwa Aisha.
"Wani abin ma sai gobe."
Aisha tayi dariyar mugunta "Zakiyi bayani ne."
...


Read / Download BINTU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On BINTU
avatar
ikleemah

2 months ago

Reply

The novel is good and sweet

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album